← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 78

Sashe 74

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana d'aga labulen idanun ta suka mata mugun gani mijinta dai mijinta d'an,ladi shine kwance kan wata mace tsirara haihuwar uwarsu suna aikata abinda taje ta gama aikatawa tana me ?

Sam d'an,ladi da suka yi nisa bama su san anwani d'aga labule ba bare su farga

Ganin bama su ganta ba har zatayi kukan kura ta dira kansu sai ta fasa ta saki labulen ta dawo tsakar gidan tana wuri wuri tunanin abin daya kamata take kawai

Idanunta ne yakai kan tukunyar da hajjo ta d'ora kan murhu da sauri ta yi wajen ta bud'e tukunyar ruwan zafine cike da ita sai tafasa yake

Batayi wata wata ba ta suri tukunyar ko zafinta bata ji tayi hanyar d'akin

'Dan,ladi da yayi nisa sai nishi kawai suke saki sai jin wata iriyar azaba ta ratsa kansu sukai

Wani irin ihu yasaki cikin sauri ya d'aga yarinyar da itama ta jik'e jagwab da ruwan zafin ihun take saki

Aisha dake sakin huci ta d'aga sauran ruwan zafin ta kelayewa d'an,ladi a jikin shi sannan ta yi kan yarinyar da duka

Kukan yarinyar da k'yar yake fitowa

'Dan,ladi kam tsabar azaba sumewa yayi daga ihunnan dayayi sau d'aya

Kukan da ake jiyowa daga cikin d'akin da kuma ihun da aisha take tana fad'ar maganganu yasa mutanen gida fitowa suyo d'akin

Hajjo ce kan gaba nan idanun ta suka mata mugun gani d'an,ladi a kwance kamar gawa tsirara fatar jikinshi gaba d'aya ta salu'be

Ga aisha kan wata kamar wadda d'an,ladin yace k'awar aishar ce tsirara tana kilarta kamar allah ya aiko ta

Bata yi wata wata ba tayi kan d'an,ladin ta rarumo zanin gadon ta lulluba mishi ta shiga jijjigashi

Tana ihun ankashe mata d'a dan kota kan aishar da ke shirin kashe yar mutane batayi ba

Saida mutane suka shigo tukun maman aisha tayi wajen su tana k'ok'arin raba aishar da yarinyar

Saida da k'yar ta d'aga ta wadda azabar duniyar nan ta isheta ga ruwan zafi ga dukan data sha itama duk jikinta ya salu'be amma ba kamar d'an,ladi ba

Ganin ta tsirara yasa matan suka rufamata zani da k'yar aka ja aisha ana k'ok'arin fitar da ita

Dan kowa ya fahimci abinda ya faru

Hajjo ganin d'an,ta baya numfashi yasa tayi kukan kura tayi kan aishar ana shirin tare ta
Ta kama aishar da kokawa da nufin ta daketa

Shegiya kin kashe shi shikenan ta kashemin yarona ihu hajjo take kawai tana kaiwa aisha duka

Aisha da zuciyarta ta kawo wuya ganin iskancin da hajjo take mata yasa ta kwace rik'on da ake mata tashiga kwallo da hajjo tana dukanta babu ji babu gani duk yadda aka so k'watar ta ankasa

Ihun azaba hajjo ta dawo yi tana fad'in ataimaketa kar ta kasheta

Aisha da dama can tana jin haushin hajjo akan irin abubuwan data ke mata nasa ido da zuga mijinta data ke suna fad'a ta shiga sauke haushinta sala,sala duk yadda akaso k'watar hajjo abin yaci tura dan

Ruwan cikinta aishar ta zauna kamar allah ya aikota tana kilarta

Muna sauka a tasha muka kira baba musa baba abdullahi ke fad'a masa mun sauka

Yayi mamakin zuwan su nan ya bud'e baki da nufin tambayar su baba abdullahi ya dakatar dashi kazo tasha ka same mu

Yana zuwa mukayi shatar mota dukan mu har k'ofar gida
Muna shigowa gidan hayaniyar mutane ta cika gidan ga mutane damk'am

Nan mukayi k'ofar d'akin hajjo inda muka ga anfi taruwa mutane ne ke k'ok'arin raba aisha da hajjo wadda ke k'asa aisha na duka ta ko ina ita kuma na ihun neman ceto bakinta a fashe dan harta zubar mata da hak'oran gaba

Ganin abinda ke faruwa mama aisha tayi wajen da niyar rabon fad'an

Cikin sauri baba abdullahi yayi saurin rik'o hannun ta kinga daka ta barsu

Ahmad kam shima yana tsaye kallonsu yake ko kad'an baiji tausayin hajjo ba bare har yaje dan ceton ta gashi duk kamar had'in baki yaranta duk basa nan

Da k'yar aka kwace ta a hannun aishar

Tana shirin tashi da k'yar ta d'ago kai da kumburarraren idonta da bakinta da shima ya suntume tana kallon mutane

Jin ana cewa sannun ku da zuwa sannun ku da zuwa

Da sauri ta d'ago kai sai tayi tozali da malam liman cikin sauri ta zabura ta mik'e kamar ba ita bace take kwance male male

Nuna shi ta shiga yi da hannun tana ja baya tana k'ara nuna shi da hannu ganin dai tabbas shid'inne dai malam liman na niger ga ahmad kusa dashi sannan ga abdullahi ga Salisu ga
Su aminatu da yaranta cikin k'oshin lafiya

Mekenan me hakan ke nufi? ta shiga tambayar kanta hakan na nufin aminatu ta dawo ita data kore ta kuma boka yace mata bazata ta'ba dawowa ba

Ganin irin kallon da ahmad ke jifanta dashi yasata zaro ido kallo ne na tsantsar k'iyayya da tsana tare da k'yama

