Sashe 75
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tambayar shi suka shiga yi shi dai kawai binsu yake da kallo yana jin jina girman sarautar ubangiji tabbas rabon yarannan ne yasa har ya auri hajjo inba haka,ba tayaya ma hakan zata faru shida,ke zaune da matarshi cikin rufin asiri
Baba abdullahi ne ya kalli shamsu ganin sun tsatstsare su da tambayoyi ga malam liman anbarshi a tsaye kuma ga idon mutane kallonsu kawai ake yasa
Yace
Kai bashir nuna mana d'akinku mukaishi sannan bakuga bak'i bane kuka tsaya kuka tsare mutane da kallo da tambaya
Sai lokacin kunyar hakan ta kamasu suka tallabi mahaifin nasu da har zuwa lokacin ya kasa cewa komai suka nufi hanyar d'akinsu
Dukammu bin bayansu mukai zuwa can dan d'akina bazai shiguba yau saboda dad'ewar da mukayi bama nan
Ganin mun bar wajen yasa mutane kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa cikin mamakin abinda ya faru haka kowa ya watse sai aisha datayi hanyar d'akinta
Akan katifar su bashir aka kwantar da baba musa tukun shamsu ya d'ebo mai ruwa baban mu ya tallabe shi baba abdullahi ya bashi
Baba malam kam tabarma na d'auko na shmfid'a mai a gefe muma nida mama aisha da kalim da walid dake goye muka zauna a kan kujerar da ke d'akin
Ahmad kam tunda aka kama,baba aka shigo dashi d'akin y fice ya je ya bud'e d'akinmu ya shiga tattara wa dan yasan dole a buk'aci d'akin tunda ga mama aisha gani sannan hajjo d'akinta anriga da ankulle ta a ciki babu wasu d'akuna
Duk aikin dayake cikin sanyin jiki yake yinsa da k'uncin zuciya wanda gwara ma ace kuka yayi da wannan zafin da yake ji a zuciyar sa
Bayan bawa baban ruwa ne malam liman da tunda muka shigo baice komai bane yace mu bashi waje mu matan zai duba baba musa
Tashi mukai nida mama aisha muka fita kowa da abinda yake sak'awa aranshi da sanyin jiki muka nufi hanyar d'aki na da nufin in d'an tattara mana musamu mu zauna
Ina zuwa nasamu ahmad bawan allah har ya share d'akin yana goge ledar data sha k'ura tausaynsa ne yakamani ganin har yana da k'arfin halin iya tabuka wani aiki bayan irin wannan abun daya faru mik'awa mama aisha walid nayi na k'arasa gare shi cikin tausayawa inajin koni dana rasa mahaifiya ba abar tausayi bace akan irin rayuwar da ahmad yayi kana rayuwa da mutum kana mai kallon masoyi konace mahaifiya rana guda kwatsam ace ba itace ta haifeka ba bayan nan kuma tazo da bakinta tace ita ta kashe maka mahaifiya mai yakai wannan takaici da tausayawa
Kawo na k'arasa kaje kasamu waje ka huta
'Dagowa yayi da jajayen idanunsa wanda babu komai a cikinsu sai tsantsar tarin damuwa da bak'in cikin halin daya ke ciki babu musu yabani tsumman yasa kai ya fice
Ina k'arasa goge ledar nace mama aisha ta zauna cikin sauri na cire zanin gadon na shimfid'a wani na jona mana ruwan zafi tukun na dawo muka zauna jigum jigum babu wanda ke iya bud'e baki yawa d'an uwansa magana kowa da abinda yake sak'awa a ranshi babu ma batun yunwa dan ko ruwa bamu shaba
Kalim ne daya ke yaro ya fara min kishin kishin d'in kukan yunwa dole na tashi na duba inda muke aje kayan tea na tsiyayi ruwan zafin da har ya kusa tafasa na had'amai shayi na bashi
Aisha shigarta d'aki tayi tozali da d'an,ladi da har lokacin ke yashe a k'asa sai zanin gadon da uwarshi ta yafa masa
K'arasawa tayi wajenshi ta sa hannu ta yakice zanin gadon ja baya tayi cikin sauri ta dafe k'irjinta ganin irin aika aikar datayi gaba d'aya jikinshi ya tashi fatar duk ta salu'be har gabanshi
Cikin tsoron abinda zai je ya dawo ta yi sauri ta tashi ta shiga loda kaya a akwatinta dan tabbas tasan tayi 'barna ba kad'anba gwara ta gudu kafin hankalinsu ya dawo kanta danta san dole sai anbinciketa duk da ita akaiwa laifi amma ta kassarashi ba kad'anba
Lokacin data fito anfara kiran sallar magrib babu kowa tsakar gidan kowa yashiga d'akinshi ana jinjina al,amarin daya faru
Tazo dai dai k'ofar d'akin hajjo ta ji yadda hajjon ke ihun azo a bud'eta ita ta fito wallahi ba a isa ba a tona mata asiri ba
Lalla'bawa tayi cikin sauri ta nufi hanyar wajen kici'bus sukai da bashir wanda malam liman ya aika ya siyo ruwan zam,zam d'in da za awa baba musa addu,a
Tana ganinshi taja bya sai dai ganin ya shiga binta da kallo alamar kamar baisan abinda ya faru ba yasata cikin sauri taja a kwatinta tayi waje
_*😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE😍✍️*_
13/11/2022, 6:35 am - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*
*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*
*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*
_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_
_*PAID PAGE 49*_
