← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 78

Sashe 22

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka dai har ya hakura da zuwan nikwa nace yadaifi
***************"******

*_BAYAN SHEKARA BIYU_*

lokacin munyi saukar makarantarmu nakara hankali Shekara daya ta ragemin inkammala makarantar secondary nayi samari kala kala saidai suna zuwa nake fada musu anmin miji wasu su hakura wasu kuma suki daina zuwa saina dinga hadasu da baba malam yana musu bayanin sunmin miji

A lokacinne kuma babanmu yasamu wata bazawara ya aura inda bayan auren ya bukaci amsarmu inda babu wani ja kakanmu ya amince mai dan yasan yayi hakurin barinmu

Bayan munkoma gidan baba da matarshi mai suna mama rukayyah ba laifi tadan manyanta dan yayanta biyar hudun suna gidan babansu tazo da daya

Tunda muka koma sai ya zamana mama rukayyah babu ruwanta da hidimar su ilham nice ki musu komai kama yadda nasaba kafin inje makaranta saina musu wanka na gyara tsakar gidan na share dakinmu tukun in wura mata wutar abin kari amma sai lokacin data ga dama zata fito

Tayi kullum sai munyi latti gashi nikuma jarabawarmu ta karato nafi bukatar tafiya da wuri dole tasa na amshi abincin karyawar kafin natafi nikeyin komai

Haka babu ruwanta da harkarmu bandamu ba dan nasan saboda kannena nakeyi

Duk da samari na yawan kawomin hari amma,bana kula kowa duk da lokacin nakai minzalin tsayawa dasu din amma tun lokacin da baba ya zaunar dani ya bayyanamin kudurinsu

Na cirewa raina cewa zan tsaya wata soyayyah dan nasan koda sukace sai inaso za ai bawai yana nufin in bijirema bukatar su bane shiyasama banma faraba duk wanda yazo babanmu kan fadamasa yamin miji

Wasu sukan hakura wasu kan kafe da nacin zuwa amma rashin fitowa ta kansawa su daina zuwan bandamu ba dan yafimin ace nafara soyayya kuma karshe ban auri mutumba yaga na yaudareshi

Kokuma ni in hadu da wanda zanji bazan iya rabuwa dashiba ba inzo in bijirewa umarnin mahaifina bana fatan hakan

Ranar wata alhamis da yamma nadawo daga gidan baba malam ina shigowa naga takalma a kofar dakin yaya yusuf na maza sai kuma muryar auty nafeesa danaji a dakin mama rukayyah

Haka nashigo cikin sake sake shin baki mukai maza aka bude dakin yaya yusuf da yammar nan ?

Sannan aunty nafeesa ce yau nakejin muryarta a gidannan ita da kanta ikon allah kome ya kawota? oho naba kaina amsa ina mai karasawa kofar dakin mama rukayyah

*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE_*😍✍️

*Wannan littafin na kudine idan kinason cigaba da karantawa zaki same shi akan farashin normal group 300 VIP 400 masu so ta private 1000 ki turo kudi ta wannan account number 2375144550Lawali ahmad zenith Bank ki turo evidence ta wannan number 09138320449 katin MTN ta wannan number 09138320449*

*Idan kuma littafin mu guda biyu kikeso TUSHEN MU DAYA da FANSAH 2022 Zaki turo normal group 500 VIP 800 ta private 1000*

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
09/11/2022, 2:16 pm - Maman Dan Albarka Ce: *🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE_*😍

_*FREE PAGE SUN KUSA KAREWA MAZA KIYI KOKARI KI MALLAKI NAKI YAR UWA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI RAHUSA 300 KACAL NORMAL GRP POSTING SAU BIYAR A SATI VIP 400 PASTING KULLUM MASU SO TA PRIVATE 1000 SAU BIYU KOWACCE RANA*_

_*IN KUMA DUKA LITTAFIN BIYU KIKE SO FANSAH DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI BIYA 500 VIP 800 KARKI BARI ABAKI LABARI YAR UWA YANZU WASAN YA FARA 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻MAZA KI TURO KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK INKUMA SAIKI TURO EVIDENCE TA WANNA NUMBER 09138320449 KO KUMA KATIN MTN TA WANNAN NUNBER 09138320449*_

*_SAI NA JIKU😍_*

*_Littafin tushen mu daya labarine daya danganci Wata zuria wadda babu abin daya yiwa zuriar nan lullubi face Cin amana zalunci rashin tausayi rashin tsoron allah sannan ga sassanyar soyayya labarin Aminatu da surukarta labarine da zaka zubda mata hawaye sannan ga kannen miji suma sun sako ta gaba shin dama haka yakamata surukai su zauna da matan ya,yansu? Duk sai kun tsunduma cikin wannan labari mai suna TUSHEN MU DAYA_*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EucvvhNS397F3LJeJGZuUS

*09131164861 Royal jelly yana ciko da mace tayi dumdum breast naki ya ciko hip's dinki yaciko da wanda tayi bleaching fatarta ya yamutse*

*Ko kinsan female care na taimaka ma wanda niimar jikinsu ta tsane*

*Fat bunner ina macen da kitse ya mata yawa ajiki tayi kiba sosai tafiya da kyar tashi da kyar to ki gar zoyo ki mallaki fat bunner*

