Sashe 65
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gefen yayanta.malami suka gani yayi sallama yashigo yazama qaton saurayi yanata karatunsa a n.d.a kaduna. Su suka biya suka daukeshi.duk suka miqe malami kun iso?yace mun iso kawu.ina anty maman?tana zaune jugum takasa motsi jin cewa abbanta ya iso.idanuwanta tuni suka fara tara kwalla.gabanta na faduwa !malam.ta kirashi.yayindaake nuna masa ita.kai ina baiyarda.duk da yafara manta kamanninta yasan anty maman sa.kyakkyawar gaske ce mai kwarjini wanda yake burge manya da yara.dan takaitaccen tarihin da yaji a mota yasa duk tausayinta yamasa bargo.idonsa ya cika da kwalla.ta mike tana fadin kunxo min da abba na? ya kamo hannunta gasu nan a waje.zo muje ki tarboshi.sukabibayan sauran ayarin dasukayi gaba.suna kawo kai zauren farko ana turasa a keke.anan ta qame suka xubawa juna ido.abbanta ne a keke?duk tsufa ya mamayesa? zuciyarta taci gaba da bugawa shiko tasbihi yakewa ubangiji wanda yayi nufin sake hada fuskarsa da diyarsa.shi sauyin kamanninta bai damesaba ganinta yadanne duk abunda ke cikin xuciyarsa Batasan malami najantaba.ita dai ganinta tayi daf da keken abba.muryarsa dataji ya qirata yasa tayi lau zata xube.amma ina yan uwanta.basu bariba.caraf!suka cafketa.yaya soja ya amshe yasa hannu biyu ya girgizata.mama!ke mama!ya ali ya miqo kofin ruwa.ga ruwa yaya.ya zuba masa a hannu ya shafa mata a fuska.tayi ajiyar xuciya..tafara kuka abbana!da dorata jikinsa ya rungumeta.irin kukan datayi sai da tabawa kowa tsoro.domin ji sukayi dif babu rai.daukarta sukayi cak sukayi cikin gida da ita.babu abunda BAKIN CIKI Baya bayarwa.haka zalika FARIN CIKI!dan saiya gigita mutum take nan har ya iya fadawa wani hali.mama kam farin ciki yasa sai da yan uwanta sukayi da gaske ta farfado.tadawo hayyacinta ta bude ido taganta kwance jikin abba.ta zura masa ido yakada kai yace mama ki taima keni kar farin ciki ysa ki sake jefamu a yanayin da muke sallama dashi Ta hadiye miyau da kyar tace har yanxu cikin BAKIN CIKI nake.abba.na kuma tabbata bazan taba fitaba daga cikinsaba.menayiwa danliti ya lalatamin rayuwa?menayi masa dazaya karya dukkan gabobin tatbiya ta da kima ta da asalina...sannan yawargaza dangantaka ta da iyayena,,,ya rabasu da komai najin dadi...har umma tabar gidan duniya?yaya soja kana kallo duk hakan ta kasance?meyasa baka jefani gadi rum ka rufeba?meyasa baka hadani da sojoji sukayi ta dukana harna mutuba?dukknku kuna nan?kun san wanda nakeso kunsan zabi na,,,amma kuka barshi yatafi maimakon ku tilasta inbishi duk. Yaya soja ya rufe bakinta,,mama ya kamata kiyi shiru haka.zuciyarki zata buga.idan kina fadin irin wadannan kalaman.ni yadda nake gani ma ke baki ga BAKIN CIKI Ba tamkar yadda muka ganshi kiri kiri.amma bamuda maganinsa.kisani duk abubuwan da kika lissafa babu wanda bamu kwatanta akankiba.sai dai abin ya faskara.saboda anriga an mallaki zuciyarki mama.karki danganta laifin akan kowa.don babu wanda yasan gaibu sai Allah.shidin kuwa mukayi ta roko ya warware mana abunda ke boye.agame da lamarinki.ina ganin yakamata ki kalli uzirinmu.kiganecewar munyi iya kokarinmu. Hargashi Allah ya shige mana gaba ya kwato mana ke.ayanzu mukeda damar nunawa danliti cewar lalle ya debo ruwan dafa kansa.dazai kaisa har lahira.ki kuma sa ido kigani. Da sauri tadawo wajensa shima ta rungumeshi murya na rawa take cewa karka barshi da rai yaya!kasa a masa azaba mafi radadi harya mutu.ya lafe kanta a kirjinsa zuciyar maxa ta motsa.idanuwa suka qara jirkita.kawai gani sukayi yasaketa ya miqe cikin hanxari zaiyi waje,,,abba yayi azama yace ku riqo minshi don Allah!su alh basiru suka cafke hannayensa.dawo ciki ka zauna ya qame a tsaye suna ganin yanda jikinsa ke rawa.namansa na girgiza saboda