Sashe 75
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mungode Allah mamina!141,ya juya kan dady dadina!yace nidai ansaba min son kai.ai de ba haka akeyi ba!yadawo gunsa yana dariya yace dadina albishirinka?yace goro fari yace to duk ku taso muje falo in nuna muku wani abu.meye shi? mami ta tambaya.dady yace miye naki na tambaya taso muje kawai.suka nufi falo.yauwa! to ku rufe idanuwanku!kuma dai?inji mami.kedai rufe dadi yafada suka rufe ido suna dariya.yace minti daya yakoma waje da sauri ya kamo hannunta tana fisgewa yashigo da ita.ya tsaidata gabansu.kunya kamar ta nutse qasa yace kuna iya budewa yanxu..alokaci guda suka bude duk sukayi mutuwar tsaye.dadi yafara fadin sakeena! taja mayafi ta rufe kai.mami kuwa da saurinta ta rungumeta.Allah sarki sakeena! ashe Allah zai hada fuskokinmu?kwalla suka cika idon mami.mama kuwa ta goce da kuka.mami ta dagota hannu biyu menene abin kuka sakeena? don Allah ki dena.wannan ranar farinciki ce.dan na tabbata dan tilon dana zaisamu farinciki data dade dayin qaura daga jikinsa.karki damu da komai kisaki jikinki kamar da kinji ko?ta durqusa qasa baba ina yininku? haryanxu yana mamaki lafiya qalau sakeena.haka shima alameen idanu suka dauki kwalla.yace ashe har umma ta rasu.mami ta kamota sukazauna a 2 sitter,tana rungume da kafadarta tace munji rasuwar ummanki amma rashin jin dadin abinda kikayiwa alameen shiya hanamu zuwa gaisuwa.kuma bamu gaya masaba.karkiga laifinmu sakeena.Allah kadi yasan wahalar da mukasha kafin musamu mu ceto ransa. Allah kadai yasan yan kudaden da muka batar dan neman taimakon addu'ar Allah ya cire mishi sonki.muka samu son yasuma.dan kuwa suma yayi tunda gashi daga ganinki ya farfado.kiyi haquri sakeena wannan al'amari duk cikin rashin sani akayi.ta silale qasa tasake durqusawa wlh babu komai mamii.idan kuwa dame laifi ni yakamata nabada haquri dan angayamin dakanki kikazo rokona.kina bani haquri amma naqi sauraronki nima ku yafemin,,,,,ta jawota ta rungumeta karki damu sakeena.wannan wani qaddararren al'amarine daga Allah.babu mai iya kauda shi.amma dayake bakida hakki gashi ubangiji yabayyana komai....shikuma yaga makomarsa.to Allah ya jiqan hajiya halima.kidage dayi mata addu'a ita kadai ce ribarki gareta.kinji?ta dago tana amsawa dakai tana share kwalla!dady ya numfasa munyi farin ciki da ganin wannan rana.muna masu tsananta godiya ga Allah ta'ala mafificin dukkan komai.saboda haka muke roqonsa ya karemu daga dukkan sharri.yakuma jikan hajia halima ya yafe mata dukkan kurakurenta.143Suka amsa amin summa amin, bayan dadi ya gama addu'oinsa alameen ya dubi mami yace ina iyata?tace suna can bayan gida suna hira.ya miqe yana fadin barin kirasu suga sakeena ta.ta dawo mami tace yakamata.yashige kicin kofar dazata sada shi da waje.mami ta dubi mama tace inaa fata komai ya dai daita?biki kawai zamu shako?ta sunkuyar dakai dadi yace kema kinsan bazata iya fadaba.ki bari ya shigo muji daga bakinsa,,,,sai ga hayaniyarsu dasu iya suka shiga tafa hannu suna sallami lalle matar mutum kabarinsa.suka zauna gefe suka gaisa.iya tace ubangiji yanuna mana ranar auren nan.suka ce amin.al'ameen yazarce da fadin musha rawa ko iyata?baki har