← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 78

Sashe 76

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kama hannunta kawai nayi nayi hanyar d'akina da ita dan ni tausayima take bani yaya zata ji intaji irin mugayen ayyukan da mahaifiyar ta ta aikata

Koda nakaita d'akin wajen mama aisha na kaita mama ga salaha yanzu ta dawo karki bari ta fita nan na barsu ita tacigaba da kukanta

Umr nagani na kirashi duk da shima yanzu ya girma ya d'anyi hankali tambayar shi nyi ina yayanshi nan ya fad'amin sunje asibiti kai d'an,ladi

Shina bawa kud'in kayan miyar yaje mak'otanmu ya amso min dan dare yayi anfara kiran sallar ishsha yana dawowa na yi sauri na kunna gas na mana jalof nan da nan kowa dai yaci abincinne badan dad'iba sai dan yunwa
Su ahmad kam tunda suka kai d'an,ladi aka shiga dashi babu wani labari sai can wajen k'arfe goma tukun wani likita ya fito

ya musu bayanin yanayin jikin nashi inda ya ce gabanshi na barazanar samun matsala saboda ruwan zafin ya cinye wata jijiya sosai amma in akai sa,a zai iya warkewa sai dai ko ya warke ba lallai kuzarinsa da mazantakarshi ya dawo irin nada ba

Sun riga dasun 'bare fatar jikinshi da ta taso gaba d'aya sun wanke inda suka ce ya farfad'o sau d'aya lokacin da ake wanke ciwon amma azaba tasa ya kuma suma sundai yimai allurar barci ko zuwa gobe zai iya farkawa

Kowa jikinsa yayi sanyi dole tasa aka bashi gado nan ahmad da babanmu da baba abdullahi suka dawo gida anbar bashir da shamsu acan

Dan dama basu je da malam liman ba shi ya tsaya wajen baba musa dake barci har lokacin

Koda suka dawo zuwa lokacin sani ya dawo gida yazo ya tarda tashin hankalin hankalinsa ya tashi jin irin abubuwan da suka faru dan salaha bata gamsu da zaman d'akin aminatu ba har saida taje ta tambayi maman aisha meya faru bata 'boye mata komai ba tunda ga kan kama d'an ladi da aisha tayi har zuwan bak'i da kuma irin tonon asirin da hajjo tayiwa kanta

Salaha tasha kuka jin wai yaya ahmad ba uwarsu d'aya ba hajjo ba ita ta haifeshi ba ashe shiyasa duk ya fita daban ciki y'ay'an d'akin bawan allah jin irin abubuwan da hajjo ta mai bak'aramin tausayinsa taji ba

Ashe shiyasa koda takama shi ya tsaya kallonta koda sani ya dawo ita ta fayyacemai komai da ya faru yana shirin binsu asibitin kenan suka dawo

Hajjo kam tun tana 'bare,'barenta har barci ya kwasheta dole salaha d'akina ta kwana

**************"*"********

*_Washe gari_*

Zuwa safe baba musa lafiya ya tashi sai dai rashin k'arfin jikin dake damun shi jinshi yake wani sakayau kamar bashi ba

Nan malam liman yasa aka bud'e hajjo wadda lokacin da aka shiga d'akin tayi kaca,kaca da d'akin bata parlourn can uwar d'aki suka hangota a rakube jikin gado barci take hani,an sai dai duk ta yaga kayan jikinta

Dama bashir ne da sani suka shiga da suka fad'a wa malam liman nan ya ce su lallla'ba su d'ad'd'aureta tunda dole parlourn ta za,azo ayi maganar amma ana tsoron ta watse wajen dan yadda ta dinga yi jiya yabawa kowa tsoro

Allah sarki tsakanin d'a da mahaifi akace sai allah ba ason ransu ba suka lallaba suka d'aure mata k'afafuwa da hannaye inda a wajen d'aure hannun ne ta farka taso k'wacewa basu bata dama ba

