← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 78

Sashe 47

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta karaso waje na cikin sauri sannu aminatu
Sannu kinji
Zaki haihu lafiya lau
Sannu
Binta nashiga yi da
Kallo cikin tsananin mamaki ni hajjo kewa sannu dan ciwon dana
Keji ya lafa bana jinshi .
Yanzu nidai ban iya
Cemata komai ba
Har ahmad ya fito ya
Kulle kofar
Hannun shi rike da
Jakar

A a meye ka dauka a jaka
Kuma ? Ta tambayeshi

Kayan daza a bukata ne a asibitin dole ai sai
Munje dasu .mugani dame dame ne ne ciki
Ya mika mata nan
Ta bude a A lokacin
Ne kuma marata ta ta karta kafafuwa na suka.
Rike na durkushe a wajen ina murkususu

Ahmad ne yayo kaina da sauri
Ya kalli hajjo dake bincika jakar tana cewa
a a kuce har kunyi siyayyar ku bansani ba

Ahmad yace hajjo zoki kamata kinga abin data ke bawan allah duk ya rude da sauri ta karaso
To,to kamata zakai ai
Mu tafi daurewa ake.
Dan haka tayi dauriya
Allah na tuba inba ku
Yaran zamani ba
Ai mu a gida muke
Haihuwar mu lafiya
Lau da zaka bi ta tawa
Ma ai bawani asibiti da za a kaita
Bare su ciwa mutane
Kudi ka kamata mu
Kaita daki kawai na amshi haihuwar tunda
Mu ma dai haihuwar ba yau muka fara ta ba

Ta karashe maganar cikin son ya yarda shiyasa ta faro daga farko
Kamar zata bashi shawara ta kare da ya
Kamata a kaita dakin
Tunaninta in har ita ta
Amshi haihuwar a gida yazo cikin
Sauki saita cika.
Burinta salin alin
Zata matse yaron ta
Hana shi kuka kafin
Uwar ta farfado ita
Kuma uwar bazata wani taimaka mata ba harsaita ga ta galabaita
Yadda ko anje asibitin
Ma zaiyi wuya ta rayu
Ta sani sarai ba ason
Haihuwar gida yanzu saboda zamani ya canza

Ahmad yace a a hajjo
Gwara dai asibitin yafi
Saboda can din sunfi
Sanin yadda za akula
Da mutum kuma
Koda wata matsala suna
Sani suna kokari wajen
Ganin sun maganceta
Gwara muje can din

To dan ubanka ni zaka
Fadawa wani sanin haihuwa da yadda za a amsheta ninace gida zata
Haihu inkuma kai
Ka haifi kanka bismillah
Ka dauketa ka kaita asibitin mugani

Duk maganganun da
Suke ina jinsu sama sama
Saboda ciwon daya turnike ni na fahimci
Suna jayayya ne akan
Kaini asibiti
Na rike hannu ahmad
Da dama ajikin shi
Nake kwance da kyar na
Bude bakina wanda nasan shi kadai ne zaiji
Please kukaini asibiti
Dan allah kaji

Hajjo dai na tsaye dan bata san ina masa
Magana ba dan a d'an gefe take ta kasa ta
Tsare tana jiran ya kaini
Daki ta amshi haihuwa

Hajjo ba maganar bin
Maganar kiba ce bazanyi
Ba abin danake so kigane ba a wannan yanzu asibitin yafi

Nace kamin shiru ka
Kamata ka kaita daki

Amma..

