Sashe 17
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A kwanaki biyar din da sukai hajjo jinta take a takure tana bakin cikin kulawar da malam musa kebawa yan uwansa ganin hakan burinta nason tarwatsa su nakara girmama a zuciyarta
Haka dai sukai sallama suka dawo kano
************************
*_BAYAN SHEKARA GOMA_*
Zuwa lokacin
matar abdullahi ta haifi yara biyu Salim da kuma muhammad sunan kakanmu
Sai matar salisu wato mahaifiyata ita ma haihuwarta biyu Yayana namiji Yusuf saini Aminatu sai cikin na uku
Hajjo dake can ita kuma ta kara haihuwa daya wato shamsu lokacin dai yaranta hudu kenan
Rayuwar gidanmu rayuwace mai cike da kaunar juna muna tafiyar da rayuwarmu cikin rufin asirin ubangiji inda mahaifina shima sana ar gwarin yake lokacin yayana yusuf nada shekara sha daya saini yar shekara takwas maman mu nada wani cikin
Mahaifinmu na matukar kokari akan hidimar mu yayi kokari gurin samu a makaranta ta private me dan rangwamen kudi yayana Primary3 nikuma a Primary 2
Muna zuwa islamiyya dake unguwarmu dai dai gwargwado dukanmu muna da kokari
Har zuwa lokacin kuma hajjo bata taba takowa zuwa kano ba baba musa dai yana zuwa jif jifa sai mama aysha da suke zumunci sosai da mamarmu
Ya,yan zainabu sam bama shiri dasu innaje gidan mama aysha saboda kiri kiri suke nunamin tsana biyu daga cikinsu sunyi aure Aunty Nafisa ita ce babba tayi aure a unguwar tudun murtala sai Aunty hafsa ita kuma tana aure a sharada
Sai salima da hajara sune suka rage yammata
Duk juma a maman mu na samu mu shirya in ansakko masallaci muje gidan aunty nafisa da kuma gidan mama aysha duk dan mukara sanin cewa su yan uwanmu ne mu koyi zumunci duk da cewa nafisa bata taba zuwa inda mamanmu take bare ta aiko yaranta hakan baya hana wata juma ar muje
In munje gidan mama aysha inhar su salima,basanan mukan sake muyi wasanmu amma inhar sunanan bamu da wani katabus
Haka gidan auty nafeesa ita batawani bamu fuska haka dai muke zuwa
Daga baya sai yusuf yafito da dabara in munje bama zama saimu wuce gidan kakanninmu wato mahaifan mamanmu
Haka muke rayuwarmu muntaso cikin son junanmu da tarbiyar mahaifiyar mu da kaunar da mahaifinmu ke nunawa garemu
Ana haka mamanmu ta haifi diyarta mace aka samata bahijjah inda nafi kowa farin cikin haihuwar dan mama ta dade rabonta da haihu tun haihuwata bani da kani ko kanwa
Baba abdullahi yatsaya tsayin daka wajen taimakawa mahaifina a lokacin hidimar haihuwar dan lokacin kasuwancin mahaifina yayi kasa kasancewar sana ar gwari ta gaji haka wani lokacin kayan sukan samu matsala to lokacin hakace ta kasance wa mahaifina baba abdullahi shi yasayi ragon suna da duk wata hidima ya daukewa mahaifina
Bahijjah bada shekara uku mamanmu ta kara samun ciki wanda tunda tasamu cikinnan yazama yau lafiya gobe babu lafiya haka take yawan zaunar damu nida yaya yusuf tana mana nisihar kula da junanmu da kuma tsoron allah akan kowanne lamarin rayuwa ni bawani fahimtar ta nakeba gwara yusuf yafini wayo
Takance yusuf yayi kokarin kula damu akowanne hali nan gaba shine gatanmu karya taba bari muyi kuka
Ahaka dai har watan haihuwarta ya shiga lokacin ni muna daf da zana comment entries yaya yusuf kuma na Aji biyu a secondary
Maman mu ta tashi da nakuda wata ranar litinin inda tasha wuya amma haihuwar shiru haka aka kwasheta sai asibiti inda aka amsheta amma takasa haihuwa da kanta dole mahaifina yasa hannu aka shiga aka mata tiyata inda aka ciro yarinyarta lafiyayyiya amma kuma ita sai a hankali
Satinsu biyu a asibiti amma jikin na nan sai addu a haka gidammu ya zama mu kadai ba dadi in mun taso makaranta sai dai mu wuce gidan kakanmu indare yayi baba ya dakkomu amma bahijjah dole kakarmu ta dauketa dan bamu da hankalin kula da ita
