← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 78

Sashe 45

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kalle su yace ku kyale
Shi mana kuma.
Kunsan halinsa ai
Da jawowa su hajjo
Magana
Da da ne d'an,ladin fada
Zai taso masa dashi
Amma ga mamakin
Su sai suka ga wajen .
Kwanciya kawai ya nema
Ya kwanta
Nan kowa ya ja bakin
Shi yayi shiru suka
Nemi makwanci
Kowa ya kwanta

Hajjo kwa tana koma wa
D'aki ba dade wa baba ya dawo
Nan tayi ta hamdala da
Har aka gama bai
Dawo ba

************************

Tafiyar da su ahmad basu yi ba kenan
Sai bayan sati biyu
Saboda rasuwar
Mahaifiyar ogan nasu
Inda koda zasu koma
Da kyar ahmad ya yarda
Zai bisu gani yake.
Kamar wani abu zai
Same ni da k'yar dai
Na taushe shi ya yarda zai koma

Kuma har lokacin kamar
Yadda yayiwa hajjo
Alkawari bai tada maganar
Ba amma shida d'an ladi fa basa shiri iya kacin sa
Amsa gaisuwar sa
Kawai
Nikwa dama daga ranar bankara
Sashi a idona ba

Haka naci gaba da renon
Cikina cikin kaffa kaffa
Da kowa a gidan
Zaman dakina ya fiyemin
Indai na gama komai
Saina shige daki .na
Rufe inba dole ba ban
Fitowa
In kwa na fita a gidan to
Ranar da zankoma
Asibiti awo ne tayi

**********"**********
_*KANO*_

Da sauri ya maida murfin
Kwanon abincin daya bude zai fara ci
Ya kalli mama rukayyah
Wake sallama kikace
Ta kalle shi cikin halin
Ko inkula yace abdullahi ne

Cikin sauri ya zabura ya tashi a a bazaka ci
Abincin yanzu ba

Ya juyo ya kalleta baki ji
Ance yaya abdullahi bane
Ke kofar gida ina zuwa
Yaya zai tsaya waje kamar wani bako

Fitar shi kofar gidan
Kamar yadda yayi tsammani kam yayan nashi ne tsaye alamar shima daga masallacin juma ar ya dawo
Cikin hanzari ya karasa gare shi

Yaya kaine tafe da ranar nan baka shigo ba ka
Aiko sai kace wani bako
Ya fada yana mai karasawa gare shi cikin
Mikamai hannu

Shima hannun ya miko
Mai suka yi musabaha
A a ba shigar ne bazan yi
Ba kawai dai nafi
Bukatar ka fito dinne naganka

Cikin mamaki ya shiga bin
Fuskar yayan nashi da kallo sai yaga duk kamar
Ba yaya abdullahin daya sani a yan shekarunnan ba ya koma mishi yayan shi na ainahi daya sani
Me sanyin hali me
Nuna kulawa gare shi da nuna mishi qaunah

Yaya allah yasa dai lafiya? Lafiya lau salisu
Inaso dai muyi magana ne
Inba damuwa

Kai yaya wacce damuwa kaida d'an uwanka
Ina zuwa bari na dauko mana tabarma tukun
Sai mu zauna a zaure
Tunda baka bukatar shiga
Cikin

Nan ya juya cikin tunanika kala kala shin wacce magana zasu tattauna yaga yayan nashi duk ya canza
Daga abdullahin daya
Sani mafadaci mai
Saurin fushi da nuna
Masa isa ya koma yayan shi na ainahi daya sani
Ya allah ka tabbatar da zato na akan hakan
Allah ka dai daita tsakanina da d'an uwana

Yana shiga yace mama rukayyah ta karo abincin akan wanda ta zuba mishi ta bashi tabarma
Nan ta karo ta mikomai tabarmar nan da nan yazo ya shimfida
Ya aje abincin da ruwa

