← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 78

Sashe 68

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun mijin baya nuna damuwa har ya fara nunawa ya fad`awa hajjo hajjo kam dama tun a wajen k`in aikin data ke mata suka fara samun matsala bare kuma data fara rowa da kuma k`azanta duk wannan son da ake nuna mata sai ya fara wucewa

Amma dai tana tsoron a `batawa aishar rai tunda yar manya ce dole tasa hajjo ke aika salaha itama ba ason ranta ba tana koya mata yadda ake girkin

Haka dai suke zaune mutanen gida kam ansamu abin yi kowa zund`en aishar yake akan tacika k`azanta

***********************

Ahmad kam bayan biki da sati d`aya yacewa su hajjo zai je wani aiki suleja fatan samun nasara suka masa dan ko baba bai fad`awa gaskiyar cewa niger zaije ba dan baya son abinda ya faru a waccan tafiyar ya k`ara faruwa

Yafi son dai inma zai fad`awa baban ya kasance bayan sunje cand`in

Zuwan ahmad kano da kwana biyu muka d`aga dani da babanmu da yaya yusuf da ahmad da kuma mama rukayyah

sai salima data kafe akan saita bimu itama inda da k`yar baba abdullahi ya yarda ta bimu
Sai fatan saukarmu lafiya ina cikin tsananin farin ciki ba kad`an ba dan ganin yau nice zan bar nigeria baki d`aya zan ziyarci garin kakannin mu abinda na dad`e ina mafarki

Bangaren ahmad kam haka kawai tunda motar ta tashi yake jin gabanshi na yawan fad`uwa baisan mai ye dalili ba sai innanillahi daya ke ta mai maitawa

***********************

Tun muna tafiyar cikin marmari harta fara gundirarmu kowannen mu yayi barci ya farka

Kallon baba nayi baba wai har yanzu bamu zo ba
Bamu zo ba tukun aminatu ai muda isa garin sai gobe da asuba
Kinga yanzu k`arfe ukun dare sauran awa biyu kenan

Allah ya sauke mu lafiya shine abinda aunty salima tace

Kamar yadda baba yace sai da muka kwana lokacin da ake kiran asuba muka fara shiga cikin gari tukun

Mudai kalle kalle kawai muke baba duk da dadewar dayayi rabonshi da garin da kuma sauye sauyen da akasamu hakan baisa ya manta abubuwa ba

Shi kan shi kallon garin yake da canje canjen da aka samu amma hanyar gidansu ta na nan a idonshi

Mun tsaya a wani babban masallaci
Mazan suka sauka sukayi `bangaren maza muma muka tafi na mata bayan idar da sallar mu muka shiga motar baba nayiwa direban kwatance daya ke shatar motar muka d`auka

Wata unguwa muka shigo tana da manyan gina gine alamar dai unguwa ce ta masu hannu da shuni sai da mukai tafiya mai nisa tukun muka iso k`ofar wani gida
Na jar k`asa babban gida ne sai dai yafi kowanne gida tsufa a unguwar ko shafen suminti babu

Baba ya shiga bin gidan da kallo yana jinjina kai tabbas gidansu ne amma abin mamaki ko ina gine gine ya lullube unguwar ta cika kamar ba ita ba sannan duk tsoffin gida jen angyara su fes gidansune dai yadda yake haka yake babu wani canji

Nan muka firfito muka sallami mai motar
Daya ke safiya ce unguwar tsit babu mutane sai jifa jifa da suke wucewa

Ahmad ne ya matso kusa dani cikin rad`a qaunah wai wanne ne gidan su baban ?

K`asa nayi da murya nima nace ba gamu ba dai kana ganin mun sauka magana tace ta katse sakamakon ganin.su baba sun nufi cikin gidan kowa rik`e da kayanshi
Bin bayansu mukai

Zaurene babba ko shafen suminti babu zauren yayi kaca kaca da shara

Da sallama muka shiga baba ne a gaba sai yaya yusuf dake gefnshi da ahmad sai kalim dake kafad`ar ahmad yayi barci nida mama rukayya da salima muna bayan su

Gida ne babba babu laifi irin ginin da d`innan ne dakuna ne jajjere sun kai biyar a hannun hagu sai wasu yan zagaye daga gefe guda biyu suma d`akuna ne

Kai jamilu jamilu nace kazo kabani butar inyi alwala tun d`azu ka shanya ni tsugunne
Cewar wata mata dake gindin makwarara da sanda a hannunta ta dan duk`a

Jin sallamar mu yasa ta amsawa wa alaikumussalam bak`i mukayi ne tace tana mai d`an daddogara sandar hannunta ala ma dai makauniya ce

Baba salisu da sauri yayi wajenta cikin tsantsar mamaki inna asabe ya kira sunanta

Na am waye ne ta fad`a tana mai lalubar wajen

Da sauri ya k`arasa gareta inna kin makance ne ?

Waye wai ?

Nine salisu fa inna

Salisu tace da k`arfi jikinta na rawa ta taho inda take jin muryar sauran kad`an taci tuntube cikin sauri baba ya tare ta

Talatuwa dake d`akinta tana sharar barcin asara ko sallar asuba bata yiba jin an anbaci sunan salisu yasa ta tashi cikin sauri dan yana yin yar hayaniyar data ke jiyo wa sai kuma sunan da asabe ta ambata da k`arfi

Salisu kaine ta shiga cewa tana lalubar fuskarshi da hannayenta ta fashe da kuka salisu kaine ? Ashe zan k`ara jinka a duniyar nan ashe ina da rabon had`uwa da kai kafin ta allah ta kasance min

Ashe dai allah zai bani damar sauke nauyn dake kaina allah na gode ma allah na gode ma ta fad`a tana mai fashewa da kuka

Kama hannayenta yayi cikin lallashi inna ki daina kukan haka dan allah

Mukam dai duk munyi cirko cirko muna kallon ikon allah da kuma yadda wannan makauniyar tsohuwar

Salisu wanne salisu naji kina cewa
yar makauniya ?

