← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 79

Sashe 2

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BAKIN CIKI 1***1 Sarautar Uban dawaki babbar sarauta ce a garin fandagori can cikin jihar naija. Babban gari ne wanda al'ummar cikinsa suka bunkasa wajen noma da kiwo. Gidan uban dwk Alh Awaisu Malami katafaren gida ne cike da zuri'a masu yawa na kannensa guda 2 kuma shine babbansu kat! Sassan sa yafi na kowa girma da tsari ginin zamani. Matarsa daya Haj Halima da yaya maza uku a jere. Abdulkadeer, Abdulkareem da Abdulrahman sai kandensu "ya mace tilo a cikinsu Sakina, sunan mahaifiyar uban dwk gareta shiyasa suke kiranta "Mama". Santaleliyar yarinya wacce Allah yayiwa sura tamkar ita tayi kanta kusan zuri'ar gidan haka suke da kyau na fulani. Amma ita mama ta fita daban wajen cikar sura daka gganta dole gabanka ya fadi sbd tsabar kyau. Shiyasa tun shekarunta basu kai ko'ina ba samari suka yanyameta kowa na so, musamman cikin gidansu watau yan'uwanta abin har yana so ya zama rigima a tsakaninsu. Saida Uban dwk da kansa ya tara su ya soke maganr soyayya da Mama ya kuma kar wanda ya kara kiranta da sunan tadi. Yayi haka ne don a sami masalaha da zaman lfy. Allah kuwa ya taimaka kowa ya gama bacin ransa ya hakura. Baya ga haka yana ganin Sakeena bata kai shekarun da zata tsoma kanta kogin soyayya ba alhali tana tsaka da karatunta mafarin kenan da zata tafi babbar sakandire yayi kokari ya samar mata makarantar kwana ta yanmata dake bakori (FGGC Bakori) Sannan hankalinsa ya kwanta amma wann hukunci nasa yayiwa wasu daga cikin iyaye mata ciwo har suna ganin sbd kyaun da Mama take dashi ne yasa ake wulakanta yayansu suka rinka ganin kamar suna sn su dauki dogon buri ne su dora mata. Tabbas uban dwk nada buri akan yarsa tilo mace saidai yasha bamban da irin burin da matan gidan ke nufin ciki zukatansu wanda bazai wuce ya aurar da ita ga hamshakin me kudi ba ko basarake. Shi burinsa yarsa tayi zurfin karatu kamar sauran yayyinta maza wadanda a halin yanzu Abdulkadeer major nr na soja, Abdulkareem accountant ne a CBN, sai Abdulrahman dake NYSC a Jalingo. Ya kuwa lashi takobin ko bashi da rai yan'uwanta su cika masa wann buri nasa. Kwanci tashi Mama ta shiga SS2 kuma yau sukayi hutun 2nd term tun safe Uban dwk ya tura drivernsa ya daukota, basu iso fandagori ba sai bayan la'sar kowa na ta murna musamman yara da suka yanyameta suka kwashe mata kaya zuwa sassansu. Ta shigo da sallama Ummanta ta tarbeta ta rungumeta, ta shiga sauran sassan ta gaishesu, Salisu da Danlami kadai ta samu acikin samarin sassan. Ta zauna suka taba yar hirar skul sannn ta tashi koma sassansu tana shiga ummanta tace Abbanki na nan ya dawo ta wuce da sauri ta sameshi a falonsa, bakinta har kunne ta dan rankwafa tace Allah ya taimaki mai martaba! Fara'arsa ta karu: Allah yabar min Mamana na shigo akace kin shiga sassa. Ta zube gabansa tace eh naje gaishesu ne, ina yini Abba? Lfy lau ya karatu? To mungode Allah, yace ina report sheet a kawo na gani. Ta mike taje ta kwaso duk takardun yayi ta dubawa yana fadin da kyau! Bayan ta kammala ya dubeta