Mamanmu ta kai wata a asibiti amma shiru jikin sai kara rikicewa yake dole tasa aka sallamosu a ka wuce da ita gidan kakanmu
Aka fara mata na gargajiya
Mukuma muna gida a lokacin ina yar shekara sha daya alhmdlh na dan iya wasu ayyukan dan mahaifiyata tun kafin ta kwanta ciwo takan bani girkin data san bamai wahala bane saidai takan dubamin wasu abubuwan dan haka sai yazama nike girkin in kayanmu sunyi datti kuma yusuf ya hada ya wanke shara da wanke wanke banida matsalarsu dama na iya
Wasa wasa saida mamanmu tayi shekara biyu tana jinya inda yarinyar data haifa taci sunan ta Khadijat amma muna cemata ilham madara aka dinga bata tunda mama bata da lafiyar shayar da ita zuwa lokacin ilham ta yi wayo abinta tana tafiyarta ko ina
Bazan taba mantawa ba wata rana na dawo makaranta kenan ina hada wutar mangal da gawayi ina son dora mana taliyar dana biya kasuwa wajen baba na amso cefanen sainaji sallamar daya daga cikin kannen mamana baba Umar na leka nace kashigo baba yace a a ina dan uwanki yake dan baya fadar sunan yusuf kasancewar sunan mahaifinsune
Nace baidawo daga makaranta ba shi muna cikin maganar sai gashi kwa yace yawwa maza maza ku kulle gidan kuzo mu tafi
Ni a wauta ta zamu koma can gidanne kamar yadda muka fi son komawa kusa da mahaifiyarmu amma baba ya hana da saurina na tafi dauko hijabi harda kayana kala biyu sai yaya yusuf nema naji yana tambayar shi lafiya kawu?
Yace kuzo muje dai haka ya goyamu bayan mashin dinshi muka nufi gidan kakanmu
Isarmu muka tarda gidan cike damkam can na hango mahaifina zaune a tsakiyar mutane fuskarnan tashi tayi jazir abinka da farin mutum
Nayi kokarin karasawa gareshi kawu umar yace inwuce cikin gida yaya yusuf ya karasa gurin baba
Haka na wuce muna shiga naga gidan kowa kuka yakeyi kawai bankawo komai ba na nufi dakin da mamarmu ke jinya Wata kanwar kakarmu gwagwgo Binta tayi saurin jawoni kinga dawo ki zauna anan
Can naga Aunty sameera mata ce ga kanin mamarmu Salihu tashigo cikin kuka tana fadin allah sarki yaya hadeeza allah yajikanki a lokacin ne fa hankalina ya fara dawowa kenan mama ta rasu kenan bansan lokacin da nashiga kuka ba saikuma aka dawo lallashina saboda lokacin kowa mu yake tausayawa
Haka aka shirya mama a kira baba da yaya yusuf sumata addu,a inda nayi nayi abarni inje nima aka rikeni aka hanani inda bahijjah bawani wayone da itaba bare kuma ilham yar yaye
Haka aka dauki gawar mamanmu munaji muna gani aka fita da ita
Bayan sadakar bakwai
Kasancewata nadan tasa lokacin inada shekara goma sha hudu yasa kakanmu yace ni bazan koma dasu baba ba yusuf da baba su tafi nida bahijjah da ilham kuma zamu zauna nan saboda gidan babu mace bazai yiwu mu bishi ba
Haka kuwa akayi daga gidan kakanmu nake zuwa makaranta nida bahijjah wadda itama lokacin ansata yusuf kuma kullum zaizo da safe yaganmu kafin shima ya wuce makaranta
Bayan wata daya muka samu ziyarar baba musa inda yaji rasuwar mahaifiyarmu yazo yiwa mahaifina gaisuwa a lokacin shida hajjo suka zo amma kuma hajjo bata biyoshi gidan kakanmu ba ta saukane gidan baba abdullahi dan babanmu yayiwa baba musa jagora har zuwa gidan kakanmu
Inda aka masa iso har dakin baba malam dan haka muke cewa kakanmu bayan wani lokacine baba ya bukaci da inzo nida su ilham mu gaisa da babanmu tunda dama rabonshi damu
Tun wani zuwa dayayi lokacin nida yusuf ne kawai ba ahaifi ilham ba
Mun je mun gaida baba musa inda ya jawo ilham jikin sa da bahijja yana sama na albarka ya dago ya kalleni wannan itace babbar babanmu ya daga kai eh itace ai aminatu
Baba musa yace masha allah aminatu anzama yammata yanzu a aji nawa kike?
