← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 78

Sashe 29

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko minti goma banyi da ajiye wayarba naji hayaniyar yara ana murnar dawowarshi wajen hajjo ya fara sauka

Inda yana shiga ya tarda ta zaune ita da salaha sai kuma hauwa akusa da ita kallo daya yayiwa hauwa ya dauke kai ya shiga gaida hajjo salaha dake gefe ta gaidashi ya amsa mata yana mai fara,a danshi mutumne mai son yan uwanshi har ya tashi zai tafi hajjo tace

A a yaukuma da wuri zaka tafi babu dan zamanma daka saba inkadawo muyi firar yaushe gamo sannan bakaga hauwa bane

Ya juyo ya kalleta hajjo na kwaso gajiya ne da yawa ina bukatar wanka inhuta yanzu in anjima zanzo sannan ita hauwar ai ina tunanin ita,yakamata tafara gaidani tunda taganni koba komai sama nake da ita

Eh yau zaka cemin ka kwaso gajiya mana inace da inka dawo komin gajiyar da ke jikinka,nan kake zama saimun gama fira kake tafiya amma yanzu ka nunamin ban isaba kenan hankalinka nacan wani waje bayan

Ita kanta hauwar da kake cewa bata gaida kaba saboda kai tazo aikasan bada ban kaiba dai bazaka ganta anan ba yarinyar kirki harda abinci tayoma ta kawo maka amma ka kulatama yazama aiki

Ya juyo ya dawo ya zauna bayason fitinar hajjo amma maganar ya dinga zama inyadawo daga tafiya adakintama aibata tasoba tunda yanzu ba da bane yanada aure kuma yanada tabbacin aminatu taji shigowarshi tayaya zai zauna yanason kasancewa da iyalinshi hajjo nason tareshi

Sai lokacin hauwa cikin karya murya ta shiga magana ita lallai sai ta burgeshi yaya ahmad ina wuni

Ko kallon inda take baiyi
Ba yace lafiya
.
Ya aikin? fatan kadawo
Lfy?

Bai kara magana ba
Ya bawa banza ajiyar
Ta a rayuwr shi ya tsani
Mace mara aji da
Kamun kai kuma
Ya fuskanci inma akwai
Abin daya fi hakan hauwa duk ta tarasu
Yarinyar sam bata da
Nutsuwa

Nan ya zauna tashiga masa surutai duk dan taja hankalinsa karya tashi ya tafi wajena nan su shamsu da umar da sani suka fado dakin suma suka zauna aka shiga fira tun bayasa baki har ya fara sa baki tunda yaran sukazo nan suka fara mai lissafin bukatunsu yana sauraronsu dan sun riga sun saba indai yayi tafiya yana sauka za afara amsar kudi a hannunsa amma yau dasuka gama sai cayayi duk su bari ya huta zai duba nan suka tambayeshi tsarabarsu nan ma yace sai ya kunce kaya dan yana dawowa adakin hajjo da yake kuncewa

Ina can ina zuba idon shigowarshi tun ina irga mintuna har aka share awa daya da yan mintuna tukun can wajen biyar da rabi saigashi salaha ta shigo da jakarshi da kuma wata jakar daban ta kalleni dama sallama bata dameta ba tace yaya ahmad yace inkawo nace to can harta juya saikuma ta juya wallahi kinyi kyau yaya ahmad kikayiwa kwalliya ko?

Na kalleta dannasan bawata kunyace da itaba shiyasa bana sakarmata na dauke kai nace kije abinki mana

Ta tabe baki danma nace kinyi kyau

Nan dai ta fita na tashi na gyarawa jakar zama na dauke basket din da hauwa ta kawo dan naci alwashin bazan taba bari yaciba dan bansan masifar data hado cikin abincin ba na fita dashi na kaishi can bayan robobin ruwana dake
Waje na aje

Sallamar ahmad na ji nayi saurin dagowa ya tsaya bakin kofa yana karemin kallo nima kallon na shi na shiga yi
Ganin ya kara wani kyau
Da cika duk da
Tafiyar da suka sha
Amma jikinsa fes
Sai yar kurar hanya da baza a rasa ba

Ganin na tsaya ya budemin hannayenshi
Da sauri na karasa
Na rungumeshi
Yasa hannayen sa ya
Rufe yana mai da da,
kankameni yana mai sauke wata sassanyar ajiyar zuciya ya matseni a jikinshi kamar zai ballani ya yana mai tura kanshi cikin wuyana yana bina yana shinshina yanata sakin numfarfashi wanda nima shinake saukewa da kyar cikin shakakkiyar murya ya fusgo kalmar I miss you qaunah ta ya kare fadar yana mai dago kaina jone bakina da nashi ya shiga sakarmin wani rikitaccen kiss kafafuwanmu rawa kawai suke bansan lokacin da nima na zura hannuna ba cikin gashin kanshi ina ya mutsawa ba ganin zamu fadi yasa yayi saurin daukata ya daura akan kujerar dake gefenmu ya bini cikn sauri yacigaba da ya mutsani ji mukai anshigo ko sallama babu

Ahmad yayi saurin dagani nima natashi da sauri ina gyara rigata dan har ya zuge min zip din na dau dan kwalina na daura ina kai kallona ga wadda ta shigo din bawata bace hauwa ce

Ahmad yayi kokarin dai dai ta kansa muna jiran muji me zatace

Takalleshi tana kokarin zama kusa dashi tunda kujerar mai uku ce
Wata tsawa daya daka mata nikaina saida na tsorata

Keee baki da hankaline me kike haka? Ke meyasa sam baki da
Kamun kaine
Shin baki iya sallama
Bane ko kuma duk
Tarbiyar ce taki
Haka

Da sauri naga taja baya amma kuma ko gizau batayiba kamar ba ita yayiwa tsawar ba

Sai kashe murya danaga tayi ta fara fari da ido sorry my Dear dama na zone in zubama abincin da nayi maka dan nasan kana sonta shiyasa namaka ta kare tana mai kai kallonta ga inda ta aje abincin

Nace miki ina bukatar hakanne ko kuwa
Bani da matar da zata
Min ?

