← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 79

Sashe 28

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikinta sun dau xafi ba kadan ba. Ta fasa kara mai shiga xuciya. Tace wayyo Allah na shiga uku! Na shiga Uku! Yaya Ali ya mike a afirgice, gabansa ya yanke ya fadi, ya fito da sauri yana tsinkayar kukan mama, ya nufi sasan. Umma ke fadin baki shiga uku ba Mama, sai nan gaba muddin baki dauki nasihar da mukeyi ba miki ba! Hannu biyu Ya Ali ya sa ya ciccibeta ya mikar da ita, xafin duka da tsananin BAKIN CIKI da ke dankare cikin ranta ya sa ta kwakume Ya Ali. Bakin gado ya xaunar da ita ya dago fuskar ta hannu biyu yake share hawayen ta, yayin da nasa kwallan ke neman sauka. Yace, haba mama kiyi wa kanki fada mna! Murya na rawa tace, me nayi musu Ya Ali? Saboda Allah me na yi? Me kikayi? Yanxu a wajenki wannan ba laifi bane? Haba mama! Ba haka kike ba, kin sauya da yawa kar dadin bakin Danliti ysa hankalinki ya gushe. Laifin me Al- ameen yayi miki, kike son ki masa wannan sakayyar? A xato na koda babu a alameen, ni ne mutum na farko daya kamata ki fara dawowa ranki, don na dade ina yawo da ciwon sonki Mama, ki tausaya mana, zai sa ki canja halayenki? Ta xuba masa kwala- kwalan idanuwanta da suka kara fitowa waje jajur! Tace, Yaya Ali ina ganin girman ka, ka kyale ni da wadannan surutan, don ba xa suyi tasiri ba. Ni nace ina so Al-ameen, yanxun kuma bana son shi Danlilti nake so. Ra'aryi nane, ba sai a kyale ni ba, ko akwai wanda zai zauna min da shi? Ya bita da kallo, ta sa aya kafin yace, ki daina tunanin wannan ra'ayin na ki mai yuwuwa ne, kin dauko katon aikin da xai rushe martabar gidan nan a idon jama'a. Idan baki son Al- ameen, ki musanya da ni Mama, zai fi miki kyau a bisa shirmen da kie sonyi. Ta runtse ido tace, yaya Ali je ka kawai! Ba ki son gaskiyya? Ta kauda kai kwalla na tsiyaya. Ya sanya murya yace, xan bar ki ki kwanta kiyi tunani sosai, cikin kan ki. Ina rokon ki girma da Allah, ki manta da kudirin da kika dauko. Bata tanka ba, haka bata dube shi ba yace, A bakin tofa ya tsaya ya kare mata kallo kafin ya sake fadin, bana so ana taba jikin ki mama, tamkar ni ake tabawa nakeji. Pls ki sauya tunaninki. Haushi ya kara kuma ta, ta juya masa baya. Ya fice yana kara waigen ta. A daren nan daga ita har Yaya Ali babu wanda ya iya cin abincin balle barci. Tunanin Mama shine xata ga yadda za'ayi a raba ta da garin nan. Cikn xuciyar ta tasha alwashin ko sun maida ta, zata dawo, dole su gaji su kyale ta da wanda take so. Dalilin da yasa ke nan, yau kwata-kwata taki bude kofar ta, kowa yayi bugu, iyayinsa har kawunninta, sai dai kalaman bakin su suka kare. Amma mama taki bude kofarta. Duk wanda ka duba ransa bace yake, musamman Abba, fuska kamar gobara ya dubi Umma yace, dauko min tabarya! Ta mike a salube ta shiga kicin ta dauko masa tabarya, ta mika masa. Alh basiru yayi caraf! Ya karba. Yace karka balle kofar nan yaya, asara biyu xa'ayi..... Yace yarinyar nan dole ta bar garin nan, ba xata xauna tana jawo min xagi ba, ana kallo na