Sashe 25
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka aunty nafeesa ta amsa cikin rashin kunya,tace dan zaku bani sako saikun wani fadawa mutane magana ai karshen son da zaku nuna mata shine ku bita koda kwa motar kanku zaku haya daga nan har Niger state
Ita dai gwagwgo binta ta kama hannuna zata a motar na muka rungume juna nida siyama muna rirgar kuka saboda bantaba tunanin za aki zuwa da itaba nashaku da siyama kawar arziki ganin munki sakin juna yasa gwagwgo binta kama hannuna ta rabamu da kyar ta sa ni a motar inda a kusa da aunty nafeesar aka ajiyeni kuka,kawai nake ina bakin cikin rashin zuwan gwagwgo binta da siyama haka inaji ina gani motarmu ta tashi muka dau hanya sai Niger
***** *******************
Bamu sauka ba sai wajajen sha daya na dare kasancewar bamu fito da wuriba kuma,ga yanayin hanyar sai a hankali
Inda nidai nasan motarmu na sauka naketa jin hayaniya da zantukansu na yare wanda ba komai nake fahimta ba
Can wata mata tazo ta kama hannuna ta fara jana dakin hajjo aka fara kaini inda mutanene dankam ita kuma ta hakimce nan dai suka shiga gaggaisawa inda aunty nafeesa ce naji tanawa hajjo bayanin komai ni hankalina ma ba akansu yake ba ni tunanina ya tafi duk akan allah yasa dai ba awannan gidan zan zaunaba duk da ban bude fuskata ba naga gidan amma daga yanayin yadda muka yi tafiya zuwa dakin hajjo da kuma hayaniyar mutanen na fahimci kamar babban gida
Can naji muryar hajjo tana cewa ga bangarenta can ku karasa da ita
Haka kwa aunty nafeesa ta kama,hannuna muka nufi wani lungu har munkai bakin kofar daki naji muryar wata mata cikin gurbatacciyar hausarta
Karku shiga bari akawo buta tafara alwala tukun haka kuwa akayi saida aka bani buta na bude kaina nayi alwala wajen duk da dare yayi amma cike yake da jama a ta ko ina duk kuma sun lullubeni ne suna,kallo
Bayan nayi alwala matar ce tazo ta kamani tace inyi bismillah inshiga da kafar dama haka nayi bismillah nashiga
Sai ta dauko daddauma ta shimfidamin ta nunamin gabas tace in rama sallolin da ake bina in na idar nayi raka a biyu na nemi addu ar zaman lafiya nan dai na tada sallah bayan na idar na juya naga dakin babu kowa zuwa lokacin aunty nafeesa dama tunda zantada sallah naga ta fita su hajara kwa rabona dasu tun a cikin mota
Can saiga wata mata tashigo hannayenta dauke da kwanika inda ta ajiyemin kusa dani ta bubbude tace yawo ga abinci kaci
Sai lokacin na dago na kalli abincin tuwon shinkafane fari tas da miyar wake a wani dan kwano miyar yar mitsitsiya sai bushashshen kifi sai ruwa data debo a wani kofi
Madadin ta tafi saita nemi waje ta zauna akan kujerar dake gefe na tace kaci mana
Duk da inajin yunwa banajin zan iya sa abinci abakina wannan lokacin saboda nikaina takamai mai bazance ga abinda nake tunaninaba
Saina girgiza mata kai dan banajin konayi magana zataji saboda muryata data dashe
Tace baka ci a samomaka tea nan ma na girgiza kai can sainaga ta tashi ta,fita
A lokacinne kuma nasamu damar dago kaina na kai kallona ga kayan dakin da akace ansaimin saida gabana ya fadi kayane irin jan katakonnan nada sai wardrobe mai biyu itama sai dan madubinta a gefe sai kayan kallo ita tv ce ta kasa dayake dakin babbane harda kujeru Me biyu da me uku shikenan kayan
Azuciyata nake sakawa dama sunbari baba yayimin kayana amma ai anbawa baba abdullahi kudi shima inya duba yasan ko su aunty nafeesa ba irinsu aka musu ba bareni da akai auren yanzu zai canzamin
Ina cikin tunani aunty nafeesa ta shigo ta balbaleni da fadan anbani abinci naki ci ubanwa zanwa yanga kar allah yasa naci din da dai sauran maganganunta matar da ta kawo abincin cema dan tare suka shigo tashiga cewa ta bini ahankali harda kewar gida
Tace bawani kewar gida iskancine kawai
Nan dai matar ta fita can saigata da kofi shayine ta hadomin me kauri sai biredi tace insha zama da yunwa ba kyau
Haka dai na dauki ruwan shayin na kukkurba dan naga matar ta damu dani inda aunty nafesa tayi tsaki ta fita
Basu dawo dakinba sai can wajen karfe daya inda nida su hajara muka kwnta a gado aunty nafeesa ta hau kujera sai yaranta da ke wajen hajjo
**********************
Sai da safe tukun muka sa ahmad a idonmu inda yazo ya gaishemu bayan nan aka zo akace in shirya zan je gaida mutanen gida haka nayi wanka na shirya nasa hijabina iya gwiwa wannan matar data bani ruwan alwala ita ta kama hannuna ta fara kaini wajen hajjo muka gaisa tukun tafara zagaya gidan dani hasashena yazama gaskiya gidane babba ginin gargajiya sashi sashi haka ta dunga zagayawa dani
