← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 78

Sashe 31

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaki kawo dubu ashirin yanzu in kindawo a kwai wata laya da zan baki kiyi kokarin ganin kinsata a karkashin gadon ita mahaifiyar yaron indai kinsata shikenan komai zai yi dai dai amma wannan inzaki zo dubu talatin zaki riko

To shikenan sai ka ganni haka ta zuge jakarta ta ajiye mai kudaden kamar yadda tasa ba

Nan ta baro wajenshi cikin farin cikin samun abubuwa gani takema kamar har komai ya faru

******************"*"*****
Ina nan zaune naji alamar shigowar sako na duba

_Ki zo ina bayan katangar_

Shine abin da aka rubuta kawai
.na tashi nasa hijabina na fito na leka lungun tukun saida naga babu mai tahowa tukun na dau kujera na taka nace gani ya ziro hannunsa dake rike da wata leda na amsa da sauri na sauka a kujerar na shiga daki

Tukun ya zagayo ya shigo banko taba ledar ba har lokacin zuciyata bata amincemin da shawarar sa ba

Ya kalleni ki bude ki duba kigani me dame za akaro? Sauran ki ajiye gobe zan yoh siyayyar baki daya wannan dai kifara yau

Nasa hannu na bude ledar sainaga su taliyane da macaroni da su kayan miya harda kifi bushashshe da danye

Na kalleshi nace sunyi allah yakara budi

Yace amin ba saikin kunna wutar gawayiba bare ta gani ki kunna gas dinki kawai adaki inyaso kisa sakatar net kinga,bataganibama

Nace bafa zai yihuba ranar da wani yazo fa ko ita zaifi tashin hankali akan ace tasani ko tagani a waje

Kinga to fitar wajen kinji nidai jalof din taliyar zakimin kawo attaruhun indaka miki kigani ina turmin na kalleshi

A a kabarshi bari na je na dora kaji ninace kikawo ai to ai baza ai jajjage adakiba kuma kasan bazai yiyu mu fita waje kaminba saboda yanayin gidannan

To shikenan bari na dan kwanta jeki dora

Nan da nan na fitar da gas da duk abin bukata amma cikin fargaba nashiga aikin inda na tsara jalof din taliyata dataji kifi da kayan hadi
Nan da nan kamshi ya budade lunguna

Saura kadan ta karasa dahuwa duk da cikin fargaba nake gudanar da aikin ina addu ar kar allah ya kawo wani sai dai addu ata bata amsuba sam ina nan zaune saiga maman Aisha ta shigo ta kalleni ta kalli tukunyar dana dora

Kai amarya yau me ake mana ne nakejin kamshi har kofar dakina shine nace bari nazo naji me ake mana

Na kalleta cikin mamaki ikon allah wato gulmace ta kawo ta kenan ina ruwanta dani ni banma san yadda take girkinta ba amma ita jin kamshi kawai ya tasota to ince mata me

Bari mugani dai tunda naga kin zubamin ido gwara mugani wannan kamshi haka ta karasa tana mai bude tukunyar

A a a lallai wannan ai irin nakune amare bari kiga na dauko kwano dan allah ki yammin dan yau zanci dadi

Mamaki ya hanani tanka mata haka ta wuce

Na tashi da sauri cikin fargaba na karasa daki na tarda ahmad danasan yaji komai nace kaga wannan matar tazo karfa taje ta fadawa hajjo mu shiga uku na karashe cikin fargaba har ga allah badaban ahmad ya matsa ba ina tsoron masifar hajjo duk da ina son nima,na dora tukunyar kaina amma hanyar lafiya abita da shekara

Ban rufe bakiba naji dawowar maman aisha ga kwanona nan amarya kedai allah ya biyaki yau dinnan ai baruwana da cin wani tuwo sai yara

Ahmad ya kalleni yace kinsan me?nace a a ki zubawa hajjo tukun sannan ki zubawa su umar daban kinji kikai tukun

