← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 79

Sashe 12

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

su ameera, haka ya zura mata ido ya rasa inda zai tsoma tsumman ransa. Gajiya tayi da tsayuwar ta kada yaran tace, "ku wuce muje". "sakeena!" ya kirata, ta tsaya cak! Sannan ta dawo baya ta tsaya saitinsa. Bata kalle shi ba sai da yace, "pls ki dubeni sakeena" Ta dago su raurau da kwalla ta kalle shi. Yace, "ki taimakeni ko fasfot ne na hotnki ki bani na wuce dashi". Tace, "sai dai in duba maka wajn anti". "hnzarta don Allah ko na iya tfya". Da sauri ta wuce ta barshi da yaran. A daki ta sami anti rabi tace, "ki taimakeni anti, Dr. yaki tfya wai sai na kawo masa hotona". Tayi dan murmushi, "ai wannan likita naki sai a hnkali, je ki dauko album ki duba masa". Ta kwaso manyan album guda 4 ta darzar masa guda 2, daya nata, daya suna tare da su ameera. Ta nemo ambulan ckn takardn yayanta ta saka su ciki, tayi waje. Tana mika masa ya bude ya zaro su ya duba, yayi jim! Kafn ya sumbaci hoton, 'yar kunya ta kamata, ta kauda kai. "Sakeena!". Ta dube shi, yace, "na gode, kinga na sami abokiyar hira ko? Ga kuma abokina da babbar kawata". Tayi shiru, ya sake cewa, "kinyi shiru, are u jelous?" Da mamaknta tace, "na me?" "zan wuce da madam dina, kuma a gabnki na fara nuna mata love". Tayi dan murmushi, "lokaci na wucewa Dr. ban son dare yayi maka" Ya lumshe ido, ya bude yace, "zan tafi sakeena, sai munyi waya ko?" ta amsa da kai. Ya juya kan yaran, "to ameera, sai wani satin ko?" tace, "zaka kira waya?" "sosai ma. Ameer sai na kira ko?" suka yi musabaha ya tafi yana fadin, "to yaya?". Ya shige mota suka rufe masa, "Safe journey! Allah ya tsaye". Ya amsa, "amin SAKEENA TA! I love u". Tace, "me too". Ya yiwa mota key, ta janye yaran gida. Yayi kwana ya bar harabar gidan, suna yi wa juna bye-bye! Al'amura sunci gaba irn haka, kullm son sakeena kara zama yake wani wuri na musamman ckn zcyar al'ameen, tamkar ynda mama ke jin rayuwarta ba zata taba tfya daidai ba, ian bata jin ko da muryar Dr. nata ba. A haka ta kammala hutnta na sati 3, duk sati yake zuwa suga juna. Yau shine satin karshe da mama zata koma gida, daga can sai makrnta. Akwai alkawarn zata je gaida maminsa kfn ta koma, sbd haka tana zaune ckn shiri tare da 'ya'ynta 'yan rakiya. Karfe goma na safiya yana kofar gidan. Babu bata lokaci ya kwashesu ya aje katafaran gidan mahaifnsa. Suna ckn mota basu fito ba yake fadin, "saura ki shiga kina min kauyanci, sai nai miki allura a gaban mamin, inga tsiya" . Ta watso masa harara, kunyar me zanji? Muje ckn ka gani". Yace, "kamar da gaske" "uhm.... Bari ka gani". Ta bude murfn mota ta fito tana fadin, "ameer ku fito mu je". Ya fito yana drya, ya budewa su ameera kofa suka fito, ya kamo hannaynsu ya dubeta, "to muje ko?". Tace, "muje mana". Yana murmushi yana fadin, "ha! Ha!! Yarnya yau zanga ynda zaki yi a gaban surika". Ta yamutsa fuska tace, "kasan Allah zan koma". "to shikenan!" "wlh baki isa ba, idan na rika kururuwa ina ihu, duk sai na tara miki jama'ar unguwar nan". Ta