← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 78

Sashe 70

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Insha allahu inna na yafe miki kuma suma zan nema miki yafiyar su zaku ma su yafe miki ki kwantar da hankalinki ki daina kuka
Ya fad`a cikin jin tausayinta ganin yadda take kuka

Salisu bakasan mai na aikata maka ba shiyasa kake fad`ar haka

Ko mene na miki alk`awarin insha allah na yafe miki allah ya yafe mana gaba daya

Amen aka amsa gaba d`aya

*_TUNA BAYA_*

A lokacin da muke zaune da mahaifiyar ku hak`ik`a mun kasance masu bak`in ciki da ita da kuma nuna,mata tsana kasancewarta ita ce uwar gidanmu amma kuma ita keda ya`ya` maza duka

Duk da cewar nima inada aliyu amma hakan bai hanani nuna mata tsana ba dan ina ganin ai sai tafimu samun gado in malam ya rasu

`Bangaren talatuwa ma haka ne dan ita tama fini nuna bakin cikinta dan ita duk ya`ya`n mata ne sai ya kasance bama fatima kawai take nunawa bak`in ciki ba hatta ni bata bari ba saboda tana ganin nima ina da aliyu
Talatuwa ta kasance mace mai shige shigen bokaye duk burinta shine ta mallake malam ta maida mu baya muda ya`y`anmu allah bai bata sa,a ba

Duk wannan abun ni bawani shiri muke da ita ba sai dai wataran nakan taya ta mu muzgunawa fatiman tare

Ana haka watarana bazan manta ba tazo ta same ni har d`aki da babbar magana akan tana son ayi aiki akan fatima a kwantar da ita ciwo yadda dole duk soyayyar ta da malam ke nuna mata inhar tana kwance dole zata ragu

Farko ban aminta,ba sam amma da na tuna yadda malam ke nuna mata so sai na amince mata haka kwa akai nan da nan ta amso wani magani ta zuba a inda fatiman zata taka ta taka daga lokacin ta shiga ciwo babu ji babu gani har allah yayi k`arshe ciwon yaza ma ajalinta

Ganin hakan na samu talatuwa akan aiba haka mukai da itaba ya zata kashe fatima danni gaskiya duk k`in dana ke mata bazan iya kasheta ba

Nan ta fashe da dariya ta shiga nuna min amfanin mutuwar tata da kuma yadda zamu juya yaranta da malam d`in kanshi tunda bata gidan haka dai ta cigaba da d`orani ahanya a cewar ta ai yanzu mu kad`ai ne dole hankalin mijinmu ya dawo kanmu

Badan na wani gamsu ba na bar maganar danni gaskiya ta fara bani tsoro duk da kasancewar ina d`an shige shigen malaman nima amma sai na fuskanci talatuwa ta dame ni ta shanye

Sai na yanke shawrar neman tsari a jikina da y`yana dan karta cutar dani

Tun rasuwar mahaifiyar ku muka d`inke dani da ita duk wani abu tare muke shiryawa sai dai wani tashin hankali malam tun rasuwar uwar gidan sa yake rashin lafiya a tsaitsaye sam jikinshi yak`i dadi ahaka

Watarana na shiga d`akin shi lokacin yana cikin jinyar bayan na taimaka mai ya tashi ya jingina ya sha furar da ita kad`ai yake iya sha
A lokacin har zan maida shi ya kwanta ya d`aga min hannu akan in barshi

Cikin zafin ciwo ya bude bakin shi yace asabe hak`ik`a ina da maganar da zan fad`a miki da kuma amanar da zan baki ina rok`onki akan ki rik`e min amanar nan ko bayan raina ki tabbatar kin Rik`emin alk`awari

Abinda yasa ban kirawo talatuwa ba nasan halinta da son zuciyarta kuma bana so tasan komai akan maganar nan dake na yarda shiyasa na nemi dana damk`ata a hannun ki

Nan ya nuna min wata akwati akan in d`auko mai ita na janyo ta da k`yar dan akwatin kayanshi ce haka yace in bud`e na bud`eta yace incire kayan cikinta na ciresu can k`asanta sai ga wasu ta kardu nan yamin bayaninsu d`aya bayan d`aya takardun filayenshi ne dana gonakin sa da gidajen sa ya kuma fad`amin buk`atarsa gareni shine na adana takardun har zuwa lokacin data allah zata kasance mai bayan ranshi in anzo maganar rabon gado in fito da su in mik`asu ga malam liman in tabbatar an yi rabon gaskiya anbawa kowa hak`k`in shi ya k`ara da jaddada min da in rik`e amana

A lokacim harga allah na amshi amanar hannu biyu kuma nayi na,am na k`udurtawa raina zan aikata duk abinda ya umarce ni

Bayan kwana biyu allah yawa malam cikawa mutuwar shi ta buge mu sai dai a `bangaren talatuwa sai na fuskanci ita dad`i tama ta bayan rasuwar malam da kwana takwas ta sameni da batun muyi k`ok`arin binciko dukiyar malam a inda,ya `boye mu raba tsakanin mu muda ya`y`anmu na nasanar da ita badai dani za aci amanar nan ba haka dai ta dinga ta kurani rana d`aya naji ina sha,awar bin ra,ayinta sai dai duk da hakan ban fad`a mata ina dukiyar take ba duk da kwa burinta kenan taji inda dukiyar take

Ahaka muka had`e kai da ita muka shiga gallaza muku har zuwa lokacin da rabon gado ya tunkaro a lokacinne kuma talatuwa ta d`aukeni muka je wajen bokanta akan yamana aikin da za a rufe bakin kowa akan maganar gadon har mu murk`ushe su.

