← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 78

Sashe 49

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*********************
Yanzu ahmad dan munafurci shine kaje
Ka zagaye kabawa fati
Kudi tayo siyayya har haka
Saika ce hauka ni dana ke mahaifiyar ka bani da
Matsayin da zaka bani
Ne ko kuwa kana tunanin
Bansan abubuwan da ake
Siyowar bane dai dai
Talaka amma kun tashi
Kun dingimo abin
Daya fi karfinku
Shegiya ita fatin
Nasan duk ita ta tsara ka
Akan hakan wato yadda
Ta mallake mijinta
Take juya shi sai
Abin data ce haka.
Ta zo ta tsaraka kai
Kuma ka danka mata
Kud'i ko ni baka bani ba
Saboda ita tafini ko

Ahmad da ke zaune kan
Tabarma daga bakin
Kofa ya dago
Ba haka bane hajjo

To yaya ne uban tsari da tsare tsare wallahi
Kadaiji kunya kowanne
'Da na kishin mahaifiyar sa amma kai sam baka
Damu dani ba

Kiyi hakuri hajjo

To yazan yi dama inbanyi
Hakuri ba yanzu dai
Abin da zan fadama tunda
Ta haihu dole abincin ku
Ya dawo nan kasan da
Wannan dan haka
Ka kwaso kayan abincin dakin naku sai adinga
Hadawa da na nan ana
Dafawa sai ana dibar
Muku dan kasan dai
Ba wani iya girki zatai
Ba

Sannan maganar kudin
Iccen da za ana dafa
Ruwan zafin wankan
Jegon shima zaka bada asiya da yawa a ajiye

Hajjo zan dai bada ki karo kayan abincin
Amma na dakin mu
Abarshi sannan nawa ne
Zai isa asiyi iccen?

Too kayan abincin dakin
Naku ne baza a ta'ba ba
Ko yaya ina ce dai girkawa za ai ko ?

Adai bar wannan hajjo
Ga wannan ku karo
Ya irgo kudin ya ajiye
Mata ta kalleshi ganin
Kud'in da dan dama
Yasa bakinta yin
Shiru

Sauran na iccen shi
Ka kawo dubu biyar

Nan ya lissafo ya ajiye mata

Nan dai ya tashi ya tafi

Koda yazo da daddare kwanciya dan lokacin naga daga wajen
Hajjo aka kawo min
Abincin dare saina
Dauka tunda
Yau na haihu shiyasa
Ta kawo min

Shine yake sanar dani
Girkina zai koma wajen
Hajjo intayi zatana bani
Saboda jego
Banso hakanba
Amma dan karna cika
Korafi sai na bishi
Da to kawai

*************************

Tunda na haihu yau kwana
Uku kenan da safe yawo jummai zatawa yaron
Wanka nima tamin
Dan hajjo
Tace ita ta barwa yawo
Jummai ta dinga yimin
Nima kuma nafi son
Ita din tamin
.
Sai dai wata al,ada da hajjon
Ta tsiro daga gari ya waye zata shirya ta fita
Unguwa bazata dawo ba
Wani lokacin sai
Karfe biyun rana
Tukun ta dora girki ga jego bata gama wa sai bayan la,asar adan zuboshi bashi ba yadda
Yake dole da dare
Saina hada shayi na
Sha
ina yin baki yan
Barka haka suke zama
Su tashi babu abincin
Basu

Dan ma ni
Aunty fati
Kullum in zata zo zata
Riko abinci ta kawo
Min ta tambayi ahmad
Kud'in kayan da zata siyomin yabata

Ta saimin less da atamfa biyu duk ta bada d'inki harda takalmi
Da gyale harda jaka
Yaron ma ta kara siyomai.wasu kayan

Ahaka dai muke tafe har ya kasance jibi suna

Da safe aunty ummi ta
Kirani suna tafe ita da
Aunty sameera matar kawuna cikin farin
Ciki na bisu da addu,ar
Sauka lafiya