bishi da kallo yana mata drya, ita kuma tana wani irin murmushi mai sace zcya. A zahiri ya ganota kunya take ji, shi yasa take 'yan kame- kame. Kawai fitowar mami suka gani, "oyoyo sakeenar mu!". Nan da nan ta daburce, kasa zata shige ko sama? Da sauri ta durkusa, "sannu mami!" ta mika hannaynta ta dago ta, "taso, taso muje". Ta rungumeta jiknta, "yan yarori sannunku da zuwa". Ta fadi tana kallnsu ameer. "shigo dasu mana". Ta wuce rike da mama, ya bisu da kallo kamar ya zubda kwalla sbd murna da farin cikn da ya lullube shi. Ya sauke numfashi, ya ja hannunsu ameera ya bi bayansu mami. Har dakn barci ta shige da mama, ta nuna mata kujera, "zauna nan!". Ta zauna kai a sunkuye, ya shigo da yaran, yaynda mami ke fadin, "ki saki jiknki sakeena, nan gdnku ne, kuma ni bana surukar, 'yata ce ke. Kinji?". Ta kara rufe fuska da mayafi tana dan murmushi, ta silalo ta kwashi gaisuwa, mami na amsawa baknta kamar gonar auduga. Yaran ma suka gaisheta, ta tambayi sunaynsu, kowannensu ya gaya mata. Kusa da mama al'ameen ya zauna baknsa har kunne, "mami ya kika ganmu? Munyi matchn ko?" tace, "ai kana zama kawai naji na kosa ta shigo gidan nan, yanda kasan in boyeta". Yace, "kinsan ynda za'a yi? Mu kulleta a wani daki, muce bamu ganta ba". Dariyar mama ta karu, ta kara sunke kai tana jan mayafi. Mami tace, "idan ma muka yi hakuri dan lokaci kankani ne, Ubangiji dai ya bamu aron rai da lfya. Kuma Allah yayi muku albarka, na gode kwarai da gaske sakeena. Duk mai son tilon dana gaskiya nima bani da kamar sa. Sbd haka ku rike amanar junanku, kinji sakeena?". Ta amsa da kai. Yace, "ina su Iya? Basu san amaryata ta iso bane?" tace, "suna kicin tun safe suke shirya mata abncin tarba". Ya mike, "bari in kirasu, ai ko ladi bata zo ba ya kamata Iya tazo taga amaryar dan Iya.!" tace, "maza jeka". Ya fice. Mami na masa drya, wannan amarya ana ji da ita. 'Yar dattijuwar na zaune tana yankar ganyen latas, ya fado yana kira, "ina Iya ta ne?" tace, "gani nan dan Iya". Ya tsugunna baynta ya yada kansa a kafadar ta, a shagwabe yake magana, "baki san amaryar dan Iya ta iso bane?". Ta kara fadada fara'arta, ta aje wuka, "ina na sani? Ynzu tana nan ciki?" "tana dakin mami, taso muje. Iya yau mu 2 zaki goya". Tace, "ya zama dole". Ta yunkura ta tashi tana kiran Ladi, "maza kizo amarya ta iso!". Tayi gaba ya biyota suka shigo dakin, yayi azama ya koma kusa da mama. "ya kika ganmu?". Ta rangada guda, daidai ladi na kawo kai, "lallai iya harda guda?". Tace, "abnda yafi guda ma zanyi ladi, wannan amarya zubin larabawa? Gskya dan iya kayi sabe, Allah ya tabbatar da alkhairi". Gaba daya suka amsa, amin. Shi kuwa ji yake tamkar yau yake angwanci, bai san lokacin da ya kai hannu ya rungumo kafadarta ba yace, "Iya kenan, mai raino na". Da sauri ta zame ta sulale kasa ta makure. Mami tace, "hayaniyar ta isa haka, aje a kawo musu abin sha" Kafn kace kwabo tsakar dakin mami ya cika da kayn lashe- lashe da jus kala-kala. Al'ameen ya zuzzuba musu, ya mikawa yaran. Sannan ya juya kan gimbiyar ya miko mata, taki karba. "nifa ban son