← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 78

Sashe 24

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fara bani magungunan sanyi masu inganci tukun muka shiga gyaran fata da hade hade masu kyau marasa illata fata irinsu lalle turarruka da su ganyen magarya dasu kurku da dai sauran su sai sabulai masu kyau data bani nake wanka dasu inda ruwan wankan ma kafin nashiga saita mai hadi na musamman

Saida na gama shanye maganin sanyi har na tsahon sati tukun tafara bani magungunan dasu dahuwar kaza dasu gumba haka dai take ta dirkamin su tana mitar bata saniba da wuri lokaci ya kure yanzu

Nan danan jikana ya fara amsar gyaran fata ta takasance ruwan tarwada ce sai gashi ta kara haske da kyalli sai wani sihirtaccen kamshi na musamman danake fitarwa nida kaina nasan na canza

Biki ya rage sati daya ranar asabar su inna da gwagwgwo binta suka shirya an aiko bahijja wai ankawo kayan lefe su zo susa albarka inda inda inna ta aikawa gwagwgo binta akan tazo da yamma suje da yamma suka shirya suka wuce

Bayan sun dawo gwagwgwo binta sai banbamin fada take tana kara fadar abin data gani

Nan naji tanacewa inna yanzu fisabilillah lefe kenan saikace bazawara aiko bazawara nakega a darajata ba asamata atamfar roba a cikin lefe ba kuma dudu du kayan fa kala takwas ne amfofin masu dan damar hudune fa,kawai sai shadda itama su rasa wadda zasu sa sai bts sai dan iskan less dinnan wanda koni da tsufana naje kasuwa bana daukarshi na zamani zan zaba fisabilillah ina ake haka kai wannan yarinya nafeesa bata da kirki dan kawai andanka miki komai saiki yi yadda kikeso amma ba komai itama ta haifa ai ga yammatan nan gabanta maji magani duk abin dakawa dan wani za aiwa naka

Inna ta kalleta haba binta dadina dake rashin hakuri badai sun kawo ba mu mene namu fatanmu dai allah yasa ya riketa amana yabasu zaman lafiya nawa akawa lefen na kece raini auren baya zuwa ko,ina yake lalacewa

Mu mata fatan allah yasa intashiga ya kyautata mata tunda yanzuma ba laifinsa bane

Nan dai suka cigaba da tattaunawa maganar ina jinsu araina nace hmm indai aunty nafeesa ce dama ni tunda yace zai bata kudin komai nasan bawani abun arziki zata minba amma banyi tunanin yadda sukace ba

Can na watsar da tunanin ni banida lokacin wannan fargabata rabuwata da iyayena da yan uwana da kuma irin rayuwar da zanje na tarar

Inajin inna na fadawa gwagwgo binta ita zata min kayan fitar biki dan duk cikin kayan akwatin bata ga na kirkiba inda suka shiga tsara yadda zasuyi abin

*************************

Biki ya rage kwana uku su inna da sauran dangin mahaifiyata inna tasa duk suka hada gudummawar su aka hada aka saimin kayan kitchen dasu labulaye da zannuwan gado inda suka yanke shawarar zasu bawa baba sauran kudin shima yakara yayi hidima

Sun kai kayan gidanmu kamar yadda suka tsara tare da bawa babanmu kudin inda ya musu godiya sosai tare da addu,o,i dan sunyi kokari ba kadan ba

Kuma aranar ne yaje ya samu baba abdullahi duk da har zuwa lokacin bawani shiri sukeba dalilin aurennema yasa suka dan fara magana tunda duk wasu kudi da ake bukata daga bangaren su ahmad baba abdullahin ake turowa sai dai har zuwa lokacin baicewa mahaifina ga kwandala ba

Baba yaje ya masa bayani akan hidimar da su inna sukai inda baba abdullahin ya ce angode musu anan baba ke tuntubar shi akan maganar kayan daki tsarin daya kamata ayi duk da bawai da kudin aurena dake wajen baba abdullahin ya dogara ba danshi ya tanadi kudin kayan dakina tuni

Kawai dai yana tambayarshi anan za asiyane ko kuwa sai anje can saboda nisa

Nan baba abdullahi ya shiga cemai ai yaya musa ya kirashi yace basai ankaini da ko cokali ba dan shima mahaifinane ya riga dayamin komai

Anan baba yayi kokarin fahimtar dashi yadai kamata ace suma sunmin kodan ba asan can din dame dame sukayiba

Anan baba abdullahi ya rufe baba da fada wai ko yana tunanin zai cinye kudin auren ne shiba cizaiba kuma bada yawun sa ba za asaimin kayan daki danshi bazai bulawa yaya musa kasa a idoba yace sun raina mai ba

Nan baba yace to shikenan tunda kace haka dama ba kudin hannunka nace zan amsa ba dan aminatu yar kace duk yadda kayi dasu dai dai ne amma ni ga kudin danayi niyar saimata kayan dakin dama na dade ina tarasu

Inyaso tunda dakai za ai tafiyar inkukaje inkaga babu wani abun saika bada asiya mata

Haka baba abdullahi ya sa hannu ya amshe kudin wajen baba babu kunya kuma bai tada maganar kudaden auren ba bare kuma ayi batun gudummawarshi

Haka baba ya baro wajen shi ba cikin dadin raiba

Ranar alhamis da safe mukaje gidan lalle aka zana min lalle mai kyau nida siyama sai su ilham da suka mana rakiya suma nasa aka musu daga nan bayan angama muka biya shagon salon aka wanke min kai

Karfe hudu muka dawo lokacin gidanmu ya cika da dangin mamanmu sai su mama aysha banga mama zainabu ba bare ya,yanta

