Sashe 3
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nayi sauri na karasa na dauki dankwalin kayan na tsara daurin dankwalina na zamani ya zauna das akaina natashi tsaye Na fito a amaryata sak na fara feshe jikina da turarukana masu dadin kamshi wanda koyaushe ahmad na yawan tambayata da wanne irin turare nake aiki gasunan dai akan mirro amma sai ya rasa wanne ne yake fitar da daddan kamshinnan sai dai na yi murmushi kawai
Nakarasa
Na tsaya gaban madubin ina kallon irin baiwar da allah yamin ta sihirtaccen kyau wanda atashi daya inka kalleni da wuya ka gano shi farat daya
Ban kasance kyakykyawa ta kuzo mugani ba yadda baza asakani a layin kyawawa can can ba haka baza asani a layin munana ba na kasance niba doguwa ba kuma ba gajera ba ina da diri me kyau ana yawan fadamin saboda haka tun ina budurwa nake ta ammali da hijabi da wuya ka ganni da mayafi Fuskata yar madaidai ciya mai dan fadi sai hancina masha allah dan madaidaici akasanshi kuma dan karamin bakina ne wanda innayi murmushi jerarrun hakorana farare tas kan bayyana sai idanu da allah yamin tubarkallah dara dara farare tas asaman su kuma Gashin girata ne kwantacce me yalwar cika
Nidin baza a kirani fara ba haka baza asani a layin bakake ba nakasance wankan tarwada ce na juya ina mai godiya ga allah da baiwarshi gare ni
Na dauko turaren wutana na tsinke kasancewar lokacin damuna ne kuma bana son komawa gurin hajjo dana samo gaurashi nasa na kwalba sai na sa ashana na kunna na sokashi ajikin kaskon turaren wuta na dauki room freshener na kara fesawa a dakin take dakin ya gauraye da daddadan kamshi
Sallamar ahmad naji na amsa ina mai yimasa sannu da zuwa.....
ban rufe bakiba ya budemin hannayen sa alamar yana bukatar in taho na noke kafada ina rufe fuskata da hannayena
Yace haba mana taho mana inji duminki inshaki kamshinki
Na make kafada nasa hannu na rufe fuskata
Daya ga bani da niyar motsawa sai jinayi an dagani sama da sauri na makalkaleshi na cusa kaina kirjinsa ina shakar daddan kamshin turarensa
Yayi ta juyi dani yana zagaye dakin dani
Ina dariya nashiga cewa don allah saukeni
Yace um um aisaina fanshe kin zuwan da kikayi yarinya
Nace inada nauyi fa zaka gaji
Waya ce miki ina gajiya da daukarki ko jin nauyinki aijinki nake kamar wata yar baby ahannuna ya kasara yana me direni akan doguwar kujerar dake gefen kofar shigowa
Yana direni nayi kokarin tashi in gudu yayi saurin bina ya danne yana tura kanshi wuyana yana shinshinata tare da fesamin numfashin sa
Na dan dago da kanshi da hannuna sai naga idanun sa a lumshe ya bude su ya zubamin yana min wani irin kallo da yake sani kara jin kunyar shi nayi saurin sunkuyar da kaina ina mai wayancewa da dan kama hannunsa
Kaga My tashi muje muci abincin karya huce nasan kana jin yunwa
Ya make kafada ni um um kibarni ahaka kawai dumin jikinki kadai ya isa ya kosar dani
Na zaro mishi dara daran idanuna nace rufamin asiri katashi muje kaci kajii
Ya yi murmushi ya busa min iskar bakinsa to mai da idanun adaina hukuntani da su haka
sai kunya ta rufeni nayi dabara na zame na tashi nayi hanyar bayan kyaure inda kwandon wanke wanke na ke aje na dauko flet din abinci nazo na shimfida dadduma na dauki farantin abincin na kawo na aje naje na dauko kofin ruwana naciko shi da ruwa na aje na zuba mana abincin a flet daya don bayason yana nan inci abinci banjirashi ba yafison muna ci tare
Na ce sakko muci abincin kaji
Ya sauko ya zauna nima nakaraso zan zauna yayi saurin jawoni ya min masauki bisa cinyar sa ya dau cokalin yafara dibowa yabani na bude bakin ina mai bismillah a kunyace na amsa har yanzu nakasa sabawa da hakan
shima yace saura ni
Na amshi cokalin na debo nadan juyo ya bude bakin na bashi muka ci gaba da ci
Can Naji anturo kofar net din ba sallama sai bayan ta shigo tayi nayi sauri na zabura na sauka daga cinyar sa na dan matsa gefe
Ba wata bace face salaha data shigo ko unifoam din jikinta bata cire ba da alamar yanzu ma tashigo halin salaha nacimin tuwo a kwarya ita data ke mace ma kenan insu mazan sunyi anmusu uzuri ai ita macace ko banza gidan wani zata amma sam bata da da,a da tarbiya in anyi magana intayi abu hajjo tayi caraf tace ai yarinyace zata daina
Yarinya wacce ke cikin shekara ta goma sha hudu itace zatayi abu ace yarinta ce ko tayi wani ance haka wani ai ya wuce yarinta sai wauta
Ta tsaya ta shiga binmu da kallo tukun ta zabe wanda zata gaisar
Yaya ahmad ina wuni ta fada Tana mai kallonshi
yace lafiya kalau salaha
yanzu kika dawo makarantar?
tace eh
yace amma yau kun dade kin tsaya biye biyen gidajen kawayen ko?
tayi shiru tana daga inda take alamar dai ta aikata ..
.
