Sashe 6
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai kinga wadancan da yake ya ku bayi ne bata ce tana so ba". Umma ta dube ta sosai, "me kike nufi gaje?" tace, "me kuwa? Ita gaskya ai daya ce, sannan arziki na Allah ne. Daga ali har sa'eed bamu fidda masu rai ba". Ta tsura mata ido cike da mamaki, kfn tace, "na wuce kiyi min habaici gaje, domin ni ba sa'arki bace. Kasancewar ali da sa'eed 'yan uwa ga mama bai zama dole wani a cknsu ya aureta ba, domin shi aure nufi ne na Allah. Shi ke kullashi, kuma duk fassarar da zaku yi man kun dade ba kuyi ba. Allah yasan zcyrmu akan komai". Ta tashi ta bar sasan. Wata uwar shewa suka kwasa hannu bibiyu suka tafa, "tabarmar kunya....," inji h. Gaje, "da hauka ake nade ta!" h. Hajo ta bata amsa.! AKIN CIKI 1***4 Sasan alh. Basiru suka tasu da matansu suka kwnce musu abnda ya wakana a falon uban dawaki. H. Hajo matar alh. Basiru ita ta fara tsoma baki, "amma kuwa idan baka mutu ba zaka ga abin mamaki kala-kala. Ynzu da gske alh. Babba ne ya iya tararku da wannan maganar? Ko ya mance abnda yayi a kan su ali ne?" Alh. Adamu yace, "ya manta? Babu abnda ya manta. Hasali ma sai da ya kara maimaita zancn su". "tafdi!" inji h. Gaje, matar alh. Adamu. "kai dai kaga dan-uwa kawai, ai dama tun farko na fada, ba wani karatn da ake so tayi, burnsu mai kudi ko basarake, sbd su ganin mama tafi kowa kyau a duniya. Shi yasa suka dauketa a matsayn wani jari gare su. Ai shikenan, Allah ya bamu lfya. Muma namu 'ya'yan bamu fidda ran Allah zai azurta su ba. Ba Dai kowannensu ya kama aiki ba? To muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Harda wani za'a tara kudi a banki, don kawai kar ya baku wani abu ne a ciki, shine yake muku 'yan dabaru" "ni dama bance a bani ba, me zanci da su?" inji alh. Basiru. Alh. Adamu yace, "balle kuma ni, ai tuni na haramtawa kaina komai na alh, tnda ya nuna mana kiyayya a fili". Ya tashi yayi waje, alh. Basiru yabi baynsa. Yaynda h. Gaje ke fadin, "sai musa ido mu gani, da wane bakin h. Halima zata gaya mana zancan". H. Hajo tace, "kema dai da son jin baki kike. Tnda mijnta ya furta, ai ba sai ta maimaita ba, tana nan tasa ido muje mata murna 'yarta tayi farin jin". Tayi 'yar shewa, "Allah mai iko, kiri-kiri an raina mana wayau?". H. Hajo ta ja tsaki, "mtsww! Kina mamaki kenan, dama kin daina wlh, domin an jima ana ruwa kasa na shnyewa. Ba girin-girin ba dai, tayi mai. Ba auran gidan kudin ba, kwancyar hnkali!" Tana rufe baki tare da sallamar umma, suka amsa suna wani yatsina suna yarfarwa. Ta zauna tana fadin, "na shiga sasanki yara suka ce kina nan" "uhm! Ina nan" "dama maganar 'yarku ce, ban sani ba ko su alh. Sun gaya muku halin da ake ciki?". H. Hajo tace, "sun gaya mana, yanzu haka ma shirn zuwa sasan naki muke, sai kuma gaki. Ashe kuma mama an fasa karatu aure za'ayi?" Tace, "to yaya zamu yi, mutane sun cikawa alh. ido, sannan da alama ita ma maman tana son yaron. 