← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 78

Sashe 57

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na tsugunna wajen inhar
Yarona ya mutu dan allah kifad`amin na yarda da k`addara nasan dama allah shike rayawa kuma shike kashewa aduk sanda yaso zan rungumi k`addara pls kifad`amin

Na had`e hannuwa na waje guda alamar rok`onta

Kallona likitar tashiga yi cikin tsananin tausayi ta dafa kafad`ata yaronki bai mutuba aminatu suma yayi taso muje

Nan natashi na bisu muka shiga office din tare ta nuna mana wajen zama

Ta kalli ahmad da duk mun baza kunne muna jiran jin mezata ce

Gaskiya bansan ta ina zan fara ba amma hak`ik`a rayuwar yaronku tana cikin had`ari
Yaya akai kuka yi sake har aka cutar da k`aramin yaro haka?

Munyi scaining mun gano k`usa ce aka saka masa a mak`ogwaronsa irin k`ananun k`usarnan da farko nayi zaton iya nan ne sai nayi tunanin kunbarshi yana wasa ne har ya had`iya

Dukanmu zabura mukai nida ahmad har muna had`a baki wajen tambayar ta k`usa kuma
Meya kawo k`usa wuyanshi

Ku kwantar da hankalinku

Ni wallahi bana ajiye shi shikad`ai yana wasa ko zama fa baifara ba

Tabbas wani ne yasaja mai abin mamakin shine dana ciremai Pampers
Ina bincikar shi hatta
Cikin pampers d`in wajen da yake bahaya an tura k`usoshin har guda uku wajen shima ya kumbura

Tashin hankali wanda ba asama sa rana shine ahmad da aminatu suka shiga kowanne tambayoyi yake wa kamshi shin wanne marar imanine ya aikata haka ga jaririn da baisan komai ba

Zuwa lokacin shi kanshi ahmad dauriyar shi ta kare hawayen yake jin irin abin da likitar tace

Cigaba tayi da fadanta tayaya zamuyi sakaci haka ta faru tabbas wanda yay hakan yayine da niyar kashe shi tunda babu yaddaza ai hankali yayi saurin kaiwa wuyanshi ko ayi zaton abin anan yake ko kuma pampers dinshi
Da bamuyi saurin kawoshi ba tabbas za a iya rasashi ko yanzu haka babu tabbas akan zai rayu ko bazai rayu ba
Yazama dole dai amai aiki zata rubuta mana takarda mutafi babban asibiti dole amai aiki a ranar kar ya wuce awa uku nan gaba dan ko
K`usar bayan nashi ba su iya cirewa ba tunda tariga data shige can ciki kanta ne kawai ya rage kad`an ake hangowa

Cikin tsananin tashin hankali wanda zamu iya cewa nida shi duk bamu ta`ba tsintar kanmu cikinshi ba muka tashi .
Muka nufi d`akin da aka kaishi

Allah sarki yana kwance
Har zuwa lokacin baya numfashi ahmad kanshi kuka yake .
Ya shiga tambayata waye yawa yarona haka qaunah
Kalli yadda aka maida min kalim bawan allah shin meya sani me ya tsarewa wannan mutumin
Kalli fa baya numfashi k`usa a jikin d`an adam fa ko k`aya ce ya aka yi da ita bare k`usa tabbas anso kashe min shine
Wa salaha tabawa shi?

Ni kukana kawai nake na rungumeshi maganganun ahmad sama sama nake jinsu
Dan ni zuciyata tafara k`issima min wani abu tabbas ina zargin hjjo akan hakan dan ita kadai ce bata k`aunata a gidan
Sannan bata son kalim k`iri k`iri take nunawa bata boyewa
Sai kuma nayi saurin istigfari duba da zato zunubine koda ya kasance gaskiya ne allah shi yasan wanda yamana hakan

*_😍MAMAN `DAN ALBARKA CE😍✍️_**_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

