← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 78

Sashe 60

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE_*✍️
09/11/2022, 2:23 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

*_PAID PAGE 34_*

Har lokacin bawani shiri muke da hajjo ba saidai ta rage abubuwa dayawa dan sam bana nuna tsoronta kwata kwata har zuwa lokacin kuma bamu san wanda ya aikata hakan ga kalim ba amma kullum nayi sallah ina addu,ar kowa ye allah ya tona asirin sa ya kuma sakawa yarona da nakasta shin da sukai

Salaha ta zama budurwa tubarkallah manema sun fara fitowa ita muna shiri da ita sosai tayi hankali kamar ba ita ba
Sai dai har zuwa lokacin babu labarin wanda yawa kalim haka maganar ma kamar an rufe bakinmu ko tada ta ba ayi sai dai kullum ina addu,ar allah ya saka masa ya tona asirin ko waye

A lokacinne kuma d`an,ladi yasamu sana,ar
Saida fetur a kofar gida an gyara wani d`aki dake gaban na hajjo
Su shamsi sun koma aka barwa d`an,ladin na bakin k`ofa a lokacinne yasamu damar cin karen shi babu babbaka y`an mata yake kawowa da abokanshi kala kala

Haka dai rayuwar taci gaba da tafiya

Kamar yadda hajjo taso ahmad ya fara gini amma fa d`akuna ne aka yanka har guda goma biyar na kallon biyar acewarta kowa ya dauki d`ai d`ai nida ita biyu biyu
Ba ason ran ahmad akayi hakan ba amma koda ya fad`amin cewa nayi ya k`yalesu ya gina yayi addu,ar allah yaba shi wani nashi daban

**********************

Ina kwance a tsakar d`aki kalim na gefena a kwance yayi barci
Naji sallama na tashi
Ina,mai amsawa

Nashiga bin wadda tashi go da kallo ina son tantance a inama nasanta
Dan ta rufe fuskarta da hijabinta ta sunkuyar da kanta zama tayi kan kujera ta sunkuyar da kaina tashiga gaisheni amsawa nayi ina mai k`ara binta da kallo

Tace Cikin mak`e murya da iyayi baki ganeniba ko?

Abin mamaki hausa rad`au a bakinta gaskiya ban wayekiba

Uhm um aisha ce

Aisha aisha? Nashiga tunanin ina na taba jin sunan gashi dan salon iyayi tak`i bude fuskarta sam bare ingani
Gaskiya banganeki ba

Matar d`an,ladi cefa

Sai maganar tamin banbarakwai matar d`an,ladi kuma?

Uhm ashefa ku hausawa budurwa kuke cewa to nufina nice wadda zai aura

Nace allah sarki sannu na tashi na dauki kofi na debo mata ruwa na ajiye mata na zubo mata abinci na kawo mata
Bak`onka annabinka a ganina bai dace in wulak`antata ba duk da bama shiri da d`an,ladin
Komawa nayi na zauna na jingina da gado ina kallonta

ta ja filet din abincin dan jaraba kuma tak`i bude fuskarta sam
Ahakan abin mamaki take cin abincin
Shinkaface da wake da mai da yaji dan ita nake yawan yi yanzu tunda nasamu ciki itace abinci
Wasa wasa yar tahalikarka babu kunya ko d`an rage wa batayiba ta share shi tsab ta kora da ruwa sai lokacin ta bude fuskarta bakace sosai dan harta fini bak`i ma tubarkallah tana da dogon hanci har baka saj dai tana da fad`in fuska sai bakinta shima fankacece idanunta kam har tsoro suka so bani manya manya ne sun wani firfito da sauri na d`auke kaina daga ganinta ba yarinya bace ta kusa cimma talatin

Sai bayan taci d`inne take tambaya ko d`an,ladi na nan taje wajen sana,ar shi baya nan kuma tayi dashi zata zo shine wani yaro ya rakota wajena data ce a rakata wajen matar yayanshi

