← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 78

Sashe 18

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna shiga hajjo tafara bin dakin da kallo wata yar yololuwar katifa ce a yashe a kasa gefenta kuma wani buhune alamar dai kayan sawar zainabunne a ciki

Sai kulli kullin kayan wanki wasu alamar anwanke ba azo amsa bane wasu kuma ba awanke ba

Haka zainabu tashiga cewa ki zauna mana hajjo hajjo tabi dakin da kallo wai zainabu kina nufin nan ne kike kwana?

Zainabu ta kalleta cikin murmushin takaici eh

Hajjo tace cab gaskiya kinci baya abdullahi yana can yayi kudi ya gyagije harda fa tumbinsa yanzu sai wannan jimammiyar matar tashi dana tarar aysha take ko?

Kekuma kina nan jiya iyau babu auran babu wani cigaba sai uwar walaha da kikesha

Wai shin ina shige shigen dana sanki dasu ko kindaina ne kin karaya harkika dauki wannan dogon lokacin abdullahi baizo ya durkusa gabanki yace kitaimaka ki koma maiba?

Zainabu ta kalli hajjo cikin wani irin yanayi tare da wani kunci dake taso mata tunda ga kasan makogwaranta har daci daci takeji a bakinta

Tace hajjo duk abin da kike tunani zanyi inyi abdullahi ya maidani dakina wallahi nayi duk a kan abdullahi na kadar da kayan dakina da duk wata kadara tawa na siyar duk dan ya maidani amma shiru kikeji

Karshe sai labarin aurensa naji ko wata matar batayiba inaji ina gani yazo ya kwashe yaransa rabona da insa abdullahi a idona tun auren su nafeesa shima dan yazama dole mu hadune

Kuma ikon allah duk tsawon shekarunnan babu wani bazawari da yazo neman aurena koda wasa

Haka nake zaune babu irin zagin da inna batamin har casukai nice naki wani auren saboda inajiran abdullahi

Su suncire hannunsu a hidimata da girmana bazanzo inzaune musu ba indora musu nauyiba bayan suna ganin sun gama da matsalata

Haka yasa nafara wannan sana,ar tawa ta wankau da kika ganni inayi da ita nake duk wasu bukatuna insun tasomin dan su salima mahaifinsu yadauke musu komai saidai suzo su gaisheni ko kwana baya barinsu indai bawani babban dalilibane ya taso

Hajjo tayi kuri tana kallonta tace cab lallai ruwa ya daki babban zakara amma insha allah wahalarki ta kare dannima haushin wannan matar tashi nakeji

Zaki koma dakin ki amma fa da sharadin inna taimaka miki nima zakimin wani aiki

Zainabu dake cikin tsaka mai wuya sannan taji zata koma dakin masoyinta tuni tace komai kike so zanmiki indai zan koma dakina

Hajjo ta kalleta tace kintabbatar karsai na fada miki kicemin a a bayan kingama jin sirrina dankinsanni farin sani ni ba kanwar lasa bace

Zainabu tayi dariya tana girgiza kai tace hajjo rai ne kawai bazan iya kashewa ba akan cikar burina ..........

*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE😍_*✍️

*Wannan littafin na kudine idan kinason cigaba da karantawa zaki same shi akan farashin normal group 300 VIP 400 masu so ta private 1000 ki turo kudi ta wannan account number 2375144550Lawali ahmad zenith Bank ki turo evidence ta wannan number 09138320449 katin MTN ta wannan number 09138320449*

*Idan kuma littafin mu guda biyu kikeso TUSHEN MU DAYA da FANSAH 2022 Zaki turo normal group 500 VIP 800 ta private 1000*

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
09/11/2022, 2:16 pm - Maman Dan Albarka Ce: *🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE_*😍

