Sashe 38
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba! Yace, ah! Al-ameen! Saukan yaushe? Yace daxun da la'asar Abba. Ya xauna suka gaisa, sannan ya sake tambayar jikin mama. Abba yace ciwo na nan Al-ameen. Halima kawo masa abinci ya ci, kafin muyi magana. Abba bana jin yunwa, domin na riga na saba da ita, tun tym din na sami labarin tashin hankalin da kuke ciki. Abin daya hana ni jurewa kenan, nace dole in xo inga halin da Mama take ciki. Abba yace, gaskiyya ne. Mama na nan cikin lularar da ta sameta sai dai al'amuran zai ba ka mamaki idan na gaya maka alabari ya sha bambam Al-ameen, nasan an boye maka komai coz of karatunka, amma yanxun dole ka sani, tunda ka zo. Jikinsa ya kara sanyi, yayi xuru yana sauraron abba, al-ameen rayuwa ta sauyawa mama, wanda muke ganin sa tamkar a mafarki, daga ni har 'yan uwanta kaf! Babu wanda ba shi ckin alhinin wannan abu. Balle kuma kai da soyayyah ta hada ka Mama, kuma ita da kanta takwo mana kai cikin gidan nan. Shi yasa nayi rantsuwa, idan mama xata mutu, sai dai ta mutu a dakin ka tunda tun farko ita ta kawo ka. Ashe kuwa babu wani dalili ko uzuuri da xata kawo mana mu saurare ta. Nasan har yanxun kana jina a hagunce ne, baka gane inda na dosa ba. To bari na fito maka a mutum kada ka wahalar da kanka, Magana daya ce, mama ta gano wani kuma idanuwanta sun rufe ta manta cewar tayi xafin farko kuma na karshe a swajena. Ka fahimce ni? Gaba daya kansa ya kunce, daga yadda yayi kuri idanuwan sa kafe yana kallon Abba, suka gane bai fahimci su ba. Saboda haka yace, dole ka shiga rudu fiye da wanda ka shuga a baya, amma ina so ka sani, mu muna tare da kai, ba mu san kowa ba face kai, ba don komai ba sai don tun farko kai tafara kawo mana. Abinda nake son ka gane shi ne, xuwanka ya sanya ni farin ciki. Domin kai kadai nake jira in tabbatar wa Mama cewa lallai ni ba tsohon banxa bane, kuma bana magana 2. Ina mai tabbatar maka ba xaka koma ba sai na daura auranka da sakeena da yardan Allah. Na gama magana ta, ka tashi hankalinka kwance, kashiga wajenta tana nan cikin dakinta. Ya mike ya bar falon. Umma ta dube shi tace, Al-ameen! Murya dishe ya amsa, na'am Umma tace kayi hkr, ka kwantar da hankalinka. Mama bata isa ta xubar mana da mtunci ba. Kai zata aura da yardar Allah, domin da kai ne akayi mata baiko. Tashi ka shiga wajenta ku fahimci juna. Ta mike tabashi guri, don yaji dadin tashi......... Me kunnuwan Al-ameen ke ji yau? Ya runtse ido tamau! Ya girgiza kai wai ko barci yakeyi ne? Abba ya xo masa a mafarki. Ya bude idanuwan ya ware su sosai, tabbas zaune yake cikin falon su Mama. Kenan dagaske ne maganganun da Abba ya gaya masa? Kirjinsa ya soma bugawa ji yake kiris! Yarage ya zare masa rai, saboda wani gagarumin ciwo da yaji cikin xuciyarsa, nan take ya kama shi. Motsin kirki ya kasa yi har Umma ta sake fitowa da nufin dauko wa Abba abincinsa. Ta danyi jim, tana masa kallon tausayi, sannan ta matso tayi kiransa, ya dubeta firgigi idanuwa sun juye jajur! Tace, ka