Allah sarki bansaniba ko yana nan

Ok bari na je dan allah ina ne wajen momyn tamu inje in tambayeta ko ita zata san inda yaje

Mamaki nakuma shiga ikon allah hajjon ce kuma momy ko kuma wa sai dai na daure dariyar data ke tahomin saboda firiritar data ke da kuma wai in nuna mata wajen momyn su nace inkika fita daga lungun nan dakunan dake hannun damar ki nan ne wajen ta

Ok nagode tasa hannu a hijabinta ta ciro 1k ta ajiyemin gashi ki ajiyewa babanmu in ya tashi asai masa sweet bansan zan shigo ba dana siyo masa tasa hannu ta shafi kan kalim
Ni sai bayan ta shafi kan kalim d`in sannan na fahimci shi take nufi

Tamin sallama ta tafi
Tabarni da mamakin ta

Hajjo dake wanki tsakar gida jin sallamar bak`uwa yasata d`agowa
Tana amsa sallamar cikin boye fuska ta tsugunna har k`asa momy ina wuni

Sakatoto haka hajjo ta tsaya tana kallonta momy kuma can kuma sai tace lafiya lau
Wace ce saita d`an bude fuskarta kad`an aisha ce ta d`an,ladi

Ayyoh aisha ya kike ya su mamanki ta fad`a cikin washe baki tana mai tashi daga tsugunnon data yi
Ta kama kafad`ar aishar tashi kinga bismillah zo muje d`aki

Zauna zauna anan ta zaunar da ita kan tabarmar data shimfid`a dadduma akai
Bari na kawo miki ruwa

Cikin rawar jiki ta fita ta aika asiyo mata pure,water ta dawo ta zauna yakuke ai d`an,ladi nayi min maganar ki sosai yasu ciroman?

Suna lafiya lau masha allah nan aka kawo ruwan ta ajiye mata gashi kisha

Aisha budurwar d`an,ladi ce da suka had`u a yawace yawacenshi dayake sun had`une a wajen wani party da abokinsa ya shirya na birthday dinsa ita ta fara masa magana shi kuma dayake mayen mata nan da nan suka d`inke suka musayar number waya
Shikanshi ya manta da wata aisha sai daga baya data kira shi tukun ta mai bayanin kanta tukun ya ganeta

Daga nan suka fara soyayya

Aisha yace ga chiroman gari su biyu ne a wajen mahaifinsu ita da k`anwarta aisha ta taso sam babu k`waba bare k`yara yar gata ce batasan komai ba saidai tayi wanka ta shirya ta fita ko in ana da party ko biki itace gaba gaba wajen zuwa nupe,day
Aisha nada shekara ashirin da bakwai sam bata da kamun kai daga ka ganta da wannan yau sai ka ganta da wannan gobe

Tunda suka had`u da d`an ladi taji a ranta tabbas ta samu mijin aure duk da tana tsoron kaishi ga chiroma kasancewar su nupawa shi kuma bahaushe amma tuna duk abin da tace a gidansu shi akeyi yasa hankalinta kwanciya tasan inda zata samu matsala kawai daga wajen mamanta ne dan akwaita da kishin yarenta amma ko itama inta dage akan cewar sai d`an,ladin ba a da yadda za ai da ita

Inda shikuma d`an,ladi koda suka dawo suna soyayya da aishar ya d`auketa a matsayin abin rage zafinshi ce kawai dan so dadama yakan d`auketa suje d`akin abokanshi suyi abinda za suyi dan sam bata hanashi kanta
Baitaba kawowa a ranshi zai aureta ba dan shi yafi son yarinya k`arama kamar dai aminatu lokacin da aka aurota
Wadda sai yadda yayi da ita sam baya son manyan y`ammatan nan
Bai yi sha,awar aurenta
Duk lokacin data masa maganar aure sai ya zille ganin zai bata matsala tuni tayi maganin abun ta hanyar mallakeshi