'ya mace kuwa idan ta nuna tana son aure, to yi mata auran shine mafi alkhairi ga iyaynta". H. Gaje tace, "gaskya kuwa, gidan hutu ai dole a so shi. Ai kinga wadancan da yake ya ku bayi ne bata ce tana so ba". Umma ta dube ta sosai, "me kike nufi gaje?" tace, "me kuwa? Ita gaskya ai daya ce, sannan arziki na Allah ne. Daga ali har sa'eed bamu fidda masu rai ba". Ta tsura mata ido cike da mamaki, kfn tace, "na wuce kiyi min habaici gaje, domin ni ba sa'arki bace. Kasancewar ali da sa'eed 'yan uwa ga mama bai zama dole wani a cknsu ya aureta ba, domin shi aure nufi ne na Allah. Shi ke kullashi, kuma duk fassarar da zaku yi man kun dade ba kuyi ba. Allah yasan zcyrmu akan komai". Ta tashi ta bar sasan. Wata uwar shewa suka kwasa hannu bibiyu suka tafa, "tabarmar kunya....," inji h. Gaje, "da hauka ake nade ta!" h. Hajo ta bata amsa.! Umma na shiga sasanta ta iske baraka, shigowarta kenan suna murnar ganin juna ita da mama. "a'a baraka ce?" "nice umma, ina yini?" "lfya kalau. Ya babanki da innar taki?" "duk suna lfy. Tace a gaisheki. Wai dinkunan sunyi miki kuwa?" "wle sunyi kyau" Mama ta cafe, "baki ga ta cabawa abba ado ba yau tun safe?". Ta yo mata dakuwa, "gidanku!". Ta wuce suna mata dariya har da tafawa. Janye ta mama tayi ckn daknta, "kamar kinsan ina nemanki kawata" tace, "nima haka kawai naji ina son ganinki, nacewa inna zanzo nan. Har tana min tsiya, wai anyi hutun kenan, bama gajiya da bin hanya". Suka yi 'yar drya, kafn mama tace, "kinsan wani abu?" ta kada kai. "kawai dazu da rana sai ga mahaifn al'ameen........" ta katseta ido waje, "don Allah? Sai aka yi yaya?" tace, "uhm! In gaya miki Abba ya amince! Kimji ynda nake ji yau a duniya?". Ta cika da mamaki, "tafdi! Allah ya saka masa da alkhairi" "ameen ke dai. Ni ynzu al'ameen din nake son gani, idan yaji wannan albishir din. Kinsan Allah, da ni duk na hakura ina 'yar dabara inje hutu minna, idan Abba ya hana ma rika gaisawa a can" Tace, "amma idonki ya rufe, wa ya gaya miki a minna yake da zama?" "nasan a zariya yake, amma dole yaje minna, musamman idan yasan zai ganni a can". "ke mama......" "meye?" "meye kuwa? Allah dai ya nuna mana lokacn lfya". "to ynzu zaki je hutun ko kin fasa?" "Gobe insha Allahu zan tafi, amma dole in dan saurara in ga ko zaizo goben" Tace, "kema kinsan dole gobe ya dauko hanya, wannan babban albishir ina zai tsoma ransa, idan bai zo ya ganki ba?". Suka tafa suna 'yar driya. Har gab da magariba suna tare, sannan mama tayi mata rakiya ta koma gida. Inna saude kanta tayi farin cikin jin wannan labari.! Duk da cewar maganganun su Haj Gaji sun bala'in batawa Umma rai sam bata gayawa Uban dwk ba gudun tashin hsnkali da sabani, hakan yasa bata kwana da zancen cikin ranta ba taci gaba da sabgoginta kamar ba abnd ya farau. Mama kuwa ta kintsa kayanta a jaka tare da sakonnin Umma wanda zata tafi dasu don yin tsaraba, Abba da kansa yake gaya mata kar tayi gaggawar tafiya watakila Al-Ameen yazo kada suyi sabani, ya wuce gona da kazzin idan har ya dawo daga goba bai zo ba shi zai kaita, ba karamin dadi Mama taji ba sbd a zahiri Abbanta