Yaya bismillah shigo
Mana nan ya shigo suka zauna suka kara gaisawa

To mu fara cin abincin
Tukun ko nasan kaima
Ko gidan baka karasaba
Nan suka bude kwanon
Dambun zogale ne daya ji wadataccen zogale da
Gyada sai kamshin
Man k'uli ke tashi suka yi bismillah suka fara ci
Kowannen su da sake saken dake cikin zuciyar shi

Babanmu farin cikin dake zuciyar sa shine d'an uwnsa ya dawo gare shi
Duk da bai fadi komai
Ba amma daga alamun
Daya gani kadai
Sun tabbatar mai ba abdullahin daya Sani
Bane abdullahin sa ne
Nada mai tsananin qaunar shi

Shi kuma kunyar d'anuwan nashi ce kawai
Ta addabe shi tunawa da
Irin abubuwan daya dunga
Yi masa da tozartawar daya dinga yi masa
Bayan bashi da wani wanda ya fishi duk fadin
Garin bayan barin yayansu musa salisu
Shi ya maye masa gurbinshi amma abin
Mamaki baisan dalilin shi na wulakanta d'an uwan nashi ba daya tallin tal ba shidai kawai yasan
Inya ganshi zaiji ya tsani
Ganin shi duk abin
Dayake gani yake baya dai dai
Shi yasa yake rufe shi
Da fada gaban ko waye
Sannan wani lokacin sai yaji kamar bai kyautawa amma sai zuciyar sa wadda kejin zafin salisun ta kuma tunzura shi

Bayan sun kammala ya
Kalli kanin nashi
Salisu maganar dana
Keson yi maka akan
Abubuwan duk da suka
Faru tsakaninmu ne
Marasa dadi wanda
Duk nine mai laifin
A matsayina na babba
Hakika na takura maka
Sosai na yimaka abubuwa na rashin kyautawa wanda ni
Kaina bazance ga dalilin
Yin hakan ba nadai san
Kawai ina jin zafinka
Kayi hakuri kanina
Bansan meya kaini ga
Hakaba nida yakamata na zame maka bango kuma majingina
Kaida iya,lanka amma
Nine me maka abinda ko
Bare bazai maka ba

Hakika na aikata kura kurai dayawa ko lokacin
Auren aminatu nasan
Ban kyauta ma ba
Kudaden auren dana rike
Madadin ni indau nauyin
Kayan dakin sai gashi
Nine na rike kudin auren
Sannan na amshi na hannun ka na hada
Koda muka je can bansai mata kayanba ka yafeni
Duk da naga kayan da yaya musa ya siya ba wasu kayane na kwaraiba duk da shima ba laifin shi bane
Nasani matar shi zata
Aikata hakan amma har hajara ta sameni da maganar akan acanja ma aminatun kayan amma madadin in canza mata sam saina k'i sai
Dubu talatin din dana bata cikin dubu dari biyun
Daka bani ni kaina bansan
Me ya kaini ga hakan ba
Duk kudaden suna nan ajiye banci ko kwndala ba
Kama daga kan kudin auren dukansu dubu tamanin ne ga kuma
Dubu dari da saba,in di da suka rage in an hada dubu dari biyu da hamsin kenan suna nan a ajiye kayi hakuri zan dauko
In kawo maka innaje banki ya kare maganar yana mai dauke kwallar data taho mai hakika yana jin ciwo akan abinda yayi wa dan uwanshi sosai inya tunawa har kunyar kanshi yake ji

A a yaya nifa dama ban
Kullace ka ba akan duk abubuwan suka faru
Nidai nasan d'an uwana
Ba haka yake ba to aikaga bazan baka
Laifi ba ni tunanina ko duk wani laifin na aikata .
Maka amma bantaba kullatar kaba fatana
Kullum shine allah ya
Dai,daita tsakanimu
Kuma alhamdulillah
Yaya na yafe maka
Nima ka yafemin
Maganar kudi kuma.da
Kai da kaya duk mallakar
Wuya ne nida abinda na
Mallaka da y'ay'ana baki daya kana da iko damu
Ni koda ka rike
Banji komai ba ai aminatu diyar kace duk yadda kayi yayi .
Bama saika dawo min
Dasu ba yaya na barmaka
Fatana allah ya kara hade kanmu

