← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 78

Sashe 21

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inda shima babanmu innaje can nakan masa maganar dan uwanshi amma sai ya rufeni da fadan yanakeso yayi shi bazai jure wulakanciba abdullahi hanyar wulakantashi yake nema dan yaga yafishi arzikine shi ba arzikinsa yakesoba

Cikin bacin rai muke kare maganar kuma nima nakasa daurewa muddin zanje gidan baba abdullahi indawo sainayiwa mahaifina batun amma saina fuskanci ko maganar abdullahin bayason akawomai yanzu ranshi zai baci tuna irin wulakanci da yakemai

Haka dai suke rayuwar basa ga maciji da juna

Zuwa lokacin muna shirin shiga aji hudu kuma lokacinne alamun budurcina suka kara fitowa lokacin inada shekara goma sha biyar banida cikar kirji amma inada hips gwargwado dan dalilin dayasa kakarmu bata barina ina fita da gyale kenan nima kuma sainafi jin dadin hijabin

A lokacinne kuma samari suka fara kawomin hari ba damar inje makaranta kona fita saina samu wanda zai biyoni inda koda anyi sallama dani ba fitar nakeba dan nikaina kunya nakeji ace anganni ina zance

A lokacinne kuma mahaifina yazo yasamu kakanmu akan maganar da sukayi yayanshi akaina

Inda kakanmu yasawa abin albarka yaji dadin hadin da suka ce zasuyi

Inda bayan wucewar babanmu ya kirayi kakarmu yana mata bayani

Lokacin nazone in tambayi kakarmu zani gidan su siyama kawata inason zuwa ta aramin wani novel dan ina dan karance karance

Ina kawowa kofar yayi dai dai da fadin kakanmu ke yanzu ya kike gani za a fitone a fadawa aminatu tun wuri kokuma yaya dan karfa aje tafara son wani azo da maganar kinga abin zaiyi wuya kenan tunda dai ya riga da yace yabawa dan yayansa kinga ai dole tasani ko

Kakarmu ta gyara zama tace a a malam mudakata tukunna bakaji hikimar shi yayan nashiba nacewa sai ahmad yazo sunga juna insuna so ai abune mai sauki allah dai ya kaimu lokacin zuwannashi suka amsa da amin

Labe in ana magana ba halina bane asalima ko magana kake da wani akusa dani inna fuskanci bakason naji nakan tashi inbar wajen amma bansan meyasa na tsaya na saurari firar su baba malam ba inda kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka naja kafafuna da kyar nakai kaina daki

Nan nafada tunani yanzu ni za abawa wani wanin ma da bansansa ba kuma har can garin su baba musa a yadda nakejin baba na fadar nisan garin haka za arabani da yan kannena farin cikina yanzu shikenan bazan zauna kusa da su kaka ba nan nashiga tunanika daban daban inda karshe na fashe da kuka nasan tabbas da mama na da rai babu maicewa zai badani wani gari amma daga rasuwarta har anfara maganar aurar dani nawa nakema da za asamin ido gasu aunty salima nan da hajara saini za abada

Amma tunawa da irin son da mahaifina kemana tunda naga har ya amince nasan cewa tabbas bakaramin dalili bane zaisashi amincewar haka dai naketa sake sake karshe kuma saina dawo bawa kaina dariya

Ni daga jin magana saina sawa kaina damuwa bayan ma naji inna nacewa babu dole to yasen in hakane yana zuwa zance ni banasonshi bashikenan ba magana ta kare da haka na tashi nacigaba da harkokina sai Dai gidan su siyamar da banjeba kenan ranar

*************************

Haka muka cigaba da rayuwarmu gidan kakanmu sai dai duk ranar alhamis da juma,a nakanje kasuwa wajen su baba na amshi makullin gidanmu inje in wanke kayansa wani lokacin harda na yaya yusuf saboda shima bawai zama yake samu ba