Anan ya duba mana ya tabbatar mana muddin muna son hakan ta faru sai dai in salisu baya garin dan shi zai iya bamu matsla dan yaron yana da kafiya sosai
Nan muka tambaye shi yaza ai hakan ta faru

Kurciya yace za aiwa salisun inda babu `bata lokaci talatu ta amince nidai canai a a amma ganin yadda bokan ke zare zaren ido da kuma yadda yace sharad`insa indai aka bashi za`bi ya za`ba ba a canjawa dole tasa na amince bayan kwana biyu kam aka nemi salisu aka rasa

Nan dai taci gaba da bada labarin har zuwa lokacin da yan uwanshi suka tafi neman shi da kuma yadda baba liman yaso a raba gadon suka k`i yarda har kawo lokacin da musa yayi aure da asirin rashin haihuwar da sukawa hasana da kuma yadda k`arshe asaben ta kama talatuwa da k`anwarta suna k`ok`arin halakata duk saboda dukiyar
Har kawo canjawar data yi ta nesanta kanta da talatuwar

*_😍MAMAN `DAN ALBARKA CE😍✍️_*
09/11/2022, 2:24 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

_*PAID PAGE 44*_

Lokacin da na canja mata ba komai yasa hakan ba sai dan ina tsoron ta cika k`udirinta a kaina sannu sannu ta fahimci inda na dosa daga nan muka fara takun sak`a da ita

Kwatsam sai na tsinci zance wai mero k`anwarta zata auri musa zance ya girgizani amma ganin bani da abin yi akai yasa na yanke shawarar yin nesa da dukiyar daga gidan dan tabbas nasan ba banza ba talatuwa zata so k`anwar ta ta auri musa ba

Tunda tama fini k`in musa nan na dauke takardun kadarorin na tafi can wani tsohon gidan malam na sasu a wasu ledoji sannan nasa cikin wata yar akwati na bunne su dan kada watarana tayi yunk`urin cutar dani ta yi bincike ta kwashe dukiyar

Bayan faruwar hakan kuma sai gashi tunda musa ya tafi da mero bai k`ara wai wayar gida ba har saida ya dawo da marigayiya hasana cikin ciwo lokacinne mero tazo ta same ni da shawarar yakamata a fito da dukiyar a raba dan tana son in musa ya koma kar ya k`ara yunk`urin dawowa garin

Daga shi har abdullahi a lokacin na nuna mata ina tare da ita dan ina son duk shirin da zatai ya rushe yazamana nasan sirrinta dan naga ja bayan dana yi da ita yasa ta fara `boye min wasu abubuwan

Haka kwa akayi ta dai cemin muzo muje wajen bokanta kuma munje yabamu maganin da za a aiwatar su musa karsu dawo gida koda muka dawo kam tabbas bayan ta binne maganin da kaina naje na hak`e shi shine dalilin da yasa har musa ya k`ara dawowa bayan hasana ta haihu

Ko lokacin haihuwar hak`ik`a nikaina na girgiza da jin cewar hasana ta haihu ganin kuma shige da fice da talatuwa ta shiga yasa na biye mata koda gidan su hasanar za a je tare muke zuwa duk da cewar ana hanamu d`aukar jaririn gwara ni na d`auke shi sau d`aya amma talatuwa k`in d`aukar shi tayi sai daga baya ta fad`amin k`udirinta akan zuwan tana son abata shine ta d`auka duk zuwan da muke akwai wani magani data ke shafawa a hannunta muddin ta d`auke shi to tabbas zai kamu da rashin lafiyar da zatai silar ajalinshi

Duk lokacin da muka je akace yayi barci nakanji dad`i dan nasan burinta ba zai cika ba Tun daga haihuwar shi har zuwa rasuwar mahaifiyar sa ina sani nake biyewa talatuwa duk dan in dauke hankalinta akan muna tare daga baya ne nasamu labarin d`aukar shi da musa ya zo yayi inda a lokacin da ya d`auke shi tabbas ina cikin fargaba dan nasan mero zai kaiwa kuma ina jin tsoron kaidinsu

Bayan barin musa garinne watarana naji talatuwa nabawa k`awarta data zo labarin irin tuggun data shirya akan su musa ashe duk ta fahimceni ina rakata ne nan naji tace tasa ayi aiki akansu yadda babu wanda zai k`ara waiwayi garin tasa andasa musu tsanar garin me girma

Sannan nima kuma ba barina tayi ba sai tayi maganina badai tace ga abinda zata min ba

Ganin abinda tace yasa nima na tafi wajen nawa bokan akan ina son a makantar min da ita tasamu idon da zata cutar damu naso in d`an bigi cikinta inji wani abu dangane da irin asirin datawa su musa in karya shi amma sam saita nuna min bata yi komai ba

Kamar yadda nasa a makantar min da ita kam hakane ya faru dan tafara ciwon ido a hankali kamar yadda boka yace zata kasance har idanun su rufe

Kwatsam kuma wani zuwa da mero tayi ita da wata mata suka d`auki talatuwa suka fita dawowarsu da kwana biyu talatuwa ta warke nikuma na kamu da ciwon makanta kwata kwata bana gani

Kuma ikon allah bamu ta`ba yunk`urin neman magani ba
Chapter 70 · 0% Book details