Sashe 46
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ganin laifi na ni kadai? Nace ga wanda nake so, ba sai a ba ni shi ba. Ina ruwan kowa da rashin asalinsa? Ai dai ba daga sama ya fado ba, da uwarsa da ubansa. Yace, Maganar banza ce wannan mama, don na tabbata Daliti bai fi miki iyayenki ba. Kin kuwa san halin da umma ke ciki tun ranar da kika sa kafa kika bar gidan nan? Kin daure min kai, ban taba xataon zaki aikata irin wanan mummuna aiki ba. Tace hakan kadai xai memin mafita kuma akan bakana na dawo ko Danliti, ko su rasa ni baki daya. Ya xura mata ido, yana kada kai. Afuwa ya kamata ki nema ku sulhunta da iyayenki, su sa miki albarka, ko kin ga rayuwa mai kyau da anfani nan gaba. Saboda haka ki xauna anan ki jirani, xan shiga wajensu in kwantar musu da hankali tukina, gaskiyya bana so ayi miki taratsi cikin jama'a, kuma gidan cike yake da baki. Baki? Me akeyi a gidan? Ya amsa, biki na akeyi dana seed. Kana nufin kunyi aure? To Ya xanyi, tunda kinki ni Mama? Akan dole na yi auaran nan, su Baba sun matsa min. Ina muku murna, nima Allah yasa ni a danshinku. Ya xura mata ido gwanin tausayi. Yace, nasan ba xaki ji komai a ranki ba, tunda ba so na kike ba, amma ni har kwanan gobe ina sonki, shi ya sa abinda ke faruwa da ke ya xame min ciwon cikin raina, ki yiwa girman Allah mama ki sanya tunanin ki dawo sak! Yadda kowa ya sanki. Karka damu dani Ya Ali, ko da yaushe ina gaya ma kai dan uwana ne, kauanar mu ta jini ce mai asali. Kwanciyar hnakalina kuwa Danliti ya zama mijina. Ina fatan iyayen Al-ameen sunyi xuciya su fasa? Ko baka ji komai akai ba? Ya xuba mata ido yana mamakinta, ya jima bai amsa ba, kafin yace, Al- ameen ya koma Rasha da ciwon xuciya Mama..... Ta katse shi ido rufe ta dafe kirji. Tace, nagode Allah! Har naji sanyi cikin raina. Ya kada kai yana kallonta. Yace, baki masa adalci ba, baki tsoron amanarsa ta ciki? Akan me? Bafa dole bane na aure shi, ina son kowa ya gane wannan, kawai kaje ka gaya masu na dawo din, kaji me xasu ce? Yace ni ne nayi niyyar yin hakan, ba sai kin bani umarni ba. Yi hkr Yaya, bai tanka ba, ya tashi ya five, ta bi bayansa da kallo tana fadin cikin ranta, je ka dawo, duk na kosa in san babin da nake. Cikin dakin yayi sallama, abba ya amsa masa yana kokarin hadawa Umma shayi ta samu ta dan sha, ya akayi Ali? Ya xauna gefe kusa da shi, yace babu komai abba, wata alfarma naxo nema wajenku. Hankalin abba ya dawo gare shi, yace ina jinka. Allah ya sa batafi karfi na ba. Ya kada kai ya amsa, bata fi ba Abba, duk mai laifi idan ya nemi afuwa, me yakamata ayi masa? Ya dube shi da kyau da mamaki yace, ayi masa afuwar, domin Allah yana son masu yafiya ga bayinsa. Su kuma masu laifin su yi alakwarin ba xasu sake komawa ga wancanm laifin ba. Laifin me kayi? Ya amsa, laifin mai girma ne Abba, a misali Mama ta dawo ta nemi gafara, abba xa ka karbi tubanta? Ba abba kadai ba harda Umma dake kwance ta xubo masa ido, abba ya jima kafin ya numfasa. Yace Bansan dalilin da yasa ka min tambayar nan ba, amma ina so ka sani, mama ta aikata laifi mafi muni a shafin tarihin gidan nan, da mu karbeta da kar mu karbeta, bakin fentin da ta shafa mana yana nan baxai goge ba, ina so ka sani Ali, xaiyi wuya a fadin gari na Mama ta sami wani mijin, face katon daya dauke ta ya boye wani wuri tsowon watanni 3. Abu na karshe da nake so ka snai, shine bai kai kadai ka rokeni ba. Al-ameen ma ya rokar mata gafara kuma nayi masa tare da alakwarin ba xanki karbarta ba. Saboda haka ka kwantar da hankalinka, muddin Mamma ta dawo gidan nan, ba xan ce ta koma ba, haka xalika idan bata sauya ra'ayinta ba, ba xan ce mata a'a ba, Allah na kallo, nayi kokarin na, don nuna mata hanyar kwarai da samun abokin zama na kirki mai kyan asali. Ko duniya ta zageni, alhakin Na suka duka kuma zamuyi shari'a da su gobe kiyama. Kawai ji yayi kwallah na xubo masa, saboda tausayin Abba, yasa hannu ya goge, abba ya riga shi sake magana, ka daina kuka Ali, kaddara ce, tashin hankalina daya, mahaifiyarta da ta kasa samun nutsuwa. Ina jin tsoron kar ciwon xuciya ya kamata kamar yadda likitocin da ke duba ta suke gargadin ta kullum. Dalilin da yasa kenan nake fatan Allah ya sa mama ta dawo, watakila ya zama waraka ga mahaifiyarta. Na tabbata hankalinta xaifi kwanciya idan tana ganin ta koda a dakin auran Danliti ne. Ya Ali ya gyara xama yace, gaskiyya ne abba, kuma naji dadin bayanan ka. Saboda haka ina mai farin cikin