← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 78

Sashe 43

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muna cikin magana aka kawo wutar nepa
Nan ya kara jona ruwa
Daya tafasa ya juye
Ya sirka ya kama hannuna
Zuwa lokacin kafar ta dab saki
Ina iya takawa
Ya kaini bandaki
Da kanshi ya gasa min
Jikin babu ma batun wata
Kunya dan nida kaina
Nasan ba iyawa zanyi
Ba dan hannayena ciwo kawai
Suke min duk da bamu
Taba wanka tare ba

Haka muka dawo daki ya nemamin rigar arci mai dan kauri yasamin tukun ya je yayi wankan shima ya
Dawo ya jawoni jikinshi kamar wani zai kwacemai ni

Sai lokacin yake fadamin
Ashe lalata makullin
Yayi ya shigi dan daya zo kulle kofar ne yanzu yagani
.
Haka mukwa kwana kowa da sake saken dake ranshi ni dai jina jikin mijina nan da nan barci ya kwashe ni shine dai bansan lokacib dayayi barcin ba

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE😍✍️*_*_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

_*PAID PAGE 24*_

Nariga dana rintse idanuna kawai ina jiran naji ya aiwatar da mummunan kudirinsa

Sai jinayi ya fasa wani irin ihu da sauri na bude idanuna nakai kallona gareshi saina ganshi a can gefe ya dafe kanshi jini ne ke zuba

Da sauri na kai kallona gaba na nan naga ahmad ne rike da katako ya yarda katakon yayi kanshi ya yafinciko shi nan yashiga kai masa duka ta ko ina yana kai mai naushi

Shikuma ya kasa kare kansa bare ya rama tuni ya hada mai jini da majina tun yana dukan shi a daki har ya jawo shi filin tsakar gida

Amanata zaka ci d`an ladi ina dan uwanka mutumcin auren nawa kake kokarin ketawa abun da kake aikatawa a waje shine karasa inda zaka aikata sai akan mata ta

Fada yake cikin daga murya shi kuma d`an,ladi ihu kawai yake da naiman dauki kiran sunan hajjo kawai yake akan ta zo ta ceceshi

Dan zuwa lokacin ya fara dawowa hayyacinsa dan duka ahmad yake mai bana wasa ba

Hayaniyar muryar ahmad ce da ihun d`an,ladi tasa mutanen gida fara fitowa dan lokacin bawani dare ne yayi haka ba duka duka 11,05pm

Hajjo data ke jin murya kamar ta ahmad yana magana sai kuma ihun dan ladi daya karade gidan da yake kiran sunanta

Ta taso da sauri zani a hannu ta nufo lungun mu data ke jin hayaniyar mutane wanda zuwa lokacin mazan gidan ke kokarin amsar d`an,ladi amma ahmad ya hana haka naushi kawai yake kaimai ta ko,ina

Matan gidan kowacce ta tsaya sunyi cirko cirko cikin tsananin mamaki dan zuwa lokacin sun fahimci abin da yake faruwa

Cikin mutanen ta keto ta shigo ganin anata kokarin amsar d`an,ladin amma ahmad yaki sakin sa

Yasa ta karasa cikin tsananin tashin hankali ta shiga kaiwa ahmad duka dan ubanka sake shi kashe shi kakeson yi?

Kokari take ahmad kawai yasaki d`an,ladin inda ta dinga antaya mai zagi tana dukanshi

Wallahi inbaka sake shi ba saina tsinema albarka dan iskan yaro me ya maka haka kake kokarin kashe shi yana dan uwanka

Jin furucin hajjo ne yasa ahmad sakin d`an,ladi ya fadi rajab a wajen yana mai dafe kanshi da hannayen shi biyu hawaye na zuba a idon shi cikin kunar rai

Dan ladi da hajjo ta samu ta kwata a hannun ahmad da yagama fita a hayyacinsa gaba daya jinine kawai yake fita ta bakinsa da hancinsa ga kanshi inda ya buga masa katako shima yana zubar da jini idanunsa lumshewa kawai suke jikinsa yasaki gaba daya