Ihu take tana zare ido tana cewa su kunce ta hauka dai ya tabbata tuburan ta dinga k'ok'arin kunce k'ullin amma ta kasa

Juyawa sukai kowa na goge k'wallar data ke zuba masa

Nan suka tattara parlourn tukun su malam liman suka shigo aka zazzauna

Muma aka kiramu dukanmu hatta salaha ba a bari ba

Baba liman shi ya bud'e taron da addu,o,i tukun aka fara magana akan abinda ya taramu na irin abubuwan da suka faru tunda ga farkon tarihin su baba aka k'ara badawa da irin abubuwan da aka musu har zuwa ayyukan da hajjo ta aikata

Y'ay'an hajjo duk kuka suke saboda jin irin 'bannar da mahaifiyarsu ta aikata nan suka shiga nema mata afuwa akan abubuwan data yi kowa kuka yake ita kuwa har zuwa lokacin sambatu take a d'aki

Salaha ce cikin kuka ta kalleni tace tana da magana dan allah in yafemata lokacin da aka sakawa kalim k'usa hajjo ce kuma ita ta gargad'eta akan karta sake ta fad'a inhar ta fad'a saita kasheta

A lokacin bawai nasan zata iya kashenin bane a gaske duk da banida tabbacin bazata iya d'inba duba da yadda babu imani babu tausayi ta cutar da jaririn da baisan komai ba

Kawai na rufa mata asirine a matsayinta na mahaifiyata saidai ko yaushe ina tsoron ranar da allah zai kamani akan irin zalincin da nabari akayi nasani kuma nakasa fad'a a d'au mataki

Daga lokacin na fuskanci hajjo bata son yaya ahmad amma duk da haka bata ta'ba fad'amin cewar ba ita bace mahaifiyarsa ba
Sai dai ni ina tunanin tsanar datawa aminatu ne ta shafi yaya ahmad d'in

Jin cewa hajjo ce ta aikatawa kalim hakan yasa ni fashewa da kuka mama aisha na tayani dan ita tunda take bata ta'ba ganin zalinci irin wannan ba da kuma cin amanar zumunci irin wannan ba wacce irin zuria kenan

Nan nima nashiga basu labarin irin zaman danayi da hajjo da kuma yadda naji na tsani garin gaba d'aya

Hajjo da duk maganganun da ake tattaunawa tana ji k'ok'ari take kawai ta fincike k'ullin da aka wa hannun ta tukun ta kunce na k'afar dai,dai lokacin da aminatu ke fad'in irin abinda d'an,ladi yaso mata ne hajjo ta fito firgigit

Ta tsaya tana binsu da kallo can ta bushe da dariya hhhh salaha salaha wato dana ce ki rufamin asiri karki fad'a zan kashe ki bakiji ba ko hhh aikwa saina kasheki yau d'innan kan salaha tayi

Cikin sauri su bashir da suka tare ta da k'yar suka iya rik'eta tana ihun abarta ta kasheta

Nizaki tonawa asiri saboda aminatu shegiyar yarinyar nan dama ni na tsaneta tun farkon auren wallahi bana sonta sam shiyasa naje wajen boka kawai dan ya koremin ita daga garinnan baki d'aya amma daya ke ked'in mayyace saida kika dawo tace tana zare idonta da suka yo waje baki d'aya tana kallon aminatu kamar zata yo kanta sai dai rik'on dasu bashir suka mata bana wasa bane

Shegiya nice nan bayan na sawa d'an naki k'usa kuma naje wajen boka a kurmantar min dashi shegen yaro hhh dama banso yazo duniya ba dan nasan burinshi shine ya cinye gadon ahmad

Filin dana so y'ay'ana su mallaka shege saida ya iso duniyar dan ya cinye gadon hhhhh baku sani bafa har asiri nawa musa danfa kar ya hanani yin yadda naso hhhh

Baba musa ya sunkuyar da kanshi kawai shi kad'ai yasan mai yake ji a zuciyar shi

'Dagowa yayi cikin k'unar zuciya ya kalleta mero tsakanina dake da yayarki sai dai allah yasaka min kije nasakeki saki uku bazan iya zama dake ba