kauynci, kinsan Allah zan miki dure!". Mami tace, "wai tsaya, bakuwarka ce ko tawa?" yace, "taki ce maminmu". Tace, "to tashi ka bamu wuri. Don me zaka dameta? Duk ka kanainaye min ita, maza tashi ka tafi harkoknka". Ya marairaice, "baki tausayina mami? Daga yau fa bazan sake ganinta ba sai karshn watan da zamu shiga, sannan ba waya ba komai? Pls mami ki barni in zauna". Ta tafa hannu, "ya Rasulu, ni indo! To bari in tashi, watakila ni take jin kunya". Ta yunkura zata tashi, "don Allah kar ki daka ta tashi, ki dauki komai ki ci, ki sha lemu kinji? Sai kinci kin koshi a gidan nan zan tabbatar kina son dan Aminu na". Ta fice, al'ameen din yana drya. Ya kara matsowa, "kinji abnda tace ko? Nima yau zan gani, kina sona ko a'a". Ya jawo tiran soyayyen naman kaji, meat pie, donat, lafiyayyen cincin da samosa, yace, "to Bismillah, iya cinki iya son da kike min". Ta dubeshi tace, "wannan wayau ne, a wane ckn zan zura tulin kayan nan?" yace, "oho! Ni dai na kare magana, kuma kina jin abnda mami tace". Tayi shiru tana kalln tire, kafn ta dubeshi, "don Allah ka tayani ci". Yayi 'yar drya, ya dauki samosa ya kakkara wa yaran. Ya sake daukar daya ya kai baknsa, "mu tayaki, kema fara ci". Duk kunya ta isheta, da kyar tasa hannu ta dauki meat pie, ta juya gefe ta gutsira. Ya zura mata ido jim! Sannan ya dauki kofin lemun ya miko mata, "sha in kara ganin ynda kike so na". Ta karba ta dan kurba. Ya jawo ameera jiknsa ya rungume, "kinga ynda antinki ke so na?". Oho! Ina ruwan ameera, me ma ta sani banda drya, tana amsawa da kai. Sai ga ladi dauke da wani tiren ta aje wani dan matsaikaicn kek da duminsa. Yace, "a gaida ladi". Tace, "likita irin wannan zaman da kake yi kyanshi a buga muku hoto". Yace, "ko ladi?" "gaskiya". Ya fice suna masa drya, jimawa kadan ya dawo da 'yar karamar kyamara a hannunsa. "ai kema zaki iya daukar mu ladi, ba wuya. Duba nan ki gani, saman nan kawai zaki latsa". Yana saitawa ya fara bada misali, sai dai kawai mama taji wal! Haske ya wuce. "ai kin gane ko ladi?" "na gane likita". Ya mika mata. Mama kuwa sai kalln ikn Allah take yi, ya dawo gefnta ya zauna, ya taro su ameera, ladi tayi ta yi musu hotuna. Wasu tare da yaran, wasu su kadai. Ladin ya tura ta kira mami, itama ta zauna suka yi hotunan tare, fadi take, "wannan shagali yayi kyau". Mama kuma bata sake ba sai da al'ameen ya tafi sallah. Sunci sun sha, sun bar gara birjik! Kamar ma basu taba ba. Kafn ya dawo ta gama shirin tafya. Ga ledoji tuli, kayayyakin da mami ta bata. "ban gane ba?" Ya tambaya, har da kama kugu hannu 2. Tace, "gida mana". Ya langabe kai, "gaskya ba haka ake yi ba, ba haka ake yi ba sakeena. Ai dai sai la'asar ya kamata ko?'. Tuni take ta drya zancnsa, kafn tace, 'ka manta yaya na jirana ne?'. Ya runtse ido tamau! "oh my God!". Ya bude ya kara matsota, ya zura mata ido, "kamar ki ta zama a gidn nan sakeena, bana so ki tafi". Ta sauke numfashi, "kayi hakuri". Yace, "yaya zanyi sakeena? Ya zama dole, amma ki bari zuwa karfe 3 sai mu tafi" "Allah yaya zai yi fada, kana
Chapter 12 · 0% Book details