← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 78

Sashe 14

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kwa zaije cikin yarinta in ya kawo mata ta cire naira goma ko ashirin a cikin kudin ta bashi tana samai albarka sata takeso ta koya masa ta karfi da yaji

Ko makaranta wani lokacin inya shirya zaije takan kwabe masa uniform tace kaje kayi wasanka ba kullum ake karatuba haka zai fice abinshi yana murna yana ganin mamanshi tafi kowa sonsa

Malam ma ya farga ana mai sata amma baitaba kawowa ahmad bane sabo da ganinshi ai bai isa daukar kayan wani ba kuma duk wata bukata yana kokarin saukewa iyalansa yadai yi shiru ya kudiri niyar zaisa ido akan duk mai mai hakan yadai san babu
Mai shigarmai daki inya dawo daga
Ahmad sai hajjo

Ana haka rannan ya kwabe kayansa zai shiga wanka har yakai ruwan sai ya fasa ya leko ta bandaki yaga ahmad ya fito daga dakin hajjo ya doshi dakinsa cikin sanda

Sai ya fito ahankali yabi bayanshi bayan yagama shigewa da yake rigar daya cire nacan sakale sai yaga yadauki wata yar kujera yasaka da kyar ya janyo rigar yasa hannu a aljihun yana lalubawa ya ciro kudin ya bar rigar nan dan bashida wayon wani
Mayarwa

Ya juyo kenan suka ido hudu da malam musa wanda ke kallon shi hawaye na zuba a idonshi

take jikinshi ya fara rawa yafara kuka saboda shima yafa ji ajikinshi cewa babu kyau abin da yakeyi kawai dan hajjo ta fison hakanne kuma sannan ta mai kashedi karya sake
Yace ita ta ke aikenshi

Inba hakaba zata yankashi

Malam ya karaso ya durkusa a gabanshi ya kama hannayensa yana kallon kudin sannan ya dago kanshi

Da kyar yace ahmadina meyasa kake daukar abin daba naka ba me zakai da kudade harhaka um me kake son siya da bazaka iya tambayata ba naba ka ?

Ahmad ya girgiza kai babu komai baba Ba abin dazan siya

Yace tom kuma kake taba kayan daba nakaba bakasan babu kyau taba kayan wani ba koda kuwa na mahaifane allah yana kona duk me daukar kayan wani

Kasan barawo?

Ahmad ya daga kai yace eh baba irin wanda aka wuce dashi rannan ta bayan layi anata dukanshi yara na masa ihu

Malam musa yace shima daukar kayan mutane yayi kuma daga gida ake farawa ahmadina banason watarana akamamin kai kana aikata hakan kaji kadaina karka kara kaji

Ahmad yana kuka yace nibanaso a konani kuma,banason adakeni ana yawo dani baba

Ya janyoshi jikinshi ya rungume yana shafa bayanshi yawwa ahmadina allah yamaka albarka yakare ka daga sharrin masu sharri

Yaron yace amen baba

Hajjo dataji ahmad shiru baidawo ba ta biyo bayanshi harzata daga labule saitaji abin da suke cewa gabanta na faduwar

Karfa ahmad yace ita ke aikoshi ya zubda mata mutumci gurin malam
Sai kuma.
Taji sabanin hakan
Bai tambayeshi wake aiko shi ba

Sai kokarin hanashi dabi,ar da taji yanayi

Tayi kwafa ta juya ai wallahi malam ka makaro indai ina raye sai ahmad ya lalace koda kwa zanyi yawo tsirarane

Nadai san ta bangaren fadamasa bani ce mahaifiyarsa ba nagama da kowa ta wannan fanni saboda har ita zainabun dake takamar zata tona na rufe bakin shegiya bare wani sakaran mijinta

Takarasa maganar tana mai shigewa daki

Haka dai malam musa yayi kokarin canzawa ahmad makaranta can kusa da shagonsu dan yana zargin yaran makarantar da yake zuwane ke dorashi a hanyar inda ahmad na dawowa ta makarantar boko zai wuce shagonsu in yadawo nan yake zama

