← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 78

Sashe 38

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kudi kam tana samun su
Da yan iskan samarin ta
Ahaka ciki yazo ya bullo
Ganin samuwar cikn
Uwar tashiga tashin
Hankali duk da dama
Ta dade tana fargabar hakan tunda ita kanta
Tasan abinda yar tata ke
Aikatawa cikin tashin
Hankali suka shiga neman
Hanyar da cikin
Zaizube amma abin
Tashin hankali

Ranar data sha maganin
Ranar jini ya balle
Mata sai asibiti suka.kwana koda likitoci.suka yi bincike sun
Tabbatarwa da fadimen .ba wannan ne na farko ba kuma tabbas
Akayi yunkurin cire cikin
Zata iya rasa ranta
Mafita abarta ta haifeshi
.
Koda jin haka sun shiga tashin hankali
Ganin duk jinin data zubda cikin baizube ba

Gashi kuma basason tonon asirin su dole tasa fadime tayiwa mahaifin
Hauwar karyar zata je ganin gida can garinsu sokoto tare da hauwa
Bai musaba yace sai
Sun dawo

Iyayen fadimen sun rasu
Yayanta kawai ya rage
A raye a kauyen sokoton
Yayanta mutum ne
Me tsananin son zuciya da son kudi indai zaka
Bashi kudi to kome
Kake so zaiyi kisa
Ne kawai bazai aiwatar ba

Koda suka isa fadime bata boye mai komai ba
Tace tana son hauwa ta zauna wajen shi harta haihu inta haihu ya rike musu dan amma tanason ya rufa mata asiri akan cewar mijin
Hauwar yasaketa da ciki
Shine ta dawo wajen shi

Farko ya bijire amma yana jin hauwar ta ambaci makudan kudin .da zata bashi tuni
Ya amince haka ta baro hauwar

Data dawo tayiwa mahaifin karyar yayanta yace ta zauna wajen su kwana biyu

Haka har hauwa ta haihu
Ta samu danta me kama
Da ita sak babu inda
Ya barota bama tasan ubanshi ba koda baiyi .kama da ita ba dan
Ita kanta batasan yawan
Mazan data ke mu,amalanta ba

Haka bata shayar da yaron ba ta bar musu ishashhen kudi akan adinga bashi madara ta juyo ta dawo gda nan fadimen ta shiga gyarata
Kamar wata megejon kirki
Tana warwarewa ta dora daga inda ta tsaya

Inda taga ahmad kwa ranar fadime ta ce tazo ta rakata gidan hajjon
Su dubata lokacin hajjo
Bata jin dadi

To aranar ahmad yana gari
Tunda hauwa ta kyalla ido taga ahmad taji
Duniya babu wanda ya mata ta aura sai shi

Koda suka koma gida ta
Tambayi fadime wye
Nan ta fada mata dan hajjon ne babu kunya
Ta bayyana wa uwarta
Burinta na auranshi

Cikin jin dadin hakan dan dama uwar tafison hauwar tayi aure tace
Zata tuntubi hajjo

Koda ta tuntubi hajjo
Hajjon ta mata alk'awarin ahmad bashi da mata sai hauwa
Dan lokacin kawancen
Nasu yana garawa
Sosai dan duk tare suke
yawace yawcen gidajen
Bokayensu akan mazajen su

Sai kuma ga maganar da
Malam musa ya dauko
Ta auran aminatun da
Ahmad hajjo taso nuna
Tirjiya akan batun amma
Lokacin baba abdullahi
Yayi ruwa yayi tsaki
Ya fituttuke mata akan ahmad fa ba danta bane
Bari yayi mata tuni
Su suke da damar zaba maimata

Koda jin haka hajjo
Ta fadawa fadimen cwa kawai mahaifin yaron
Bai amince ba yazaba mai mata jin haka ya tashi
Hankalin fadime da hauwa inda hauwar ta fara zaryar gidan duk dan
Da ja hankalin ahmad akanta amma ina
Lokacin duk da basu hadu da aminatun ba.
Amma baya kula ta
Yagama fuskantar ta
Tsaf kota gaidashi baya
Amswa dan ya tsani
Mace marar aji

Ahaka har aka shiga maganar auran shi da aminatun suna ji suna gani har sabani suka samu da juna fadime na
Ganin hajjon ce
Bataso lamarin ba ai ita zata sa ahmad din
Ya auri yarta tunda ita

Ta haifeshi nan kwa batasan dawan garin ba

Wannan kenan

**********************
*Mundawo labari*

Ni yanzu bukatata kawai akara mallakemun musa dan yanzu ya fara bijirewa umarni na sona ke ya zama na duk abin dana ce kar ya tsallake umarnina inhar hakan ta samu boka komai zaizo min da sauki

Zaki mallake shi fiye da dama sai dai akwai wata matsala inhar kika yi sake wani yaji sirrin da kike boyewa akan ahmad to tabbas komai zai warware musa kuma zai koma mahaifarshi dashi da sauran yan uwansa kinga yaro dole zai san bake kika haifeshiba ki gujewa hakan

Karka damu indai wannan ne nidai yanzu a mallakemin ubannashi arufemin bakinshi yazama kome zance sai dai yace to ahmad zanciga da amfani da matsayina a wajenshi har na cimma gaci

Indai wannan ne kinga wannan turaren ya miko mata wani kulli ki tabbatar kin turarashi dai dai lokacin da zai shigo indai ya shaka to tabbas babu shi babu zallake maganar ki

Ya dauko wata laya ita kuma wannan ki samu wajen da babu mutane kin tabbatar babu yadda za ai wani ya hake ki tona rami ki binne ki dauki dutse mai nauyi ki daura akai indai kinyi yadda nace to yadda kika binne layar nan kika dora dutsen haka mijinki bazai taba tsawatar miki ba akan komai da zakiyi

