← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 78

Sashe 41

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta duba jikinta babu sutura sai lokacin abin da ya faru ya dawo mata nan ta fashe dawani razanannan kuka kukan ta shiya tasheshi nan yashiga tambayarta lafiya takemai kuka nan tashiga antayamai allah ya isa ta na tsinemai abarka ganin zata taramai jama a kuma ihun datake mahaifanshi zasu iyaji yasa yashiga lallashinta tare da alkawarurruka masu yawa ciki harda alkawarin aurenta

Anan takai kallonta ga agogon dakin shabiyu sauran minti goma ta kara rushemai da kukan ya maida ta gida inda yace tabari da safe ya maida ta nan ta tuburemai akan ita,lallai ya,maidata dan tasan tabbas babansu yadade da dawowa kuma sai ya duba makwancinsu kafin ya kwanta duk da yau ba dakin mamanta yake ba amma tana cikin fargaba tasan intayiwa mama karyar gidansu kawarta datace mata zataje taraka biki tsaf zata yarda inta ce amarya suka kai suka rasa motar dawowa

Nan dai dataga baya da niyar kaita ta yunkura zata tashi ta ji wata azaba ta ratsa ta ta fashe da kuka haka ya dauketa yakaita bayi taimaka mata ta gasa jikinta da kyau yadda zata iya takawa ya ta fito ta maida kayanta tace ita lallai ya maidata gida

Haka ya fito da mota ya maidata inda yasauketa nesa da gidansu ta karasa kofar gidan cikin dingishi tasan yanzu sun rufe gida batama tsaya bugawa ba ta yanke shawarar kiran mamanta a waya nan ta kirata ita ma data kasa barci cikin fargabar kar mahaifinsu ya tambayeta salima da sauri ta rarumi wayar tayi kasa da murya duk da tasan bakowa a dakin hello salima ina kofar gida kizo ki budemin kofa shine abin datace kawai ta yanke wayar cikin tsoron layin nasu taciga da kallon bayanta dan unguwar tasu an dauke wutar nepa bakikkirin take

Sadaf sadaf tazo ta bude kofar a hankali dan kar mazan da dakinsu ke bakin kofar suji allah yataimaka babu wnda yaji tayi saurin shigowa da ledojin siyayyar a hannunta tana dingishi

Uwar tayi saurin amsa ledojin wuce muje ta rufe gidan duk maganar da suke ahankali suke

Nan ta wuce gaba tana binta a baya danta tsaya rufe kofar nan taga tana tafiya tana dingishi nan gbanta ya fadi tayi saurin jan hannun ta daki ke lafiya me yasameki?

Nam tashiga bata labarin data shirya inda tace suna tafiyane wani kare ya biyosu da kyar suka sha sai sannan hankalin uwr ya kwanta ta jawo ledojin batare da la akari da karyar data shata mata ba taya kare ya biyosu harta fadi kuma ledojin hannunta suka tsaya a ina ma tasamu ita da suka kai amarya ina babu ruwanta burinta ta cika cikinta

Tunda ga ranar faisal yaciga a yaudararta yake biyawa kanshi bukatarsa tare da mata karyar shi zai aureta harta fadamai tana da ciki yaso a zubar taki shikwa ganin meye damuwarshi yabarta da abinta inda da zainabu ta gano hankalinta ya tashi taso a zubar itakwa salima taki dan tanaganin cikin shi zaisa faisal ya aureta kuma sannan tana tsoron mutuwa

_Wannan shine abin daya faru_

Firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data tafi jin an daka mata tsawa
Wai bake nake tambaya ba kikasani gaba kika yi shiru

Cikin kuka take sanar mai faisal ne

Tabbas yasan faisal dan gidan alhaji ibrahim dake nan bayan layinsu yaro mara tarbiya dajin magana wanda iyayenshi suke bashi daurin gndin duk iskancin daya ke

*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE_*✍️
09/11/2022, 2:22 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

_*PAID PAGE 24*_

Nariga dana rintse idanuna kawai ina jiran naji ya aiwatar da mummunan kudirinsa

Sai jinayi ya fasa wani irin ihu da sauri na bude idanuna nakai kallona gareshi saina ganshi a can gefe ya dafe kanshi jini ne ke zuba

Da sauri na kai kallona gaba na nan naga ahmad ne rike da katako ya yarda katakon yayi kanshi ya yafinciko shi nan yashiga kai masa duka ta ko ina yana kai mai naushi

Shikuma ya kasa kare kansa bare ya rama tuni ya hada mai jini da majina tun yana dukan shi a daki har ya jawo shi filin tsakar gida

Amanata zaka ci dan ladi ina dan uwanka mutumcin auren nawa kake kokarin ketawa abun da kake aikatawa a waje shine karasa inda zaka aikata sai akan mata ta

Fada yakecikin daga murya shi kuma dan ladi ihu kawai yake da naiman dauki kiran sunan hajjo kawai yake akan ta zo ta ceceshi

Dan zuwa lokacin ya fara dawowa hayyacinsa dan duka ahmad yake mai bana wasa ba

Hayaniyar muryar ahmad ce da ihun dan ladi tasa mutanen gida fara fitowa dan lokacin bawani dare ne yayi haka ba duka duka 11,05pm

Hajjo data ke jin murya kamar ta ahmad yana magana sai kuma ihun dan ladi daya karade gidan da yake kiran sunanta

Ta taso da sauri zani a hannu ta nufo lungun mu data ke jin hayaniyar mutane wanda zuwa lokacin mazan gidan ke kokarin amsar dan ladi amma ahmad ya hana haka naushi kawai yake kaimai ta ko,ina

Matan gidan kowacce ta tsaya sunyi cirko cirko cikin tsananin mamaki dan zuwa lokacin sun fahimci abin da yake faruwa