Nidai ina zaune ina kallon ikon allah ji wani karfin hali da rashin ta ido mace da mijinta kizo kice kinzo bashi abinci har yana miki miki wulakanci kina nuna ko ajikinki ikon allah

Nan naga ta shiga dube dube bataga ko alamar basket dinba ganin hakan yasa ta dago tana kallona nidashi da muka zuba mata ido muga iya gudun ruwanta da haukarta

Nice na tashi na je na shimfida daddumar da muke cin abinci na dauki kayan abincin wajen hajjo na kai wajen tukun na kalleshi nace wanka ya kamata ka fara kafin komai ko

Yace eh fara zubamin ruwan wanka tana tsaye bakin kofa har zuwa lokacin sai dai tacika tayi fam kamar zata fashe na rabeta na wuce da ruwan zafi a hannuna wanda dama nariga dana jona naje na juye na hadamai ruwan wankan tunanina ko zata bamu waje dataji zai shiga wanka sainaga ta nemi waje ta zauna a dayar kujerar

Ganin haka ahmad ya tafi wankan da kayan jikinshi na dauki jallabiyar shi da kajeran wandonshi da towel din da zai goge jikinshi na bashi dan naga bata da alamar fita zatai ba

Bayan ya tafi Sai naga ta ta nemi wajen zama
Haka muka zauna nida ita can ta kasa daurewa

Ina kika kai abincin da na kawo masa inna kulata to bangon dakin ya kulata

Dataga bance komai ba sai tayi shiru amma fa bata motsa ba har ya fito ya zo nasamana abinci muka ci har akai magrib muna zaune da ita a dakin bata ga fuska ba sam a wajen ahmad dan ya hade ranshine dalilin dayasa bai mata magana bama saboda karta hadashi da hajjo bayason wani kayan bacin rai yanzu yasan dai bazata kwana nan ba dole zata tafi..

Bata tafi ba har wajen karfe tara na dare a gabanta ahmad yaje masallacin magrib wanda bai dawoba saida akai ishsha,i tunaninshi zata tafi zuwa lokacin amma nan ya tarda ta ya kalleta cikin takaici ke sai yaushe zaki tafi

Tace ba yanzuba sai anjima zantafi da dai yaga rashin hankalin nata yayi yawa wajen 9 yace mata zamu kwanta munason rufe kofa shima saida ta jima tukun ta tashi ta fita

Saita aiko umar wai a amso mata basket din abincin wanda nasan shakkar idon ahmad ya hanata maganarshi a wajen na tashi dama a waje na ajiyeshi can bayan robobin ruwana na dauka na danka ma umar

Adaran ranar nasan lallai nikaina danake karyatawa cewa nayi kewar mijina tabbas nayi mun faranta ran junanmu sosai inda ahmad ya zamamemin kamar mayunwacin zaki duk da gajiyar danayi hakan baisa na nuna masa gajiyawata ba

Da safe ya rarraba tsarabar da yazo da ita inda ya ware tasu hajjo data kannenshi sai yaran gida daya rabawa sweet nima yayomin tsaraba ba laifi inda hajjo ta raina tata acewarta ba haka yasaba kawowaba nan dai naga yazo ya diba nawa ya tafi nasan kara mata zaiyi tunda agabana ta fadamasa yace inyi hkuri nace bakomai

Fadime wallahi kindaiga abincin ko tabashi ba aiba duk irin kudaden da muka kashe hauwa da ke zaune dakin fadime ke fadar haka

Fadimen na kusa da ita ta leka abincin tabbas kam amma ke ya akai baki san yadda kikai yaciba

Haba fadime harfa dakin matarshi nakai abincin amma yar marasa mutumcinnan ko bari yaga abincin batayiba wallahi ina kallo yagama cin abincinsa harfa zama nayi dakin duk dan ingani kozata fito dashi shiru gashi ina shakkar ahmad din wallahi ko magana kasawa nayi kamar an rufemin baki

Fadime ta kalleta cikin takaici to ita hajjo din tana ina duk akai hakan?

Tana can wajenta mana bama tasan baiciba koda zan tafi ko sallama banmata ba abin da ya hanani fadamata kuma dan karta zargi wani abu tace ko zamu cutar dashine tunda dai nasan na sa mata kwalaben a cikin fulullukanta nasan bazata gaza kwanciya kan daya ba dan bansan a wanne take kwana ba
Gwara daya baki guda
Ukun na tabbatar yau bazai samu komai ba

Fadime ta kyalkyale da dariya
Ai boka ya tabbatarmin muddin ta kwanta a kai to shikenan jini zai ballemata mai masifar wari wanda ko kusa da ita ahmad din bazai iya kwanciya ba kuma ya tabbatarmin bazata warkeba kinga kenan dole hajjo ta tada maganar auren nan dan naga sai wani sanyi sanyi take danni gaskiya na kagu ayi aurennan inhuta inji da zainab daje gabana

Fadime nikaina inason
Yin auren dan ahmad shine irin mijin danake da burin aure kiduba duk maneman nawafa sun watse kowa kace aure ya tsere bazan bari wannan damar ta kubcemin ba
Chapter 29 · 0% Book details