kunne tace sosai kuwa dan iya.Allah dai yanuna mana lokacin lafiya.anata raha suka bar falon.ladi ta tafi takawo musu ruwa da abinci.mami ta gyara zama tace yadai? ya ake ciki? nafa kosa..yayi yar dariya yace komai dai dai mami.kinga tun jiya muka baro zariya muka tsaya kaduna makarantar su waleed.mukaje suleja gun waleeda yar rigima.muka wuce abuja gidan abba.bakuga yadda ya karbeni ba murna da farin ciki ba a bayani.ya rungumeni yana kwalla.yanxu maganarku muke jira yace ko yaushe nashirya nazo adaura mana aure ai baza a bata lokaciba ko dady? bakin mami har kunne tana fadin masha Allah! dady yace me za a jira?Mu ai a shirye muke in sha Allahu gobe zan tafi abujar mu sasanta dole in durkusa in nemi afuwa zan karbi lambarsa da adres kafin ku tafi Allah ya shige mana gaba ya kore dukkan fitina suka amsa amin al- ameen ya zarce da fadin amma dadi karya wuce sati uku ayi komai a gama kowa BAKIN CIKI 3******11 kunga kuma zan sami wata shida anan abin zai yi daidai suka yi dariya mami tace gaskiya ne sati uku ai sun wa duk shirin da za'ayi kai Allah ka nuna mana lfy, murna cike da zukatansu bata misaltuwa mami kamar ta hadiye mama ta tasa ta a daki suka ci abanici tare bayan sallar azahar sukayi shirin tafiya haka ta baza mata kaya kala kala tun daga sutura zuwa kayan shafe shafe tace ta zafi duk wadanda ta keso ta cire kunya ta zabi yan tsiraru Al-ameen na taya ta shine ma ya jido mata kayayyaki masu yawa dadi ya kwala wa mami kira ta tashi ta fita mama ta dubi al- ameen tace wai ka manta da tsarabata ne yace ina sane kyale ki naiy in gani komawa zakiyi dasu ta dan shagwabe fuska kai dokta saboda Allaj baka san kunya ba maimakon ka taimake ni, ya zuba mata ido maimakon ka taimakeni ya maimaita a shagwabe tayi yar dariya tace don Allah in ta shigo ka gaya mata gani ma na shigon me za'agaya min mama ta sunkuyar da kai ya fara dariya yana fadin wai tsaraba tayo miki shine ta bari a mota tana jira ni in gaya miki wanda ya siyo abu ba shi yake daukowa ya bada ba? Mami ta dafa ta tace Allah sarki sakeena kyale shi karya gadi din so yake ya manna miki laifi dame dame kika kawo min cike da kunya tace fruit ne kawai mami tace Allah yasa da karot ciki suka kalli juna suna dariya akwai mami ta ce to shine ki ka ki gaya min abinda na ke ta marmari kwana biyu ban ciba ta yunkura da sauri tacr bari a kwaso miki shi ma ya mike yabi bayanta mami ta bisu da kallo tana dan murmushin jin dadi jim kadan suka dawo daddauke da ledojin guda uku manyan gaske mami taji dadi sosai tana sa albarka sannan ta mika wa mama rafar kudi dubu ashirin tace wannan dadinku yace in baki tasa hannu ta karba tana kada kai haka da yawa mami to nagade Allah ya saka da alkairi tace amin sakeena al-ameen yace mun gode mami bari inje wajen dadin mu za mu wuce ya wuce suka zauna jiran fitowarsa basu dade ba suka fito tare mama ta zamo daga kujera ta tsunna tayi godiya yace ba wani abu Allah ya sauke ku lafiya tace amin suka rankayo waje al-ameen ya daga murya yace iya ta na wuce suka fito tare da ladi sukayi masa sallama sannan suka karasa wajen mota sai da suka bar get suka koma cikin gida suna masu addu'ar sauka lafiya ,, lafiyar kuwa suka