← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 78

Sashe 55

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muguwar tsohuwa kawai
Duk muguntar da kike
Wa matar d`anki ai
Munsani muna da labarin
`Dan labarin bai buya ba
Munaji a unguwar nan
Harda akuyancin
Da d`an ladi ya aikatawa
Matar ahmd tsaf
Munsa mu labari
Amma saboda son zuciyarki harkina da bakin
Aibata wasu
Tunda d`an ladi yaso
Haikewa aminatu
Kika
Daure masa gindi
Da ikon allah watarana
Ke zai haik`ewa

Fadime tayi tayi hauwa
Tayi shiru tak`i
Hajjo kuka kawai take
Tunda take a rayuwarta
Ba ataba cimata
Mutumci irin na
Yau ba amma agaban
Fadime fadime ta kasa.
Hanawa

Ta kalli fadimen
Cikin rishin kuka.
Fadime kina kallo
Diyarki na zagina
Zagin cin .mutumci
Kika k`yaleta

Ashe dama baki isa
Da y`arkiba fadime aikwa
Kinyi asara kuma daga
Yau sai yau
Babu ni babu ke
Ta na fadar maganar
Tana kokarin gyara
Zaman hijabinta
Sakamakon karkacewar
Dayayi dalilin
Shakar da hauwa ta
Mata

Kinga hajjo bafa tsoronki
Nake jiba ko wani abu
Yasa tun d`azu nake
Baki hakuri ba wallahi
Neman zaman lafiya
Ya kawo hakan amma.
Naga cin mutumcin
Na neman yawa

Ke kin isa da y`ay`an naki
Ne da kike cewa ban
Isa da nawa ba to bari
Kiji ni nagodewa allah
Na isa da tawa tunda
Isar tawa ce tasa har
Baki ci d`ankaren kashiba
Yau kinga ko haka
Ya nuna nawa y`ay`an
Sunfi naki jin magana

Kuma ki maza maza
Sanki a likkafa kibar
Min gida kafin
Insa hauwa ta fasamin
Bakin ki ta karya
Shegiyar kafarki
Yar iska kawai

Cikin al,ajabi
Hajjo ta shiga kokarin barin wajen zata fita
Amma bakinta baiyi
Shiru ba

Ganin hakan hauwa tayi kanta da gudu ta kwasa zani a hannu tayi zaure

Ganin ta fice yasa hauwar dawowa tana
K`yalk`yala dariya
Wallahi fad`ime hajjo
Karamar mara kunya
Ce kiga yadda ta kwasa
Da gudu zani a
Hannu ai naso ingani
Zata tsaya

Hmmm hauwa
Bansan munafikin
Daya kaimata gulma ba
Wallahi

Yoh zai wuce huwaila
Kinsan ita kad`aice tasan
Zance

Aikwa indai har ya
Tabbata itace kam
Ta shiga uku dani.
Duk kud`ad`ena data
Ci bashi saitayi amansu
Shegiya bak`in
Ciki take da auran
Da zakiyi
Dan ita yayanta basu
Auruba bari kema.
Ta miki buk`ulu

Barta fad`ime nidama.
Ko bata fadaba nasan
Baza a rasa munafikin
Da zai fadan ba

Amma wallahi wannan
Hajjon da kace na
Auri ahmad wallahi
Ko ganin shi sai naso
Zata yi inkwa ta
Kawo min wargi ko
Zagi wallahi lakad`a mata
`Dan banzan duka
Zanyi
Tsohuwar banza
Kawai

Nidama na cire raina
Da auran `Danta
Tunda baba na sokoto
Yace ind`auki dana
Nasan inhar nazo
Dashi asirina bazai
Rufu ba sam

Ni yanzu inhar kinga
Nayi aure tofa zan
Fadawa mijin nawa
Gaskya inyaga zai .
Iya aurena shikenan
Inba zai iya ba babu
Dole gari da yawa ai
Maye bazaici kanshi
Ba

