← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 78

Sashe 69

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad kam tunda yaji inna tace ga ahmad d`an marigayiya hasana ya shiga mamaki sai yaji kamar ba dai dai innar ta fad`a ba yana cikin tunanin hakan yaji bayanin inna asabe da kuma jin wai kakanshi na zuwa cigiyar shi mekenan ko dai ba shi ahmad d`in ake nufi ba

Maganar aminatu ce ta kashe masa tunanin shi jin tana cewa a inna da d`ai d`ai dai ga kalim nan mai sunan yaya musa sai kuma mai sunan babanmu gashinan ta mik`awa inna asaben dke mik`o hannunta zata d`auki yaran

Tunda aka kai inna talatuwa d`akinta babu wanda ya sake bi ta kanta tana kwance akan shafaffiyar katifar ta hawayene kawai ke zuba a idonta tana kaico da rayuwarta wai yaune aka ga salisu salisu dai wanda sukawa kurciya ya tafi da nufin bazai taba dawowa garin ba shine dai tagani da idonta me kenan amma ai boka ya tabbatar musu ba zai taba dawowa garin ba muddin kwa ya dawo to ba shakka sai sun amshi dukiyar su tana sane da cewar yana nigeria dan tana samun labari wajen hajjo shiyasa koda kakan ahmad ke sintirin jin labarin jikanshi bata sanar musu komai ba duk da tasan koman
Bakin ciki takaici dana sani mara amfani shi ya cika mata zuciya takai dubanta ga jikinta ganin yadda halittarta ta koma lokaci d`aya ta fashe da kuka tana son yunk`urawa ta tashi ta kasa gashi tunda suka ajiyeta basu k`ara bi ta kanta ba

Yanzu ina ranar zalinci ina ranar mugutar tata yayan nata da tayi dominsu kowacce na d`akin mijinta suna zaman hak`uri dan zaman hak`uri za a ce kowacce garin da take aure da ban babu wadda ke jin dad`in gidan mijin bare su taimaka mta ita ke wahala wataran ta basu in sunzo suma kuma ga iyali kowacce ta tara

Dukiyar data yi dan ta samu shegiya asabe ta danne komai ta hana ta kuma itama bata ga abinda tayi da ita ba
Har sawa tayi boka ya makantar da asaben sannan ta mallake aliyu dan asaben dan karma ya taimaki uwarshi sai abinda tace masa yakeyi duk dan ta gano ina dukiyar take amma ta bincike gidan kaf tasha shiga d`akin asaben ta bincike tunda ba ganin ta take ba amma bata samun komai duk burinta na mallakar dukiyar ya tashi a banza kenan

Kaga aliyu maza tashi kaje ka kira malam liman yanzu yanzunnan kace masa munyi bak`i daga nigeria kaji

Baba liman dake zaune dawowar shi daga masallaci kenan yana zaune a d`akin shi inna ta kawo masa abin karyawa dan baya dawowa masallaci da wuri yaji sallamar aliyu

Nan ya fito suka gaisa aliyun ke sanar masa inna asabe ta aiko shi ya kira shi sunyi bak`i daga nigeria cikin sauri baba liman ya kama hannun aliyu bak`i kace kukayi suwa ye

Nima duk bansan sauran ba amma harda yaya salisu da yaranshi duk dai yan uwane

Muje muje muje maza ko gida bai koma ba ya biyo bayan shi suka taho
.
Ba jimawa muka ji sallamar malam liman
Nan aka masa iso lokacin mun shinfid`a babbar tabarma a gindin iccen dake tsakar gidan ankawo mana abin karyawa

Dukanmu kallo muka shiga bin mutumin da aka kira da baba liman

Babban mutum ne ya manyanta sosai dan za a iya sa shi matsayin sa,an baba malam kakana sanye yake da manyan kaya da malum malum harda rawanin sa shiga dai irin ta malamai

Tun kafin ya k`araso ya k`ure ahmad da kallo ya kasa d`auke idon shi a kanshi ko min daren dadewar da za ai bazai manta ahmad ba komin girman da zai yi kwa duk da tun baifi shekara uku ba

Aka tafi da shi ahmad ma haka kawai ya k`ure baba liman da kallo ya kasa d`auke idonshi

Cikin sauri baba liman ya k`arasa kan tabarmar ya nuna ahmad da hannu wannan jika nane tabbas wannan jinin hasana tane ashe da rabon zan sake ganin ka ahmadi

Ya fad`a jikinshi na rawa

Ahmad dai kam kanshi ya kulle tun d`azu suke sashi cikin rud`ani shidai a sanin shi kakansu ya rasu wato mahaifin su baba sannan baban hajjo ma haka kuma yaji suna ambatar sunan hasana marigayiya suna cewa shid`in d`anta ne mekenan suke nufi ?

Baba salisu ne ya kama hannun baba malam yana murmushi ya zauna dashi a tbarmar dan ya kasa zama yace tabbas kam ahmad ne baba malam ahmad dai d`an wajen hasanarka

Mu kanmu jin abinda suke cewa mun shiga mamaki me kenan?