Shigowa yayi gida yana tambayar kanshi to meyasa zata tafi duk da yana jin haushin ta ance tayi dambe da hajjo amma kamar ba akan damben bane ta tafi haka dambe kawai bazaisa ta fita haka a firgice ba
Haka dai ya shigo yana tunane tunane amma zuciyarsa sam bata yarda da fitar da aisha tayi ba
Har yaje ya bawa malam liman ruwan zam,zam d'in tunanin fitarta bai k'yale shi ba ga kuma ihun hajjo data ke har yanzu daga d'akinta anrasa wazaije gare ta ya bud'eta
Salaha ce data dawo daga islamiyya ita da umar ta shigo ta nufi d'akin mahaifiyar tata abin mamaki d'akin a rufe sannan ga ihun hajjo data ke akan ita a zo a bud'eta tana k'ara tona asirin kanta
Tsoro ne ya kama salaha da sauri tayi d'akin su aisha dan ta duba aishar ta tambayeta meke faruwa dan tun kafin ta shigo gida taga mazan wajen k'ofar gidan sai binta suke da kallo
Tana bankad'a labulen idanunta suka mata mugun gani d'an,ladi ta gani kwance duk da and'an rufa masa zanin gado amma duk k'unar jikinshi ta bayyana sai taga kamar ma baya numfashi sannan babu kowa d'akin yayi kaca,kaca
Cikin sauri ta fito har zuwa lokacin hajjo bata daina ihun data ke ba
Ganin kamar d'akin su bashir a bud'e danta hango haske da takalma da sauri ta nufi d'akin ta fad'a a firgice
Dai dai lokacin malam liman ya gama tofa addu,o,i a ruwan zam,zam d'in ya gama ba wa baba musa yashafemai jiki sun tashi suna shirin fita masallaci
Ganin mutane haka saita shiga binsu da kallo tabbas ta san baba abdullahi sannan ga wani mai kama da babannata sai kuma ahmad da tsohon da bata san waye ba da yaya bashir da shamsi sannan ga babanta kwance gado kamar ma barci yake
To meke faruwa a gidan? Kenan ta shiga tambayar kanta ga hajjo d'aki a kulle sannan ga yaya d'an,ladi kmar ya mutu ga kuma baba shima da mutane a kanshi yaushe baba abdullahi yazo?
Cikin rawar murya tana k'ok'arin danne kukan daya taho mata ta shiga gaidasu a gaggauce tukun tana yarfa hannu
Tashiga magana yaya ahmad yaya d'an,ladi kamar ya mutu fa ta shiga nuna hanyar waje duk jikinsa ya k'one bama tasan ta kamo hannunshiba ta na janshi sannan ga hajjo itama a d'aki ankulleta sai maganganu take wad'anda bangane musu ba zo kaga yaya tashiga jan hannunshi cikin rud'ewa
Kowa yayi mamakin jin d'an,ladi wai yana d'aki ya k'one mekenan?
Bashir ne tunawa da yadda yaga aisha ta fita a firgice da kuma yadda yaganta da akwati yasa shi zabura cikin sauri ya figi hannun salahar dan ahmad tsayawa yayi kawai yana kallonta
Ya kasa ta'buka komai kamar ma bayajin abinda take cewa
Suna zuwa suka tarda d'an,ladin yadda yake
Salaha kam tsoro ya hana ta k'arasa kusa da d'an,ladin sai bashir da shamsi daya biyoshi ne suka k'arasa su kansu sun tsorata da yadda suka ganshi a kwance duk ya k'one
Babu inda ya rage wuyanshine kawai zuwa fuskarshi basu k'one ba sai wasu y'an wajajen a jikin shi da basu samu ruwan zafin ba
Bud'ewar da bashir yayi cikin sauri ya maida zanin gadon ganinshi tsirara cikin k'arfin hali ya shiga dube dube ya lalubo wani zanin aishar dake kan k'yaure ya yafa masa sannan ya kasa kunnenshi ko yana numfashi nan yaji baya yi alamar suma yayi
Fita yayi da sauri yasamu su baba abdullahi dake alwala ya fad'a musu abinda ke faruwa duk da basu san meya faru ba baba abdullahi ne yabi bayan shi
Ganin halin da d'an,ladin ke ciki hankalinsa ya tashi nan yashi ga tambayarsu yaya akai kowanne su cayayi baisani ba bashir ne yace yaga aisha ta fita da akwati a firgice
Baba abdullahi ne ya duba shi yace suma yayi a bashir yazo suyi sallah sai su d'auke shi zuwa asibiti koda baba abdullahi yasamu babanmu da malam liman da ahmad ya musu bayani suna idar d sallah aka zo da k'yar da dubara aka cicci'beshi suka yi asibitin fmc dashi
Emergency aka nufa dashi suna zuwa aka shiga dashi
'Bangaren mu kam ganin ankira sallah yasa muka tashi muka yi sallah tukun ganin zaman bayi mana zaiba na tashi na juye ruwan zafin nayiwa su kalim wanka dayake yasha shayinsa mai kauri nan da nan barci ya d'auke shi da walid daya ji dadin ruwan zafi
Ganin sun samu barci saina shiga tunanin abinda zan nema mana muci dan babu batun in tambayi hajjo tunda bama tasan meta keyi ba yanzu
Duba kayan abincin dana tafi na bari nayi saina ga ina da taliya da macaroni da mai da maggi kayan miyane kawai babu da albasa cikin sauri na fito na nufo cikin gidan kozan samu yaron da zai siyomin
Ganin salaha nayi bakin k'ofar d'akin hajjo zaune tayi tagumi tana kuka hajjo dake bugun k'ofar harta gaji ta koma 'bare b'are a d'akin tana surutanta
Ganina kusa da ita yasa cikin sauri ta tashi ta nufo ni tana kuka tana min bayanin abinda,tazo ta tarar ni sai lokacin ma nasan wani abu yasamu d'an,ladi kenan shiyasa nazo naga hajjo na fad'a da aisha