Hmm hauwa kenan
Kina zaton akwai
Namijin da zaisan
Kinyi cikin shege har kina
Da yaro ya aure ki

Baza a rasa ba fadime
Insha allah zanyi aure
Nafison dai inda innaje.
Zan zauna zama na Din din din kinga ahmad fa
Ba sona yake ba
Nida kaina nayiwa kaina
Fada duk da ba sonshi ne
Banayi ba

Amma abinda za azo ana
Dana sani barinsa
Yafi akhairi

Haka ne kam ki kwantar da hankalinki allah zai
Baki miji wanda ma yafi ahmad din baki daya

Allah yasa haka fad`ime
Dan ni yanzu gaskiya na
Tuba allah ya yafemin abubuwan danayi da

Amen dai

***********************

Tafiya take kawai bama
Tasan inda take jefa kafar ta ba
Lallai ita yau hauwa
Ta daka yarinyar data
Haifeta sau uku ita
Yau ta mara kuma gaban
Fad`ime lallai zata nuna musu basu da wayo daga
Uwar har y`ar sai sunyi nadamar hakan
Ahaka ta kai kanta gida da kyar bakin ciki kamar ya kasheta

*********************

*_KANO_*

Yau allah yasauki salima lafiya saidai ikon allah d`an baizo da raiba
Bakaramar wahala tasha ba

Lokacin da labarin rashin zuwan d`an da rai yazowa zainabu bakaramin farin ciki
Tayi ba ita dama burinta
Kenan

Koda baba abdullahi yazo asibitin sun kira mahaifin yaron inda yazo suka bashi d`an aka mai
Sutura aka binne shi
Daga nan aka sallamo su

Amma bangaren mejego bata so rasa d`an data yiba dan dashine taso ta
Dogara har sai faisal ya aureta amma tasan
Yanzu zaiyi wuya ya aureta tunda koda ya zo
Asibitin ko inda take be
Kallah ba har ya tafi
Tayi kuka sosai tasan
Yanzu da wuya tasamu mijin aure duk da yaron
Ya koma amma ta riga da tawa kanta tambarin
Da zaiyi wuyar gogewa

Amatsayin ta na budurwa wacce bata taba aure ba
Ace ta haihu sannan inta jewa mijin da ya aure ta
Me zata ce masa inma
Tasamu kenan kai
Gaskiya bata kyautawa
Kanta ba amma insha allahu zata gyara rayuwarta ko allah zai ji kanta ya azurta ta da
Miji nagari

Insha allah duk abin data ke zata daina ta nutsu ko zata samu miji islamiyya ma zata koma

Hajara dai kamar yadda baba yace ta fito da miji
To tafito da wani amma sai dai yanada mata d`aya da yara hudu
Mama zainabu bata so haka ba amma ita ta dage sai shi dole tasa
Uwar ta hakura

Ita kanta zainabun yanzu
Ta kintsu zaman lafiya kawai take nema da mama ayshar saboda ta gano tshin hankalin
Babu inda zai kaita gwara ta lallaba auran nata
Tayi nadama sosai akan biyewa hajjo data taimaka mata wajen aikata muna nan ayyukanta kullum da fargaba take kwanci da ita take tashi
Tasan cewa duk abinda
Ya faru da salma harda hakkin yan,uwan da suka
Raba kullum tana rokon allah ya yafemata
Duk da tanajin bazata iya
Fitowa ta nemi yafiyar abdullahin ba da kuma son k`ara rufuwar asirinta
Tana dai rok`on gafara
Wajen ubangiji da kuma alk`awarin bazata k`ara yarda da zuwa wajen boka ba bare harta cutar da wani

mama aysha kewa salimar wanka komai nata ita ke kulawa dashi .dole uwar ma ta watsar da komai ta rungumi salimar

