← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 78

Sashe 78

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Rasuwar d'an,ladi ta dawo ne daga sokoto taji kuma labarin abinda ya faru da hajjo dan allah na yafe mata abubuwan data min tasan bata kyauta min ba
Ita ma zata d'aura aure watan gobe

Allah yasanya alkhairi namata nace na yafe mata allah ya yafe mana baki d'aya nan na fad'a mata muma zamu bar garinne zuwa gobe insha allah

Nan ta mana fatan sauka lafiya ta tafi tana mai min godiya akan yafema tan dana yi duniya kenan kamar bata so auren mijina ba

Gashi har ya rage gobe zamu bar gari amma har zuwa Lokacin ba asan yadda za ai da hajjo ba baba dai yace babu ruwan shi da ita tunda babu komai tsakaninsu

Yaranta kam sun shiga damuwa dan basu san yadda zasuyi da ita ba
Sani
Da shamsi
Da salaha da umar su sunce dai baba zasu bi abinsu bashir ne bawan allah yace shi bazai iya tafiya yabar mahaifiyar shiba kowa baya iya zuwa kusa da ita saboda k'azantar wajen ga kuma duka data ke kaiwa sai bashir kawai ke iya mik'a mata abinci inya fuskanci tayi barci ya lallaba ya tattara d'akin

Gari duka ya d'auka hajjo ta hauka ce

Kamar yadda muka tsara da asuba motar mu tazo har k'ofar gida dan shata mukai babu yadda muka iya haka muka bar bashir da hajjo dan babuwanda ya matsa masa akan sai ya biyo mu
Tunda mahaifiyar sa ce salaha na kuka haka motar mu ta tashi
Zuwa kano

Bashir bawan allah lokacin da motar ta tashi cikin sanyin jiki ya koma gida bashi da yadda zaiyi shine dolen ta duk da bashi kad'ai ta haifa ba amma shine kad'ai ke tausaya mata mahaifiya tafi k'arfin wasa

*********************"""

Bamu sauka kano ba sai shida na yamma a gidan baba abdullahi muka sauka dukanmu daga baya babanmu ya wuce gida ya bar mu nan

Bayan dawowar mu ne kuma ahmad ya shiga nema mana gida ya siya mana dan batun aikinshi mai sauk'i ne tunda dama ba acan niger state d'in yake yiba sai ankira shi ba matsala bace wannan

Satin mu biyu ya siya mana gida d'an k'arami dakuna biyu ne sai

Kitchen da tolet a a waje suke duka

Nan muka koma na d'auki salaha dan ina ganin intana kusa dani zata fi sakewa
Saboda tarin damuwar data sawa kanta

Baba musa kam a gidan baba abdullahi aka ware masa d'akinshi daban su shamsi ma haka tare suke kwana da su salim

A fad'insu in ankwana biyu zasuje niger su saida kadarorinsu su zo baba musa yakama sana,ar shi anan

Yasai gida shima

***********************""*

*Niger state lapai*

Kamar yadda ya saba tunda su baba suka tafi baya iya tsayawa wajen sana,ar shi ya dad'e yana k'ok'arin dawowa gida lokaci zuwa lokaci saboda ya duba jikin hajjo ya bata abinci

Yauma haka ce ta kasance ana idar da sallar azahar ya nufo gida ya bud'e d'akin da hajjon ke ciki cikin sand'a ya nufi inda yake aje mata abincinta

Ya tsugunna kenan hajjo da ke gefe ta zaburo ta shak'emai wuya iya k'arfinta duk yadda yaso ya k'wace daga rik'on ya kasa ita kam sai zare ido take tak'i sakin shi gashi mutanen gida kowa na 'bangaren saida ya galabaita ta war'bar dashi

Ta bude k'ofar ta fito da gudu sam bazaka ta'ba gane taba inhar ba kamata farin sani ba duk tafita a kammaninta kamar wata dodo ta rame ta fige ta fice a hayyacinta kayan jikinta duk sun yayyage idanun nan a warwaje

Maman aisha da fitowar ta kenan d'aki ta ci karo da hajjo da sauri ta koma d'aki ta rufe

