← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 78

Sashe 42

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tashi daga tsugunnon daya yayi gaba na yadawo kan gadon ya jawoni jikinsa ya isa ya isa kiyi shiru insha allah
Saina dau mataki akan
Abin da ya miki

Kuma yazama dole inbar wannan gidan nagaji da
Abubuwan da suke faruwa

In muka bar gidannan ina zamuje yanzu ?

Gwara inkamamiki haya
Kafin allah ya horemin insamu ingina nawa na
Kaina kiyi hakuri kinji

To wai baki rufe kofar bane kika kwanta ko kuma yaya?

Na rufe kofar wallahi bansan tayaya akai
Ya shigo ba amma
Kafin inkwanta
Tabbas naji ana taba kofar amma dana yi
Magana sai naji shiru
Andaina bansani ba ko
Taya ya bude ya shigo ba
Dan kwanakima ya shigo
Min to ranar bansan ma
Shine ba ya gudu dana yi ihu
Ranar na manta ne ban rufe kofa ba
To bayan ankwana biyu
Ma ya balle sakatar net
Dina ya shigo aranar shine na yan keshi da wuka
Washe gari shine na gane shine

To daya san nagane shi shine yazo har dakinnan
Ya dinga zagina akan sai ya cika burinshi a kaina
Sai ya illata ni ban dauki.
Maganar shi ba ina
Tunanin duka borin
Kunya ne amma dai na kunna recording din
Wayata dan watarana
Ashe shi yana nan bai manta ba

Cikin sauri ahmad ya ture kaina daga cinyar shi
Wai duk wadannan abubuwan sun faru
Amma kika kasa fadamin
Indau mataki cikin
Fushi yake maganar
Alamar abin ya mai ciwo

Na kalle shi cikin kukan
Daya dawo min
Ina tsoron in fito in
Fadamaka ka kasa yarda
Tunda koba komai
Dan uwanka ne
Kuma in hajjo taji
Ita caza tai sharri nake
Mai tunda babu wanda nake da shi shaidar hakan

Da sauri ya daga min hannu kinga wannan ba
Hujja bace yanzu da ba dan

Allah yasa andaga tafiyar nan tamu ba saboda rasuwar da mahaifiyar oganmu tayi ba da haka
Zai cutar dake
Babu wani wanda zai kawo miki dauki
Kinga kenan shirunki
Baiyi amfaniba

Kidaina irin wannan abu irin wannan ba a boye shi
Da kinfito kin fadamin
Tun farko da ba akai
Ga hakaba tunda
Kince lokacin da yazo
Yana miki warning kinyi
recoding din maganar shi
Dole hajjo zata yarda
Tunda za a ji muryar shi

Yanzu ina wayar taki?
Gata can a kan madubi

Nan ya tashi ya dauko wayar tawa
Ya bude ta nan ya shiga
Ya mikomin kunna min
Inji

Na kunna masa ba bashi saiga maganganun dan ladi tiryan tiryan har zuwa lokacin dana yanke
recoding din

Ya kalleni har yana wannan ikirarin kikasa fadamin nan ya dauki wayar shi ya tura yace wannan ma ya isa shaida
Koda kuwa hajjo zata
Nemi musawa ko
Kuma shi

Acan waje kam ganin ahmad ya shige daki yasa mutanen gida fara zamewa da dai,dai,da ,dai,dai, kowa na tafiya dakin shi cikin fadin allah ya kyauta kowa yana allah wadaran da halin
Dan ladi

Inda hajjo dake tsugunne tallafe da dan ladi
Cikin tsananib tashin hankali
Dan ya riga daya sume tuni
Jijjiga shi take kawai
Gashi cikin yan uwanshi
Babu wanda ya shigo
Gidan har zuwa lokacin
Dan basa kwantawa da wuri
Umar ne kawai kuma.
Tuni yayi barci

Malam musa,ma baidawo daga
Wajen sana,arshiba ganin
Dai babu wanda ya kama
Dan ladi yasata tashi
Ta nufo dakin
Mu

Ta banko kofar cikin
tsananin masifa

Da sauri na dago kaina
Ina kan gadon ahmad
Na daga gefe
Shima kallonta
Yake

Nan tashi ga kare mana
Kallo ka tsaya kana
Kallona mana tunda ka
Kusan kashe min
Da,

Ahmad ya sunkuyar da kanshi cikin
Mamaki shin har
yanzu hajjo bata san
Abin da dan ladi
Yayi bane kome

Ba canai ka tsaya kana,
Kallo na ba tashi zaka
Yi muje ka,kama shi
Akai shi daki
Dan ya suma
Sannan saika kora min
Bayanin dalilin da yasa
Kake neman rayuwar dan
Uwan ka ?

