← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 78

Sashe 19

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajjo ta fashe da wata mahaukaciyar dariya tace

Zainabu kina ganin zan karayane dan wasu kananun bokaye sun fadamin maganar banza to sam dalilin dayasa nazo gareki kenan in yi musu mai gaba daya

Zainabu tace kamar yaya kenan ?

Hajjo tace kinga tunda nayi aure banje can gida niger ba wanda rashin zuwan nawa ba komai yasa naki zuwa sai don kada inma tunawa da musa mahaifarsa yace zai dau ahmad suje

Duk da nasan su yaya talatuwa basu barsu haka ba tunda duk cikinsu babu wanda yakara zancen wata niger bare suje
Amma nasa boka yakara dasawa musa kiyayyar garin shiyasa nima banta yunkurin zuwa ba duk da inason zuwan kodan inga bilkisu dan nasan zuwa yanzu ko sun mata aure ko kuma ana shirin aurar da ita

To yanzu tunda nazo nan da gobe zamu koma wanda dama ni bawata gaisuwa ta kawoni ba nataho shirin wucewa Niger ne dan inziyarci uban shaidanu wanda shine yawa yaya talatuwa aiki harta kashe mahaifiyar su musa

Kuma shine nima yamin aiki akan hasana nasan ahmad bazai gagareshiba

Sannan inason gabatarmasa da kudurina na gaba shine tarwatsa salisu da abdullahi asamusu kiyayyar juna ta yadda zasu zama makiyan juna kamar basu taba sanin junaba

Kinsan mene hikimar hakan?

Zainabu data shanya baki ta ji da ganin shu,umancin daya dame nata ya shanye tace a a saikin fada

Saboda karma su kawomin tangarda akan cikar burina tunda sunsan ahmad ba dana bane dole watarana nasan asirin zai karye kobai karyeba salisu nada karfin addu a dan kafin arufemin bakinsa boka ya tabbatarmin nadan wani lokacine aikin

Shiyasa nakeson inmunje akara datsemin bakinsu sannan ajefa kiyayya atsakaninsu

Yadda basu da kwanciyar hankalin ma bare hankalinsu yadawo kaina har burina yacika

Kekuma aikinki shine inkin koma gidan abdullahi ki tabbatar duk abubuwan da boka yabamu kin aikata shi kuma salisu nashi zai yi aikinne kawai sannan ayi amfani da zafin zuciyarsa dan kinsan baisan wulakanci kekuma zaki dinga zuga abdullahi yana mai abin da dole zai nisanta kanshi dashi

Kinga banida matsala da musa danshi inhar muka koma yanzu zansa amin aiki mai zafi akansa yadda shima zaina goyon bayan abdullahi yana ganin laifin salisu kinga shikenan inyayi zuciya zai fita a harkasu

Shikenan burina zai cika cikin sauki

Zainabu da tashiga tunani shin mai hajjo ke nema me zata samu inta rusa wannan zuriar sannan wacce riba zata samu inta lalata rayuwar ahmad shin bai isheta wa aziba da abin yadawo kan danta?

Ita da tayi alkawarin tadawo daga rakiyar bokaye saboda sun kasa sawa abdullahi ya maidata duk irin wahalar da bannar kudin datayi amma yanzu jin maganganun hajjo yasa tanaji zata aikata komai dan ta koma amma fa ita tana tsoro hakkin zai yi yawa

Duk da tasan itama tayi abubuwa amma bata taba kashe raiba hajjo kwa ta kashe tana tsoron watarana su samu sabani itama hajjo ta cutar da ita

Ganin zainabun ta lula tunani yasa hajjo dafata tayi firgigit ta dago ta sharce zufar goshin ta

Hajjo tace kidaina wasu tunanina kan banza zainabu dole ki taimakamin tunda kika bari na bude miki cikina inba hakaba dayan biyu koki samu cikar burinki na komawa abdullahi kishiga dakinki salin alin kokuma ki fara yawo akan bola inafatan dai kin gane hausartawa ta kare tana dan darawa irim dariyar muguntarnan

Zainabu da taji haka sai wata zuciyar tace yanzufa inkin koma dakinki kindaina wahalarnan kenan sannan kin huta da gorin su inna da mutanen unguwa na kinki aure kin tsofe kinga kuma ga yaranki gabanki kiyarda kawai

Ta dago tace shikenan hajjo ba matsala na amince da sharuddanki

Amma tayaya za ai duk hakan?

