← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 78

Sashe 67

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda na fadawa babanmu maganar ahmad nan ya shiga mamakin bikin d`an,ladinne har ya rage sati biyu basu jiba yaya musa bai fad`a musu ba
Koda ya kira baba musa cayayi shima ji yayi yanzu yana shirin sanar musu ne

Ya tausayawa yayan nashi dan yasan yana tare da muguwar mace ita ke zartar da komai ba dan haka ba ai dole sune zasu karbawa d`an,ladi aure

Baba abdullahi daya ji shine yace zaije wajen d`aurin auren
Dashi da mama zainabu

Mama zainabu bata so zuwa ba sam dan bata son abinda zai k`ara hadata da hajjo sam
Amma bata nunawa baba abdullahin bata son zuwan ba ta dai shiga shirin zuwan tare da k`udirin kome hajjo zata yi bazata biye mata ba

*************************

Fad`ime da kanta tayi tattaki tazo har wajen hajjo inda ta mata allah sanya alkhairi dan tasamu labarin komai akan bikin dama dai irin yarinyar da d`an,ladin zai aura da biyu tazo nan ta dinga yadawa hajjon habaicin akan anan aka k`are sauran maza za a kwaso mata hajjo dai bata biye mata ba

Sauran kwana uku biki saga gidan su aishar aka kawo akwati guda hudu acewarsu insun kawo gidan su hajjon su kuma su hajjon sai su maida a zuwan sune sukai saboda dangi da kuma yan sa,ido
Sai dai anyi shuka a idon mak`urwa ne dan ranar fad`ime tazo dan dama taji kishin kishin d`in cewar and`auke musu lefen uban yarinyar yace zaiyi

Aikwa nan ta shiga yad`a maganar kan sadaka aka bashi uban yarinyar shiyayi komai koda hajjo taji bata ji dad`in hakan ba bataso fad`ime taji ba dan ita taso ta bata haushine akan auran sai gashi ita ke difgar ta kaici

Ga maganganun mutane dake yawo akan yarinyar kowa ya bud`e baki baya fad`ar alkhairi akanta haka ta toshe kunnuwanta dan ita dai burinta d`anta ya yi aure na kece raini

Biki saura kwana d`aya baba abdullahi da mama zainabu suka sauka
Sun samu tarba kadaran kadahan dan shi dama baba abdullahi basa shiri sam da mutuniyar bare mama zainabu da ake jin haushinta

Bata sa zainabun cikin harkarta ba itama sai ta kama kanta ta dai zuba mata ido da ita da sabbin k`awayenta ta ga dai kowacce tazo tana gabatar da ita a matsayin matar k`anin mijinta

Washe gari aka d`aura aure inda bayan d`aurin auren hajjo hak`oranta kamar gonar auduga gani take yanzu ne tasamu sirika

Da daddare aka kawo amarya kamar yadda al,adarsu take katifar da mijin yasiya da yan kayayyakin nan sune zata tare dasu sannan k`awayenta zasu kwana da ita tukun washe gari su tafi in anyi wasa gidan su ango wasu ma sai sunyi kwana biyu sai dai angon ya dinga bin d`akin abokai

Sai amarya ta yi kwanaki uku zuwa hud`u tukun za akwaso mata kayan gado in iyayenta suna da k`arfin hakan in basu da k`arfin hakan kuma to iya kayan kitchen ne kawai za a kawo mata

Kamar yadda hajjo tayi tsammani kam ankawowa aisha kaya masha allah komai yayi yadda take so dan bak`aramin kashe kud`i iyayen aishar sukai ba wajen ganin su gwangwaje d`iyar su

Kayan kitchen kam harda na banza dana wofi
Sai dai fa ba anan gizo ki sak`ar ba duk abinda suke babu wani mutumtawa a harkarsu komai da gadara suke yinsa dan koda suka ji a d`akin da aishar zata zauna ca sukai basu yarda ba yarsu tafi k`arfin d`aki d`aya dole tasa hajjo basu d`akunan dake gaban nata su shamsi suka koma d`akin d`an,ladi dakunan suka zama biyu
***********************

Zainabu ina mai k`ara gargad`inki wallahi wallahi kar naji kar na gani kinsan dai abin da zai biyo baya inkika yi yunk`urin tona min asiri

Hmm hajjo kenan kisani badan tsoron ki dana keba ya sa nak`i tona miki asiri ba sai dan inbarka allah shida kanshi yasan yadda zaiyi dake akan zalintar bayinsa da kikayi tunda shi allah da kanshi ya haramtawa kanshi zalinci bare mu bayinsa kisani allah baya yafe hakkin wani akan wani har sai wanda yayi zalinci ya nemi yafiyar wanda ya zalinta in ya yafe masa

Dan haka ni yanzu bakya gaba na ta kaina nake ya,ya,na da basu auru ba har yanzu sun isheni ishara fatana allah ya basu miji nagari in aurar da su abubuwan dana kam har yau ina nai man gafara wajen ubangiji akan ya yafemin duk da nasan cewa tabbas nima na bada gagarumar gudummawa ta lalata zumunci amma alhamdulillah tun ina raye allah ya nuna min sun shirya da junansu sai fatan allah ya yafemin

Me kike nufi da sun shirya kina nufin salisu da abdullahi sun shirya da juna? hajjo tace tana mai gwalo idanu waje

Hmm zainabu tayi murmushi ikon allah kenan hajjo ai shi zumunci da kike ganin shi wata k`udira ce ta ubangiji zumunci nada matuk`ar girma wajen allah dan haka duk wanda k
Yayi k`ok`arin datse shi sai yaji kunya duniya da kiyama tun aduniya allah ke nuna masa ishara