Kafin lokacin islamiyya yayi inda nan tsallaken shagonne malam musa da kanshi ke mikashi in antaso sai ya kara zama zuwa lokacin tashin malam musa sai su dawo gida tare

Hajjo bataji dadin wannan hukuncin da malam ya yanke ba amma ganin
Kartayi magana malam yace tanada wata manufa saitayi shiru

Saboda ita yanzu ta kanta take laulayi yasakota gaba

Amma fa taci burin duk tsaron da malam zaibawa ahmad,saita rushe shi kota tsiya kota arziki indai tana raye kuma bokaye suna wanzuwa a bayan kasa

************************

Dare ya raba inda kowanne me rai ya na makwancinsa sai dai wadan da fitar ta zamewa dole da kuma wadanda ke fitar dan radin kansu

Buga kofar gidan ake iya karfi abdullahi da dakinsu shine farkon shigowa shi yafara ji ya fito lokacinne kuma malam musa yafito a lokacin karfe biyu da rabi na dare

Ya kalli yayanshi yace yaya buga kofa akefa

Malam musa yace eh muje muga waye da tsohon darennan allah yasa lafiya

Nan suka karasa sai malam musa yaji muryar daya daga cikin .masu gadin kasuwar da suke ne

Suka bude suka ganshi a firgice yana haki

Malam musa kuzo muje babu lokaci shagonku yakama da wuta kuma abin mamaki shi kadaine babu inda wutar ta taba sai shi anyi anyi a kashe wutar taki mutuwa

Innanillahi wa,inna ilaihirraji,un shine kawai abin da suke maimaitawa

Sukayi saurin juyawa gida abdullahi da babu riga jikin sa yasako

Malam musa da yatarda hajjo ido biyu yace maza kizo ki rufe gidan fita ta kamamu

Malam lafiya meyafaru?

Ta tareshi da tambayoyi

Yace inmundawo kwaji ki tabbatar kin rufe gidan cikin hanzariya fita

****************"********

Tashin hankali wanda ba asa masa rana sunje sun tarda shagon gaba daya wuta ta mamayeshi babu wani guri da ya rage

Anyi anyi wutar ta mutu amma kamar karata ake

Kuma abin mamaki iya shagonsu ne haka akaita fama amma wutar tayi biris

Saida ta cinye kayan shagon kakaf babu abinda tabari sannan cikin wani ikon allah kuma saita fara raguwa da kanta harta mace sai hayaki

Shagon yakoma kamar bashiba tuni Abdullahi ya sume aka kwashe shi ranga ranga sai asibiti

Malam musa kwa yadai zauna ne a dandagaryar kasa ba um ba um um

Zuwa lokacin asuba tayi sai zuwa jaje ake musu ana allah yakiyaye gaba cikin tausayawa

Haka malam musa ya lallaba da taimakon abokin kasuwancinsa da shima ya taso

Samakon labarin dayasamu shaguna naci da wuta shagonshi na jikin nasu malam musa shine yataimakawa malam musa sukaje masallaci sukayi sallah

Daga nan suka wuce asibiti inda suka tarda Abdullahi ya farfado

Likitan yace razana ce tasashi suma andubashi babu wata matsala aka basu sallama

Suka dawo gida jiki a sanyaye

Hajjo da zainabu da sunkasa tabuka komai suna cikin fargaba suka tare su harsuna hada baki gurin tambayar lafiya

Yanayin yadda suka shigo malam na rike da hannu abdullahi shima kanshi kokari yake da zaisamu mai rike shi so yake

Haka suka zauna a tsakar gidan jigum jigum dan duk babu wanda ya iya magana a cikinsu

Can dai malam musa yayi karfin halin dagowa da kyar yace kuyi hakuri mu rungumi kaddarar data rinkemu

Shagonmu na kasuwa ne ya kone kurmus babu abin da aka samu aka fitar duk wuta ta cinyesu

Hajjo ta zabura da karfi tana mai kama kirjinta

Kana nufin shagon ku dai ya kone

Wayyoh mun shiga ukunmu mun lalace shikenan shikenan wayyoh allah na

Haka take ta sambatu

Wanda zainabu ita batasan ma lokacin data karaso kusa da abdullahi ba ta kama kafadunsa tana girgiza shi

Wai baban Ummi sunan diyarta ta fara

Kana nufin kace min Shagon da muke samun abinci ta hanyarshi ya kone?