Da sauri ta daga masa hannu banason wani iyayinka da surutu
Nace nice nan zan amshi
Haihuwar jikana da kaina
Bawani asibiti ehee

Duk yadda ahmad yaso fahimtar da hajjo amma
Ina fir taki fahimtar shi
Akan dole ya kamani
Yabi umarninta ya bude
Dakin ya kaini ya jinginar dani
Jikin kujera

Ya nemi waje ya zauna
Hajjo ta karaso ai ba zama
Zakayi kasani gaba ba
Fita zaka yi kabamu waje

Haka ya tashi ya fita ya tsaya bakin kofa bawan allah sai zuwa yake da dawowa

Tunda ahmad ya fita juyi kawai nake hajjo dake kan
Kujera hankalinta
Kwance ko taba ni bata yiba
Anjima kadan dai
Zata ce sannu kinji
Snnu bi ahankali tana daga zaune ko tabani
Bata yi ba ita sannun dan ahmad dake bakin kofa ne yaji

Shi dai ba a son ranshi ba hajjo ta hana akaini
Asibiti sam amma baisan yadda zai yi da
Ita ba

Haka har akayi sallar ishsha,i amma shiru sai azabar ciwo dana ke sha
Ni kad'ai nake juyi.
Hajjo na zaune abinta
Ita addu,a ma take allah
Yasa karna haihu na
Mutu ma gaba daya a huta dani da d'an

Abu kamar wasa har karfe sha biyu shiru
Shigowar baba hajjo na dakin mu

Ahmad ne daya ji shigowar baba ya karasa ya
Amshi laidar hannun shi
Suka karasa kofar
Dakin hajjon yana tambayar shi
Lafiya har yanzu baiyi.
Barci ba
Nan ya fada masa abun
Daya faru

Wannan ai shashanci ne yarinya na cikin ciwo tun
Magriba har yanzu kace
Tace karku kuje asibiti
Ina ita hajjo kira min
Ita ka shirya matarka
Ku wuce asibiti me
Zata iya mata a gida
Maza kaje kuwuce bari
Na kira Alhaji baba

Alhaji baba makocin mu ne dan

Dan Allah ya taimaka mana
Da motar shi tunda dare yayi yanzu a wuce a sibitin

Nan ahmad yazo ya shigo lokacin jikina gaba daya yayi laushi ni kadai nasan halin dana ke
Ciki hajjo na zaune
Saika rantse wani abun take tsinanamin .

Ahmad yace hajjo baba
Ya dawo yana kiranki

Baka cemai matarka ke
Nakuda ba nake tare da
Ita

Na fadamai yace dai inkiraki nan ta tashi to bari naje naji kiran na dawo

Hajjo na fita da sauri ahmad ya karaso wajena ya kamani sannu kinji sannu ya tashi ya kara dauko min wani zanin
Ya taimakamin na daura
Yasamin hijabi tashi
Mu tafi nayi magana
Da baba asitibi zamu
Wuce ganin na kasa
Ta shi yasa ya kamani
Ya dagani da kyar nake
Takawa muka nufi waje
Ya kulle kofar muka yi kofar dakin
Hajjo

Tana shiga ta tarar dashi yana waya akan dan
Allah alhaji baba ya
Taimaka mana da mota
Inda yace ba matsala
Mu fito
Ya sauke wayar yana
Binta da kallo
Ita tayi saurin magana
Motar me kuma kake
Cewa a taimaka mana da
Ita
Ya kalleta aminatu za a kai asibiti
Au ahmad d'in cemaka yayi nakasa amsar haihuwar ne da har sai anwani je asibiti

Ya kalleta haba mero meyasa kike hakane
Taya ya zaki ce ke zaki
Amshi haihuwa?

Zata yi magana yace kibari kawai a wuce asibiti da yarinya

To shikenan ai sai a wuce asibitin tunda ni kun raina kokarina
Ta karasa fadar tana mai neman waje ta zauna dai,dai lokacin mun iso kofar dakin nata

Babane ya lek'o ahmad kufita kofar gidan alhaji baba ya fito da motar

Yace to baba nan muka nufi Kofar cikin takawa a
Hankali mun tarda motar
Mutumin yana tsaye bakin motar nan ya bude mana ahmad ya zaunar dani a hankali zai zauna kenan

Sai muka ga hajjo ta
Fito da ita da maman aisha kowa ya taso ta ita kuma naji dai hajjo na
Fadin ta koma basai ta
Biyo mu ba
Amma tayi mirsisi ta karaso bakin motar
Inda dole ahmad ya koma
Gaba shida alhajin
Ni kuma hajjo da maman aisha suka sani a tsakiya