shaida maku cewar mama na nan ta dawo. Abba ya xura masa ido. Umma kuwa ciccibawa tayi ta tashi xaune. Ba fahimce ka ba Ali? Inji Abba, yace Mama na nan a cikin gidan nan, idan kun ban izini, zan shigo da ita ta roki gafararku. Suka dubi juna shi da Umma baki sake, tuni hawaye suka tsinke mata, tana kada kai tare da salatin Manzo. Abba ya dube shi yace, je ka ashigo da ita Ali. Har ya mike ya sake komawa ya xauana, yace Abba ina fatan ba xaku daga mata murya ba, kasan gidan na cike yake da baki. Yace Insha Allahu, ba xan daga mata ba. Yace nagde abba. Ya mike ya wuce, abba ya bishi da kallon, sannan ya dubi Umma, ashe haka Ali ke da hankali? Nayi kuskuran hana masa auran Mama tunda farko. Umma ta goge hwaye tace, hakika mama tayi asara masoya 2. Haka Allah ya so, ba mu da abinyi, dai yi masa godiya, abba ya sauke numfashi, sukayi xugum suna sauraron ta yadda mama xata bayyana garesu. Jimawa kadan suka tsinkayi muryar Ya Ali yana fadin ki shigo mana! Na gaya miki komai ya wuce, ki shigo kawai. Make-maken munafurci takeyi ba wai ainihin tsoron bane cikin ranta, da su abba xa suyi kuskuran cewa ta juya, fes! Zata juya babu waiwaye sukayi sallama dakin. Ya ali na dauke da kit dinta. Ta toge bakin kofa, yasa hannun ya janyo ta har gabansu abba dake sake da baki suna kallon abin al-ajabi. Gata abba, umma ga Mama, ku mance da abinda ya faru, ku amince da xabanta, ku sa musu albarka, sai kuka ga Allah ya basu zuri'a abin alfahari. Mama ki durkusa ki roke su gafara. Ko dama a durkushen take kuma tuni hawayen suka tsunke mata, murya na rawa, tace.. BAKIN CIKI 2***12 Abba kuyi hrk, Umma ki yafe min. Abba ya numfasa yana kada kai. Ya ce a rayuwata gaba daya Mama ba tba xataon xaki min irin wannan mugun butulcin ba. Na dauke ki 'yar da na dauki burin duniya na dora a kanki. Kece kika bambamta da kowa cikin xuciyata, kuma na nuna miki dukkan gata amma dare daya, kika numa mana akwai wanda ya fi mu muhimmaci a rayuwarki. Tabbas na yarda da hakan, don a tunani na xan ga kin dawo kin bushe a lalace saboda tunanin kin barmu cin BAKIN CIKI sai gaki Fes! Kinyi kiba. Ban miki baki ba, ba kuma xan miki ba, amma ina mai tabbatar miki in rasa masoyi, kin rasa mai tsanin kaunar ki tsakani da Allah, kuma a yau na kara nadamar hana Ali auaranki tun farko. Maganata karshe itace, tunda kin nace sai Danliti to ki gaya masa ya turo magabatansa, muyi magana, sannan kiyi wa Yayanki Ali godiya, domin yayi miki dukkan taimako. Zaciyarta fara sol! Jin Abba ya ambato Danliti ya turo. Ta kara dukawa tana goge kwalla. Tace, ngde abba, kuma ina kara baku hkr, don Allah ku yafe min. Ta rarrafa gun Umma ta cusa kanta jikinta, umma kiyi hkr! Ta share hwaye tace ai ya wuce Mama, kinci albarkacin al-ameen da ali. Amma gyara kayanka, ai baya zama sauke mu raba ba. Ki bi duniya a sannu, domin ita duniya budurwa ce mai kyale-kyale da yawa, da zarar ka biye mata, to ka bace ka kuma shiga uku ka lalace. Ban da abin kari a gareki, don nasiha anyi miki, amma kin rushe saboda batan basira. Allah ya ganar da ke, ya sa ki a hanya madaidaiciya. Ya ali ya amsa da amin, yayin da mama ke ci gaba da gugar hawaye. Alin ne ya cigaba da cewa, don Allah abba karku nuna kowa ta dawo har tym din bakin nan xasu koma. Ko su Baba a kyale su tukuna. Ke mama ina son ki cigaba da xama cikin dakinku dan Allah, na san xuwa gobe da yamma kowa xai watse, sai a kam magana ta gaba, kinji? Ta amsa da kai, Abba yace shikenan Ali, kana son ka rufawa 'yar uwarka asiri, asirin kuwa da ya riga ya tonu. Yace kayi hkr dai abba, yace babu komai, ta tashi ta koma dakinta, idan tana jin yunwa, akwai abinci, yace xaki ci abinci ne? Ta kada kai, to taso na raka ki dakinki. Umma mun gode, tace Allah yayi albarka, ya amsa da amin. Tare suka mike suka bar dakin. Umma ta tafa hannu tana salati, sannan ta buga tagumi. Yanxun alh. Danliti xata aura? Yace, t ya xamuyi, wa kike ganin xai fito neman auranta, bayan ya san wannan kwamacala? Haka nan xamu hkr da abinda Allah ya kaddaro, yanxun dai bana ce ya turo ba? Sai mu sa ido mu ga wadanda xai turo din. Ta numfasa, tace Allah shi kyauta yace amin. Ke dai ki kwantar da hankalinki, ki daina xa damuwa a ranki don Allah. Tace naji alh. Ya ciga ba hada mata shayin suna tattaunawa. Kamar yadda ake tattaunaea da mama da Ya Ali. Shawarwari kawai yake bata, tana sauraronsa kamar gaske. Har kusan sha daya da rabi suna tare. Dagab bisani yayi mata sallama ya