*Masu son a tallata musu hajarsu ko link din group dinsu zasuyi magana ta wannan Number 09138320449*

```Bismillahirrahamanirrahim```

*Free page 14*

Nayi sallama suka amsa tukun nashiga na gaida mama rukayya na juyo na gaida aunty nafeesa ina tambayar yaranta

Ta amsa tana mai karemin kallo

Na juya nafita har lokacin ina cikin mamakin zuwan aunty nafeesa

Suna gidan har akai sallar magrib wanda ni tunda nayi alwala na fada daki bankara fitowaba saidai naji motsin mazan sun fita alamar masallaci sukaje

Can sai naji sallamar baba da yaya yusuf

Ina kan abin sallah da hijabina na fito na masa sannu da zuwa ina mai amsar laidar hannunsa sainaga kamar baba yana cikin farin ciki saboda sai fara,a yake

Ya kalleni yace allah yamiki albarka aminatu nace amen baba

Yaya yusuf ya kalleni yace ji yadda take wani washe baki dan ance allah yamata albarka na kalleshi cikin murmushi yaya yusuf waye za asawa albarka baiji dadiba ai inajin dadin albrka da baba kesamin allah dai yabarmana baba yakara lafiya da nisan kwana mai amfani

Baba ya kallemu yayi dariya yana mai amsawa da amen yarinyar kirki

Nakara kallon yaya yusuf dake kallona yana tafa hannu yace keko duk salon wayo kin iya kin ga yanzu dai kinkuma samun wani yabon

Na kyalkyale da dariya nayi hanyar dakin mama rukayyah da ledar da na amsa wajen baba duk da cewa mun saba yana dan jana da wasa wani lokacin amma hakan baisa na rainashiba muna kokari wajen mutumta junanmu

Ina shiga naji baba dake kallon aunty nafeesa dake zaune kusa da mama rukayyah alamar sallah suka idar yana cewa a ah ah lallai yau munyi manyan baki tunda gashi a sanadiyyarsu har nafee ta tuna da gidan babanta

Aunty nafeesa cikin jin kunya dan ni kaina da wayona bazance ga ranar dana ganta tazo gidanmu ba

Tashiga cewa a a fa baba ayi hakuri zamu gyara insha allah

Ya kallleta yace to allah yabaku ikon gyarawa amma shi zumunci ai yanada dadi ga lada koda yan yaranki kike aikomin ina ganinsu

Tace insha allah baba

Nikwa na ajiye ledar hannuna na fita

Fita ta tayi dai dai da shigowar su salim da muhammad yayan mama aysha sai wani na ukunsu nidai banwani kare musu kalloba na gaishesu na fada daki

Bayan sallar ishsha,i ne naji mama rukayyah na kirana na tashi na fita saina tarda ta da farantin abinci ta jera kuloli akai da kofin ruwa a gefe

Ta kalleni kinga dauki wannan abincin kikaiwa bakin dasuke dakin yayanki

Na tsugunna ina mamaki su yaya salim dai bawasu baki bane a gidannan dan kafarsu bata daukewa agidannan kuma insun zo wani lokacin Muhammad da kanshi ma yake zuba abincin dan shidin kusan sa ana ne inma yazo yaga inaci wataran saidai ya jefa hannu muyita fada

Kuma sune za ace wani in kaima abinci harda wani karramawa sai kuma nace to kodan bakon da sukayi ne oho musu na dai dauka nayi hanyar dakin

Ina mai sallama saidanaji sun amsa tukun na bude labulen nashiga su hudune yanzu harda yaya yusuf da shima ya shigo

Bakon da suke cewa yana zaune a bakin katifa daga gefenshi yaya yusuf ne sukuma su salim nakan kujerar dake dakin guda daya me cin mutum uku

Na karasa ina mai kara gaishesu na ajiye abincin

Yaya salim ne ya dago yace aminatu ya makarantar ?

Nace alhamdulillah

Yace masha allah

Muhammad ya tuntsure da dariya ai makaranta ma tazo karshe tunda ammatan baba angirma

Na kalleshi na gallamai harara ina mai tashi na juya zan tafi

Har na kai bakin kofa sai naji sallamar yaya nafesa na amsa ina mai kokarin rabeta na fita

Ta kalleni ta na mai cewa koma tukun

Na kalleta kamar zanyi magana mezan koma inyi kuma nadai koma

Kamar yadda tace sainaga su yaya yusuf sun tashi dukansu sunkama hanyar waje

Bakon kawai shi ya rage a zaune

Na kalli aunty nafeesa cikin mamaki

Ta makamin harara tana mai wucewa kan kujerar da su salim suka tashi ta zauna

Ta nunamin kusa da kafarta tace zauna nan

Na karaso na zauna na sunkuyar da kaina dan jina nayi awani takure dalilin wannan bakon dake zaune da ko fuskarsa bazan tantanceba bare nagane daga ina yake

Ta kalleni ta ce kinsan wannan nadan dago da kaina na kalleshi lokacin shima yayi dai dai da dago kanshi da yayi muka hada ido

Subhanallah na furta a zuciyata lokacinne naga fuskarshi farine irin mai sirkin jaja dinnan masha allah yanada hancinsa tubarkallah sai gashinsa daya kwanta lufluf baki sidik idanuwansa tubarkallah masha allah dalilin dayasani sunkuyar da kaina kenan saboda sainaga idanuwansa sunmin kwarjini

Aunty nafeesa ce takara tabani ke tambayarki nake kinsan shi?

Na girgiza mata kai dan banajin ma zan iya magana

Ta kalleshi to kai kaga bata sankaba ana mana fadan rashin zumunci kuma dai kuna ciki ta karasa fadar tana mai kara jefomin tambayar dawa yamiki kama ?

Haushinta ne yakamani ya zata wani sani gaba da tambayoyin da tasan ba amsata mata su zanyi ba

Nakwa yimata shiru

Dataga bance komai ba

Sai tace to ki gaishe shi

Sai lokacin naji yayi magana ai mun gaisa

Sainaji muryar shi kamar irin ta yare dan gaskiya hausa bata wani zauna mai ba dan yadda yanayin da yayi maganar

Tace saiku kara gaisawa ai

Nace ina wuni

Yace lafiya lau
Chapter 22 · 0% Book details