_*FREE PAGE SUN KUSA KAREWA 💃🏻💃🏻MAZA KI YI KOKARI KI MALLAKI NAKI YAR UWA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI RAHUSA 300 KACAL NORMAL PASTING SAU BIYAR A ASATI GROUP VIP 400 POSTING KULLUM MASU SO TA PRIVATE 1000 NE SAU BIYU KOWACCE RANA INKUMA DUKA BIYUN KIKESO FANSA DA TUSHENMU DAYA ZAKI BIYA 500 NORMAL GROUP VIP 800 KARKI BARI ABAKI LABARI YAR UWA YANZU WASAN YA FARA💃🏻💃🏻💃🏻MAZA KI TURO KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK SAINA JIKU😍*_

*_Littafin tushen mu daya labarine daya danganci Wata zuria wadda babu abin daya yiwa zuriar nan lullubi face Cin amana zalunci rashin tausayi rashin tsoron allah sannan ga sassanyar soyayya labarin Aminatu da surukarta labarine da zaka zubda mata hawaye sannan ga kannen miji suma sun sako ta gaba shin dama haka yakamata surukai su zauna da matan ya,yansu? Duk sai kun tsunduma cikin wannan labari mai suna TUSHEN MU DAYA_*

*Masu son a tallata musu hajarsu ko kuma link din group din su suyi magana ta wannan number 09138320449*

```Bismillahirrahamanirrahim```

*Free page 12*

Hajjo ta kalli zainabu tace da kyau yanzu nasan ina tare da zainabun da nasani sukayi dariya dukansu

Tukun hajjo ta fara magana zainabu maganar danake son tattaunawa dake magana ce da babu wanda na taba budawa cikina yaji ko yasan sirrina saike da zaki ji yanzu

Zan fada miki ne kema dan inason kimin wani aiki sannan in taimakeki da sharadin bazaki fallasa min sirrina ba har abada nikuma na miki alkawarin kamar kin koma dakinkine

Cikin zakuwa zainabu tace karki damu hajjo fadi duk maganarki zaki sameni me rufa miki asiri fiye da tunaninki sannan babu maiji

Hajjo ta mike tsaye ta fara zagaye dan tsukun dakin daga bisani ta juyo tana kallon zainabu

Tace zainabu kamar yadda kika sani ahmad ba dana bane inda dagani saike sai musa da kannensa ne muka san hakan

Zainabu tace hakane

Hajjo taciga ba dacewa lokacin danace zan rike ahmad harna ja miki kunne kinyi wata magana ta cewa indai kina raye zaki tabbatarwa da ahmad cewa bani na haifeshiba a dalilin haka naje gurin boka nasa ya rufemin bakinku dan kar wanda ya kara tada maganar domin inason cikar burina ta ruwan sanyi

Kinsan mene burin nawa?

Zainabu data kure hajjo da kallo kamar tasamu tv tace a a

Burina shine na reni ahmad yadaukeni kamar uwarsa na masa tarbiyar danakeso sonake ahmad ya tashi a matsayin mara jin magana dan shaye shaye manemin mata inason ya zama kasurgumin barawo inda akarshe nake son rayuwarsa ta kare a gidan yari saboda tun daga farko bana kaunar uwarsa ma bare shi da kwatsam naganshi an kawomin shi sama taka

Dalilin tsanar danayiwa hasana yasa na kada ta gida nasa mata tsanar garin kano baki daya daga karshe nasa boka ya jefa mata cutar datayi sanadiyyar mutuwarta

Bansan ashe na kashe macijine bansare kansaba domin danasan tanada ciki lokacin danasa ya kashemin su baki daya amma kash ban sa amin bincikeba akan rayuwarta da ahmad bai kasance a raye ba

Bani da burin da ya wuce a ce nikadaice a gidan mijina da ya,ya,na amma kash hasana ta ruguzamin shirina inda hukuncin hakan shine in lalata rayuwar danta

Amma kinsan me ?