Muka nufi asibiti maman
Aisha ke ta min sannu
Har muka isa

Muna zuwa akayi labour room dani inda ga mata nan birjik nan aka shigar dani wani daki mace daya ce a gefe na ta na kwance kamar ba nakuda take ba

Likitar da zata dubani tace na kwanta na kwanta tace na zare pant din jikina na cire shi da kyar ta bude kafafuna
Ina ji ta zurmuk'a min hannu wata azaba ta ratsani ta ciro hannun tace na sakko
Na sakko

Biyoni na bita muka fito
Ta kalli su hajjo gaskiya da alamar ta dan dad'e cikin nakudar amma dai har yanzu da sauran lokaci sai zuwa 5am zata haihu dan haka zamu bata gado

Hajjo ce tayi caraf wajen cewa a a dai gwara mu koma gida gaskiya danni
Banyarda da kwanan asibitinnan ba in biyar din ta kusa dai ma dawo
Babu yadda ba ai da hajjo ba akan gwara mu tsaya amma ta tubure sam bata san wannan ba
Sai dai mu koma gida

Haka muka juyo gida duk
Irin azabar dana keji.
Muna dawowa muka shiga daki hajjo da
Maman aisha suka wuce
Dakunan su suka kwantawarsu
Ahmad ne keta faman yimin sannu ya rasa yaya zaiyi baba ma yazo bakin
Kofar tamu dan hajjo ta fadamai wai sunce ba yanzu zan haihuba shiyasa tace mudawo

Yamata fada akan meyasa zata ce mudawo
Inda itama ta hayayyak'o mai dole tasa yayi shiru

Nan yace ahmad yamin ya jiki me yasa ka biyemata kuka dawo
Aida itan andawo da ita
Kai saika zauna da aminatun amma bari ajima din inyaso sai a koma

Wasa wasa har zuwa 4,30am ban haihuba dole tasa muka koma asibitin
Nan ma suka kara dubani suka ce har yanzu kan
'Dan bai tahoba
Nan alhaji baba wanda shi ya kuma kawomu yana da karamci mutumin sosai

Yabada shawarar mu koma gida kawai a kwai
Wata babbar likita dake
Bayan layin mu yasan ta na gida yau muje saita zo har gida kawai ta dubani in takama mu kara dawowa asibitin saimu dawo

Munkoma gida ankirata nan tazo da kayan aikinta ta dubani tace haihuwar tana kusa insha allah ta fara tabo kan yaron nan maman aisha da mutanen gida suka zo suka cika dakin saika ce hauka

Likitar ta,kallesu kudan bamu waje dan allah
Haka dai aka samu suka
Fita hajjo tazo ita lallai saita shigo dan taji takaici daba ita bace zata amshi haihuwar ba
Tasan zaimata wuya burinta ya cika a yanzu
Ita ma kuma likitar tace basai ta zauna ba
Ta fita

Haka likitar keta fama dani harta nishin da zanyi ita ta dinga koyamin cikin lallashi .
Gashi ta hanani hade kafafuna ta rike su
Haka mukaita fama da dai taji shiru sai ta dauramin ruwan nakuda ko minti biyu ban cika ba da fara shigar ruwan jikina wani irin ciwo ya taso min wanda duk da banji irin shiba
Inda na dinga wani irin nishi karfe dayan rana
Dai,dai allah yasauke ni lafiya na haifi baby boy dina inda aunty hajiya sunan likitar ta shiga gyara babyn lokacin ne kuma wani ciwon ya taso min ita ta taimakamin har mahaifa ta fado

Har lokacin su hajjo na bakin kofar lokacin da hajjo ta ji kukan jaririn bakarin min faduwa gabanta yayi ba shikenan dai ankara nasara akan ta ta nufo kofar zata shigo amma ta jita a rufe dan aunty hajiya ta kulleta daga ciki
Chapter 47 · 0% Book details