fishi.alh adamu yace alh ne zaiyi magana dakai..abba ya daga murya yace abduqadeer dawonan ka zauna!a hankali fishin yarinqa sauqa sannan su alh basiru suka dawo dashi ya zauna.yayinda mama tasake baro jikin abba tadawo gunsa ta zauna. Abba ya numfasa dukkanmu musulmai ne,,kuma munyi imani!da ko waccw qaddara ce.ina ganin fushin farko banamu bane.kar zuciya tasa mu aikata aikin nadama.yaya soja ya kasheshi babu nadama dan an harbe azzalumi macuci.irin danliti.karka manta muya fesa mana gubar mutuwa.mun shaqa harta shige mana da ginshikin gidan nan abba,!bazamu yafewa danliti ba abba.koza a kasheni saina harbeashi.abba yace kenan bamu godewa ubangiji ba daya nuna mana wannan ranar?wanda yace muyi afuwa a tsakaninmu.domin shi yanason masu yafiya.ko bamuyi fansa a gun danliti ba.nayi rantsuwa Allah bai gama walaqanta shiba.tunda ya walaqanta ayoyin alqur'an.inaso mugane wannan.ba haqqin mama kadai ke wuyansaba. Banajin akwai hukuncin dazamu yankemasa face mu qyaleshi da wanda yabasa ikon aikata wannan aiki akan mama.na tabbata bazai qyaleshiba yaci bulus!ba.ina roqonku da muyi haquri.mu sadauqar da yafiyarmu a matsayin godiya ga Allah daya musanya mana bakin ciki da farin ciki.ina fatan yaya soja zaibi umarni na? jikinsa yayi sanyi yadan kada kai..yace ya wuce abba yayi dan murmushi. Yace nagode! mama zonan...!ta rarrafo ta dawo jikinsa ya jawota. Yace ki nitsu nasan kinrasa komai na tsarin rayuwarki yanda kika shirya....saidai inaso ki gane cewar shirin Allah shine gaba da komai...saboda haka ki rokesa sabon rayuwa mai albarka.muma zamu tayaki zakiga kamar wannan abun bai faruda rayuwarki ba.ki sani har ummanki ta rasu bata taba yi miki baki ba.kullum addu'arta Allah shiyaki.idan zatasa albarka tare takesa muku da sauran yayunki.don haka tsakaninku adda'a ne kawai. Na tabbata hasken addu'arki zaije gareta.harta gane cewa lallai albarkar ta na tare dake kinji mama?ta dubeshi kwalla na zuba tace naji abba.don Allah kayafemin ya goge mata hawaye yace baki min komaiba mamana.ayau nagane baki da laifi ko kankani saboda haka ki saki jikinki.tace nagode abba intambayeka abba?yace tambayeni mamana.ta karya wuya gefe tace al'ameen fa?ya kada kai yace allahu akbar!alkairi Allah yakai mas duk inda yake.haqiqa bantaba ganin tashin hankaliba irin wanda nagani a fuskar al'ameen..saboda rashinki mama kiris yarage ya zautu amma qarfin adda'a ya miqar da imaninsa zuciyarsa ta daidaitu bisa shirin ubangiji.ya rungumi qaddara yawuce da ita rasha.gaskia bansake jin duriyarsa ba haryau din nan danake magana dake...kuma hulda ta yanke tsakaninmu.ni kaina bansan daliliba.watakila iyayensa sun nisancemu don qara nesanta rayuwar dansu ga tinaninki.hasashe nayi amma bansan musabbabinba. BAKIN CIKI 3***7 Tacire kai ta dubesa kwalla na zuba tace tabbas zai iya zama hakan abba!nima nayi alqawarin zanyi masa addu'a Allah qara nesantamu.ya mance ya taba sanina a duniya..ko a hanya kar Allah ya qara hadamu.abba yashafa kanta Allah ya shige miki gaba.yayi miki jagora a sabuwar rayuwar dazaki fuskanta nan gaba.kowa yace ameen yace muyi addu'a.sun raba dare a falo suna hirarrakin duniya abba yace aje a kwanta a huta.mama ta turashi a kekensa zuwa dakinsa wanda tuni anty amina ta dade da gyarawa.suka kamasa yakwanta a gado.sannan sukayi sallama takoma dakin umma!inda anty amina da baraka suke. Kowa ya kwanta barci ya kwasheshi.amma mama ta kasa.kawai tunanin yanda tayi cudanya da danliti take.nan da nan ta ji kyaman kanta ta kamata.tafara sunsuna jikinta.hankalinta tashe batasan lokacin data diro tashige bayiba.ruwan sanyi ne a bokiti da anty amina ta dibo.mama ta duba ba soso ba sabulu.haka nan tahau kwara ruwan sanyi ajikinta.tana dirjewa da hannu hawaye na xuba.ruwan ya qare