Kinga mu munyi asirin amma da allah ya kawo lokacin karye warshi kinga ya karye

Kuma sun shirya abinsu

Dan haka ya rage naki ki bar su ya rage naki kiyi k`ok`arin k`ara shiga tsakanin su amma kisani da da da yanzu ba d`aya bane ba lallai kici riba ba kuma tabbas kika yi yunk`urin cutar da su wallahi saina tona miki asiri ninasan duk abin danayi nafila ne akan irin tarin abubuwan da kikai dan haka ya rage naki ni kisani wata banzar barazanarki akan zaki haukata ko ki tona min asiri ta daina tasiri akaina na yarda da allah shi zai tsareni daga sharrinki

Tass ta d`auketa da mari ni kike fad`awa maganganu haka zainabu wallahi baki isa ba ki `baromin aiki kin yi kad`an hajjo ta fad`a cikin masifa tana huci

Zainabu da tsananin zafin marin ya ratsata ta dago ta kalli hajjo dake tsaye kanta tana huci ta dafe kumatunta da tunda take da girmanta babu wanda ya taba d`aga hannu ya mareta kai ita bazata iya tuna lokacin da aka mata mari na k`arshe ba sai gashi yau god`ai god`ai da ita hajjo ta d`aga hannu ta mare ta

Cikin masifa ita ma ta tashi bata yi wata wata ba ta kifawa hajjon mari ta k`ara mata
Bata barta ta dawo daga tunanin data tafi ba ta fara magana

Ni zaki mara hajjo kike tunanin kin mari banza to wallahi k`arya kike dan kina son in rufamiki asiri akan ta addancin da kikai bai isheki b har saikin mare ni me kike nufi kinmari banza
Lallai kinyi wauta kuma asirinki kamar ma ya gama tonuwa matsiya ciya kawai

Hajjo da ta shiga wani hali sakamakon marin data ji a fuskarta bata yi zato ba bata ta`ba tunanin zainabu zata iya marinta ba ta d`auka zainabun data sani ce da mai mata biyayyah akan komai

Lallai d`an,adam butulu zainabu duk irin k`ok`arin dana miki a rayuwa da abinda zaki sakamin kenan kinyi kuskure kuma sai kinyi dana sani akan hakan

Baba abdullahi dake k`ok`arin shigowa parlourn maganar hajjo ta k`arshe ce ta daki kunnen shi

*_😍MAMAN `DAN ALBARKA CE😍✍️_*
09/11/2022, 2:24 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

_*PAID PAGE 41*_

Fasa shigowar yayi ya tsaya

Ai ni banga ranar da kika min ba hajjo gidan abdullahi ne dai zaki ce kin taimakamin na koma to kisani bawai da taimakonki na koma ba dama can allah ya k`addara zan koma

Sannan nice zance kin ha,inceni saboda kinsa na cutar da su batare da hakkin hakan ba
Ni yanzu bana tsoronki
Wallahi duk abinda kike ganin zakiyi ina jiranki inkin fasa nikuma zan nuna,miki iya karki
Gobe ma zamu bar garinnan insha allah

Jin motsin tawowarta yasa baba abdullahi saurin barin wajen
Yana tambayar kanshi me kenan me maganganunsu suke nufi kardai ace zainabu itama tana biyewa hajjo duk da ada yasanta da irin halin

Yanzu ya tabbatar ta daina amma jin abinda hajjo tafad`a yasa mishi tunanika kala kala sai dai amsar zainabun ya nuna kamar a kwai wani abu mekenan waye hajjo tasa zainabu ta cutar da irin wad`annan tambayoyin daya kewa kanshi ya bar wajen tare da k`udirin sakawa zainabu ido muddin ya kamata da wani laifi makamancin wanda yake zarginta tabbas sai ya hukunta ta

Bangaren hajjo da zainabu kam haka kowaccen su ke fushi da yar uwarta ahaka suka wayi gari inda a ranar su baba abdullahi suka juyo zuwa kano

*************************

`Ban garen amarya aisha kam da farko rimi rimi ta fara wa hajjo biyayya kullum da safe zata zo ta gaida ta sannan ta mata wanke wanke

Dan samun gata hajjo keyin abinci ta zuba musu kullum safe da rana haka take musu

`Dan,ladi ango kam sai warka jaminshi yake yana hura hanci shi yayi amarya

Matsalar farko da suka fara fuskanta daga wajen hajjo shine ta daina zuba musu abinci saboda yau kwana biyu aisha ko wanke wanken ta daina mata iyaka cinta da ita gaisuwa saita shige d`akinta sai dai inta girka ta zo ta d`auka suci

`Dan,ladi ganin haka yasa baice komai ba yayiwa aishar magana akan ta dinga dafa musu tunda tana da kayan abincin

Sai dai kash aisha ko yadda ake dafa taliya bata sani ba bakuma tace bata iya ba haka take kwabawa a hakan da taimakon salaha aci dai kar a mutu

Sannan ga yar banzar rowa intayi abincin a hakan sai taga dama zata sawa hajjo duk da wataran shinkafar kamar tuwo ake yinta

Ga shegiyar k`azanta sam bata da tsafta bata san gyaran d`aki ba bare gyaran jikinta duk wannan tsftar babu ita gwara farkon zuwanta tana yin wanka kullum ta canza kaya amma daga lokacin data fara girkin kanta sai tace aiki ya mata yawa sai tayi kwana biyu bata yi wanka ba sannan zani sai yayi kwana uku ajikinta bata canza ba
Chapter 67 · 0% Book details