Maganarta ce ta mak`ale sakamakon ganin mutane tsaitsaye dukanmu kam mun maida hankalinmu gareta

Baba dake rik`e da inna asabe da jikinta ke rawa ne ya juyo yakai kallonshi ga inda maganar ke fitowa

Inna talatu ce tsaye sai dai tsufa ya risketa sosai daure take da wata tsohuwar atamfa duk tako kod`e zani da ban riga da ban

Tana had`a ido da shi ta shiga nuna shi jikinta na rawa tana motsa baki alamar magana take sonyi kuma ta kasa nan da nan ta yanke jiki ta fad`i bakinta ya karkace
Hannunta ma haka da kafarta idanun duk sun juye a takaice dai ta kamu da cutar barin jiki

Dukanmu babu wanda yayi wajenta sai baba dake k`ok`arin raba hannun shi dana inna asabe yayi wajenta

_*😍MAMAN `DAN ALBARKA CE😍✍️*_
09/11/2022, 2:24 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

*_PAID PAGE 42_*

Inna asabe da taji k`arar fad`uwar talatu ta shiga magana tana mai kamo hannun baba salisu

Salisu ne kam talatuwa
Allah ya rubuta zai dawo kinga ikon allah ko duk abin da mukai k`arshe ga shi nan ya dawo

Baba salisu sakin hannun ta yayi ya tafi ga inna talatuwa yana fad`in innanillahi wa inna ilaihirra,ji,un
Ganin haka ahmad da yaya yusuf suka k`arasa suma

Nikam haka kawai badan nasan inna talatuwa ba naji ko tausayinta banji ba wajen inna asabe nayi na kamata ganin tana lalubar hanya tana k`ok`arin fad`uwa tana tambayar baba meya faru ne?

Zauna inna najawo kujerar dake gefenta

Baba kam da yaya yusuf suka kama inna talatuwa da ta k`urawa baba ido ta kasa d`auke kallonta akanshi tun sanda ta fito har zuwa fad`uwarta

K`ofar kusa da mu aka bud`e wani mutum ne ya fito da babbar rigar shi kamar su d`aya da su babanmu abin mamaki sai dai babanmu ya fishi yarinta kuma ala ya nuna shima bawai tsufan bane yau da gobe ne kawai da wahalar rayuwa ta maida shi haka

Inna hayaniyar me nakeji haka ?. ..
Maganar shice ta mak`ale sakamakon ganin mutane tsaitsaye ga kuma wasu maza suna kinkimar inna talatuwa daya ke sun juya baya baiga fuskarsu ba baisan su waye ba

Jin muryar shi yasa inna asabe cewa k`araso aliyu allah ne ya cika min burina kaga yayanka salisu ya dawo gida alhamdulillah sauran su musa suma allah ya nuna min su insauke hakk`insu dake kaina

Inna yaya salisu dai yayana ya fad`a da sauri yana mai tahowa wajen innr tashi

Baba salisu jin abind inna asabe tace yasa shi mik`awa su yaya yusuf inna talatuwa ku mik`ata d`akinnan
Da sauri ya juyo yakai kallonshi ga d`an uwanshi allah sarki kallon juna suke

Duk da aliyu tun bashi da wayo yayan nashi ya `bata amma hakan baisa ya kasa gane shiba
Da sauri suka nufi juna suka rungume kowa na hawayen had`uwa da d`an uwanshi

Mukam dai har lokacin muna tsaye abin mamaki anrasa wanda zai ma kula damu ko wajen zama bamu samu ba saida wata mata ta fito daga inda baba aliyu ya fito tukun ta mana iso zuwa dakin inna asabe

Nikam ni na mik`owa inna asabe buta tayi alwala dan ban manta ba shigowar mu abinda take shirin yi kenan

Bayan komai ya lafa kowa ya zazzauna aka shiga gaishe gaishe da tambayar bayan rabuwa inna asabe dai tunda tayi sallah ta kasa gusawa a wajen kuka take kawai tana neman gafarar babanmu tare da tambayar yan uwanshi

Inna ki kwantar da hankalinki duk suna lafiya lau muna tare da su ma acan nigeria din suma zasu zo

Dan allah ku yafemin salisu na cutar daku ko nace mun cutar daku ku yafe mana

Inna tare muke da d`iyar yaya abdullahi ga kuma yarana guda biyu sai mai d`akina itama

Sai d`an wajen yaya musa babban ahmad gashinan

Ahmad dai d`an hasana allahu akbar yana ina bawan allah malam liman yasha zuwa nan tambayarmu ina kuke ina labarin jikanshi nakance ban sani ba talatuwa kam data san inda musa yake tunda yana auran k`anwar taki fad`a mana

Ikon allah suna ina ta shiga lalube da sauri na k`arasa kusa da ita nidai haka kawai na ji ina k`aunar tsohuwar nace inna nice aminatu

Masha allah yar wajen wace kenan

Nan baba ya shiga mata bayani dukan mu harda su kalim
Miko min su
Chapter 68 · 0% Book details