Sashe 61
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kinga yaya talatuwa ko nazo ko kar nazo hakan bazai sa inna ta dawo ba inna dai tariga data rasu fatan allah yajikanta haka kawai wallahi saboda rasuwarta bazan ruguza burina ba na tsahon sama da shekara talatin
_*😍MAMAN `DAN ALBARKA CE 😍✍️*_
09/11/2022, 2:23 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*
*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*
*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*
_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_
*_PAID PAGE 35_*
Yanzu mero saboda wani banzan burinki shine bazaki zo rasuwar mahaifiyarki guda ba lallai kinyi nisa bakyajin kira sam
Kome zaki ce yaya nidai ba zuwa zanyi ba daga baya inkomai yayi dai,dai nazo
A a nidin karki kirani da yayarki inda inada matsayin hakan ai bazaki ce bazaki zoba bana tunanin ni inna mutu zan samu darajar da zaki kira waya ma kiyi gaisuwa dan haka daga yau sai yau muddin dai baki zo gaisuwar nan ba wallahi babu ni babu ke ki manta ma da kina da yaya talatuwa
Tunda har zaki iya haka
Yaya ki fahimceni mana....
Kinga babu fahimta tsakaninmu allah ya kyauta kit ta katse wayar
Kallon k`aninta tayi me bimata wanda shine hajjo ke bi tace sale bazata zo bafa yarinyar nan ace inna ta rasu amma mero ta kasa zuwa harni take fadawa bazata zoba
Ki k`yaleta tayi abinda take so sai dai nima na cireta cikin layin yan uwana babu ni babu ita inhar bata zo gaisuwar nan ba
Hajjo su ukune wajen mahaifansu mahaifiyarta Ladi wadda suke kira inna talatuwa ita ce babba sai k`aninta Sale sai kuma mero wato hajjo kenan kasancewar hajjo auta yasa duk soyayyar duniyar nan mahaifiyar su ta tattara ta d`ora akan hajjo wanda har su yan uwan nata ke ganin kamar ba asonsu
Ahaka suka taso har talatuwa tayi aure inda daga baya ita hajjon ta auri wani dake a nan k`auyen nasu na tasawa inda taje ta tarda uwar gidanshi masifarta da shegen kishinta yasa wataran ta kwarawa yar kishiyar ruwan zafi tafashashshe lokacin haihuwarta d`aya mijin yasaketa dan yace bazai iyaba nan ya kwace yarshi wannan shine silar rabuwar ta da mijinta na farko
Tana sauke wayar taja tsaki ni zaku fadawa wani babu ruwanku dani aikin banza da wofi ai ba fina son innar kuke ba harda wani zaki ce inzo haka kawai ina zaman zamana ki janyomin aiki
Koshi ahmad d`in daya ke maganar tafiyar ai saida yarda ta za a yita dai ko ina ce sai inada lafiya hakan zata yiyu
Rashin lafiyar karya ma zan tsira dole innace ban iya zuwa sai an kwana biyu a k`yaleni maganar ta shashance kona je ba dawowa zatai ba
Haka ta cigaba da mitarta
Kamar yadda ta tsara haka ta tsiri rashin lafiyar karya babu yadda ahmad baiyi da ita ko shine ta mai kwatance ta fadi masa sunan garin ta bashi number su inyaje ya kira su yayi gaisuwar a madadinta bai kamata ace babu wanda yaje ba
Ta rufe idonta akan ita da kanta take son zuwan inta samu lafiya haka dai aka shashantar da maganar zuwan
**********************
Bayan wata hudu alhmadlh zuwa lokacin allah yasaukeni lafiya na kara samun d`a namiji wanda yaci sunan babanmu ina amma muna cema sa walid
Koda aka tashi suna kam wannan karan yan kano sunzo harda gwagwgo binta da bahijja aka zo naji dadin zuwan su anan ne nakejin labarin ansaka auran yaya yusuf watanni shida masu zuwa naji dad`in hakan sosai tunda dama tunda nazo garin banta `ba zuwa ganin gida ba
Wannan karan sunan yasha banban dana farko .saboda gwaggo binta ta tsaya akan komai su suka soyamin namam sunan da aka agama ma ita ta kasafta ta kaiwa hajjo
Hajjo kam haihuwar dana yi bak`amin bak`in ciki take ciki ba ganin cewa wannan karon ma namiji nak`ara haifa
Tana dai dannewa na amma kamar wancan babu ruwanta damu
Koda aka kai mata naman sunan a wulak`ance ta amsa bataso tsarin ya juye haka ba amma tuna k`udirinta nagaba yasa ta danne jira take kawai asamu a gama wannan taron ta je wajen bokanta yazama dole tayiwa tufka hanci tayi maganin aminatu tun yanzu ta fara cika gida da y`a,y`a
Haka harsu gwaggo binta suka koma nan nacigaba da gudanar da jegona cikin kwanciyar hankali babu ruwana
Da kowa wankan yarona
Na iya nima nikewa kaina wankan awajena nake d`ora ruwan wankana ahaka har na kammala wankan jegona
Hajjo ce durk`ushe cikin tsukakkiyar bukkar da babu abin da ke tashi cikinta sai wari da hamami ta sunkuyar da kanta tana sauraren abinda bokan yake fad`a mata
Tabbas d`an,ladi zai auri aisha kamar yadda kike so saidai na hango wani duhu mai tsanani a gaban auran nasu nayi bincike amma iya bincike na banga no komai ba
Abu daya zan fad`a mik zan iya baki zabi ko dai ki hak`ura da batun auran nasu baki d`aya dan tabbas akwai abinda zai faru ta silar auran ...