tsahon banza, bansan abinda nake yi ba! Buge min kofar nan, ko ka ba ni da kaina, in sauketa! Kowa yayi cirko-cirko. Alh. Basiru ya kai wa kofa duka da tabarya, sai ga sallamar Yaya abdul- kareem. Basu gama amswa ba, yaci gaba da tambaya, lfya? Me ya faru da kofar? Abba yace, nayi farin cikin xuwanka, don ni ma a yau nayi niyyar tafiya gunka. Me ya faru abba? Umma ya naga kamar kina kuka? Yace, mama ce.... Me ya sameta? Ya kwashe kaf halin da suke ciki ya gaya masa. Kai! Bai gaskanta kunnuwansa ba, shi yasa yace, abba ban yarda da wannan maganar ba, ya kamata asake bincikawa. Abba ya xuba masa ido jajur! Yace, wannan maganar ni Uwaisu nake gaya maka ita. Abdul kareem kasan kuwa ba za ayiwa mama kage ba, domin ni na haifeta. Saboda haka gidan ka xata xauna can har xuwa lokacin bikinta! Yace, ya xama wajibi, don ganin nan da kuka yi min xuwa nayi in tafi da ita dama. Al'ameen ya damu kwarai har yana ganin kamar wani abu ne ya faru da ita ake boye masa. Wlh jiya ya turo mahaifiyarsa da yamma wai ta zo ta bincika masa lfiyar mama, shine nace shi kwantar da hankalinsu Insha Allah da kaina xanje in dawo da ita. Wannan al'amari ya daure min kai. Yaushe mama ta canza haka? Kawu Basiru yave xancan banza takeyi, tunda ita ta kawo Al'ameen har aka sanya musu rana, bata isa tace ta canza shi ba! Wannan karya take yi. Haushi ya kara kure yayanta, ya mike ya suer tabarya ya kaiwwa kofar duka sau biyu kofar ta balle, bata a dakin. Ya nufi kofar bayi ya murda can ma garkamen yake, bai tsaya wata-wata ba, ya maka mata tabarya. Bugu daya kofar ta wangem, sai ga mama jikin bango ta fita hayyacinta saboda tsabar kuka. Al'amarin tamakar mafarki yayana yake gani. Ya xura mata ido, yace hauka kikayi mama! Me Al-ameem yayi miki? Iye? Yayi miki laifi ne da ba zaki fada ba! Sannan ki rasa wanda zaki bi, sai dan liti! Kinji abinda nace? Kin yi karya ki xuabar mana da mutunci a garin nan! Zo mu wuce, ban son jin komai daga gareki! Ta sulale kasa hannaye biyu bisa kanta, ta kara fasa kuka mai tsananin gaske. Matan gidan suka kutso kai cikin bayain suka tarairayo ta, suka fito da ita dakin. Yaya yana fadin ko mutuwa zakiyi yau, sai na tafi dake mu je can idan Al- ameen ya kira waya, in tambayehsi a gabanki, muji abinda ya hadaku! Amma yaro na sonki yana tattalinki. Iyayeynsa na ririta ki, tashi guda kice ba kiyi da shi, aikin san wannan karya kikeyi. Ina kayan ta suke umma? Hada mata si don baxan bata lokaci ba! Gaba daya suka yanyame ta da fada kowa na fadin albarkacin bakinsa, su Umma na hada mata kaya. Su Hajiya Hajjo na rarrashi ta suna bata baki tare da gyara mata jiki da fuska. Yaya Ali kuwa yana xaune gefe rayuwa tayi masa bakikkirin! Ana janta, tana togewa suka saka ta gabn motar yayanta. Ya jefa jakar ta gidan baya, daga nan yayi sallama ransa bace, ya ja motar yayi gaba da mama. Dole ne ya saurar daidai shagon Danliti, domin akan mahada shagon yake. Tsayuwar su wajen, ya jawo hankalin Danliti xuwa garesu. Ya xuba wa Mama idanuwan sa suka sha kwalli rangadau! Haka ita take kallonsa