Inna gama in gyagygyara gidan in share in rufe in maida makullin wajensu

Bazan manta ba wata ranar juma a bayan ansakko masallaci naje maida wa baba makullin gidanmu kasuwa bayan nabashi na juya inata sauri dan inason inje in biya karatuna na islamiyyah dan nasan gobe dole malam idris zai amsa gashi ko rabin shafi ban biya ba kuma shafi biyune

Nakai bakin titi ina,neman adai dai ta sainaji anyi sallama kusa dani na juyo banmayi tunanin dani yake ba inda saida yakarayi ya hada dacewa malama magana nake na juyo na kalleshi bakine dogo sam bashi da jiki irin dai siraran mutanen nan ne sai uban hanci har baka da zanenshi irin na barebari kana kallonsa ma zaka gane hakan na amsa sallamarsa a tsorace

Yace sunan malamar nakeson ji sainayi banza dashi dan ni mutumin sam baimin ba kwata kwata ga wani uban zanenshi a fuska dai dai lokacinne kuma,nasamu a dai dai ta nayi sauri wajen fadawa ina allah allah ne dama in rabu da wannan mutumin danakejin tsaiwa kusa dani ma dayayi na tsaneshi ballema niba wani zance nakeba samarin ma kansu tsoronsu nake

Ina shiga mai adai dai ta yaja

Muka tafi muka barshi a wajen

Bayan kwana biyu ina tsakar gida nida inna muna cin tuwon Masara da miyar danyar kubewa inda ina ajiye da yajina agefe ina sawa a gabana dan fadan damuke da inna kenan nace ni da ita zanci ita kuma tace bazan sa yaji ba ina sawa agabana ta na balbaleni da fadan cin yajin inda nayi biris da ita naci gaba da cin tuwona

Saina ji yaro na sallama wai ana sallama da budurwar gidannan inna ta kalleni na kalleta na kwashe da dariya inna wace budurwa a gidannan dan allah?

Ta mikomin dakuwa ungo nace akwai wata budurwane a gidannan bayan ke

Saina hade rai ina turo baki nace ni wlh yarinyace ba budurwa ba kai kaje kace babu budurwa a gidannan

Yaron har ya juya zai tafi inna tace kai kaje kace tana zuwa

Na kalleta yanzu fisabililah inna kinsan bana zance zaki wani ce ace ina zuwa sai dai kitashi ki rakani danni bansan mai zance ba innaji

Inna tashiga salati tana tafa hannu aminatu nidince zan rakaki zance ni yau naga abin daya fi karfina kinci gidanku tashi ki fita mara kunya inkinje karkice komai ki tsaya maga ta yadda zamu aurar dake ja,irar yarinya kawai

Haka na tashi ina maijin haushi ina diddire kafa na wuce na wanke hannuna na kuskure baki na zumbula hijabina nakama hanyar fita

Ina isa zaure na dan leka kaina naga banga kowaba har zan juya sainaji ance gani nine mai nemanki na dada lekowa sainaga mutum zangangan tunda akwai hasken kwan nepa a kofar gidan tuni na ganeshi bawani bane sai wannan mutumin da ya tareni a bakin kasuwa

Nan naji wani takaici ya turnikeni gashi dama banso fitowar ba

Nashiga karemai kallo yaci rigar shaddarshi me dan saukin kudi saidai dinki irin nada dinnan ne tazarce sainaga kayanma kamar sun mai yawa yawani kima uwar hula kamar ya arota sai wani bakin glass daya kwama wlh kadan ya rage na kwashe da dariya nadai maze

Shikuma sai dashare min baki yake ya karaso bakin zauren

Nima,saina dan fito na kalleshi nama kasa magana saboda takaicinsa

Shiya fara magana gimbiyar mata fatan nasameki lafiya?