na xaune, baka shiga ba? Tashi ka shiga mana, ka kwantar da hankalinka, komai xai wuce Insha Allah, ya mike a kasale, ya nufi dakin ba tare da yasan me xai je yayi ba. Tana zaune tsakar daki ba ta hade kai da guiwa, tsiyayar hawaye kawai takeyi, domin tana jin duk kalaman da Abba ke fadi. Daf! Da ita ya tsugnna, bai san lokacin da yasa hannu ya dago fuskarta ba. Sukayi wa juna xuru tsawon lokaci kafin yace, kin ganeni sakeena? Al-ameen ne, kin gane ni? Ta kau da kai abinta. Da sauri ya kara juyo da ita, kiyi min magana sakeena ko na sami nutsuwa saboda ke na dawo kasar nan, don na duba jikin ki. Ina can tunani da xulimmi sun addabe ni, idan kin gane ni, ki amsa min, ya jikin ki? Ta watso masa harara, hawaye na kwarara. Tace waya gaya maka banda lfya? Yace, haka kowa ke gaya min tun tym din da na daina jin muryarki a waya, komai nawa ya tsaya sakeena, radadin ciwon daya sameki, ya hanani sukuni. Ina fatan gani na ya zama sanadin samun saukin ki. Ta goge kwalla. Tace duk wanda ya gaya maka banda lfya, ya maka karya, kalau nake, gani kuma kana kallo na xaune, sai dai na tabbata dawowar ka zata iya zame min cuta! Ya kara xura mata ido , kina nufin abinda Abba ya gaya min yanxun gaskiyya ne? Tace ka daina kokwanto. Ya langwabe kai gwanin ban tausayi. Yace dole nai kokwanto sakeena, don nasan akwai alkawarin a tsakanin mu, kuma bana tunanin zaki yaudare ni, wannan ya tabbatar min da tsantsan son da kike min. Ban taba kallonki da xuciya 2 ba sakeena. Shiyasa har halin yanxun da nake magana dake ban yarda kin karya alkawarin mu ba. Ta kalle shi a dage, ta watsar tace, ya kamata ka amince, tunda gashi da bakina ina gaya maka, tsutsun soyayyarka yayi fiffike yayi dogon tashi. Ya dafe kirjinsa a natse idanuwansa tam! Da wahaye, yace, bai tashi ba sakeena, nayi rantsuwa kina so na. Akwai miskhila dai a wani wuri, ki gaya min laifin da nayi miki. Wlh da kaina xan hukunta kaina, koda da jinin jikina ne xuba, idan har zai zama fansar tarin laifin da nayi miki. Gaya min da sauri inji. Ta ya mutsa fuska, hawayen ta ya bushe tace, Al-ameen ka farka daga barcin da kakeyi ka saurareni, ni sakeena na gaya maka a da naso ka, amma yanxun ban son ka, ba kuma zan aure ka ba, idan sama da kasa za su hade! Kaji ni ko? Sai na maimaita? Ya matse ido, kwalla masu zafi suka yo waje da gudu, ya dan kada kai murya shke yace, kin xuba min dafi, kin xuba min dafi sakeena. Baki tunanin amana? Yasa hannu ya kamo yatsunta, ya kura wa zobensa ido, ya ciga, baki kallon zoben alkawarin mu? Me yasa kika mance da dimbin kalaman da kika sha gaya min? Wadanda suka jaddada imani na akan son da kike min? Ta kwace yatsunta a hankali ta zare xoben, ta jefa masa, ga tsiyarka nan, idan shi kake kallo a matsayin alkawari, ni ma cire min nawa ka bani. Yaci gaba da kallonta, kafin ya dauko zoben yace, kiyiwa Girman Allah ki maida zoben nan sakeena.... Bazan karba ba! Idan ma ka aje shi, zan jefa shi masai! Kuma nima dole ka ban nawa! Yace sai dai ki kashe