Kowa a wajen babu wanda yayi mamakin jin sakin da yayi dan basuyi tsammanin hukuncin zaizo da sauk'i ba

Sai dai da akace uwa uwa ce yaranta basu ji dad'i ba

Ihu tayi ta k'yalk'yale da dariya hhh kasakeni saki irin wanda abdullahi yawa zainabu hhh nice fa na je na zugata na rakata har wajen boka nasa abdullahi ya dawo da ita

Hmm kunsan butulcemin tayi daga k'arshe akan ta daina bani goyon baya naso in haukata yar,iskama fa ta fad'a tana mai zazzare ido

Can saita fincike kuma daga rik'on da suka mata ta fara rawa tana jujjuyawa yasakeni kai kai yasakeni kai kai
.haka dai tai ta hauka

Ganin abin nata bana k'are bane yasa da k'yar aka kamata aka k'ara rufeta a uwar d'aki nan suka k'arasa tattaunawarsu aka nemi afuwar juna sannan malam liman ya isar wa da baba musa sak'on inna asabe na yayafe mata

Nan yace ya yafe mata
Amma shi zai bar wannan garinne

Gwara ya koma cikin yan uwanshi dan duk wannan abubuwan da suka faru harda rashin wani nashi a garin

Kowa ya bashi goyon bayan hakan saidai yaran basu soba koba komai ya zauna dansu nan bashir yace

Baba inkatafi mukuma ina zamu?

Duk wanda ya zai iya sai ya shirya ya bini nan da kwana uku insha allah zantafi dasu abdullahi mahaifiyar ku kuma dama babu abinda ya rage tsakanin mu da ita

Sani ne ya d'ago baba to inmuka bika yaya za ai da hajjo a cikin irin wannan halin da ta ke ciki gashi bata da kowa a garinnan

Sannan ga d'an,ladi dake asibiti rai a hannun allah baba sunce ma gabanshi yaso samun matsala sun kwantar dashi kud'in da za a kula dashi ma baba babu iya na jiya da yau kawai muka iya biya gashi sun rubuto magungunan da za a siyamai

To yaya kake son inyi mai allah ya gani nayi iya yina dan inbaku tarbiya ingantacciya amma mahaifiyarku duk ta rusa komai

Ashe abin kunyar nan har a gidana yaso faruwa wai k'ani na neman matar wanshi subhanallah bayannan mahaifiyarku tasani sannan a sanadiyyarta yazama d'an,iskan ta lalatamai rayuwa sannan yau sanadin hakan har ya d'auko karuwa har gadon matarshi subhanallah

Yanzu me gari ya waya ina son zuciyar tata ta kaita ina ribar hakan ta cuceni ta cutarmin da yara ta lalata min d'an,ladi
Ya d'auke k'wallar dake shirin zubo masa bakomai na d'auki hakan a matsayin k'addarata mero ita ce jarabawata ta duniya allah yabani sakamakon hak'urin dana yi da halinta a lahira

Kowa jikinsa yayi sanyi ganin baba musa na kuka

Baba abdullahi ne yace su shirya aje asibitin abiya komai hannunka baya ta'ba ru'bewa ka yanke ka yar dole tasa mazan suka wuce asibitin

Sun tarda jikin nashi gashi nan gashi nan dai sai godiyar allah dan ya farka amma baisan wake kanshi bama

Sun tattauna da likitocin inda suka ce jikin nashi kuma ya rage a mik'a sauran ga ubangiji aga yadda lamarin zai kasance

Kowa jikinsa yayi sanyi jin hakan koda aka basu damar shiga su ganshi babu wanda bai zubda mai hawaaye ba ganin yadda yake mimmikewa duk da an sa masa belt saboda kar ya fad'o

Ganin abinda yake yasa suka kira likitocin suka zo dole aka k'ara masa allurar barci
Chapter 76 · 0% Book details