A a salisu sam baka da hurumi akan fadar hakan
Kudi dai hakkin aminatu ne bana kaba ni da kaina
Zan gyara kuskuren dana
Aikata zanje har can garin
Su yaya musan in sauke
Wannan nauyin
Kaga ko mun canza mata
Yanzu yayan bazai ce an
Raina nashin bane
In zan tafi in so samune ma
Ina son yayanta yusuf yabini shida su muhammad suje shima yaga yan uwanshi kasan sune basu taba zuwa ba
Su salima na kaisu

Shikenan yaya yadda kace
Hakan za ai allah ya shige mana gaba ya rabamu da sharrin shaidan yawwa kanina amen ya allah
Nidai fatana kayafemin
Dukkan rashin kyautawa gareka

Bakomai yaya amma kaima ka dage da addu,a yaya dan allah karda kadinga sakaci da yawan sadaka kasan ita sadaka
Maganin masifa ce

Tabbas hakane salisu
Insha allah zan kokarta
Kasan duk cikinmu
Kaine babban malami ya karasa cikin zolaya

Cikin dariya yace wanne malami yaya almajiri dai yaya

ai dai kasan duk kafimu kokarin wadannan abubuwan
Amma nima insha allah
Zan dinga kokarin tashin darennan ina kaiwa allah
Kukana dan ba asamun komai azaune
Hakane yaya allah yamana jagora baki daya amen ya allah

Can jimawa yayan nashi ya canza fuska cikin
Tarin damuwar dake dankare a zuciyar shi yace
Sai dai salisu akwai wani abu daya faru wanda sam ba dadi

Cikin damwa da halin da d'an uwan nashi ya shiga ya dube shi me kuma ya faru yaya?

Nan ya shiga kora masa bayani tundaga kan abin daya faru da salima ta hanyar sakacin mahaifiyar su
Har zuwa hukuncin daya yanke akan hajara nata fito da miji itama ckin wata biyu da kuma
Shawarar zuwa wajen mahaifin yaron

Allah sarki d'an uwa mai dadi sai gashi tashin hakalin da shi baban ya shiga yaso yafi na baba abdullahi nan ya shiga tausar dan uwan nashi akan yayi hakuri babu dadi sam amma yanda ya yanke zuwa ga mahaifan yaron ma yayi insha allah zai rakashi suje
Amma maganar aurar da hajara ga duk wanda ya samu yayi hakuri ya bari itama ta fito da wanda take so cikin kwanciyar hankali amma yaran yanzu sam ba amusu haka nan dai suka cigaba da tattaunawa sun tsaida magana akan jibi lahadi zasu je wajen alhaji ibrahim din yasan halin da ake ciki
Basu rabuba sai bayan sunje masallaci sunyi sallar la,asar kasuwar da baba baikoma ba ranar kenan ciki farin ciki ya kasance

Kamar yadda suka ce
Ranar lahadi suka samu alhaji ibrahim har gida inda suka kora masa bayani komai akan abin
Da yaronsa ya aikata ya musa da farki saida yaga bawasa dan mahaifina ya dau zafi akan zasu shigo da hukuma cikin
Batun tukun ya amince cewar zai tambayi yaronsa inshi ne ya aikata
Inda take ya nemi faisal din ya tambayeshi gabansu

Babu kunya yace shine amma gaskiya bazai aureta ba kuma yaro yace inta haihu ya barmata
Nan fa su baba suka ce sam dole ya amshi yaro inta haihu
Nan dai suka tsaida magna da kyar akan zai cigaba da kula da ita harta haihun tukun amma su bangaren su basason yaron
Sukuma su baba abdullahi sunce dole ya amsa haka dai aka rabu duk ba dadi
Chapter 45 · 0% Book details