sauka cikin yarda ubangiji ya sauketa gida ya taimaka kwaso mata kaya zainab ta fito ta tarbe su bakinta har kunne tace ga amarya ga oga shirin yayi yace kin ci ziro zainab kuma baki da sa'a da kin fada daidai Allah kadai ya san yawan ladarki tace sir zan gyara ga amarya ga ango....yace kin makara". Zai wuce ta karbi kayan hannunsa no sir ai ba wani sai ogan mu yana yar dariya yace kinyi gaskiya zainab kina damaki ashirin tace"thank yau sir mama tasa musu baki har wata godiya ki ke yi ki na kware baki kar kiyi karatu yarinya ki jira bonus" ta bude kofa suna dariya dr al-ameen ya ce ina ruwanta zainab ta amsa nima shi na gani ke ko tukuicin baki bani ba amma kina sawa oga ido suna tsaye tsakar daki ya laluba aljihunsa ya zaro dubu biyar ya mika mata karbi wannan ki kyaleta kawai sai mun hadu gobe -tana dan murmushin jin dadi jim kadan suka dawo daddauke da ledojin guda uku manyan gaske mami taji dadi sosai tana sa albarka sannan ta mika wa mama rafar kudi dubu ashirin tace wannan dadinku yace in baki tasa hannu ta karba tana kada kai haka da yawa mami to nagade Allah ya saka da alkairi tace amin sakeena al-ameen yace mun gode mami bari inje wajen dadin mu za mu wuce ya wuce suka zauna jiran fitowarsa basu dade ba suka fito tare mama ta zamo daga kujera ta tsunna tayi godiya yace ba wani abu Allah ya sauke ku lafiya tace amin suka rankayo waje al-ameen ya daga murya yace iya ta na wuce suka fito tare da ladi sukayi masa sallama sannan suka karasa wajen mota sai da suka bar get suka koma cikin gida suna masu addu'ar sauka lafiya ,, lafiyar kuwa suka sauka cikin yarda ubangiji ya sauketa gida ya taimaka kwaso mata kaya zainab ta fito ta tarbe su bakinta har kunne tace ga amarya ga oga shirin yayi yace kin ci ziro zainab kuma baki da sa'a da kin fada daidai Allah kadai ya san yawan ladarki tace sir zan gyara ga amarya ga ango....yace kin makara". Zai wuce ta karbi kayan hannunsa no sir ai ba wani sai ogan mu yana yar dariya yace kinyi gaskiya zainab kina damaki ashirin tace"thank yau sir mama tasa musu baki har wata godiya ki ke yi ki na kware baki kar kiyi karatu yarinya ki jira bonus" ta bude kofa suna dariya dr al-ameen ya ce ina ruwanta zainab ta amsa nima shi na gani ke ko tukuicin baki bani ba amma kina sawa oga ido suna tsaye tsakar daki ya laluba aljihunsa ya zaro dubu biyar ya mika mata karbi wannan ki kyaleta kawai sai mun hadu gobe.............. - Takarba mama na fadin ok mun gane dama da mun ganki da manyan maki mun san na coge ne yace eh ba komai zainab tayi dariya tace na gode sir sai ka fito ta wuce tanayi wa mama dariya yayi mika yana salati sannan ya zauna a kujera ta ware ido tace zama naga kayi kar in zauna tace gida ya kamata kaje yace korata ma kike yi ta kada kai ba haka bane zai fi kyau kowanne mu ya samu yay wanka ya huta kafin magariba ta karasa ya munfasa yace haka ne yi hakuri don Allah sai ina ganin kamar an daura ne unguwa muka je muka dawo ta ware ido iye eh wallahi kiris ya rage in fada katifar nan in kwanta fuska yamutse tace wasa ka ke kin san Allah bada wasa nakeyi ba a dai bar kaza cikin gashinta miko min ruwa in sha in gudu,,Tace sai dai in karbo maka wajen zainab