Da sauri hajjo tayi kanshi tana mai tallafo shi cikin tashin hankali da ihun kuka kutaimakamin dan allah d`an,ladiii ta fasa ihu

Mutane duk sun tsaya anrasa wanda zai taba dan ladin sai mijin yawo jummai da yayi kokari ya kama ahmad ya mikar dashi yaja shi gefe

Da sauri ahmad ya fincike hannun sa tunawa da halin daya bar aminatu a ciki a daddaure yayi dakin da gudu

Tun daga lokacin da ahmad ya bugawa dan ladi katako a kai wani farin ciki ya kamani ganin allah bai bashi ikon ketamin haddiba

Ya kawomin taimako duk da na shiga mamakin meya dawo da ahmad bayan munyi sallama ya tafi wajen awanni biyu kenan nan nashiga godiya ga allah

Duk abun dake faruwa a kofar dakin inajin su da irin dukan da yake mai da taruwar mutanen gida da zuwan da hajjo tayi tana ihun zai kashe mata da

Nidai ina kwance dan babu ta yadda za ai in kunce kaina duka hannayena a daure suke ga cikina inda na fada kanshi yana min wani irin ciwo ga bakina da ke fidda jini sakamakon marin da d`an,ladi yamin jikina duka wani irin ciwo yake min
Ta ko ina

Da sauri ahmad ya shigo d`akin cikin sauri ya fara daukar zanina ya yafamin dan pant ne kawai a jikina dan kafin ya cire shine allah ya kawo ahmad

Nan ya shiga kuncemin daurin daya min yana gama kunce wa da sauri na fada jikinshi na fashe da kuka

Kankame ni yayi ya runtse idanun sa shi kanshi duk dauriyar shi hawayen yake zubarwa

Nan ya shiga bubbuga bayana a hankali ya shiga magana ya isa haka kinji ya isa insha
Allah bazan kara bari
Wani ya cutar min dake
Ba qaunah

Ashe jinkirin tafiyar da muka samu
Alkhairine tunda gashi
Allah ya nuna min
Azzalumin dake shirin
Cutar,min dake

Mena musu ne?
Mena tsare musu?
Suna yan,uwana
Kullum burinsu su ga sun
Muzguna min
Hajjo mahaifiyata ce in
Ita tamin nayi
Shiru a matsayinta na
Uwa sufa?

Duk cin Mutumcin da suke miki
Bai ishe su ba har sai abin
Ya tsallako kan mutumcin
Ki bazan jureba akan
Hakan dole indau mataki

Nagaji dayin shirun da
Nake ina kallon su bansan
Me sukeson maidani ba

Magana yake
Muryar shi tana rawa
Alamar shima kukan
Yake saukar dumin hawayenshi naji
Akan bayana inda ya
Kifa kanshi

Duk da kukan dana ke
Saina ji tausayin sa yakamani duk
Wannan halin daya shiga
Akaina ne tabbas
Ahmad duk abin da ake
Ni kaina nasan yasani
Yasan irin rashin kunyar
Da suke min da matsin
Da mahaifiyarsa take
Min shin dayasan cewa d`an,ladi ba yau yafara nemana bafa?

Nan na ya daga ni cikin son yamikar dani inda nakasa taka kafar tawa dan bakaramin dauri d`an ladi
Yamata ba

Fashewa na karayi da kuka
Cikin tsananin azabar dana
Kejin ta ratsani nace
Bazan iya ajiye kafar
Ba

Ya kalleni cikin
Tsanananin tausayawa ya daukeni
Ya dora bakin gadon
Ya tsugunna ya kama
Kafar tawa yana dan
Matsawa ahankali