Yace hmm kinyi kenan salaha kidaina hakan baida kyau ke yanzu kin wuce wannan yarintar in an tashe ku kidinga kokari gurin dawowa gida akan lokaci kinga ko wasu yan ayyukan kya dinga taya hajjo
Ta zumbura baki tana dan kunkuni ciki ciki
Ya girgiza kai yace to ita auntyn naki baki gaisheta ba ko baki ganta ba?
Ta kalleni ta dauke kai alamar dai bazata gaisar dani din ba..
Nace dan allah ka kyaleta hankalinta ya daukeni kaga fa tana shigowa kafara mata fada taya zata tuna da gaidani na karasa fada cikin son boye laifinta duk da nasan rainine ya kawo hakan
Sai ta kalleni ta wani ja tsaki ni wallahi na tsani bakin munafurci mutum bansa dashi ba sai ya jono bakin sa cikin maganar mu ta yan uwa ina sani naki gaidakin saime aiba ke kika haifeni ba ta kare fada tana mai murguda baki....
Ahmad ya zabura zai bita ya kamo nayi saurin riko shi kaga kyaleta yarinta ke damunta don allah
Ya kalleni haba Qaunah yaya ina kallo zan bari kannena su rainaki in ita hajjo tayi a matsayinta na uwa nayi shiru aisu kannena ne yadda suke bani girma haka ya kamata su mutumtamin ke
Nadai shiga bashi hakuri cikin lallashi na dauki cokalin abinci nashiga kokarin bashi ina kokarin kawar da abin da ya faru ya girgiza kai na a a na koshi nace a a don allah ci mekaci da har ka koshi nashiga lallashi da kyar ya yarda muka ci gaba da cin abincin
*************************
Da ihu ta karasa kofar dakin hajjo ta na tumamin iya karfinta tana isa ta fadi tana birgima
hajjo da idar da sallar ta kenan ta bazamo taji kukan yar gwal ke salaha keda wa yanzunnan daga dawowar taki makaranta?
Cikin kuka tashiga cewa ba yaya ahmad bane daga zuwa dakinsu dan na tarar da su sun rungume junansu suna ba juna abinci a baki shine kawai dan na gaida shi ban gaida aminatu ba wai shine ya hauni da fada a gabanta ita kuma da bakin munafurci harda bashi hakuri shine fa nace ba za a gaisar dinba shine yaya ahmad ya mammareni ta karasa tana mai murza idanunta
Madadin hajjo ta tsawatar mata akan yadda ta bayyana sirrin yadda ta same su a a ita hankalinta na kan marin da yar gwal tace anmata
Mari?
Ta fada da karfi shi ahmad din ya mareki kan bala,i akan waccan Figaggiyar to wallahi bai mari banza ba tashi muje maza maza Ido na idonshi ya fadamin meye hujjar sa na marinki oh duniya inkana raye baka gama kallo ba ta karasa tana mai kama hannun salaha ta mikar da ita ita kuma sai kifkifta ido take tana murza su
Ta figi hannunta suna tafiya tana banbami .
Maman Aisha ce dake kofar dakinta tana wanki ta dago wai hajjo ahmad dinne ya daki salaha akan matar shi?
Hajjo ta juyo to akan wa kika sani ahmad zai daketa tunda nake da shi bai taba sa hannu akan kannen sa ba amma yau saboda waccan bakar kadarar ya da kar min ya wadda koni da nasha wahalar nakudar ta bana dukanta sai shi sallamamme ta karasa fadar cikin nuna lallai abin ya kona mata rai..
Hmm aikwa dai gwara kiyiwa tufkar hanci tun kafin abin ya girmama gaskiya karya fara sa hannu kan yaranki ina dalili maman Aisha ta karasa fada cikin munafurci da son kara hura wutar
Aikwa ba yarda zanba yanzu zanje in shata masa layi da ya,ya na duka ahto in ita ta shanye shi ya fara tsanar yan uwan shi ni bata shanyeni ba bokan uban nata bayyi nasara ba taja hannun salaha tayi gaba...
Maman Aisha tayi saurin tsame hannunta daga ruwan wankin tana wani munafukin murmushi
tabi bayan hajjo ahankali ta tsaya daga kofar lungu saboda bakar gulma ai sai naji yadda zaku kwashe ta fada tana mai kasa kunne...
*_😍MAMAN DAN ALBARKACE✍️😍_*
*Wannan littafin na kudine idan kinason cigaba da karantawa zaki same shi akan farashin normal group 300 VIP 400 masu so ta private 1000 ki turo kudin ta wannan account number 2375144550 Lawali ahmad zenith bank ki turo evidence ta wannan number 09138320449 ko katin MTN ta wannan number 09138320449*
*Idan kuma littafin mu guda biyu kikeso TUSHEN MU DAYA da FANSAH 2022 Zaki turo normal group 500 VIP 800 ta private 1000*
09/11/2022, 2:15 pm - Maman Dan Albarka Ce: *🪴TUSHEN MU DAYA🪴*
*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE😍_*
*Free Page3️⃣*
*Masu son a tallata masu hajarsu ko link na group suyi magana ta wannan number 09138320449*
Muna tsaka da cin abincin naji Nafara jiyo hayaniyar hajjo ta doso dakina da sauri na tashi na doshi kofar ahmad ma ya biyo bayana..
Wuce muje nace wuce nace mana ah lallai kin maru tunda gashinan har kina tsoron kara sowa bari ni naje naji dalilin marin hajjo tace
Na tarda hajjo abakin lungun tana janyo hannun salaha tana maganar mamaki da al,ajabi ne suka daskarar dani a tsaye