Ikon alllah saiga kiran
Yaya yusuf shima
Suna tafe dashi
Da baba abdullahi da su salem

da ahmad ya shigo na fada masa sai yace eh baba abdullahin
Ya kira ya fada masa nace to wanne abinci za a musu
Yace hajjo tace zata yi nidai bance komai ba
Haka kaza lika bangareb hidimar sunan na abinci
Bai cemin ga yadda za ai
Ba nima kuma daya ke.
Ba sanin yadda ake nayi
Ba ban tambaye shi ba

Sai aunty fati ce ke tambaya ta yaya za ai
Da abincin suna
Nace bansaniba tace
Inmasa maganar
Koda ya shigo na masa
Maganar cayayi duk ya
Sallami hajjo da komai
Ta amsa na abincin
Banwani damu ba tunda
Abincin suna ne dai
Dole ta fito
dashi ayi

K'arfe 5pm su aunty ummi suka sauka
Ahmad shine yaje tasha ya tarbosu dan basu taba zuwa ba

Nayi farin ciki sosai da ganin y'an uwana ganin
Tunda nazo babu wani nawa da nakara gani
Sosai aunty ummi
Suka shiga mamaki
Ganin irin gidan dana ke
Zaune ga shi daki d'aya tall aunty sameera ce da bakinta baya shiru
Suna shigowa
Ta ce wai aminatu ban
Gane ba kina nufin nan
Ne dakinki ko
Kuma dai d'akin surukarki ne dai

Na kalleta nasan halinta
Tsaf aunty sameera bakinta ba dai surutu ba
Da neman aibun wani
Aunty ummi ce ma
Ta danne nata mamakin
Tace tunda kika ga nan
Aka sauke mu ai alama
Kenan

Dama mama ta fada tunda taga sun dage .
Babu wanda zai biyo
Yarinyar nan lokacin
Auren akwai abin da suka.shirya cab allah ya
Kyauta dai amma gaskiya ina auren zumunci bai yiba

Nidai ina jinsu suna
Kana nan maganganun su saina yi tsit dan ni
Banga me zance ba
Koma ina nake zaune
Nidai tunda ina
Zaune da mijina lafiya ai
Nagode wa allah
Maganar daki daya bata
Dame ni ba tunda nasan.
Ba anan zamu dauwama ba kayan daki kam
Da suke kushewa shima
Bai dameni ba
Nasan komai lokacine
Tunda ahmad ya min alkawarin insha allah
Zuwa nan gaba in
Komai ya dai,dai ta
Zai canza min

Nan dai da suka ga
Bance komai ba sai
Suka tambayeni
Ina surukar tawa tunda nace gida daya muke
Nace tana can bangarenta ba ajima ba
Kam sai gata yar halak
Tazo abun mamaki ta sakar musu fuska sun
Gaisa cikin mutumci
Bazaka taba cewa ita ce ba hajjo kenan

Nan ta gabatar musu da abinci bayan tafiyarta ina
Jinsu suna ya bonta .
Bance musu komai
Ba saboda ni aganina
Baida ce ba da zan yada sirrin dake tsakanina
Da hajjo ba tun yanzu ganina ke yayi wuri ace
Har na fara samun matsala kuma in na
Fada musu yadda suke kushe gidan da komai
Ma laifin ahmad zasu gani banajin aunty ummi
Sosai kamar aunty sameera dan ina tabbacin
Tasamu abin fadi kenan in sun koma zata ce ina cikin halin rayuwa abun
Da bana fata kenan dan alhamdulillah

Sai shida na yamma su baba abdullahi suka sauka su wajen su hajjo
Aka sauke su bayan
Sun dan huta ne naje na gaishe su
Tukun daga baya baba abdullahin dasu salim
Suka zo har daki lokacin su aunty ummi suna kofar daki zazzaune wai su zafin garin namu suke ji

Nayi murna da ganin su sosai yaya yusuf ya kara zama babban saurayi masha allah
Nan suka miko min
Wasu ledoji guda biyu
Dayar yaya yusuf yace sakon babane da nashi
Dayar kuma daga mama aysha matar baba abdullahi
Na amsa nayi godiya