*_PAID PAGE 32_*

Ganin yana naiman tona mata asiri yasa ta d`auke shi tayi uwar d`aka dashi

Ai dan ubanka yau saika gane kuranka muje uwar daki duk abinda take hannunta na bakin shi ta rufe ta hanashi kuka
Dan bakamar razana yayi
Ba dalilin barcin dayake
Ta girgiza shi

Dawowa tayi parlourn ta cigaba da jijjigashi kuka
Kawai yake salaha ce
Data shigo taji kukan shi da sauri takarasa
`Dakin

`Lafiya hajjo yake kuka?
Ajiye laidar kayan miyar tayi ta tafi ta tara hannu zata amshe shi

Kinga ungo shi tunda kika tafi yake tsanyaramin ihu kamar wanda ake gutsira wai shima yasan d`afa

Baisaba dake bane shiyasa kawo shi kiga
Koda salaha ta amsheshi
Dai kin shirun yayi kuka kawai yake kamar wanda
Ake mintsina har zabura yake

Ikon allah hajjo kinga
Yaki yin shiru ko kalloba baiyiba kofa wajen mamanshi yake inna amshe shi shiru yake
Ta shiga k`ara jijjigashi
Kozai yi shiru yaro sam yak`i shiru

Hajjo data dauki kayan
Miyarta tana juyewa a
Robar da zata gyara hankali kwance ta dago kai
Kinga ki mikashi wajen
Uwarsa babu dole daga
`Daukar yaro sai kuka
Wai shima yasan
Munafurci maza ki kaishi
Kizo ki nik`a min kayan miyar nan

Hajjo allah baya k`iwa saidai in wani abunne yasame shi dai bari
Na kaishi wajen aunty aminatun na dawo
Ko zai amshi nono

Fitowar ta tayi dai dai da fitowar maman Aisha daga daki dan tun d`azu take jin ihun shi dan dai
Basa shiri da hajjon ne
Shiyasa bata tambaya ba
Sannan ihun dayayi na farko ma akan kunnen ta
Ne

Meya same shine haka salaha?

Wallahi bansaniba maman aisha kawai rigima yake ji yau

Aikam kalim bantabaji yayi kuka haka ba kodai cikinshi ke ciwo ?

Bari na kaishi dai ko in anbashi nono zaiyi shiru

Hajjo da salaha na fita ta mike ta fara taka rawa dan tasan dai yau dole yaron nan ya mutu kafin agano abinda tamai zaiyi wuya tasan koda angano
`Din baza a zargeta ba
Tunda dai ba d`aukar shi take ba

Bayan munyi wanka ina
Zaune bakin gado ina sa riga ahmad dake kwance
Kan kujera muka fara jiyo ihun kalim ana doso
Kofar mu dashi
Da sauri nakarasa sa rigar haka kawai naji
Gabana ya fadi ahmad kecewa kinji d`an halak
Ko harfa ya dawo

Bai rufe baki ba salaha ta shigo cikin sauri aunty aminatu kinga sai kuka
Yake tundazu nayi nayi yayi shiru yak`i
Ko kallona baiyi ba

Nasa hannu na amshe shi ihu yake kawai muryarshi har tafara dashewa na kalli fuskarshi yadda tayi jajir abinka da farin mutum

Kibashi nono mana ko yunwa yake ji kinsan shi baya wasa da cikinsa cewar babanshi

Zama nayi kawai na zaro nono na shiga k`ok`arin bashi amma tabbas ni nasan ba dai yunwa bace zata furgita shi har haka dan baita ba yin kuka irin wannan ba

K`in amsar nonon yayi
Nayi nayi yaro ko alamar amsar nono har wani mimmik`ewa yake k`ara yi

Ahmad ne ya miko hannu kawo shi ingani

Cikin rudewa na mika mishi shi ya amshe shi
Nan yashiga kokarin ciremai riga ya dudduba
Jikinshi kodai wani k`waronne ya cije shi
Amma babu alama

Salaha ce tace maman aisha tace ko cikinsa ke ciwo

Nan na dauko maganinshi na bashi
Amma sam yaki amsa zuwa lokacin har ya fara kakkafe min