Ahmad fa muka ji ana cewa d`an hasana marigayiya to dama ba hajjo bace ta haifeshi ko kuwa dai sunan hajjon ne haka amma ai kuma hajjo sunanta mero na fad`a a zuciyata kuma hajjo na raye meke nan meke shirin faruwa

Ahmad kam yama rasa mai zaice
Sai da yaji babanmu na bashi umarnin ya taho wajen baba liman sannan ya dawo hayyacinsa

Matsowa yayi gaban tsohon allah sarki ya rungume shi yana zubda kwallah yana mai addu,o,i ga marigayiya hasana

Shidai ahmad duk ya shiga duhu sai bayan komai ya lafa tukun aka shiga firar yaushe gamo anan baba liman ke sanar mana tarihin komai tunda ga `batan babanmu har zuwa auren baba musa na farko wanda sai sannan muka sani har zuwa neman d`an uwansu da suka tafi nigeria da haihuwar ahmad

Da kuma auren baba musa da hajjo duk ya fayyace mana

Bakaramin mamaki da kad`uwa muka shiga ba jin cewa ahmad wai ba d`an hajjo bane dan bamu taba tunanin nan ba

Sai lokacin nashiga nazarin wasu abubuwa da suka dinga faruwa d kuma irin abinda hajjo kewa ahmad

Kai gaba d`aya ma ahmad bai d`auko kamar hajjo ba ko misk`ala zarratin kamar baba ce da shi ya,ya,n hajjo kam duk da sun debo baba suna kama da ita

Shikam ahmad duk ya rikice dan baita `ba kawowa ba hajjo bace mahaifiyarsa sai yanzu shi yasa abin ya bugeshi

To amma meyasa ba ata `ba sanar masa cewa ba ita bace mahafiyarsa ba koda wasa me hakan ke nufi? ko baba bai ta`ba fad`a masa ba duk kanshi ya kulle sai yarasa ta cewa ma illa lamo dayayi jikin baba liman yanajin soyayyar tsohon na ratsa shi

Nan baba liman ya shiga bashi tarihin mahaifiyar sa da duk yadda ta gudanar da rayuwarta da kuma yadda yake sonta saboda biyayyarta gare shi
Shiru kawai ahmad yayi yana saurarar baba liman yanajin soyayyar mahaifiyar shi na shigarshi duk da bai ta`ba ganinta da ido ba amma sai yaji yana marmarin ganinta jiyayi kwallah na zubo mai kawai sai lokacin shima ya shiga tunanin irin yadda hajjo ta rik`eshi duk da kasancewar babu duka amma tabbas yadda take nuna,bambanci a tsakaninsu bai `bace masa ba sannan har lokacin da take sashi sata bai manta ba

Jiyayi wata irin tsanar hajjo ta na ratsa shi dan sai yanzu ya tuno yadda take gallaza mishi da aminatu ma da yadda ta ke nuna rashin damuwa kan lamarin daya shafe shi da ya'yan shi ashe dan ba ita bace ta haife shi ba

Dagowa yayi ya kalli babanmu amma baba meyasa baku ta`ba sanar dani cewa ba hajjo bace ta haife niba ? Dan na dinga aikawa da mahaifiyata da addu,a a matsayina na d`anta data bari a bayanta da zan zama gatanta sai gashi banma san ba ita bace ta haifeni ya fad`a yana mai rushewa da kuka sai kace ba namiji ba

Allah ne bai kawo lokacin hakan ba ahmad sai yanzu

Baba liman ne ya shiga bubbuga bayanshi ya kalli babanmu hak`ik`a baku kyauta ba na rashin sanar da shi wacece mahaifiyarsa ba dan tabbas gaskiya ya fad`a bata samu addu,a daga gare shiba

Wallahi baba liman nikaina banta`ba tunanin sanar da shiba koda wasa ba sai yau allah yayi

Nan dai aka cigaba da maganar kowa na fad`ar albarkacin bakinsa

Nan malam liman yace yana son ahmad da iyalinsa su bishi gidanshi dan ya gana da ya`n uwan mahaifiyar sa da kakar sa dan itama tana da burin ganin shi sosai kullum maganar ta kenan

Har zasu tafi inna asabe cikin kuka ta nemi alfarmar malam liman daya tsaya tana da magana

*_😍MAMAN `DAN ALBARKA CE😍_*✍️
09/11/2022, 2:24 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

_*PAID PAGE 43*_

Dawowa baba liman yayi ya zauna muma da muka mimmik`e muka koma muka zauna

Ina son dan allah inyi magana amma da farko shin talatuwa na nan zaune ? Dan naji tun farkon maganar nan banji tasa baki fa ta fad`a tana mai jujjuya kai kamar zata ga talatun

A a bata nan ai tun shigowar bak'innan ganinta da salisu ta yanke jiki ta fad`i yanzu haka tana d`akinta alamu sun nuna ta kamu da ciwon `barin jiki dan gaba d`aya halittarta ta juye ko tashi ta kasa yi cewar aliyu

Wayyoh allah na ya allah na tuba allah kasa wannan makantar itace iyakar jarabawata akan irin muna nan ayyukan dana yi allah ka yafemin tace cikin kuka

Ina son yin magana amma ina son dan allah talatuwa ta kasance anan wajen dan maganar ta shafemu baki d`ayan mu naso ma ace su musa da abdullahi na nan amma sai dai kash babu su saboda wani dalili wanda insha allah k`arshen abun yazo

Nan aka d`auko inna talatuwa data fige lokaci guda ta fita hayyacinta aka kawo aka kwantar da ita kallon kowa take kawai sai dai ko magana ta kasa bakinta sai dalalar da yawu yake

Inna asabe ce tafara magana da farko dai ina neman yafiyar ku akan duk abinda nayi da kuma wanda zakuji dan allah salisu kamin alk`awarin zaka yafemin sannan ko da yan uwanka basu tarda ni ba a raye zaka nema min yafiyar su dan allah kamin alfarmar nan ta fad`a tana mai fashewa da kuka
Chapter 69 · 0% Book details