Inda aranar su gwagwgo binta suka sani a lalle inda suka feshini da turaruka masu kamshi mama rukayya dai nata kallo babu ruwanta da sabgarmu

Inda washe gari ranar juma a kenan karfe hudu da rabi na yamma aka gudanar da walima a makarantar islamiyyarmu inda aka gabatar da wa azizzika masu ratsa zukata nasamu kyaututtuka daga wajen malamanmu saboda kokarina awajen karatu

*********"**"""***********

*_RANA BATA KARYA......_*

Yaune ranar asabar 9/2/2014mutane suka shaida daurin auren _Aminatu Salisu_ tare da angonta _Ahmad musa_ akan sadaki dubu arba,in

Inda bayan andaura auren ne lokacin ina daki nida siyama da duk cikin kawayena ita kadaice ta kwana dani dan jiya nadawo gidan baba danni banida wasu gayyar kawaye barkatai sai su ilham agefena daketa kuka anfada musu yanzu za atafi dani

Na kamosu na rungumesu nima kukan nake a lokacinne kuma wata yar yayar inna mama fati tazo ta kama hannuna inda ta kaini dakin mama rukayyah inda cike yake da dangin mamanmu

Muna shiga gwagwgo binta ta jawo hannuna ta zaunar dani kusa da ita nan suka shiga yimin nasihohi masu ratsa jiki akan zaman aure da kuma hakuri da yadda zan zauna da kowa lafiya

Kuka kawai nake wai yau nice nayi aure zanbar gaban su baba kuma zan rabu da su ilham aurenma can uwa duniya ya allah ka agajeni ya allah ka iyamin kaine gatana

Ina cikin tunanin aka aiko wai motar daukar na ta iso inda ko sallama bamuyi da baba ba

A lokacinne kuma aunty nafeesa ta karaso dakin cikin masifa wai na shanya mutane kaza kaza akaina aka fara aure wani garinne

Inda mama fati ta dago ta kalleta dan taga alamar yarinyar bata da kunya inba haka ba yaza ai kizo waje duk manya kuma kinsan bawani abu akeba nasiha ake mata ki fara banbami

Tace kyadai bari akaita ga mahaifinta suyi sallama ko duk saurin da kuke

Sai ta kallesu tawani watsar tayi gaba

Nan mama fati ta kama hannuna ta kaini wajen babanmu dake dakin yaya yusuf inda baba shima dai nasihar yamin ya hada da bani hakuri
Anan yake fadamin tsarinsu na kayan daki yace nayi hakuri da duk abin dana tarda ya bawa baba abdullahi kudaden in akwai bukatar hakan inma babu sai asaimin wani abu mai muhimmanci tunda hakkinane daya kamata yasauke

Sannan ya ce zaibawa gwagwgo binta sauran kudin itama ta dudduba abin da babu tasaimin

Nan dai gwagwgo binta tazo ta ja hannuna muka nufi hanyar waje inda mota ke jiranmu

Sai siyama data riko akwati guda irin yar kamaramar nan

Mota biyu ce aka kawo daya yan daurin aurene da suka zo daga can sai kayana da za a zuba aciki daya ce aka bamu ta amarya da wadanda zasu mata rakiya

Munkaraso bakin motar gwaggwgo binta rike da hannuna sai muka tarda motar su hajara da salima da aunty nafeesa da yaranta duka hudu sun yi kane kane a motar sai baba abdullahi da direba dake gaba dama mukadai ake jira

gwagwgo binta ce ta leka kanta tace ina motar da za asa amaryar aunty nafeesa tayi caraf wajen cewa wannan ce ai motar

Gwagwgo binta tace to in ita tashiga mu ina zamu zauna

Sai lokacin baba abdullahi yayi magana ba sai kunje bama ai tunda ga yan uwanta nan su nafee sannan gasu hajara ai ya wadatar

Gwagwgo binta ta kalleshi tace taya zai yihu ace ankaita babu dangin mamarta ko guda ai koni da kawarta ai abari muje

A a kam ba haka muka yi tsarinba suma su hajarar dan zasuje suga dangine dan basu taba zuwa ba shiyasa amma gaskiya kiyi hakuri aiduk nan dinma danginta ne

Gwagwgo binta ta kalleshi cikin mamaki wane irin kai amarya kenan babu dangin uwar amarya sannan gari ba kusa ba ina haka zata yihu

Nan tashiga banbamin fada dama tana ciki da su akan duk maganar aure dan baba yamata bayanin komai akan kayan daki har kudin daya ba abdullahi inda tayi niyar inhar sukaje sukaga kayan basuyi ba dole tamai magana ya kawo kudin hannunsa acanjamin dan bazasu barsa yaci bulus ba sai gashi ana neman hanata zuwa tome suke nufi kenan

Nan suka shiga cacar baki duk wannan abun da suke ni kuka kawai nake risga musamman danaji ance babu wanda zai bini a dangin mamanmu bare ayi batun siyama ta bini

Haka dai karshe gwagwgo binta tayi zuciya ta aika siyama ta kira mahaifina akan tafiyar inda wasu daga cikin dangin mama ma suka fito babu yadda baba baiyiba akan subari a tafi da gwagwgo binta amma baba abdullahi ya yi mursisi ya hana

Da gwagwgo binta taga sun dage ta dunkule kudin da mahaifina yabata da sunan itama ta duba abin daya dace ta saimin ta dankawa aunty nafeesa tace gashinan inkunje inkin duba allah kinji tsoron shi kin kyautatawa marainiyar allah to inkin ga abin da babu asaimata fatan mu mudai allah yabasu zaman lafiya ta kare tana mai bata kudin
Chapter 24 · 0% Book details