Shin kaida kayi tafiya ma
Me ya dawo da kai gidannan?

Haba hajjo shigowa fa nayi na tarda shi .
Ya daddaure aminatu
Yana shirin far mata
Bayan duk maganganun da
Ake kice bakisan meya
Mun ba haba hajjo
Iyalina fa
Ga ciki jikinta inya saba
Shaye shayen sa da rashin jinsa yana
Jawo mana abin
Fada yau abin nashi har
Cikin gida

Sannan ba yau ya fara shigo mata daki fa
Ta fadamin komai
Ko kwanaki fa ashe karyar yankan daya ce
Barawo ne yamai
Dakin ta ya shigo fa

Bayan nan ya kuma shigowa wanne
Irin abin kunya kenan
Fisabilillah

Duk da hajjo ta shiga mamaki akan abinda ahmad ya fada mata
Duk da zuwan ta wajen
Taso fahimtar abin daya
Faru daga irin furucin
Da ahmad yake lokacin
Daya ke kaiwa dan ladi duka

Amma ta tambayane dan ta tabbatar tayiwa tubkar hanci
Dan bazata taba bari maganar ta fita ba
Bare taje kunnen babansu
Duk da tasan bawani
Mataki zai dauka ba
Tunda sai yadda tayi dashi

Amma jin wai aminatu
ce ta yanki dan,ladin
Yasa taji ranta yayi
Mummunan baci nan
Tafara magana

A a ah lallai kace duk saboda kodaddiyar nan
Kakusa hallaka min da,
Saboda wannan abar
Tayi maganar cikin
Tsananin fushi .tana
Nuna ni kamar zata dakeni

Ashe dama ke kika so kashe min da,
Kika sa naketa faman
Hakilon tsinewa barawo
Ashe kece ta kare ta zazzare ido

Cikin tsananin mamakinta
Muka shiga binta
Da kallo jin fadan data ke
Daban bama akan maganar da aka mata ba
Ita fadan ta kar a kashe mata da,
To shi ahmad din ba danta bane data ke.
Nuna mai banbanci
Sannan duk abubuwan da aka ce yayi bata nuna damuwar ta ba sam sai fadanta take

Nan tashiga zagina kan
Meyasa zan yanki danta
Nida mijina muna son
Ganin bayan shine tunda
Ai dai bai aikata ba
Sharri na mai tunda ita
Tasan duk ba acikin hankalinsa yake
Zuwa waje na ba tunda dai
Nima nasan ai yana
Shaye shaye shine zan kashe mata da,

Ahmad ne yayi karfin halin cewa haba
Hajjo bakiji abin dana ce miki yayi bane?

Dan ubanka naji
Nace naji amma wallahi wallahi ban yarda ka tada maganar nan ba ko agaban waye ban amince mahaifinka yajita ba
Muddin kayi abin daya ji wallahi saina saba maka

Akan mace macen banza da zaku iya rabuwa kake
Kokarin hallaka dan uwanka
To wallahi kayi na farko kayi na karshe indai yamaka wani abu.da zaka ware karfin
Tuwonka ka dake shi
Ni kazo ka fadamin
Na fadama

Ta juyo da kallon ta kaina
Da tsananin mamaki
Ya daskarar dani a zaune
Ganin son zuciya
Kiri kiri ga gskiya amma
Ta kasa fadarta ranar nasan tabbas hajjo
Nason kanta
Da ya,yanta inba
Haka ba ace danki
Yana kokarin aikata irin
Wannan bannar kikasa tsawatarwa har kina ganin
Laifin mutane
Kina cewa kar maganar
Ta fita bayan gaban
Mutanen
Komai ya faru