Nace jss3 nake yanzu
yace masha allah
Sainaji baba yace ina Ahmad ne?
naga da dan ladi kuka zo kawai yace eh kasan ahmad yatafi bautar kasa can Enugu sai watan gobe zasu dawo
Baba yace masha allah allah ya taimaka
Yace amin
Ganin sun shiga wata hirar yasa na tashi nace baba mungode sai anjima yace allah yakaimu aminatu inzan tafi aizaki zo muyi sallama ko nace eh
Can bayan wani lokaci aka kirani naje mukayi sallama da baba musa inda yake fadamin cewa nan da kwana biyu zasu koma gobe hajjo zata zo mana gaisuwar itama
************************
Washe gari kamar yadda baba musa ya fada sai gasu tare da hajjo da dan ladi sai umar da lokacin baifi shekara hudu ba
Inda dan ladi na fuskanci kamar yana mana wani gani gani da mukazo gaidasu sai wani daddaga kai yake nikwa a lokacin nace kodan yaganshi shi farine oho amma ai su ilham suma farare ne nice dai nayo fatar mamanmu su baba suka biyo
Bayan tawa su kakarmu gaisuwa ta jirayi dawowar baba malam ta mai gaisuwa tukun suka shirya wai zata biya wajen zainabu dan tun da ga lokacin da suka rabu basu kara haduwa ba inda take tambayar babanmu yanzu zainabu aina take
Baba yace ai gidan da kika sauka yaranta su salima sai su rakaki sunsan gidansu ..
Ta dago wai har yau zainabu batayi wani auren ba?
Baba yace eh inkinje dai kwa ganta
Suka mana sallama suka tafi
*************************
Hajjo ta koma gidan baba abdullahi inda tunda ta sauka dama mama aysha take a takure dan wata hassada ce ta saukarwa hajjo ta lokaci guda ganin abdullahi yasamu rufin asiri fiye da mijinta sannan aysha ta haifi maza ita ma duk da itama duka mazane yaranta su biyar sai salaha amma hakan bataso aysha ta haifi mace ba
Anan ta kira salima ta bukaci ta rakata wajen zainabu inda suka kama hanya sai gidan zainabu
Sunje sun sameta da uban kayan wanki tana narkar wankewa inda daga gani banata bane dan duk kayan yarane da zannuwa gado alamar dai wankau take
Inda suka suna shiga ta tsame hannu a ruwan wanki cikin muzanta da ganin da hajjo tamata tana wankau ta kalli hajjo wanake gani kamar hajjo?
Hajjo tace nice zainabu rai kanga rai ?
Lokacin kuma inna mahaifiyar zainabun ta fito daki hajjo ta shiga gaisheta bayan sun gaisa zainabun taja hannun hajjo zuwa dakin data ke kwana
Ita kuma salima ta wuce dakin kakarta