ta dauki bokoti ta kwarara sauran. Tadauki bokitin takwara sauran ruwan gaba daya.haushin qarewar ruwan yakamata.tasanya kayanta ta figi bokitin da nufin taje tsakar gida ta debo a rijiya.su anty amina da baraka tagani cirko cirko abakin bayin.tawuce abinta ta doshi kofar.yayinda anty ameena kefadin haba mama! ashe bakiyi bacciba?yakamata kimanta komai karki zautu a banxa da wofi.ta zuba mata ido kwalla na xuba wari nake anty ku bakuji?babu wani warin da kike mama!tunaninki yagaya miki qarya.yakamata kisamu bacci ko kwakwalwarki zata huta.ta dubi baraka taga hawaye itama take,,,tace saboda Allah baraka bakiji warin danake ba?sunsuna fa kiji....takara mata hannu a hanci baraka ta goce da kuka ganin haka jikin mama yayi sanyi ta zube qasa dabas takama kai.wayyo Allah na!suka kamota sukayi ta rarrashinta.tadan nutsu.amma barcin da basu komaba kenan gabadayansu Washegari kowa ya hallara da iyalansa.ya abdulkareem da anty rabi kamar su hadiye mama sukeji.sun xubda hawaye saboda murna.ta dubi girman ameer da ameera kawai sai ta kada kai.tana tuna al'ameen shikansa docta yazama saurayi.ta zura masa ido,,,hannayenta bisa kafadunsa ta matse ido.hawaye suka kwararo..jitayiyana share mata hawayen tayi wuf! ta bishi da kallo.bakinta na rawa tace al'ameen momy nagayama inasonka?? ta taba gayamaka? ya juya ya kalli mominsa.yamaidoda kansa gareta ya girgiza kai.bata gaya maka ba?amma momy bata kyautaba.tasanfa yadda nake sonka Allah tasani boyema tayi togayamin kana sona? yadaga kai alamar eh.ta rungumeshi tana fadin nima inasonka dokta. Anty rabi ta taso ta dafata.ta dago kai ta dubeta kwalla na xuba mama!ki kwantar da hankalinki na tabbata Allah baxai barki hakaba.zai musanya miki mafi alheri wata qilama fiye da al'ameen.tayadd a rayuwarki zata daidaita tamkar da. Ta miqe a hankali ta fuskanceta tace hakane.nasan babu abunda zai gagari Allah.amma dokto shine farko shine qarshe.ta wuce ta murda kofar dakinta.ta qare masa kallo inba qarya idonta ke gayamata ba.kamar ta taba ganin al'ameen tsugunne a wajen data qurawa ido.dukda takasa tuna kalaman dayake fadi.idanuwantana nuna mata zubar kwallansa.tayi wuf!ta cafke yatsunta ta runtse su tamau.tana tambayar kanta ina zobe na?ina na ajeshi?ta wuce a hankali bakin gado ta zauna tayi shiru tana tuna kalaman dayake fadi idanunta na zubda hawaye.kai al'amarin mama qara sukurkucewa yake dalilin dayasa abba yace subar garin wataqila tafi samun nutsuwa.nanda nan suka fara shiri.kafin wani lokaci kowa ya kimtsa abba ya sallami en uwa da abokan arziki.su hajiya hajo sunata neman gafara wajen abba da mama.motoci suka kwashesu kowa da iyalansa suka miqe hanya.suka bar danliti hannun hukuma.duk abinda yakamata su masa A kagara suka sauqe baraka tukuna suka dau hanya.minna suka yada zango gidan ya abdulkareem.ko anan dinma al'amarin bai sauyaba.haka suka kwana ba barci a idon mama.washegari suka kimtsa masu tafiya abuja suka dau hanya.ya abdulrahman yayi kaduna da iyalansa da malami.shikuwa abdulkareem jirgin shabiyu sukabi zuwa legos.yan abuja suna dira gida wanka mama tafarayi.wannan wanka yafara damun yan uwanta.su wanka ma kawai suke gani basusan yanda taga dare haka take ganin ranaba!akwai fargaban rashin bacci zai mata illa.idan ba'ayi gaggawar daukan matakiba.towayasani bare ayi mata magani? shiyasa kafin sati ta birkice gaba daya.ga zama shiru ga sunsune sunsunen jikinta.wanka kuwa ba'a maganarsa.saidai in danliti bai fado mataba.nan da nan tafara mura zazzabi mai zafi ya rufeta.hankalinanty amina yatashi.data shigo dakin tasameta nade cikin bargo sanyi na kadata.cikin sassarfa tasamu abba.ta durqusa a hankali tace abba idan ba'a dau matakiba mama zata kashe kanta da yawan wankan nan. Mama zata kashe kanta da