Itakam bama tasan tana yi ba hanyar waje ta nufa abinta kawai kowa yaci karo da ita saidai ya bata hanya babu wanda yayi yunk'urin tare ta

Bashir da k'yar ya yi yunk'uri ya tashi ya fito da gudu yabi bayanta sai dai harta yi nisa duk yadda yaso ya kamota ya gaza gashi bashi da mataimaki

Ita kam gudun ta take iya k'arfinta gadan,gadan ta nufi titi dai dai lokacin wata babbar mota ta taho babu zato ta shigi motar nan duk yadda direban yaso rik'e birki abin ya gagara saida motar ta bi ta kanta

dai dai lokacin bashir ya k'araso wanjen
Hannu bashir ya d'ora aka ganin yadda motar ta markad'e hajjo rugu rugu ko shurawa batayi ba

Me motar koda ya fito mutane sun cika wajen ganin dai tabbacin mahaukaciya ce daga yanayin kayan jikinta duk da kwa yadda motar ta murjeta ko ance a d'auketa dole bazata d'auku duka ba kasancewar wasu sassan jikin nata duk sun fita a muhallinsu kannan ya dagargaje hakan yasa kowa ya fara watsewa bashir ne kawai

Ya iya k'arasawa ya tsugunna yana rusa kuka kamar mace me motar hak'uri kawai ya bashi ganin babu wanda yayi yunk'urin dakatar dashi yasa ya yi sauri ya tashi motar shi ya bar wajen

Bashir baima san yana yi ba dan mutuwar hajjo ta girgiza shi da k'yar yasamu wasu bayin allah suka taimaka mai aka kwashe ta wasu sassan jikin nata ma saida shebir aka kashe ko wanka ba asamu damar yi mata ba andai yayyafa mata ruwa aka sallace ta aka mik'ata gidanta na gaskiya sai fatan aje a tarda abin da aka shuka

Duniya kenan budurwa wawa hajjo an tafi d'an,ladi d'a mafi soyuwa gareta shima ya tafi kamar ba ayisu ba allah yasa muyi kyakykyawan k'arshe amen y allah

***********************

Bashir ya kiramu ya sanar mana da labarin rasuwar hajjo kowa allah yajikanta yace nan yake sanar mana in yagama amsar gaisuwa zai taho shima

Su salaha kam sun sha kuka ba kad'an ba koba komai hajjo mahaifiyar su ce sun mata addu,ar allah ya yafe mata zunubanta dan mutuwar ta ta k'ara dasawa kowa tsoron allah da kuma tsoron duniya ka shuka alkhairi sai ya bika har bayan ranka haka sharri inhar shi ka shuka za ana fad'ar shi koda baka raye allah kabamu ikon shuka alkhairi

Kamar yadda bashir yace sati d'aya da rasuwar hajjo yayi sallama da kowa ya baro garin Niger state allah sarki rayuwa

Watan mu guda da dawowa su baba suka shirya suka tafi niger harda ahmad da su bashir dan suma suga danginsu alhamdulillah sunje kuma sun ga juna nan su baba suka fad'awa inna asabe da malam liman cewa zasu saida kadarorinsu su koma nigeria tunda nan suke da zama

Sun basu goyon baya nan suka tattara komai suka saida suka dawo nigeria akan zasuna k'ok'arin zuwa dubo inna asabe da malam liman inna asabe kam tana nan daram abinta lafiya ta samu ta shiryu bazaka ta'ba cewa ita ceba

***********************

Dawowar su baba da sati biyu baba musa shima ya sayi gidanshi d'an madai,daici d'akuna hud'u ya bawa su bashir biyu

Biyun kuma su babanmu suka had'ashi da wata bazawara wadda mijinta ya mutu yayanta kuma duk ta aurar da su hakan yasa ya aureta bayan auran ta tare a dakunan biyu duk da cewa yaran suna da hankalinsu dan ko umar auta yanzu shekarar sa goma sha biyar amma ta rik'esu amana duk da cewa bama gidan suke wuni ba

Bashir sana,ar shi ta d'inki ya koma sai ya d'auki umar suke yi tare

Sani kuma da shamsi sai baba musa ya bude musu shagon saida kayan masarufi alhamdulillah allah sai yasawa abin albarka