Na tambayi mama rukayya suka ce tana gaisheni dama bansa rai da komai daga gareta ba
Matar da bata damu da
Mu gaisaba me zai sa
Ta damu da sha anina koda ina gidama dai hakane ranar dana haihu
Dai ta amshi waya wajen
Baba ta min barka daga nan shikenan

Nan muka shiga firar yaushe gamo anan yusuf ke sanar dani ai baba abdullahi ya bude musu
Shago su uku da shi da muhammad da salim
Suna saida atamfofi da shaddodi da lesuka
A sabuwar kasuwa nan na bisu da addu ar sa albarka tare da budi

Sallar magriba ita ta
Katse mana firar
Inda da zasu tashi yaya
Muhammad dubu biyar ya aje min duk da ina a a salim ma dai dubu uku .yabani yana tsokanata shi talaka
Ne shi aikinsa kawai a shagon aike da shara
Dariya yabani sosai dan salim bazai taba canza halinsa na tsokana ba

Baba abdullahi ke cemin
Anjima yana son magana dani

Tafiyar su sallah shi ya shigo dasu aunty ummi
Bayan sunyi sallah
Suma suka kunce kayan
Da suka zo da su .
Nan suka shiga lissafamin
Wadanda suka basu sako
Su kawomin
Yan uwan maman mu.
Inna kakarmu ma tamin dinki kala daya da atamfa turmi sai kayan yaro kala uku gwaggo binta ma dai turmin zani ta bada dana yaro kala daya da kayan gyara
Nan dai suka lissafin duka
Alhamdulillah nasamu kaya sosai daga dangin mamarmu nayi godiya

Nan na fito da kayan da
Ahmad yamin dan da safe aunty fati ta amso
Min a wajen dinki
Na nuna musu ba laifi .sun yaba
Na bude ledoji da su .
Baba abdullahi suka
Kawo ta yaya yusuf
Shadda ce aciki ruwan hantaA dinke dinkin doguwar riga daya ji aiki daga sama har kasa da turmin
Atamfa a zuciyata nace allah sarki dan uwa mai
Dadi sai dayar ita kuma kayan jinjirin ce
Da yajin daddawa dayawa a wani dan botiki
Sai wata leda dana buda ita ma kayan gyara ne dai cki

Nan su aunty ummi suka sa albarka sai aka hade kayan gaba daya
Waje guda aunty sameera ta kira hajjo
Tazo tagani
Lokacin data zo taga kayan
Tayi kokari sosai .
Wajen danne bakin
Cikin ta dan sai daddagawa take tana
Yake fuskarta kawai
Nake kallo
Haka dai tace angode allah saka da alkhairi

Bayan tafiyar tane baba abdullahi ya kirani
Nan yake bani hakuri
Yace lokacin da suka zo
Abinda ya hanadu canja min kayan saboda kar ace sun raina ne
Amma tunda jibi suna
Gobe insha allah
Zai nemi wadanda zasu rakasu inda ake saida kayan daki zai canja min
Naji dadi sosai nan namasa godiya muka yi sallama dan kofar daki
Ya kirani

Na sanar dasu aunty ummi inda nan da nan naga sun nuna farin cikinsu sai kuma suka koma yabon baba abdullahin

**********************

Washe gari aunty sameera daya ke ta iya
Kitso da kunshi ita tamin duka inda zuwa karfe sha biyu tuni mun kammala

Sun tambayeni ya ya
Za ai da abincin sunan
Nace komai na wajen
Hajjo tunda mu bamu dayawa nan suka ce eh hakane tunda jama ar da za atara ma ai duk dan ita zasu zo

Karfe dayan rana aka shigo da kayan dakin
Da suka siyomin
Hajjo na kofar dakin
Ta sai gani tayi ana shigowa da kayan
Daki ana yowa lunguna
Dasu
Cikn tsananin mamaki
Ta tashi tayo hanyar dakin nawa dan bata da masaniya akan komai
Baba abdullahi baba musa kawai ya fadawa
Chapter 49 · 0% Book details