Atsorace nace baka tunanin fadan da hajjo zatai yace ninace kiyi hakan kinji ba abin da zai faru

Nan nafito na ganta da yar madaidaiciyar samirar ta kamar ita ta dafamin na amsa nace innagama zan kawo miki ta kalleni to aida na jira nace kije na kusa ai

Tana tafiya nashiga tunanin halin kwadayi irin nata wannan ai zubdawa kai mutumcine babu dacewa

Haka dai nayi yadda ahmad yace na kammala nasameshi nace to yaya za ai da kaiwa yace ke zaki kai cikin fargaba nace ina jin tsoro fa kikai kice ga abinci kawai ki ajiye saiki dawo muci dan girkin nan naki wallahi yasani jin wata yunwa ta tasomin kiyi sauri

Haka na dauka cikin farga na jera a faranti na yi sallama lokacin hajjo na zaune a falonta tana kulle kullen kayan miyar datake siyarwa ta dago ta kalleni sainaga hannuna take kallo nace hajjo ga abinci ina mai ajewa

Au wai maganar danaji dama gaskiyace kenan to ajiye shi nan

Cikin matukar mamaki na tashi na tafi nadau na maman aisha na bata ina mamakin hajjo batace komai ba ..

Haka nadawo na fadamai yace dama bazatace ba nidai ban gamsuba dannasan shirunta ba alkhairi bane

Washe gari naje da safe aiki kamar yadda nasaba sai catai in wuce bata bukata ainima inada nawa aikin yanzu ta faramin hayagaga acikin gida tunda kekin ware kanki basaiki daina tabamin aikiba aikine kikace kingaji inda dama ba yau naji wannan ba sannan dan munafurci dake da mijin naki daya daure miki gindin iskanci harda ware tukunya wallahi dai dai nake daku bani yaciwa mutumci ba,ina mahaifiyarsa ya kasa fadamin zaku dora tukunya saboda inkun dora ni mayyah ce kenan shiyasa cikin munafurci ya cefano miki cefanen da komu baitaba yimana ba ai wallahi zaisan yayi dani harda bushashshen kifi da danye duk a girki daya dan shegen iyayi da barnar kudi duk yadda nake tausaya masa a matsayina na mahaifiyarsa baya gani cikinku kawai saikun wani ware tukunya inba barna ba

Nan dana nan wajen yacika da mutanen gida ina tsugunne a gefe tana sirfa bala,i inda duk wanda yazo yake tambayar menamata nan tashiga kora bayani

Yawo jummai ce ta kalleta haba hajjo meye abin tada hankali akan maganar nan yanzu fa andaina wannan yayin dakike magana na hada abinci da iyayen miji kowa ya waye muma kina ganinmu da surukanmu gasunan su hajara saidai su dafa nasu da ban ko aikin ma basa mana kuma mazajensu matansu da ya,yansu suka sani ki godewa allah yaronnan na miki biyayyah yana baki gwargwado in yanadashi kuma bata fasa tayaki aikiba duk da tafara aikinta bata fasa nakinba kibarta ta kamamiki abin da zata miki

Sannan yakamata salaha tana sa hannu sunayi tare aikin namata yawa gaskiya bayau nakeson fadamiki gaskiya ba amma ina kyalekine ganin kunfi kusa amma abin yayi yawa muma mun haifa kuma mun aurar in akawa namu haka bazamuji dadiba fisabilillah hajjo gwara kidinga dauke idonki kan harkar yarannan

Ah lallai uwata uwata konace sabuwr uwar aminatu sannunki da tsari naji kuma nagode amma kinfi kowa sanin banason shishshigi akan harkata aminatu dai ba kowanki bace bakuda dangi ko kusa kuma bake akabawa amanarta ba amma tunda abun yazama munafurci shine harni zakiyiwa wa azi to rike wa,azinki kiji da kanki