Inda bayan mundawone ta ke fadamin kullum da safe haka zanna zuwa ina gaida mutanen gidan al,adarsu kenan
Wajen karfe takwas aka kawo mana abin kari inda kunun tsamiya neda kosai inda babu wanda ya taba ko botikin kunun
Sai can kuma saiga wani yaro sako daga ahmad kayan tea da buredi ne
Inda sai lokacin naga su hajara sun matso ansamu abin da akeso salima ce ta tafi ta amso musu ruwan zafi nan muka samu muka karya
Bayan munkarya aunty nafeesa ta sa aka bude kayan kitchen din da aka zo dasu ta shiga gyagygyawa ta ware wani babban flask din abinci tace na hajjo ta ware wani dana miyar shi shi kuma na baba
Dan ta dudduba babu ko cokalin da suka siya kawai dai kayan katakonne sai zanin gadon da suka shimfida da labule daga shi babu wani abu da suka siya da ba azomin da kayan kitchen dinbama da yaya kenan
Ina gefe kamar wata bakuwa a cikinsu ta ce hajara ta jawomata akwatunanan guda biyu
Ta jawo ta miko mata ta bubbude
Ni sai a lokacin ma nake ganin kayan lefen abubuwan takaicin kam da yawa nan ta shiga daddagawa ta cire turmin atamfa ta dora a kan babbar colar data cirewa hajjo har zata dauke shaddar tasa a na baba sainaji hajara tace
A a fa aunty nafee barmata shaddar tunda dayace gaskiya ta juyo ta gallamata harara tace
Toke meye naki ne dan ubanki
Hajara tafara gunguni ai gaskiyace mana aunty nafee kayan lefen duka nawa suke da za awani cire kona hajjon nan gaskiya bai kamata acire ba
To uwata tsaramin dole a cika al,ada tunda bawata gara muka zo da itaba kinga kwa ai dolene abasu babu maganar wasu dangi
Salima dai ko dago kai batayiba danne dannen ta take a wayarta dan ita babu ma ruwanta da harkata inba yan rashin mutumcinne suka motsaba ta kulani tamin hajaracema ke tausayamin
Nan naga ta bude na kayan kwalliya ta dauki bra guda daya wai tata dayake akwai manya guda uku ta ware biyu tabawa hajara daya salima daya inda hajara tace bazata amsaba salima tasa hannu ta amshe ta ajiye gefe
Kayan kwalliyar da bawasuba nan ma duk ta diddiba duk hajara kin amsa tayi
.daga nan ta tarkata tace salima ta kwasu kayan sukaiwa hajjo inda suka fita suka barni da hajara
Bayan fitar sune hajara danaga alamar tausayina yashigeta ta matso kusa dani ta dafa ni tace aminatu karki damu kinji kidau komai ba komai ba ahankali duk zaki samu wadanda suka fisu nida baba zaiji shawarata wlh kayan dakinnan za acanza miki haba saika ce wata tsohowa fisabilillah bari zanga baba aunty nafeesa kwa zanmata magana kudin hannunta ta zo arakamu kasuwa akarasa miki siyayyar da baba kekuma ko bayan muntafi ki yi kokari wajen tattalin siyan wasu abubuwan dan nasan ba lallai ta miki abin kirkiba
Nidai ina jinta nadai gyada mata kai ta tashi ta fita
Can bansan mesuka shiryaba sundai cemin zasu kasuwa inda da suka dawo bawasu kayan kirki ta karomin ba daga botikai sai wata butar karfe da dai wasu kayan shirme da banga ma anarsu ba duk akwaisu cikin kayana
Baba abdullahi yazo dakin inda naji yanata sa albarka wai ai sunyi kokari babu batun canzamin kayan daki kenan ya dai dunkule dubu talatin ya bani yace babanmu yace inbabu abin siya susaimin wani abu inda nikaina nasan ba haka akabashiba kudin kayan dakina fa baba ya bashi haka na amsa
*************************
Kwanan su aunty nafeesa shida,dani inda a daki guda muke kwana tsakanin mu da ahmad yazo ya gaishemu abin da muke bukata ya bamu ya yatafi ranar da suka cika sati ranar asabar shine sukayi shirin tafiya inda aunty nafeesa ta zaunar dani da nasiharta akan inbi hajjo sau da kafa sannan girki daya zamuna yi dan hajjo ta fada mata tsarinta kenan kuma acan zanna zuwa kullum munayi dan haka karma na fito da tukwanena kana nan nan ta dauki babbar tukunya ta kaiwa hajjo data miya wai adinga dorawa da ita bayan wucewarsu ko awa ba ayiba nasamu kira daga hajjo akan infito in yi aiki wanke wanke
Bayan nagama ta mikomin girkin rana inda daga,ranar ne nafara mata bautar aiki muddin gari ya waye nice zanyi komai inda tsakanina da ya,yanta sai kallon banza dan hajjo agabansu take min gorin kayan daki bayan an cucenine inaji ina gani baba abdullahi iya kudin daya bani shikenan ya gama ya tafi da sauran batare da yasaimin komai ba aunty nafeesa ma tawuce da sauran kudin
Koda mukayi waya da su inna da baba duk sun tambayeni ansaimin komai nace eh kawai dan azauna lafiya dan banason baba da baba abdullahi sukara samun matsala dan nasan in akan wannan ne in babanmu yaji tsaf zaiyi magana kuma zai iya taba zumunci
Adaren ahmad ya tare a dakina sai dai baimin komai ba nayi mamaki nikaina inda acewarsa sai mun dan saba da junanmu tukun