← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 79

Sashe 42

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

me xaki je yi Lafai? Tace uzurina xai kaini. Allah ya kiyaye hanya, ta amsa amin. Ya daga kai dubi dady dake tsaye yace, sai na dawo dady, to ina jin ma xan sameka asibitin. Yace shikenan sai kazo. Ya juya yayi waje, su iya na kokarin fitowa su gaisa. Amma ina saurin da yakeyi, ya hana su su same shi falon, tuni ya kai ma'ajiyar motocin, ya murza ya bar gidan. Umma na xaune an jera mata filo, ruwan lipton kawai ta iya kurba, ya xuna cikinta. Likitan ne yace ta dan jingina kadan ta huta. Duk 'ya'yan sun kewayeta, abba na xaune gabanta bisa kujera. Gaba daya tausar xuciyarta suke yi don ta fidda abin a aranta. Sallamar al-ameen cikin dakin ita ta dauki hankalin kowa, suka amsa kona masa duban tausayi, ganin yadda ya xabge kamar mai ciwo, wai don ma su mami na yin iya kokarinsa akansa. Ya bisu daidai sukayi musabaha, sannan ya tsugguna gaban Abba suka gaisa. Tuni ganinsa ya sa hawayen Umma suka tsinke, yayi shiru a tsugunne. Abba ya dafa shi, yace sai ka dawo ka sami labari maras dadi? To ina so ka kwantar da hankalinka kayi imani da kaddara, ka sani yau da ace mama na da 'yar uwa xan baka ita, don in nuna maka iya kaunar da muke maka. Mama ta zabi ta wulakanta mu, shi yasa na ke son kowa ya cireta a ransa, mu manta da ita mu kyaleta duniya ta hora ta. Kayi hkr kaji? Ya goge kwalla yace naji abba, kuma nagode akan iya kokarin da kukayi min, amma abba ina rokon ka, don girman Allah ku ya fe mata, sannan ku sanya mata albarka, a auran da xatayi. Duk sukayi shiru, kowa ya xuba masa ido. Tausayin sa na ratsa su, umma ta goge kwalla. Tace Mama ba abar tausayi bace Al- ameen, don haka ka daina rokon ayi mata afuwa laifin data aikata. Ya kata matsowa gaban gadon yace, ba haka bane Umma, ki san sharrin shaidan, sannan xuciya bata da kashi, ba 'a son ran mama zata aikiata wannan abin ba, xuciya ce ta saka mata, na tabbata duk ranar da ta nutsu tayi tunani xata gane lallai bata kyauta ba. Don Allah Umma ko ina nan ko ba nan, idan Mama ta dawo ku amshe ta hannu 2, ku samata albarka. Insha Allahu shaidanin daya rinjaye xuciyarta, xai kyaleta, ta dawo diya ta gari kamar yadda take da. Abba ya kara dafa shi, yace idonka ya riga ya rufe a son mama, shi ya sa baka kallon girman laifin da ta aikata. Ya juya ya dube shi, ba haka bane Abba nasan ina son mama kuma har na mutu ba xan daina son ta ba, amma ku yafe mata, don rayuwar ta, tayi kyau nan gaba, ba farin cikin mu bane ace mama ta lalace tabi duniya, tunda gaba dayan mu nan, muna son ta. Kun yafe mata ko Umma? Tace kayi hkr Al- ameen ba xan iya cewa komai ba tukunna, ya abdulqadeer yace, ko mu bamu goyi bayan su Umma suyi afuwa gareta ba, har sai ta sauya zabin da tayi da. Tunda tace ba kai ba, to ka kawo wani dan mutunci tamkar kai, amma ba Dan liti ba. Wanna itace shawarar da muka yanke. Yana rufe baki dadi ya turo kofar ya shigo tare da gaishe-gaishe. Ya dubi al-ameen yace, dr na jiranka. Da mamai ya dube shi, dr. Lawal? Yaushe ya zo? Bai dade ba, muna shirin fitowa, sai gashi shine nace ya xauna xan biyo na gaya maka. Ya mike yayi sallama da su ya bar asibitin. Bai sami mami ba, don itama driver ya wuce da ita lfya. Dr. Lawal na babban falon gidansu, ladi sun adana shi da kayan kusa da baka, amma da ka dube shu kasan baya cikin sukuni. Yana shigowa ya mike da sauri ya tarbe shi suka kama juna. Dr. Lafai! Yace banyi xanton xaka xo ba. Dole na xo, wannnan mummanan labari ya hanani barci jiya. Yayi dan yake, kai dai bari, mu xauna aboki na. Suka zauna kujera daya, dr lawal yace, me yayi zafi likita? Idanuwansa suka kada yace, bansan me ke faruwa ba dr sama da sati 4 ina can na daina jin wayar sakeena, aka ce min bata da lfya ne, dalilin da yasa na dawo kenan don hankalina yaki kwanciya ita kawai nake son gani. Ina xuwa na iske labari ya sha bambam, wai sakeena ta sami wani ya hure mata kunne, har ta mance da manyan alkawuran da ta daukat min. Kowa yayi iya kokarinsa wajen nuna mata gaskiyya, amma sam tace ba san wannan ba. Abban ta kuwa ya sha alwashin ni da ta fara kawowa akayi mana baiko, ya sani ba xai daura mata aure da kowa ba, face ni don haka yace ba xan koma sai an daura auran. So da kaunar da nakewa sakeena yasa bana tunanin komai Illa xumudin a daura mana auran, shi yasa koda naje jiya bana nuna maka komai ba.a xato na bai kamata in tona kwanne sirri na sakeena ba, do kar