Hajjo tace dole zaki bina zuwa niger dannima nayi ma su inna laifi na rashin waiwayarsu tun aurena kinga saimuje mubasu hakuri

Zainabu tace ni mezancewa su inna inzamu tafi dan bazasu bari na bikiba

Hajjo ta kalleta wannan mai saukine zance auren bilkisu zaki rakani shine dalilin zuwana dan infada miki kimin rakiya dan boka ba amai aike kekuwa aikinki dole saikin taka da kafarki

Zainabu tace amma ke zakiyiwa inna bayani

Tace eh

Saikuma maganar kudi gaskiya ni bani da wasu kudi yanzu hajjo kin ga nayiyyi wankin duk basu zo amsaba bare nasamu kudin kirki abin dake hannuna ko kudin mota bazaiminba

Hajjo tace karki damu da wannan nashirya mana komai kedai kishiga shiri kawai

Haka sukaje wajen inna hajjo ta shishshirya karyarta inna ta yarda harda sawa auren albarka inda sukai sallama akan jibi zata zo su wuce

***********************"*

Kamar yadda hajjo ta tsara tacewa malam musa su wuce shida dan ladi ita zata wuce gida ne bai tambayeta mezata je yiba asalima bai nuna ko alamar yasan wajenba inda shima yace mata sai gobene zasu koma yanason ganawa da yan uwanshi bata kawo komai ba aranta
Inda washe garima ta riga su tafiya su saisun kintsa tukun

_Tsafi kenan gaskiyar maishi_

Washe gari hajjo ta biya ta dauki zainabu suka nausa sai kasar niger

***********************

Sun sauka garin niger inda gidan yayarta talatuwa suka fara yada zango sun tarar tana fama da ciwon ido bata gani sosai amma ahaka ta musu alkawarin rakiya wajen boka inda asabe tana nan daram sai dai fa an manyanta

Bayan kwana daya ta musu rakiya tasawa hajjo taje tabawa iyayenta hakurin rashin zuwanta sannan sukayi kwana uku daga nan sai wajen uban shaidanu
.

Dajine me cike da duhuwar itatuwa da ganyayyaki ga kwazazzabai da tsaunika dajin abin tsoro in akace maka bil,adama na rayuwa ciki bazaka taba yarda ba amma hajjo da talatuwa tafiya suke abinsu kamar sun sami saman titi sai dai insun zo gurin kwazazzaban su tafi asannu zainabu ce dai kamar kace mata kit ta zura da gudu

Haka suka ratsa tsakiyar dajin can sai gasu gaban wata bukkah ita kadai kwallin kwal a wajen bakajin komai sai kukan tsuntsaye marasa dadin sauraro abin abin tsoro haka suka doshi bukkar

Suka juyo suka ce zainabu ta cire takalmanta tacire suka rike a hannu suka fara shiga da baya baya mero kecewa

Gafara dai uban shaidanun duniya gamu tafe da kokenmu ubanmu maganin kukanmu saikai shaidani uban shagalallu takamar shaidanu gamu gabanka muna,fatan kashare mana hawayen mu

Tukun suka zube kasa kansu a kasa zainabu ce ta dago kai dan batasan dokar bokanba bataga kowaba sai wani dan tuntu na zama wanda duk wasu irin layune da fatu fatu a jiki

Bata gama karewa wajen kalloba taga wani dan tsigigin mutum ya bayyana cikin mummunar suffa jikinsa duk gashi hannunsa rike da wata sanda

Yana babbaka dariya da hakoransa jajawur idanunsa kwala kwala abin tsoro yayi nuni da zainabu cikin tsawa da katuwar muryarshi

Keee wayace miki ana dago kai anan sunkuyar da kanki baku fadamata dokata bane?