kwalla fal! Suna neman sauka. Ya daga kanka ta fito kofar shagon, irin duban da yake mata ya bayyanar da damuwarsa karara bisa fuskarsa. Tausayinsa ya lullubeta, nan da nan hawayen suka fara bulbula. Yayanta bai kula ba, kokarin sa, duk motocin da suka kawo, suka wuce shima ya samu ya haura. Yawanci duk manyan motoci ne, kamar yadda akansan babban titi ne, wanda ya mike ya tafi har lagos. Suna tsagaitawa ya cilla tasa motar ba tare da ya fahimci Danliti da mama sun ruga sun gama magana da idanuwansu ba. Kawai ji yayi ta kara gocewa da kuka mai karfi. Ya dan dubeta, ya kada kai. Yace, Al'amarin ki na bani mamaki, look kina jina? Saurare ni muyi magana ta fahimta. In tambayeki xaki bani amsa? Hankalinta sam ba awajen sa yake ba, balle ta saurare shi. Fuskar Danliti take gani, irin yadda ya shifa damuwa yana neman xubar da hawayensa, shi ya kara dagula mata lissafinta. Yace, saboda Allah zaki gaya min Al- ameen yayi miki da zaki juya masa baya? Tayi shiru, danliti na cigaba da yawo a idonta. Yace, kin kuwa san tun ranar da kika dawo garin nan. Al-ameen ya rasa nutsuwarsa? Ban iya kirga yawon wayoyinsa ba, tunaninsa kina cikin wani matsanancin hali ne aka boye masa. Kar ki saki reshe ki kama ganye Mama, domin kowa yasan Danliti lalata rayuwar ki kawai zai yi, ya kai ki ya baro ki tashar danasani. Ki ga ya min idan Al- ameen yayi miki laifi ne, ni da kaina xan masa magana in ja masa kunne. Kinji? Bai yi aune ba yaga ta balle murfin motar ta dire waje. Ta mulmula cikin ciyayi. Cikn tashin hankali ya take birki.... Allah yasa ba babu mota a bayansa, yayi fakin gefen titi, ya fito. Can ya hange ta tana kokarin tashi, amma ta kasa, kafin ya gangara wajen 'yan tsirarrun jama'ar wajen sunyi caa! Kanta. Suka ciccibota, suna sallalami tare da mamakin yadda aka yi abin ya faru. Gaba daya gwiwowin ta sunyi mugun kurjewa ta xura da gudu amma bata je ko'ina ba mutane suka cafke masa ita. BAKIN CIKI yasa ya dauke da wani mahaukacin mari daya tilasta mata xubewa kasa. Wani dan dattijo cikinsu ya kama shi. Yace, haba malam yaya haka kuma? Baka ganin kaddarar da ta sameta? Da ta mutu fa? Ku rinka kulawa da murafen mota mana don gudun irin hakan! Idanuwan sa ajuye yake magana, kyaleni da yarinyar nan baba! Da kanta ta bude murfin ta fito! Iskanci ne kawai, dama kin mutu, mu huta da wannan BAKIN CIKIN da kike son jefa mu! Saboda haka xan koma in gayawa abba kin bude mota ki diro, ni kuma ba xan tafi dake ba, ki xauna kiyi duk abinda kika ga dama agarin nan, tunda lalacewa kika xaba. Allah ya shirye ki! Ya shura takalmansa ya koma mota ya tayar yayi kwana ya koma gida ya bar Mama anan tana faman kuka, jama'ar dake wajen suna mamakin wannan abu har sun kasa fassara shi. Dan dattijon nan shi ya riko ta hankali suna tafe tana bashi labarin wai auran dole ake son yi mata. Kwarai kansa ya daure jin cewar ita 'yar gidan Uban dawaki ce, don haka ya tasa ta har gidan. Amma me? Suna xuwa kofar shagon Danliti ta xarce can tayi xamanta bisa benci. Dan liti ya
Chapter 28 · 0% Book details