Tunawa da batun bokanta akan muddin ahmad ya had'u da kakanshi shikenan asirinta ya tonu

Kenan hakan na nufin komai nata ya rushe
Cikin sauri ta fusge d'ankwalin kanta hakan yasa gwaguyayyen gashin ta bayyana

*_😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE😍_*✍️
13/11/2022, 6:35 am - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

*_PAID PAGE 48_*

Ta shiga sambatu cikin fitar hayyaci

Ina wallahi bazai yiwu ba sam bazata sa'buba wallahi inaaaa

Tona min asiri kake son yi wallahi k'arya kake yi ni mero nafi k'arfinka wallahi

Ahmad d'ana ne kowa yasani baka isa ka tona min asiri ba kowa yasan nid'in mahaifiyar sa ce
Tunda na rufe bakin kowa

Hhhhh tashiga 'bab'baka dariya tana tonawa kanta asirin irin mugayen k'ullin data k'ullah tunda ga farkon auren su da musa har zuwa korar hasana data sa bokanta yayi .

Har kashetan da tayi da kuma yadda aka kawo mata ahmad da irin tsanar da ta mai da kuma rik'on data mai na kisan mummuk'e a 'boye

Da yadda ta rufe bakin kowa akan kar a tona mata asiri akan ba d'anta bane haka dai ta dinga fad'ar mugayen ayyukan data dinga aikatawa har zuwa kan irin asirin data dinga mai baya kamashi da mallake musa da tayi

Zuwa kan aminatu da tazo da irin k'iyayyar data ke mata zuwa kan yadda taso ta zubar da cikin data samu

Kowa da kowa yasaki baki yana kallon ikon allah da kuma jin irin miyagun ayyukan da hajjo ta aikata a rayuwarta abun yazowa kowa a bai_bai jin cewa ahmad ba d'anta bane

Kuka,kawai muke nida,mama aisha da wasu masu raunin zuciyar dan har mak'ota sun fara shigowa

Baba musa kam kasa tsayawa yayi da kafafunshi saida babanmu da baba a abdullahi suka rike shi jikinshi rawa kawai yake yana zubda hawayen bak'in ciki jin irin zalincin da mero ta aikata mai da yaronshi dama matarshi mafi soyuwa a gare shi hasana

Sai lokacin ma ya shiga tunanin shin meya kaishi ga auran mero me yagani gareta tayaya ma akai haka jikinshi ne yasaki gaba d'aya ya zube jikin su babnmu suka tallebe shi ya zama kamar wani mutum mutumin jiyake kamar ma ba a duniya yake ba jin irin abubuwan da hajjon ke fad'i

Ahmad kam idanun nan sun kad'a sunyi jawur kamar gaushi shi ko damar kukan bai samu yayi ba da zai samu yayi kukan ma daya huta da azabar da zuciyar shi ke masa kallonta kawai yake yana tuna duk irin zaman da sukai da juna da yadda ta dinga matsawa rayuwarshi ashe ita ta kashe mai mahaifiya

Shin wacce irin zuciyace da ita ta zalunci haka ashe har rayuwar shi take nema allah ne bai bata sa,a ba sannan da bata samu wannan ba tanemi ta kassara masa rayuwa shin meyasa me ya mata kawai dan ya kasance d'an kishiyarta kishiyar ma wadda ita tazo ta samu mahaifiyar shi

Ganin ta yake kamar wani bak'in maciji daya fasa kai zai sareshi duk ta tuje kanta tana fisgar kayan jikinta tana k'ara tonawa kanta asiri

Kowa yayi cirko cirko
Hatta aisha da ke sakin huci da aka rabata da hajjo jin irin tabargazar da hajjon ke fad'ar ta aikata

Ita kanta kallon hajjon take cikin tsoro da firgici
Bata ta'ba tunanin akwai d'an,adam mai irin zuciyar hajjo ba duk abinta bazata iya kashe raiba

Har anmanta da wani batun d'an,ladi dake kwance a d'aki bare budurwar shi da itama ta lalla'bo da k'yar ta yo k'ofar d'akin ko zaninta da k'yar ta d'aura ta lallaba ana cikin hayaniyar fad'an hajjo da aisha ta fice batare da kowa yasan ta fitan ba

Dai dai lokacin Bashir dake shagonshi usaini yaron yawo jummai yaje ya sameshi akan ga hajjo can suna dambe da aisha ta danne ta tana duka

Cikin sauri ya kulle shagon yayo gida yashi go dai,dai lokacin da hajjo kewa kanta tonan asiri tana shirin balle zanin jikinta cikin sauri ya k'araso kanta ganin kowa ya tsaya yana kallonta babu wanda ya hanata sannan basu rik'eta ba

Da k'yar yakamata dashi da shamsu da shima labarin abinda ke faruwa akan ana fad'a da uwarsu ya tarda suka kaita d'aki suka rifo k'ofar tana bige bige tana k'ara tonawa kanta asiri cikin ihun ita dai azo a bud'eta

Kowa a wajen ya fahimci kamar hajjon tasamu matsala a k'wak'walwarta ganin irin abubuwan data keyi babu cikakken me hankalin da zai aikata

Bayan sun kulleta ne suka lura da bak'in da suka zo da kuma mahaifinsu da ke kwance jikin baba abdullahi da ke tsugunne sai bak'uwar fuskar malam liman da suka gani sai kuma mu binmu suka shiga yi da kallo kowa na mamakin meke faruwa ba fad'a bane aka ce ana yi yaushe muka dawo?

Ganin basu da mai basu amsa sannan ga mahaifinsu na kuka k'annen shi rik'e dashi yasa suka k'araso wajen cikin sanyin jiki suka nufi mahaifinsu
Chapter 74 · 0% Book details