kinyi kokari sosai Mamana na baya miki amma har yanzu kina da yar matsala a biology sai kin kara bada himma kinsan dalili? Ta kada kai yace kara matsowa kiji ta matso kusa dashi sosai kafin yace: buri na ki zama likita Mamana, sbd a rayuwa ta ina sha'awar in ga ya mace likita, abin yana burgeni kwarai, shiyasa tun ranar da Allah ya bani ke nake ta addu'ar Allah ya raya minke in samu in cika burina, ko kuwa ke bakya sha'awa? Tace sosai ma nakeson zama likita Abbana. Kuma I.S.A zan kara himma don ganin na gama da biology. Ya dafa kanta cike da farin ciki yace yauwa Mamana, Allah yai miki albarka tace ameen Abbana. Daga nan suka ci gaba da hirarsu saida akayi sallama dashi ya tashi ya shiga babban zaure inda Majalisarsa ke taruwa. Mamana ta koma gurin Ummanta a kicin suna aikin abinci tana bata labarin abnd Abbanta yace, Umma tace yallabai kenan Allah dai ya cika masa wann buri nasa tace I.S.A Umma saina zama likita. Tace Allah ya yarda wai waya gane min Mama da farafen kayan nan? Mama tana dariya tace na dan ratayo wann abun da suke sawa a kunne ina takawa ana ga Dr Sakeena nan zuwa. Suka fashe da dariya. Washegari misalin 10:am Mama ta fesa ado da koriyar atamfa sannn ta dora after dress ta yafa mayafinta ta sami Umma a daki, sai ina? Zani gaida Inna saude ne. A'a kice dai zaki gun Baraka. Tayi dan murmushi Umma ai duk dayane Idan na gaida Inna ta sai muyi hira da Baraka kawata... Uhummmn... To kodai lauya zaki zama a fasa likitan nan? Tayi dariya wai kinaso ki hada ni da Abba kenan.. Lallai kam to kice ina gaida Sauden idan ta gama dinkunan ta baki kizo min dasu, shikenan amma ina fata akwai nawa aciki. Umma tace babu naki aciki duk nawa ne, Mama ta dan kirne fuska kai umma ai kuwa zan zabi daya aciki, tace duk zannuwa ne ciki da alakum rigunan kuma masu hannu ne, zan canja style ni inaso a haka, to ban yarda ba ki anso min kayana kawai idan ta gama. Ta jinjina kai shikenan umma nina tafi, adawo lfy karki dade... Ta saba jakarta tana fadin to Umma.. Salis ne zaune a kofar gida tana fitowa ya kare mata kallo sama da kasa kafin yace sai ina kuma? "Gidan Inna Saude zanje" 'Okay na kuwa ga Baraka jiya itama ta dawo". Ya mike muje in rakaki ko bakiso? "Muje mana ta wuce ya biyota suka jera. Wai Mama meyasa Abba yake takuraki dayawa? "Kamar yaya?" Baya son kina kula samari kin kuwa san har yanzu yaya Ali yana sonki? Ta dube shi farin sani kuwa tunda yana gaya min a sace amma fitinar duk waya fara daukota? Yace a'a ba don muna uwa daya uba daya dashi ba, abnd yaya Sa'ed yayi bai kyauta ba, tunda yasan shi yana sonki menene na shi na shigo nemanki? Ya fa san halin Yaya Ali ba hakuri ne dashi ba yanzun nan sai ya nuna maka hauka. Ta dan tabe baki tace hmmmnn... Kai nifa karatu ma zanyi dama sun sa ransu a inuwa, babu wanda zan aura acikinsu koda Abba bai dakatar dasu ba.. Ya zura mata ido kina wulakanci Mama kice dama kema ba sonsu kike ba? Baka gane ba.. Me kikeso ki fada? Karatu zai hanaki aure ne? Ta kada kai nutsuwa nafi bukata sbd karatuna mai son nutsuwa ne.. Me zaki karanta? "Akikin likita" ya ware ido Uhmmnn.. Dokta