ni, sannan ki zare shi, wannan din ma zan ciga da boye shi, har xuwa tym din zaki sami nutsuwa dakin auranmu. Ta kwada masa harara, sannan tayi wani dan murmushi na kaico, ta kauda fuska, y mika hannu ya kamo habarta, ta sa nata da karfi ta doke nasa, kafin tace, karka sake tabani, idan ba haka ba kuma sai na kurma maka ihun dan iska! Ta mike da sauri ta bar wajen, kai tsaye bayi ta shige, ta maida mukulli ta kulle. Yayin da Al- ameen ke cigaba da kiranta. Ya tashi ya tsaya kofar bayin yana fadin, ki fito ki saurare ni sakeena, ya kamata mu fuskanci juna, mu gane inda matsalar mu take. A zatona har duniya ta nade ba zaki taba juya min baya ba! Tana daga ciki ta amsa, bazan fito ba. Daman kasan inda dare yayi maka, yace ki tuna alkawari sakeena, don Allah karki bari ayi min dariya. Idan na rasaki zan iya rasa komai nawa, ki tausaya min sakeena, kar damuwa ta kasheni. Tace, kan ka akeji! Ni na gama magana da kai. Ko za'a kashe ni ba xan sauya ba, dama ka kama gabanka zai fiye maka alkhairi. Ya tsaya jim, shiru goshin sa jingine da kofar ya rasa inda zai tsoma ransa yaji dadi. A hankali ya soma karannto Innalillahi Wa inna ilaihir Rajiu'un. Ya fi 10mins tsaye. Sannan ya juyo da sauri ya fito yana share fuska da hankaci. Kawai arba yayi da su Abba zaune falon. Ya rage sauri ya nufi gunsu ya tsugunna, abba zan koma. Gab dayan su ido suka xuba masa, jim Abba yace, amma dai ba minna zaka nufa ba yanxu ko? Ya dan kada yace, kuma ka kwantar da hankalinka Insha Allahu Mama matar kace. Kar ma ka bata tym din wajen xuwa goben, kai tsaye ka wuce gida, ka gayawa Marafa ina tafe da kaina, muyi magana. Yace to, Abba na barku lfya. Ya mike ya fice suka raka shi da kallo. Ummma kam bata sami cewa komai ba, saboda tsabar tausayinsa. Yana fitowa Gambo direba ya balle murfin mota ya fito, ya tarbe shi ganin ogansa na ta share fuska, yaya jikin nata? Ya dube shi ido jajur yace ba sauki Gambo. Mu shiga mota, ka maidani gida. Yace yallabai ai dare yayi sosai, nayi zaton gidan gwaggo xamu kwana. Ya miko hannu yace bani keys, kai ka wuce gidan Gwaggon ka kwana! Ya dan sunkuyar da kai, yace yi hkr yallabai Allah ya sauke mu lfya. Shi tuni ya bude gidan gaba ya fada. Gambo ya xauna mazauninsa da sunan Allah ya murza mukulli yaja suka wuce, a tym din agogon motar yana nuna 09:45pm. A daren nan nake son ganin Dady na. Gambo yace Allah ya yarda mana, ita kuma Allah ya bata lfya. Ya kama kai ya runtse ido, ya jingina sosai da kujera yana fadin amin Gambo. Direba na ta tsula gudu cikin dare. Shi kuwa Al-ameen kurwarsa na can cikin tunanin baya. Itin tsantsan son da Mama ke masa, shi yake gani cikin idanuwansa, har xuwa ranar da ya xo sallama da ita a sch, kawai gambo ji yayi Al-ameen na sambatu, sosai kikace kina sona sakeena, dama yaudara ce? Me yasa sakeena? Me yasa? Hnkalin Gambo ya koma gunsa yayi kiransa sau uku, kafin yaji kiran. Ya xuba masa ido yayi da direba ke fadin, kayi hkr yallabai, yace sakeena ta yaudareni Gambo, ta xuba min