Salaha kam nawajena har lokacin dan duk da baba yayi aure amma nace bazata koma gidanba nan zata cigaba da zama har allah ya fito mata da miji tayi auranta

Auran yaya yusuf ne yazo gadan gadan muka shiga biki inda shima zuwa lokacin ya gina gidanshi madai daici a unguwar yar,aduwa kwatas a wajen bikinne kuma allah ya had'a salaha da wani abokin yaya yusuf mai suna Muhammad nan da nan soyayya ta shiga tsakanin su daya ke da niyar auran yazo sai gashi ya turo magabatan shi

Nan babanmu yace tunda haka ne dama mai son bahijja ya dame shi da zai turo sai ya masa magana ya turo a had'a bikin haka kwa akayi nan aka yanke watanni hud'u masu zuwa rai da lafiya

Su salima kam sun shiga damuwa tare da mahaifiyar su ganin kowa na aure harda k'annen bayansu amma su shiru kakeji badan suna bak'in ciki da auran k'annen nasu ba sai don kowacce mace burinta tayi aure ta ganta gidan mijinta haka suma iyayan burinsu su aurar da yayansu su kaisu gidan mazajen su

Ahmad kam alhamdulillah kwangila tana fito mai daban daban sai ya zama dawowar mu kano kamar wani mabud'in k'ofar samun arzik'insa ne

Kamar wasa shima ya bud'e shagon saida zannuwa sai gashi allah yasawa abin albarka fiye da zaton kowa cikin wata biyu yasa mu wani gida angama gina shi gyare gyare kawai ya rage nan ya sai mana ya shiga gyare gyare

Bikin su bahijja ya rage sati d'aya muka koma sabon gidan mu
Kowa yaga gidan alhamdullah sai son barka dan duk da bawani k'aton gida bane amma ba laifi dan za a iya sashi a layin gidajen masu kud'i

Inda lokacin bikin nayi busy nice nan nice can dan nice kamar uwar salaha duk da kwa gidanmu aka kai taron saboda gudun wahalarwa

Anyi biki lafiya ankai amare gidajen su sai fatan allah yabasu zaman lafiya

*************************

*_BAYAN SHEKARA BIYU_*

Zuwa lokacin abubuwa dayawa sun faru masu dad'i da akasin su ciki harda rashin inna asabe da mukai mutuwar data bigi kowa munje harcan munyi gaisuwa anan ne kuma allah ya had'a salima da wani bazawari yana da mata d'aya da y'ay'a hud'u koda ya nuna yana sonta bata wani musa ba ta amince duk da kuwa yace anan niger zasu zauna

Muna dawowa itama hajara allah ya fito mata da wani sai dai ita bata da kishiya dan irin mazan nan ne da suka dad'e basu yi aure ba

Haka kam aka had'a bikin akayi shi kowacce ta tare a gidanta munkai salima can niger sai fatan zaman lafiya

Lokacin ahmad ya zama babban dilar atamfofi da shaddodi da lesuka arziki dai yana ta shigomana sai dai muce alhamdulillah zuwa lokacin ya mallaki motocin hawa nashi har biyu nima ya saimin d'aya duk da bawai fiya fita nayi da ita ba sai in zan d'akko kalim da walid daga makaranta ko zanje gidanmu ko gidan inna
Lokacin ina da wani cikin wata biyar
Nikam rayuwa sai dai nace alhamdulillah ina cikin godiyar allah a kullum rayuwa ta dai,dai ta komai ya shud'e kamar bai faruba

_*TO NIMA ANAN ZAN CE ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALLAH NA GODE MAKA DA KABANI IKON KAMMALA WANNAN LABARIN LAFIYA KURARAKURAN DA NA AIKATA ACIKI YA ALLAH KA YAFEMIN ABUBUWA DA SUKA AMFANI AL,UMMA UBANGIJI KABANI LADAN HAKAN SAI KUMA MUN HAD'U A SABON LITTAFI NA NAN GABA INSHA ALLAH*_

_MASOYA INA MUKU FATAN ALKHAIRI DA IRIN K'ARFIN GWIWAR DA KUKA BANI NAGODE NAGODE ALLAH YA BAR K'AUNA😍🥰_

_*😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE😍*_✍️
Chapter 78 · 0% Book details