Sakeena kenan! Tayi murmushi har kasa naji gingiringin! Yayi dariya daidai lokacin da suke tsayawa gefen babban titi.. To Dr Sakeena ni anan zan juya.. "Ngd ai kaga har nayi sauri da yake ana hira" yace dadin abokin rayuwa kenan, don ma ba Ya Ali bane tayi dan tsaki get lost donAllah ka rabani da wann zancen, yana dariya ta tsallaka titi ta barshi hanya shi kuma ya juya ya koma gida. Mota yake kakkabewa ya cire shimfidar foot mat lokacin da Mama tazo wucewa, yayi tsaye yana kallon wata surar da bai taba gamo da irin ta ba.. Kai ya kasa daurewa saida yayi mata sallama.. Ta dago ido ta dube shi tare da amsawa, sautin muryarta ya kara rikita shi ya bita da sauri donAllah ko zaki 5mins kadai in tambayeki? Ta tsaya caka tana dubansa, dogo ne sosai "Allah yasa na sani" yace donAllah anan garin kike? Tambayar tasata a mamaki tace eh mana, amma ban taba ganinki ba sai yau. Tace kasan daurowa take , gsky ne, ah suna nan Al- Ameen ina minna amma nan gidan kaka ta ne, na kawo Mamana ne ma yanzu sau dayawa ina zuwa nan shiyasa kikaji na tambayeki. Haka ne yau ne Allah ya nufa zamu hadu. Ya sauke numfashi gsky ne, allah ya hadamu kuma take nan kin kwanta min a rai ko zan san sunanki? Ta dan kauda kai yanayin mata saida gabansa ya fadi tsoro ya kamashi kada ya sha kayi. Ya marairaice dan daure ki gaya min ba don hali na ba, hali? Nasan halinka ne? Yace na mita da bakin naci! Tayi dan murmushi Sunana Sakeena' kai! Sunan nan ya dace da kykkyawar fuskar nan! Anan unguwar kike? Ta dan kada kai can gidan zani wajen kanwar Ummana, ok to gidanku fa? Ta yatsuna fuska alamun ta kosa ta wuce, harta fara takawa ya biyota na dameki ko? Yi hakuri so ne ya kamani ki taimake ni, ta tsaya ta dube shi da idanuwanta farare kal dasu tace kasan Uban dawaki? Can tsallaken titi kenan? Ni yarsa ce idan kasan gidan, nan ne gidan mu saidai akwai matsala. Ya hadiye murmushin sa Matsala? Na shiga uku a ina matsalar take? Tace Abbana baya bari azo zance wajena yace sai na gama karatu hasali ma bording skul nakeyi daga hutu sai hutu ake ganina, ya danyi shiru jim kafin yace to ya za'ayi yanzu Sakeena? Gsky ba da wasa nakeyi ba ya kike ganin za'ayi? Tace ban sani ba amma ina ganin hakuri zai fi kyau, mu saurari lokacin kammala karatun, ba kai kadai bane akwai wasu wadanda suka rigaka magana kuma sun hakura. Yace su zasu iya ne nikam bazan iya ba Sakeena! Ina sonki sosai babu abnd nake rayawa a cikin rain aface na aureki. Ta dan kara dubansa sai taji ya fara zama cikin ranta. Matsalar kawai batasan yanda zatayi dashi ba har tace yaje gidansu. Don haka tace kayi hakuri Al-Ameen.. Ta wuce da sauri ta barshi yana kira Sakeena! DonAllah tsaya mana kiji.. Gidaje biyu ta wuce na ukun shien nasu Inna Saude. Ta sa kai ciki tare da sallama baraka dake tsaye tsakar gida tana gyara zaman mayafinta ta juya da sauri baki sake suka rungume juna.. Gidanku zan tafi yanzu a haba? Wllh yanzun nan kewa Inna sallama har ta bani dinkunan Umma tace dama nima ta aikoni akansu, ina Innar? Tana ciki suka shige tare Inna tace au Mama ce? Har kin rigata kenan tana
Chapter 2 · 0% Book details