Ko kuma ayi auran kome ya faru kuma wannan babu ruwana inkinason a fasa auran ni zan yi aiki a jefa kiyayya tsakaninsu yadda zasu tsani junansu kinga babu batun auran kenan
Boka nidai banason a fasa aurannan dan naci buri akan hakan sosai so nake in bawa mak`iyana ciwon kai ace d`ana da suka raina ya auri yar gidan chiroman gari kaga babu batun raini kasan yadda zakai a kauda wannan duhun da kace inyaso kaga ko anyi auran babu matsala
Batun duhu babu yadda za ai dashi dan na fad`a miki nikaina bansan meneneba
Babu matsala na zabi ayi auran kawai babu abinda zai faru
Sai maganar ahmad inason ita yarinyar asa mata k`iyayyar garinnan yadda koshi ahmad d`in zata ji batason zama dashi yadda da kanshi in ya gaji da wulak`ancinta dole ya sallameta kaga shikenan na rabu da k`aya cikin sauki tunda ita asirin zai kamata
Ba,matsala indai wannan ne ga wannan ki tabbatar kin sa mata a abinci taci muddin taci zata ji ta tsani mijin kwata kwata
Bazata taba samun kwanciyar hankaliba har saita rabu da shi
To kamar yaya zan yi aiki dashi ?
Acikin abincin da zata ci ake so kisa mata ki tabbatar ita kad`ai ce zata ci abincin
*************************
Kamar yadda nasaba yau ina tashi na kammala ayyukana tsaf na juye ruwan wankan walid na masa dashi da kalim bawan allah har zuwa yanzu dai baya um baya um um na shirya su
Na juye nawa ruwan wankan kafin intafi na dauko sauran dumamen tuwona daya rage na dora kan wutar na bar kalim dake wasan shi tsakar d`aki walid na barci kan gado na wuce wanka
Hajjo da tun safe take zarya tsakanin lungun aminatu da k`ofar d`akinta
Ganin ta d`ora dumamen tuwon ta shiga wanka yasata cikin sauri shigowa lungun dama a labe take duk abinda aminatun keyi tana kallo
Cikin sa a tana bud`e tukunyar taga dumamen tuwon semovita ne da miyar kuka duka tuwon baifi cin mutum d`aya ba ta tabbatar amintunce zata ce saboda ahmad baya nan kuma tasan kalim bawani cin tuwo yake ba yafi auki wajen taliya cikin sauri ta zazzage maganin ta juya miyar sosai
Ta rufe ta fice a wajan zuciyar ta tas ta tabbatar
Dole burinta yacika yau
Cikin kwanciyar hankali na gama wankana na shirya tsaf na sauko tukunyar tuwona na dorata kan dan faranta nasa tukunyar a gaba danni badai son dumemen tuwo ba akwai ni da sonshi shiyasa inya kwana nikad`ai kecin abuna dan ahmad bai dame shiba bare kalim dayayi gadon babanshi
Cikin kwanciyar hankali na cinye shi tsaf na kai tukunyar waje na dawo na wanke hannu na da bakina naja kalim mukayi kwanciyar mu haka muke kullum inna gama aiki ko wasa bana barinshi fita dan da yana fita amma yaran gidan ke zalintar shi sai yadawo inga idonshi jawur sun kumbura alamar yaci kuka shi gashi ba magana yake ba ba kuka yake ba to bare inji kukan shi in fita dana ga haka sai nake janshi jikina muyi kwanciyar mu inna tashi inshiga aikin rana
Cikin tsananin farin ciki hajjo ta koma d`aki
Salaha ce da shigowarta kenan yanzu taga fuskar hajjo sai fara,a take tace hajjo lafiya kuwa naga sai murmushi kike ke kadai?
Lafiya lau salaha babu komai tace tana mai tashi
Yawwa hajjo kinsan wani labari dana ji yau
A a saikin fad`a ta koma ta zauna
Kinsan makarantar akwai wata k`awata ummi to yau munadawowa makaranta sai muka hadu da aunty aishar da yaya d`an ladi keso ita da wani mutumi d`an lukuti a jikin mota
Na gaida ta ta amsa taci kwalliya da riga da wando sai wani d`an gyale data yafa wallahi hajjo kamar ba ita ce ke zuwa da hijabi har k`asa ba koda nagaidata naga kamar bata so naganta ba
Bayan mun wuce tane ummi ke cemin ai tasan ta a bayan layinsu take sam bata da kamun kai kwata kwata kuma wai tana da aljanu in suka tashi bata tsayawa a gida wataran intafita sai tayi kwana biyu ba a ganta ba wani lokacin ma ba a ganinta sai awani gari kuma aljanunta duka suke
Gaskiya hajjo karki yarda yaya d`an ladi ya auro mana ita karta zo ta na mana hauka a gida
Ke dallah yimin shiru oh ni mero har anfara kawo suka tun yanzu kiji yarinya yanzu ita ummin ina tasanta harta san tana da aljanu kinga kifita idona yarinya nutsatstsiya ace tana da aljanu harda sharrin barin gari tana yi to dan ubanki karna k`ara jin wannan maganar inba haka ba saina sa`ba miki tashi kibani waje kema bak`in cikin kikewa yayan naki akan auran d`iyar manya da zaiyi
Zancen banza da wofi ko ganinta da kikace kinyi da wando k`arya ne yarinya kullum tana zuwa nan cikin mutumci da hijabinta har k`asa