a zage ta matsayin maci amana, ina ganin kamar idan muka kebe matsayin miji da mata, xan iya rinjayar ta. Son da take take min ya sake dawowa xuciyarta. Ashe duk abin da nake zato ya wuce nan dr.lawal kawai na dawo jiyan su dady ke gaya min sakeena ta gudu cikin dare ba a san inda take ba. Al-ameen ya jingina da kujera ya runtse ido sai hawaye shar... Na malala, hankalin dr. Lawal ya kara tashim ya xura masa ido jim sannan ya sauke numfashi ya dafa shi, yace, kana cikin tashin hankali aboki na amma Allah yace duk inda tsanani yakem to tabbas da akwai sauki. Pls ka zama jarumi a cikin jarabawar nan, ka bari hkr ya xama sanadin samun saukin tashin hankalin nan. Ya bude ido taf da kwalla, yace inason sakeena Dr. Kai kasan hakan, yace kwarai da na sani kuma xato na itama tana tsananin sonka. Ya matso shi sosai yace haka ne, wlh sakeena tana sona, to me yasa ta kini tym 1? Yace mata kenan Dr. Lafai. Balle sakeenna na da kyau da xata iya wasa da hankalin kowane da namiji. Watakila kuma wancan yafi ka duk abubuwan da take bukta. Dan wani minister ne a abja? Yace ban nemi sani ba, a yau ne nake jin sunansa bakin yaanta wai shi Danliti, danliti? Daga jin sunan kasan ba wani bane. Da sauri ya amsa ai kuwa wani ne.... (Hahaha Allah sarki lazy Dr.) tunda ya sace min sakeena. Ko da kuwa kwara masai yake yi. Inda ace xan gan shi xan iya durkuwa gwiuwa 2 in roke shi, ya bar min sakeena ta. Wlh itace rayuwata dr. Ya kada kai yace, ka daina fadar haka Dr. Lafao kar fa ka mance wani hani ga Allah baiwa ne, xa iya kasancewa sakeena kyan dan miciji gareta.... Ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu.... Yace gaya min kowace kalma dr. Amma kar ka aibata min sakeena, ba xan taba ganin farinka ba. Ya xura masa ido, kunshe da mamaki, kafin yace, ba nufi nake nan ba aboki na, ina so ka gane cewar bakomai da kake bane yake kasancewa alkhairi a gareka, shi ya sa kullum ake son bawa ya roki alkhairi wajen Allah. Yace sakeen alkhairi ce gareni, tuni mafarkai na suke nuna min hakan, har xuwa yanxun kuma jiki na yana bani sakeena tawa ce, mishkila aka samu wani wurin, bana so musu da su Dady ne kawai, shi ya sa nake nuna musu na hkr da ita. Yace to idan baka hkr ba, yaya xakayi yi? Tunda batayi da kai? Babu abinda BAKIN CIKI 2***10 Amma nan da iya shkrun da xanyia duniya ba xan daina son ta ba har na koma Ubangiji. Ya xura masa ido, yace Al- ameen kar ka manta akwai gagaruminn aiki gabanka wanda kowa ya xura ido don ganin rawar da xaka taka, kasancewar kai kadai ake tunanin xaka iya taka ta kuma mutanenan arewa suna jiran daya tamakar dubu ya dawo masu da abin alafahrin a duniya baki daya. Ina ka sami nutsiwa ka fuskanci abinda ke gabanka ka tare da jadda imani a cikin ranka, lallai Allah xai iya baka wata. Ina fatan xuwa na ba xai xama abnxa ba ba, kuma addu'ar duk masoyanka a zariya ba zata fadi kasa banxa ba. Kowa yace Allah ya musanya maka da lakhairi, na tabbata Allah xai duba ya kawo sauyi na fadi daidai? Ya numfasa yace ka fadi daidai abokina na, na gode ma kowa bisa addu'ar da suka yi min. Xan koma rasha da yardar Allah cikin yardarsa xan dage na fidda kowa kunya. Sai dai abinda nake so ka sani har in mutu ina son sakeena. Yace tuni na sani, sannan ina da ilimin xuciya daya gareka, duk abinda Allah ya xuba cikin ta, babu me iya dauke shi. Ya koma ya jingina da kujrea, rungume da hannayensa, ya dan numfasa ya kada kai, dr. Lawal ya bubbuga kafadarsa ya sake fadin, ka manta kawai abokina, ya wuce, ya bishi da kallo kawai baice komai ba su dade tare. Dr. Lawal na kara kwantar masa da hanakili tare da nuna masa mahimmancinsa ga al- aumma. Bayan azahar suke asibiti ya gaida Umma, daga can ya wuce zariya, shi kuwa Al- ameen gida ya dawo, don shima ba ya son yana ganin Umma kwance tausayinta yana kara karya masa xuciya. Ya rinka jin kamar su abba ba xa su yafe wa sakeena ba. Wannan shine babban tashin hankalin sa. La'asar ta kawo jiki yana xaune shi kadai bisa gadonsa, tym-tym ya kan dauki hoton da ke bisa kirjinsa ya duba. Hotonsu ne shi da mama wanda sukayi a dakin Mami, xuwan ta farko gidan. Karo barkatai kenan daya daga hoton ya xura masa ido tsawon lokaci, sannan ya mike ya sake kife shi. Ya laluba aljihunsa ya dauko xoben da Mama da dawo masa dashi, ya xare na hannunsa ya hada su waje daya, ya xura masa ido. Sannan ahankali yake wasa da su, ya rike kowanne yana hada su karo. Cikin idanuwansa yake ganin ita ke rike da wanda
Chapter 42 · 0% Book details