Ya fada yana wani kwakwkobarewa shi lallai sai ya burgeni

Na gallamasa harara wadda nasan dole yagani amma sainaga bai ma nuna,hakan ba

Nayi banza dashi

Haba gimbiyar mata yakamata kiyi magana ko da muryarkice inji kozanji sanyi tun ranar da na ganki kika shiga raina na biyoki naga gidanku tun ranar naso zuwa amma sai wani uzuri ya tsareni kullum ina cikin tunaninki dalilin dayasa na yanke shawarar tunkararki kenan

Da farko sunana halliru ni dan asalin mai dugurine a damaturu nazo kano nemane ni kwandastan mota nake kuma kullum ina samu gwargwado ina zaune wajen yayanane da niyar aurenki nazo inhar kin amincemin sai na turo magabata na ayi komai da wurwuri kinsan ance da zafi zafi akan bigi karfe

In anyi auren zan kaiki can garinmu inyaso ni ina nan duk bayan lokaci zandinga komawa

Ina fatan dai namiki ya karasa fadar yana kara gyara zaman glass din idonshi shi lallai ya gabatar da kanshi

Wallahi daya fara magana haushinsa na fara ji amma jin yasaki baki sai zuba yake harda wani cewa shi kwandastan motane zai kaini meduguri da dai sauran soki burutsunshi sainaji kawai yafara bani dariya bawai na raina sana arshi bane sam amma ni kwata kwata baimin ba sannan daga zuwa sai maganar aure ko sunana bakasaniba

Da wani sunanshi wai halliru haka dai na maze dan mu rabu lafiya na dago nace

Bawan allah bari na koma gida kar kakanmu ya dawo yaganni dan ba ama barina zance sai anjima

Yayi sauri gurin tarar numfashina ai kya fadamin ko sunanki ne yammata sannan duk baki bani amsoshina ba kodai banmikibane yakarasa yana kallon jikinshi

Na sa hannu a bakina kamar zance eh bakamin ba amma tunawa babu kyau wulakanta dan adam yasa nace a a

Sunana aminatu amsoshinka kuma yanzu banidasu dan karatuma ninake babu maganar aure a gabana yanzu kayi hakuri kafin yakara magana nayi cikin gida da sauri ina kunshe dariyata

Dan allah allah nake naje nabawa inna labari wlh mutumin yabani dariya ba kadanba

Ina karasawa na cire hijabi na jefa kan tabarmar da inna ke zaune na zauna kusa da ita nahau babbaka dariya ina rike ciki

Inna ta kalleni kai aminatu sai kintsin allah mene zaki wani shigomin kina babbaka dariya kamar wata sabon kamu

Na kalleta nace to ai sabon kamunne yazo wajena inna kekinganshi nikam gaskiya banida sa,a daga fara tsaiwa zance saina na gamu da wannan
Kinganshi kwa inna kamar irin samarin kauyennan daga zuwa sai maganar aure nan nashiga bata labarin abin da ya faru

Ta kalleni allah ya shiryeki aminatu ai gwara da baki masa dariyar ba ko maganar banza dan arabu lafiya bakisan bakinsa ba

Nace aina fadamasa ma ni banshirya aure yanzu ba

Tace allah ya kyauta miki to mene na dariyar kuma

Nace bazaki ganeba wallahi na karasa fadar ina mai tashi na kwashi hijabina nayi hanyar dakin da muke kwana dan na manta ko net ban dauramana ba gashi su bahijja sunyi barci

Inna ta bi bayana da kallo allah ya shiryamin ke aminatu ya baki mijina gari wanda zai rike mana ke amana

*************************

Haka halliru ya maida kofar gidanmu wajen zuwanshi wani lokacin ma in ina dawowa makarantar islamiyya da yamma ina yawan ganinshi a hanya koya min magana ban kulashi dan haushin tarenin dayake nakeji

Dan ko yazo gidan ma bana fita haka inna zata karaci fadanta inyi biris dan ba najin koba halliruba zan fara zance yanzu
Chapter 21 · 0% Book details