To shikenan nagode boka ai bazan taba bari asamu matsala ba godiya nake

Nan ya fadi abin da zata bashi ta ajiye mai kamar yadda tasaba ta juyo gida cikin farin ciki

Kamar yadda yace duk ta aikata inda washe gari ita da kanta taga canji sai taga malam musa yayi sanyi akan zafin daya dauko kwana biyu intayi magana nan da nan yake bata amsa amma yau sai taga kome take kallonta kawai yake sa gayyah tasa aka kira mata

Ahmad a gabanshi ta kara jadda da masa zancen filinnan akan dole ya gina da kannen sa da su kansu inda uban ko uffan baice ba

Shi kanshi ahmad yayi mamaki amma sai ya dauka sunyi shawara tukun kafin ta kirashi

Inda yace hajjo ai bama yanzu zan fara ginin ba yanzu hidimar haihuwar aminatu ce a gabana tukun in allah ya sauketa lafiya ta haihu anyi suna ankwana biyu ne zan fara ginin insha allah

Nan dai ta yi kokarin dannar kanta taso afara yanzu inda zatayi duk wani shirinta na ganin komai yayi dai dai amma ba komai aiko aminatun ta haihu basai inda dan ko yar za ayi sunan ba ita kadai ta barwa kanta sani akan shirin data ke badai tana da dubarar in anbata abuba taki ci ai bata da dubarar hanata daukar jinjirin ko jinjirar allah dai ya kaimu

Nan ahmad ya taso ba cikin dadi rai ba baiso wannan shawarar da su baba suka yanke ba amma ba komai ai ba yanzu ne za ai komai ba sai nan gaba kafin lokacin yasan yadda za ai

***********************

Yau ne ahmad zasu koma wajen aiki amma tashin dare motar su zata yi dan haka har yamma muna tare inda yake tausata da da,da,dan kalamanshi akan ba dadewa zaiyi ba saboda yanayin jikina

Karfe tara mukayi sallama dashi inda nidai bansamu damar rakashiba ko bakin lungunmu kamar yadda na saba iya kacina kofar daki na dawo daki na kwanta

Saboda yanayin jikina da ba dadin shi nakeji ba yanzu cikina ya shiga wata bakwai kenan amma inka ganni bazaka ce ya kaiba saboda bani da girman ciki sosai

Yanayin dana ke ji yasa naji komai baya min dadi na kwanta daki farko naji zafi ya dameni duk da bawani zafi ake tsulawa ba sai na sakko kasa na kwanta kan ledar tsakar dakin kozanji dadi

Juyi kawai nake ikon allah barci sam ya gagari idanuna can wajen karfe goma sainaji kamar ana bubbuga abu a kofata na tashi naje jikin kofar nace waye naji shiru andaina taba kofar

Cikin rashin damuwa na dawo ganin nafara jin barci yasa na haye gado na kwanta can cikin barci naga an dallemin idona da fitila mai tsananin haske na yunkura zan tashi ina kare fuskata

Wanda ya shigo din yasa kafa ya maidani cikin tsananin firgici na bude baki zan fasa ihu

Da sauri ya zaro wukar dake gefen kugunshi ya nuna min ita cikin maye ya fara magana

wallahi kika sake kika yi wani yunkuri na tona min asiri wallahi saina illataki kina min ihu ina yankarki da wukarnan

Sai lokacin na gane waye dan ladi ne cikin tsananin tashin hankali na hade hannayena ina ja da baya yana kara bina bakina rawa yake kawai ina kokarin furta kalma koda guda daya ce amma rawar da bakina yake ta hana kowacce kalma fitowa

Ganin nakai karshen gadon bai daina bina ba yasa da kyar na bude bakina kaji tsoron allah dan ladi karka cutar dani dan girman allah kaduba darajar auren da ke kaina ka duba zumuncinmu kada kayi abin da zaka zo kana dana sani

Da sauri yasa hannun shi ya kwasheni da wani rikitaccen mari wanda saida naga wani haske ya gifta ta idona na fashe da kuka

Cikin muryar mashaya ya cigaba da magana Kedan abu kaza ta ubanki nikike bawa hakuri harni zakiyi wa wa,azi kinmanta irin bannar da kikamin a fuskata wallahi yau saina maida mugun yawuna akanki kuma babu mai cetonki tunda wanda kike takama dashi dinma bayanan

Hhhh ya fashe da dariya yacigaba da layi yana bina ganin ya na kokarin fadowa kaina yasa nayi kokarin kaucewa inda ganin haka yasa kafarsa ya tadoni na fadi akan cikina

Wata iriyar azaba ce ta ratsani har cikin kaina na yunkura zantashi yasa kafarsa ya dannemin hannayena kamar yasamu akuyar da zai yanka

Kuka kawai nake ina addu a akan allah ya kawo min dauki dan yau na riga dana saddakar kawai na mutu wanne irin mugun abu kenan

Kokari kawai nake in ture shi in tashi amma ina duk da a buge yake karfin ba daya ba abinka da mace kuma sannan ga ciki duk da haka ban daina kokarin kwatar kaina ba

Ganin ina tutture shi yasa ya fincikoni ya fara fesa min mari yana kaimin duka dan uwarki inkika min gaddama wallahi saina farka cikin nan naki shegiya yar iska

Yayi jifa dani ya kara sa kafar shi ya danne min hannaye tukun naga ya sa hannunshi guda a aljihunsa ya fito da wata igiya mai kauri

Na kara firgita matuka ganin yana kokarin daddaureni ne ga kuma hannun shi dayan yana rike da wukar har yanzu nunani yake da ita akan ina ihu zai yanke ni
Chapter 38 · 0% Book details