Cikin mutanen ta keto ta shigo ganin anata kokarin amsar dan ladin amma ahmad yaki sakin sa

Yasa ta karasa cikin tsananin tashin hankali ta shiga kaiwa ahmad duka dan ubanka sake shi kashe shi kakeson yi

Kokari take ahmad kawai ahmad yasaki dan ladin inda ta dinga antaya mai zagi tana dukanshi

Wallahi inbaka sake shi ba saina tsinema albarka dan iskan yaro me ya maka haka kake kokarin kashe shi yana dan uwanka

Jin furucin hajjo ne yasa ahmad sakin dan ladi ya fadi rajab a wajen yana mai dafe kanshi da hannayen shi biyu hawaye na zuba a idon shi cikin kunar rai

Dan ladi da hajjo ta samu ta kwata a hannun ahmad da yagama fita a hayyacinsa gaba daya jinine kawai yake fita ta bakinsa da hancinsa ga kanshi inda ya buga masa katako shima yana zubar da jini idanunsa lumshewa kawai suke jikinsa yasaki gaba daya

Da sauri hajjo tayi kanshi tana mai tallafo shi cikin tashin hankali fa ihun kuka kutaimakamin dan allah dan ladiii ta fasa ihu

Mutane duk sun tsaya anrasa wanda zai taba dan ladin sai mijin yawo jummai da yayi kokari ya kama ahmad ya mikar dashi yaja shi gefe

Da sauri ahmad ya fincike hannun sa tunawa da halin daya bar aminatu a ciki a daddaure yayi dakin da gudu

Tun daga lokacin da ahmad ya bugawa dan ladi katako a kai wani farin ciki ya kamani ganin allah bai bashi ikon ketamin haddiba

Ya kawomin taimako duk da na shiga mamakin meya dawo da ahmad bayan munyi sallama ya tafi wajen awanni biyu kenan nan nashiga godiya ga allah

Duk abun dake faruwa a kofar dakin inajin su da irin dukan da yake mai da taruwar mutanen gida da zuwan da hajjo tayi tana ihun zai kashe mata da

Nidai ina kwance dan babu ta yadda za ai in kunce kaina duka hannayena a daure suke ga cikina inda na fada kanshi yana min wani irin ciwo ga bakina da ke fidda jini sakamakon marin da dan ladi yamin jikina duka wani irin ciwo yake min
Ta ko ina

Da sauri ahmad ya shigo daki cikin sauri ya fara daukar zanina ya yafamin dan wandonne kawai a jikina dan kafin ya cire shine allah ya kawo ahmad

Nan ya shiga kuncemin daurin daya min yana gama kunce wa da sauri na fada jikinshi na fashe da kuka

Kankame ni yayi ya runtse idanun sa shi kanshi duk dauriyar shi hawayen yake zubarwa

Nan ya shiga bubbuga bayana a hankali ya shiga magana ya isa haka kinji ya isa insha
Allah bazan kara bari
Wani ya cutar min dake
Ba qaunah

Ashe jinkirin tafiyar da muka samu
Alkhairine tunda gashi
Allah ya nuna min
Azzalumin dake shirin
Cutar,min dake

Mena musu ne?
Mena tsare musu?
Suna yan,uwana
Kullum burinsu su ga sun
Muzguna min
Hajjo mahaifiyata ce in
Ita tamin nayi
Shiru a matsayinta na
Uwa sufa?

Duk cin Mutumcin da suke miki
Bai ishe su ba har sai abin
Ya tsallako kan mutumcin
Ki bazan jureba akan
Hakan dole indau mataki

Nagaji dayin shirun da
Nake ina kallon su bansan
Me sukeson maidani ba

Magana yake
Muryar shi tana rawa
Alamar shima kukan
Yake saukar dumin hawayenshi naji
Akan bayana inda ya
Kifa kanshi

Duk da kukan dana ke
Saina ji tausayin sa yakamani duk
Wannan halin daya shiga
Akaina ne tabbas
Ahmad duk abin da ake
Ni kaina nasan yasani
Yasan irin rashin kunyar
Da suke min da matsin
Da mahaifiyarsa take
Min shin dayasan cewa dan ladi ba yau yafara nemana bafa?

Nan na ya dago da kaina ya daga ni yamikar dani inda nakasa taka kafar tawa dan bakaramin dauri dan ladi
Yamata ba

Fashewa na karayi da kuka
Cikin tsananin azabar dana
Kejin ta ratsani nace
Bazan iya ajiye kafar
Ba

Ya kalleni cikin
Tsanananin tausayawa ya daukeni
Ya dora bakin gadon
Ya tsugunna ya kama
Kafar tawa yana dan
Matsawa ahankali

Sannu kinji qaunah
Yanzu bada ban allah
Ya dawo dani ba shikenan
Haka za a cutar min
Dake qaunah
Kiyi hakuri kinji.
Insha allah bazan kara yin nesa dake ba
Bare wani yayi yunkurin cutar min dake

Tunda yafara magana daga shigowar shi har
Zuwa lokacin ban iya
Bude bakina nayi magana ba
Saboda muryata da ta
Dashe ga kukan da nake
Daya hanani magana

Cikin dashewar murya
Nace kadai na bani hakuri
Ba laifinka bane daka tafi ai dole ka nemomana abinda zamuci
Wannan abinda ya faru
Ai kaikanka bakayi tunaninsa ba bansan
Mena yiwa dan ladi har haka ba ko bai duba matsayina na matarka ba yakamata ya
Duba zumuncin dake
Tsakaninmu
Nidin kanwar shice ta wannan bangaren
Na kasa karasa maganar saboda wani kuka danaji ya tahomin
Chapter 41 · 0% Book details