Nashiga tashin hankali ba karami ba haka babanshi
Kuka kawai nake salaha na tayani

Ki kwantar da hankakinki kibar kukan kinji
Bari na kira hajjo tazo ta duba shi dai ko ciwon cikinne tunda ita tasani
Ya miko min shi ya fita

Bayan fitarsa ne na zauna kan kujera na k`ure yaron da ido kawai
Ina kuka salaha ma takasa tashi kallonshi nashiga yi yadda cikin k`ank`anin lokaci
Ya fita hayyacinsa

Ina cikin kallonsa ne naga yayi wata mika ya zabura jikinsa ya saki
Cikin ihun kuka na fara jijjigashi

Hajjo kalim ke kuka har yanzu yak`i shiru ko nono yak`i amsa anbashi maganin ciwon ciki ma koshine bai amsaba

To ni me zan masa daka zo wajena me kake nufi ina da maganin da zan bashine ?

A a hajjo ganina yi koke zaki iya sanin abin daya same shi kiduba nima nadu ba ko wani k`waronne ya cije shi amma banga komai ba
Dan allah hajjo har kakkafewa yake yi kizo muje ki gani yace cikin
Magiya

Dan shi kanshi cikin tashin hankalin yake
Ba kad`an ba daurewa kawai yake amma jiyake kamar zaiyi kuka
Yana tsananin son kalim kamar ranshi ganin aminatu na kuka ne yasa ya `boye nashi tashin hankalin dan karta k`ara rikicewa

To kaje ganinan zuwa daka wani tsaya min akai
Kamar naci bashin ka

Har ya juya zai tafi hajjo bata motsa ba bare tayi alamar shirin tashi tana kwance abinta

Yana fita taja tsaki aikin banza kawai zaka wani zo kace yaro na kuka inje induba shi ya mutu ma
Karshe yan iska gayyar tsiya

Tunani ya shiga shin me ke damun hajjo dan kawai bakyason uwar yaro sai k`iyayyar ta shafi yaron aiko ba komai a matsayinta na mahaifiyar sa yakamata yaron yaci albarkacinsa tunda jikanta ne amma baisan wacce irin zuciya ce da itaba sam kamar shid`in ba d`anta bane tunda yayi aure ta tsane shi kwata kwata ta daina nuna mai kulawa

Kafin ya karaso d`akin muka cikaro dashi a hanya cikin kuka na mika mishi shi kaga ya mutu nashiga ukuna

Da sauri ya amshe shi .
Hannunsa na rawa ya shiga jijjigashi yana kiran sunanshi

Mik`omin shi yayi maza ki goyashi muje asibiti inaga suma yayi yi sauri

Da sauri na amshe shi salaha ta miko min zanin goyon na goyashi na figi hijabin dana ke sallah a kan k`yaure
Ahmad daga shi sai jallabiyar jikinsa muka nufi hanyar fita ko k`ofar
`Dakin hajjo bamu kallah ba bare mu mata sallama mukayi waje

Allah ya taimakemu muna fita muka samu adaidaita muka fad`i sunan asibitin da zai kaimu wani private din asibiti ne dake kusa damu

Muna zuwa aka amshe shi nan likitan ta bukaci da mumata bayanin abinda ya same shi nad`an mata bayanin cikin kuka sam bani da nutsuwa ganina ke ya mutu ma kawai

Nan ta kwantar dashi ta shiga auna shi harta gama auna shi bata ga wani abu ba ko d`aya harzata dauke abun awon sai idonta yakai
Wuyanshi wajen yayi jawur ya kumburo .

Cikin sauri ta kallemu meyasame shi haka a wuya gashi wuyanshi har ya kumbura

Da sauri muka tashi muka nufi kanshi
Tabbas wuyanshi gashi ya kumburo sosai wajen yayi jawur

Bansan abinda yasame shiba ankawo shine kawai yana kuka
Chapter 57 · 0% Book details