Zainabu data girgiza matuka dajin cewa hajjo ce ta kashe hasana ta girgiza kai a a

Tun muna gida daya dake nake dora ahmad akan hanyar danasan zata billemin cikin sauki ina aikashi ya dauko kudin malam musa inya aje amma ba aje ko inaba shirina ya rushe naso ya tashi da dauke dauke amma a banza musa ya nisanta ni dashi inbazaki manta ba dayake tafiya dashi kasuwa

Lokacin da muka koma niger state nan ma dai bansamu cikar burinaba inna aika ahmad ya daukomin bayayi yakancemin sata babu kyau shi bayaso a konashi

Nayi nayi yaron nan yana da kafiya har dukansa inayi dan har dakunan mutanen gida nakan aikashi ya dauko abu amma fir yakiyi inda asona sonake agidan ma amai tambari da barawo Danaga yakiyi ta sauki saina nemi kawata Fadime tarakani wajen wani boka tunda nidin bansan ko inaba naje ne daniyar akara mallakemin malam musa saboda intaji saboda ahmad nazo zatace badana bane shiyasa bayan kwana biyu nakara komawa nikadai

Inda na fadawa bokan bukata ta tason akangarar min da ahmad yazama abin kwatance yadda nakeson yazama yabani magani yace insa a daddawa in ajiye bera ya dauka sannan yabani wanda zansa a abinci duk nayi yadda yace amma kinsan abin mamaki?

Zainabu tace a a

Maganin bai yi tasiri akan ahmad ba washe gari saiga dan ladi wai yashiga dakin matar gidanmu ya daukar mata kudi

Bankawo komai ba nadai basu hakuri tundaga nan sai dan ladi yafara dauke dauke ban isa na aje abuba sai nanema na rasa haka dan ladi yaketa dauke dauke ahmad na rayuwarsa a nutsatstsensa

Kinsan wani abu daya dawo da hankalina kuma ya girgizani dan ladi da baifi shekara sha biyar ba shine aka kama yasa yarinyar makotanmu a wani lungu yana kwakula

Bakiga dukan da nupawan nan ba suka ma saida suka so dangana shi da hukuma da kyar nasamu sukayi hakuri

Sai gashi dan ladi ke duk abin danaso ahmad yayi shaye shayenma yafara yanzu haka maganar danake miki dan ladi kullum cikin jawomin magana yake

Sannan nakoma wajen bokan daya min aiki ya ce saidai in ba sunan ahmad din nabashi ba na tabbatarmai sunan ne sannan yace banyi aikin dai dai bane

Inda na nemi ya taimaka ya karya asirin yace min asirin bazai karye ba har abada sannan

Nace yakarayi to inhar dana zai lalace to tabbas ahmad ma sai ya lalace

Boka yayi yayi ya juyo ya kalle ni yace yayi bincike asiri bazai taba cin ahmad ba koda zan zagaye duniya ne dan akwai tsari a jikinshi mai karfi sannan ya duba kakanshi na tsaye akanshi yana masa addu a dare da rana kakansa shahararren malamine indaina wahalarda kaina wajen yimai asiri dan wahalar banza zanyi inbata kudina

Banyarda da maganar shiba dan ina ganin ya gaza haka nadinga bi kusfa kusfa wasu su amshi kudina da sunan aiki wasu su fadamin abin dana farko ya fada

Amma duka babu biyan bukata sai ma wani kwarjini dana ga ahmad din namin

dan haka ni yanzu na daura damarar koda zanyi yawo tsirara saina kassara rayuwar ahmad na wulakanta shi tunda asanadinsa nawa dan ya lalace shiya sa tsanarsa ta kara samun waje a raina

Zainabu ta dago tace amma hajjo ni wanne irin aiki kike ganin zan miki?

Sannan kina ganin akwai inda za awatsa rayuwar ahmad bayan kema kince anfada miki yana da tsari sosai a jikinsa
Chapter 18 · 0% Book details