Kekuma munafuka algunguma tun shigiwarki gidannan
Kike kokarin ganin
Kin raba shi da yan
Uwanshi baki samu da ma ba sai yau wama yasani ko ke ke masa tallan kanki shegiya matsiyaciya
Kawai kinci sa,a banason maganar ta fita da wallahi sai kin
Biya bashin yankar shi da kikayi da wuka
Amma muje zuwa da sannu zaki biya .
Bashi

Kaikuma ka tashi nace
Ka kamamin shi inkai shi daki kafin babanku ya dawo

Wallahi hajjo bazan kama shi ba.
Kamar yadda kika .
Nemi dai na rufa masa
Asiri karna tona maganar
Zan rufa masa asiri
Kodan rufuwar naki damu yan uwanshi
Baki daya amma
Badan shiba tunda
Shidin baya gudun abin
Kunya amma fa bazan taimaka mishi ba

Sannan ni na zare hannuna akan lamarin shi kwata kwata kome zaije ya jawo nan gaba in ankulle shi karma a nemeni wallahi na daina
Komai indai lamari na
Dan ladi ne karma ku nemeni abin da yake aikatawa in dai dai ne zai gani inma ba dai dai bane hajjo wataran gaskiya zatayi halinta

Cikin mamaki hajjo ta shiga binshi da
Kallo shin ita yau ahmad
Yake fadawa maganganun duk da suka zo
Bakinsa tab
Lallai kwabarta naso tayi ruwa

Ni kake cewa ka zare hannu kan lamarin dan ladi na shiga ukuna ni mero mezan gani
Amma wannan yarinya .
Kin cuceni auran ki
Bai karemu da komai
Ba sai tashin hankali
Saiki fadawa ubanki
Salisu ya karawa bokan shi kudi aiki yaci
Shikenan ta raba min kan
Yara da rushe da kuka tayi waje

Nikaina nayi mamakin yadda ahmad ya fadawa hajjo maganganu duk irin biyayyar shi gareta
Amma saina tuna shifa
Mai hakuri inya tashi fushi bai iya ba sam

Na dan matso kusa da shi na dora hannuna kan kafadar shi nace

In ranka ya baci baikamata
Ka fadawa hajjo maganganu har haka ba
Kaga kasata kuka
Mahaifiya ce fa

Saina ga ya kureni da ido
Yana ta kallona ko kiftawa
Bayayi can dai yace waike wacce irin
Macace ne?

Shin dan tana mahaifiyata saina kasa fada mata gaskiya
Kullum fa kina kallon
Abin datake amma saiki
Cemin mahaifiya ce
Ki kyaleni kawai
Tunda kedin bansan
Irin zuciyarki
Ba amma ni ankaini
Inda bazan iya shiruba sam
Karma ki sake cemin
Wani abu
Ya kama hannuna inda
Shatin igiyar daya daureni ya nuna

Kiga fa irin mugun daurin daya miki bai duba halin da kike cikiba saboda tsabar rashin imani
Sannan nufinshi da ban
Daya aiwatar da nufinshi
Fa

Meenah da bazan taba yafewa kaina ba har abada saboda nakasa rike ki nabaki kariya

Ya saki hannun nawa yana mai tashi ya je ya duba flarks dib ruwan zafi yaga a kwai ya juye yazo ina jinshi ya ciremin rigata

Nan yashiga shafa cikina ya na duddubawa kamar ance mai zaiga wani abu
Tukun ya kama hannuna yasa dan kwalina cikin ruwan ya shiga dan mammatsamin hannun
Har zuwa kafafuna inda har sun kumbura

Ya dago fuskata inda shatin hannun dan ladi daya zuzzubamin maruka ke kwance hagu da dama nan yashiga shafa wajen ahankali
Cikin tausayawa Meenah ko yanzu ya cutar min
Dake meenah ji
Yadda ya mararmin ke

Hannaye na na dora
Kan nashi na ce kayi hakuri dan ni shidinne ya dawo bani tausayi
Saboda halin dana ga ya shiga
Chapter 42 · 0% Book details