Suka hada baki gurin kayi hkuri uban shaidanu ita din bakuwace

Yacigaba da zazzare ido
Yace duk nasan abin dake tafe daku

Ya nuna hajjo ke burinki na ruguza rayuwar dan mijinki bazai taba cikaba amma tabbas zaki mulkeshi ki mulki mahaifinsa sannan bazai gano bake kika haifesa ba harsai ranar da kikayi sake ya hadu da kakan nan nasa dan shine ke ruguza duk wani aiki da kike sawa ana yi akansa

Sannan danki dan ladi aikin da kikasa akayi wa ahmad ya dawo kansa bafa zai taba karyewaba saidai inbaki maganin da zai dakushe abun yayi sauki amma sata da bin mata yariga da yashiga jininsa shaye shayen zai daina amma ba yanzuba

Sannan burinki na wargaza tsakanin kannan mijinki zai cika tabbas amma fa na salisu na wani lokacine abdullahi asiri zai yi tasiri akansa dan yanada sakaci da addu,a zan baki maganin da za azuba masa a abinci iyaci zaiji duniya bashida makiyi sai salisu

Ya kalli zainabu Sannan kekuma zanyi miki aikin da zaki komawa mijinkin shida kanshi zai zo ya bukaci ya maidaki amma fa da sharadi kokin shiga gidanshi babu ruwanki da matarshi dan macace tsayayyiya akan addu a duk ranar dakika kulata kukayi rigima tabbas aiki zai ruguje abdullahi zai sakeki

Tayi saurin dago kai ita dake da burin tana shiga ta fitar da aysha ashedai bazai yihuba amma ko hakanma ta gode

Ya kalli talatuwa yace kekuma kina can kina fama da ciwon ido ciwon da bawata ta sakar miki shiba sai asabe amma kin gujemu gashi tanason kassaraki kullum neman hanya take sotayi ki makance baki daya

Talatuwa ta dago arazane kana nufin ita tamin asirin ciwon ido

Yace kwarai zan baki makarin asirin inda ita kuma kibarta tukun kafin asan yadda za ai da ita dan bata zauna hakanan ba

Hajjo ta dago cikin tsantsar damuwa uban shaidanu yanzu babu hanyar da zan cika burina banason yaronnan yadawo ya samu aiki har yayi arziki cigabanshine banaso sam inason kassara rayuwarsa

Boka yace hanya dayace shine inya dawo zan turo aljanu sumin aiki duk inda yaje bazasu dauke shi aiki ba kinga babu maganar arziki kenan

Ta ce shikenan boka dama burina karyayi arzikin

Nan suka tambayeshi abin dazasu bashi ya fada suka bude wata kwarya suka jefa ya bawa hajjo duk magungunan da za awa abdullahi amfani dashi dana dan ladi

Ita kuma zainabu yabata nata hardasu kwalli da turaren dazata sa

Yabawa talatuwa makarin tsafin jikinta suka fito suka nufo gida kowa da sake saken dayake azuciyarsa badai haka akasoba

Amma hajjo ta tabbatar abin daya gagari uban shaidanu to tabbas babu inda zata samu amata

Haka suka kara kwana biyar bayan sun dan wuta suka shiryo suka rankayo zuwa Nigeria tare da munanan kudurorinsu

*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE✍️_*

*Wannan littafin na kudine idan kinason cigaba da karantawa zaki same shi akan farashin normal group 300 VIP 400 masu so ta private 1000 ki turo kudi ta wannan account number 2375144550Lawali ahmad zenith Bank ki turo evidence ta wannan number 09138320449 katin MTN ta wannan number 09138320449*

*Idan kuma littafin mu guda biyu kikeso TUSHEN MU DAYA da FANSAH 2022 Zaki turo normal group 500 VIP 800 ta private 1000*
Chapter 19 · 0% Book details