Yawo jummai ta kalleta cikin mamaki hajjo gaskiya dai daya ce kobakyaso ni na fada ahto ina dalili marainiyar allah keda kanki kikace bata da uwa marainiyace

Nan fa fadan ya dawo tsakaninsu inda yawo jummai tayiwa hajjo tas karshe hajjo tace karta kara ganin kafata a wajenta bata taba samun matsala da kowa agidanba sai sanadiyata dan haka ta yafeni inje wajen yawo jummai kome zaisameni karma a nemeta ita ba uwata bace incire araina mun hada komai da ita da ya,yanta tunda na juyamata hankalin da, ahmad baitaba yin wani abu batare da tasaniba sai sanadiyyata kuma gashi na fara hadata fada da mutanen gidan

Wannan kinsan duk kina fadane dole kece dolenta wallahi ko kina so ko bakyaso gaskiyace dai bakyason a fadamiki kuma dole mu mu fada

Ina tsugunne kuka nake kawai cikin tashin hankali dan ni bantaba ganin hayaniya irin wannan ba ainahima bansan wani abu waishi tashin hankaliba gaba daya saida nashigo wannan gidan

Nan dai wasu suka dinga bata hakuri akan tabari in yi mata aikin tunda ba cewa nayi na daina ba tayi tsalle ta dire ita wallahi bantamata aiki inje bani ba ita babu ya,yanta ahmad din ma ba haka na barshi ba

Yawo jummai ce ta kamani ta mikar dani da kyar aminatu ki wuce dakinki kinji muje in rakaki muna zuwa mu ka tarda ahmad zaune idanun nan nashi sun kada sunyi jawur ya dago ya kallemu

Zauna anan ta zaunar dani kan kujera ta kalleshi ahmad kayi hakuri da halin hajjo kaji ku jure kumata biyayyah allah ya gani duk cikin yaranta babu mai mata biyayya sama da kai kana kokari matuka amma bari na fada maka wallahi yadda hajjo keda hakki akanka haka aminatu ma take dashi a yanzu hakkokin aminatu sauke su shine dole a kanka kaima kasan alqawarin daka dauka da kuma duk wani abun daya kamata kaci gaba da ciyar da matarka kome hajjo zatace karka fasa bata abinci tayi saidai suma ka sauke musu nasu nauyin dake kanka matsayinsu na mahaifa karka yarda yadda kuka fara girki yanzu wani abu yasa kudaina ai allah yaga niyarka ta son kyautatawa iyalinka ce ka kara hakuri kaji komai lokacine watarana sai labari

Nan tamana nasiha dukanmu ta bamu hakuri tukun ta tafi na tashi na karasa kusa dashi na fada jikinshi na kwantar da kaina a kirjinsa hannunsa yasa yana shafa kaina yana dan bubbuga bayana alamar lallashi dan ya kasa magana ma gaba daya da dai yaga alamar ba shirun zanyiba shine ya dago kaina yace kota dakeki ne na girgiza kai

Meta miki nace cewa tayi fa wai karna kara zuwa yimata aiki sannan ita ba uwata bace babu ruwanta da lamarina kome zai sameni kar anemeta sannan wai babu ruwana da ya,yanta daga yau

To kuma shine abin kuka um?

Daina kukan bacin rai yasata fadar hakan kinji inta huce komai zaiyi dai dai ai kuma,dama allah ne gatan bawa karki damu kinji

Nadaga kai nan yashiga sharemin hawaye cikin tunanika da suka masa rubdugu hakika inbadaban yanada shaidar tare da hajjo ya taso kuma baitaba samun wani labari ba da zai nuna cewa shi ba danta bane da yace rikonshi take wannne irin tashin hankali kenan aiba haka iyaye kewa ya,yansuba dan sunyi aure bai isa yayiwa matarsa wani abu ba kenan komai idonta a kai wajen babane kawai yake samun sauki ya ilahil alamina ka kawo mana dauki
Chapter 31 · 0% Book details