Haka kawai ya tsinci kansa da son aurenta tsamo tsamo jiya ke inbe aureta ba kamar zaiyi hauka

Inda har shi da kashi yayiwa hajjo maganar aishar hajjo jin daga gidan data fito yasa itama ta aminta da had`in kodan tabawa mak`iyanta haushi irinsu fad`ime data hanawa d`an ladin auran d`iyarta
Dan taga irin matar da d`an,ladin zai aura tasan sai sun raina kansu

Wannan shine asalin haduwar d`a,ladi da aisha

Haka suka zauna hajjo sai rawar jiki take wa aishar tayi nan tayi nan koda zata tafi haka tashiga d`aki yan sabulan wankanta dana wanki da ahmad ke siyo mata ta tarkato ta zuba a leda tabawa aishar harda su rakiya aka mata

Daga lokacin kuma sai yazamana aishar na yawan kawo mana ziyara duk da ita da bakinta takance min hajjo batason tana zuwa wajena nidai ban tofawa harta gama karad`inta tayi gaba dan intazo wallahi har isata take
Tana yawan kawowa kalim kayan kwadayi amma tana tafiya nake amsa in zubar saboda ita kanta banyar da da itaba sam

************************"

Qaunah inkin gama cin abincin kije wajen hajjo kimata gaisuwa an kira daga gida allah yayiwa kakarmu mahaifiyar hajjo rasuwa

`Dago kaina nayi daga cin abincin dana ke dan yanzu nazama acici bana awa biyu banci ba bamu dad`e da cin abinci da ahmad ba amma harni nakara zuba wani ina ci cikina yanzu watansa bakwai kenan
.
Ayyah yaushe tarasu nafad`a cikin jimami

Jiya daddare

Allah yamata rahama yasa ta huta

Amen

Bayan nagama cin abincinne naje wajen hajjo wadda na tarda ta zaune idanun nan sun k`ad`a sunyi jawur
Sun kumbura alamar tasha kuka

Na gaidata namata gaisuwa

Ta amsamin jikinta a sanyaye nidai ban tsaya ba nayi gaba abina

Koda na dawo d`akin ahmad ya fita da kalim dan dama suna shirin zuwa wajen askine

************************

Wallahi yaya bawai zuwanne bazanyi ba kinsan dai sharad`in da boka ya bani banason in tako garinnan yanzu dan ahmad naji yana maganar biyoni dan shima yayi gaisuwa
Kinkuma san abinda hakan yake nufi gwara na hakura da zuwan kawai

Inna kuma zan mata addu,ar allah yajikanta kawai dan gaskiya innazo komai zai iya faruwa kinsan bazai yiyu nazo garinnan ba ace kakan yaronnan baisan nazo ba dan ahmad d`in da kanshi yake cemin dan nakaishi yaga dangin babanshi yake son bina

Daga can cikin wayar yayarta ta talatuwa ta fara magana cikin fushi yanzu ke mero saboda wani ahmad har inna ta rasu yau kwana biyu baki fara shirin tahowa ba harkina cemin bazaki zoba da baknki dan wani banzan cikar burinki?

Wai shin shi ahmad d`in uban meye kike samu wajen shi wace riba kika ci akan duk abubuwan da kike mai tunda kekanki kinsan ba tasiri asiri yake akanshiba sai wahalar da kanki kike saboda d`an iskan yaronnan zaki cemin bazaki zo wajen rasuwar mahaifiyar mu ba mutane sai cigiyarki suke ina cewa kina hanya

Duk gatan da inna ta nuna miki ta fifitaki akan mu tun kina k`arama da abinda zaki saka mata kenan ace ta mutu kikasa zuwa gaisuwa fisabilillah anya kwa mero kina ganin kinyi dai dai
Chapter 60 · 0% Book details