Sannu kinji qaunah
Yanzu bada ban allah
Ya dawo dani ba shikenan
Haka za a cutar min
Dake qaunah
Kiyi hakuri kinji.
Insha allah bazan kara yin nesa dake ba
Bare wani yayi yunkurin cutar min dake

Tunda yafara magana daga shigowar shi har
Zuwa lokacin ban iya
Bude bakina nayi magana ba
Saboda muryata da ta
Dashe ga kukan da nake
Daya hanani magana

Cikin dashewar murya
Nace kadai na bani hakuri
Ba laifinka bane daka tafi ai dole ka nemomana abinda zamuci
Wannan abinda ya faru
Ai kaikanka bakayi tunaninsa ba bansan
Mena yiwa d`an,ladi har haka ba ko bai duba matsayina na matarka ba yakamata ya
Duba zumuncin dake
Tsakaninmu
Nidin k`anwar shice ta wannan bangaren
Na kasa karasa maganar saboda wani kuka danaji ya tahomin

Ya tashi daga tsugunnon daya yayi gaba na yadawo kan gadon ya jawoni jikinsa ya isa ya isa kiyi shiru insha allah
Saina dau mataki akan
Abin da ya miki

Kuma yazama dole inbar wannan gidan nagaji da
Abubuwan da suke faruwa

In muka bar gidannan ina zamuje yanzu ?

Gwara inkamamiki haya
Kafin allah ya horemin insamu ingina nawa na
Kaina kiyi hakuri kinji

To wai baki rufe kofar bane kika kwanta ko kuma yaya?

Na rufe k`ofar wallahi bansan tayaya akai
Ya shigo ba amma
Kafin inkwanta
Tabbas naji ana taba kofar amma dana yi
Magana sai naji shiru
Andaina bansani ba ko
Taya ya bude ya shigo ba
Dan kwanakima ya shigo
Min to ranar bansan ma
Shine ba ya gudu dana yi ihu
Ranar na manta ne ban rufe kofa ba
To bayan ankwana biyu
Ma ya balle sakatar net
Dina ya shigo aranar shine na yan keshi da wuka
Washe gari shine na gane shine

To daya san nagane shi shine yazo har dakinnan
Ya dinga zagina akan sai ya cika burinshi a kaina
Sai ya illata ni ban dauki.
Maganar shi ba ina
Tunanin duka borin
Kunya ne amma dai na kunna recording din
Wayata dan watarana
Ashe shi yana nan bai manta ba

Cikin sauri ahmad ya ture kaina daga cinyar shi
Wai duk wadannan abubuwan sun faru
Amma kika kasa fadamin
Indau mataki cikin
Fushi yake maganar
Alamar abin ya mai ciwo

Na kalle shi cikin kukan
Daya dawo min
Ina tsoron in fito in
Fadamaka ka kasa yarda
Tunda koba komai
`Dan uwanka ne
Kuma in hajjo taji
Ita caza tai sharri nake
Mai tunda babu wanda nake da shi shaidar hakan

Da sauri ya d`aga min hannu kinga wannan ba
Hujja bace yanzu da ba dan

Allah yasa andaga tafiyar nan tamu ba saboda rasuwar da mahaifiyar oganmu tayi ba da haka
Zai cutar dake
Babu wani wanda zai kawo miki dauki
Kinga kenan shirunki
Baiyi amfaniba

Kidaina irin wannan abu irin wannan ba a boye shi
Da kinfito kin fad`amin
Tun farko da ba akai
Ga hakaba tunda
Kince lokacin da yazo
Yana miki warning kinyi
recoding din maganar shi
Dole hajjo zata yarda
Tunda za a ji muryar shi

Yanzu ina wayar taki?

Gata can a kan madubi

Nan ya tashi ya dauko wayar tawa
Ya bude ta nan ya shiga
Ya mikomin kunna min
Inji

Na kunna masa na bashi saiga maganganun d`an ladi tiryan tiryan har zuwa lokacin dana yanke
recoding din
Chapter 43 · 0% Book details