yana nuna jin dadinsa da sauyin da Allah ya kawo musu a lokaci guda. Mama ta caba kwalliyar mamaki irin wacce take gigita samarin gidansu duk sanda sukai tozali da ita duk da cewar basanan Ali yana aiki da karamar hukumar birnin gwari shi kuwa Sa'eed dan- sandan-bada-hannu ne a Kd. Shi Sa'eed Mamansa ce ta dauki abin da zafi tuni ya gane ta wuce ajinsa ya fara neman wata anan Kd. Can sassan ta shiga don gaishesu tare da shaida musu zata tafi hutu kamar yanda ta saba idan zata tafin. Tana shiga danlami ta samu yana wankin kayansa ya zura mata ido harta iso gunsa tana murmushi duk da cewar shi tasa fuskar a daure take "wanki kakeyi?" "Uhmmn..... Kuma a zaune don lalaci yaushe zai fita.. Yace ni banson iyayinki.. Tace iyayi?? Wai naga sai wani cin magani kakeyi baka koshi bane halan? Ya dubeta sosai Yace Eh yunwa nakeji.. Saiki kawo min abinci matar masu kudi! Baki sake take kallonsa "matar masu kudi? Ban gane nuffinka ba? Yace jeki abnd ya kawoki karki hanani aiki na.. Ta gyara tsayuwa tace maganarka tana da manufa danlami me kake nufi da matar masu kudi? Sai taji magana daga bakin Haj Gaje ai ba karya bane yaga kinyi kalar matar masu kudi ne shiyasa ya fadi haka ai kinga masu kudin suna zuwa aure ya tabbata! Gaba daya ta daburce ta rasa ina wann magana ta dosa ba shiyasa tayi tsaye tana kallon Haj Gaje. Tace ki daina kallona idan baki gane ba ki tambayi mai hankali yayi miki bayani. Ta wuce abin ta cikin daki. Take nan ran Mama ya baci. Ta juya cikin sauri ta bar sassan, kicibis sukayi da Salisu ya dubeta da kyau yace ashe dama duk abun yaudara ce koda yake dama kin gaya min su Ya Ali basa gabanki, ta kalleshi tace kwarai haka ne ko akwa me yi min dole? Sannan yin kwadayi ma ai dace ne wani idan zai like yayi kwadayin ma bai samu mtsewww... Taja dogon tsaki tabar gurin yayin da Haj Hajjo ta tsaya gabansa amma kai sakarai ne tsayawa kayi tana gaya maka magana son ranta? Kai tsaranta ne? Sakarai kawai. Itama taja tsakin ta wuce shi. Haushi kamar ya hadiyi zuciya cikin sauri ya fice kofar gida. Gaban Ummanta ta zube idanuwa cike da kwalla tace Umma meke faruwa ne cikin gidan nan ake yada habaici? Tace shine zakiwa kuka? To ina ruwanki da abnd ke faruwa? Tunda ba matsalar mu bace. Umma kinsan ban son abin haushi idan su salisu sukaci gaba da yi min habaici wllh zan basu mmk gara ki gayawa Abba yayiwa tufkar hanci tun kafin gidan nan ya yamutse. Ta zura mata ido kinga babu abnd ya shafeki da surutunsu domin ba shi zai hana abnd Allah ya shirya ba, biye masu zakiyi duk ku haukace gaba daya? Ina so ki dauke kanki daga gare su tamkar yadda nayi. Ta goge kwalla tace kema sunyi miki ne? Tace tun jiya iyayensu suka fara amma bai dameni ba don nasan wann abu bani na shkirya shi ba ba kuma Abban ki bane balle ke. Shiyasa ko shi Alhajin ban gayawa ba sbd bana son hayaniya kin gane? Ta dan yi jim sannan ta amsa da ka tana goge kwalla. Tashi ki je ki wanke fuskarki. Ta mike zata wuce yaro yayi sallama yace wai ance Sakeena tazo Al- Ameen yazo.