Ya dago ya kuramata ido can ya daga mata kai kamar karamin yaro

Ita nan tabi layin hajjo sunata karadin ihu da koke koke kamar ance uwarsu ta mutu

Makotane suka fara shigowa duk wanda yashigo sai su fara bashi labari haka akadinga yiwa su malam musa jaje

Cikin tausayawa inda ana ganin basu hajjo bane yakamata suyi kuka ba amma su sunyi tawakkali sai dai na zuci

*************************
Bayan kwana biyu hukumar kasuwa ta harhada musu tallafin datake bawa duk wanda wani ifti,la,i yasama

Amma ina kudaden bawasu masu yawa bane ko iya gyaran shagon zai cinye bare ayi maganar
Zuba kaya

Gashi dama daran ranar da aka kawo musu kaya adaran shagon yakama da wuta dai dai da cinikin ranar basu irgaba yana shagon

Gashi a lokacin bankuna basu wani yawaita ba bakowa ne yayarda da ajiyar banki ba

Basu ajiyar kudi gida kuma ga shi har bashi suka ci dan rabin kayan da aka kawo musu duk bashine saboda suna shirin raba shagon
Biyune

Kowa ya kula da nashi saboda halin rayuwa kowa ya fara tara iyali

Saiga wannan kaddarar

Haka suka hakura da gyara shagon suka dawo gida suka zauna kudin da ke hannunsu dashi suke hidimar gida

Haka dai har aka shafe wata guda babu wata hanya da suka gani da har zasu san yadda zasuyi

Lokacinne kuma mai kaya yasakosu gaba inda babu sani babu sabo ya uzzura musu

Ganin basu da wata hanyar da zasu biyashi

Yasa suka yanke shawarar saida gidan inyaso su kama haya sai su biyashi sai yabasu wasu kayan inyaso sai suyi kokarin gyara shagon da sauran kudin

Ai zainabu najin labarin za asaida gida ta tashi hankalinta masifar yau da ban ta gobe da ban ita saidai abdullahi yasaketa baza a saida gidaba

Tun yana lallabata har karshe ta kaisu ga sakin ta tattara yaranta ta yi gaba inda yabar mata sune kafin hankalinsa ya kwanta ya amso yaransa dama yagaji da halinta

Gwara rabuwarta su matar da bazata so rufin asirinka ba meye amfanin zama da ita

Ita hajjo ta bangarenta tafi nono fari alhininta kawai akan dukiyar da suka rasa ne amma ita burinta yanzu su bar garin suyi nesa da kano inyaso ta
Cika burinta cikin ruwan sanyi babu wanda
Yasanta tafiyar zainabu ma

Tafi komai yimata dadi dama fargabarta kenan kuma ta tafi

Saita kwantar da hankalinta

Inda,daga karshe aka yi cinikin gidan aka saida

Suka kama haya suka biya mai kaya kudinsa sai dai

Wata sabuwa yace shi sam bazai kara musu kayaba yama gode da kudinsa ya fito haka suna ji suna gani suka yi hakuri

Inda suka shiga buga bugar hanyar da zasubi don samun rufin asirinsu da kuma na su hajjo

Inda allah ya hada malam musa da wani abokin sa amma shi ba mazaunin kano bane

Yabashi shawarar. Ya bishi suje can inda yake aikin biredi yakeyi a Niger state Lapai insunje ko allah zaisa adace

Malam musa yayi na.am da shawarar sa yace amma sai dai inje nikadai nadinga dawowa ? Saboda iyalina bansan ina zan ajesuba
Chapter 14 · 0% Book details