********************"*

Kinga yaron nan dariya
Yake Qaunah

Na juyo daga linke kayan wankin da nake na kallesu ahmad da kalim
Dan watanni hudu yanzu masha allah bazaka ce
Watansa hudu ba dan yayi wayo tubarkallah .
Ga jiki yayi bul bul dashi
Nice dai na yi rama wai ance tsoron tsotso nake

Kalim dake ta babbaka dariya ahmad na taya shi
Nace kai yau kafara ganin dariyar yaronnan kenan ko
Ehmna ina gani amma kiga yau harfa k`yak`yatawa yake

Aikam ba yau yafara ba
Wannan yaron da kake
Gani badai wayo ba
Kofa barci yake yana shan
Nono ina cirewa yake fasamin kuka dole sai na maida mai

Aida gaskiyar ka d`an albarka gwara a baka ka koshi yace yana kallon
Kalim din shikuma
Kamar yaji abinda yace yashiga kallonshi yana gwarancin sa

Sallamar salaha naji
Saida tabari na amsa
Dan nafada mata ta daina shigowa waje babu sallama kuma alhamdullillah ta daina
Tana k`ok`arin yin sallamar ko yaushe

Aunty aminatu ina
Wuni lafiya lau
Salaha harkun dawo
Makarantar eh mun dawo

Ta gaida yayanta kamar yadda ta gaidani
Ta mik`a hannu ta amshi
Kalim wanda yana ganinta dama yashiga mika mata hannu ta d`auke shi dan yasan ta
Sosai yanason ta dauke shi ko rigima yake ikon allah tana daukarshi yake
Yin tsit

Ta dauke shi ta zauna kan
Kujera
Aunty aminatu nikwa
Akwai sauran abinci
Wallahi yunwa nake ji
Gashi hajjo bata nan
Kuma bata yi abinci ba
Ta fita

Akwai bari na zubo miki
Nan na zubo mata doyace fara da miyar jajje sai bushashshen kifi dana sa

Kai aunty aminatu naji
Dadi kinyi mutuniyata

Aisai kiyi taci kawo shi tukun kici abincin
Aikwa yaro yace sam baisan zance a amshe shiba ya canyara ihu

Kinga barshi muci abincin
Mu ko ba babana daya ke haka suke kiranshi wani
Lokacin
Nace aisai kuyi kecedai bazaki ji dadin cin abincin ba

Ahmad duk yana jinmu
Baice komai ba

Kai bari ma dai intafi d`akinmu inci dan inada wani assignment dana keson dubawa bari kiga na goya shi ko zaiyi barci
Bani zani aunty aminatu

Nan na dauko zanin nabata ta goya shi ta
`Dauki robar abincin ta
Tayi gaba naci gba da linkin kayan

Jinai anrugumoni ta baya
Kinga zo kiji dani ki ajiye
Linkinnan haka kinji
Yar albarka kafin
Adawo da shi

*********************

Tana zaune kan tabarmar parlourn hajjo kalim a gefenta ta kwantar dashi yayi barci rubutunta take kawai bilhakki ta ma manta da gargadin hajjo
Akan karta dinga ganin .
Kalim a hannunta ranar data ganta dashi ranta zai baci
.
Sallamar hajjo ta jiyo .da sauri ta zabura ta tashi
Kafin ma ta dauke shi .har ta shigo
Binsu ta shiga yi da kallo

Ke waya ce ki dauko yron nan wato ban isa na fadamiki magana ba kenan ko salaha na rabaki da uwar yaronnan kinki ji ko ?

Hajjo ya hakuri bari na
Maida shi amma hajjo shifa kalim bai mana komai ba asalima fa
Jikanki ne kawai dan bama shiri da mamarsa sai muki daukar shi

Ta dauki kalim din ta nufi hanyar waje

Wani tunanine ya fadowa hajjo cikin sauri ta mikawa salaha hannu kawo shi hakane kam
Gwara da kika tunamin
Miko shi indaukeshi

Kamar bazata mika mata
Shiba sai kuma taga murmushi a fuskar hajjo
Ta mika mata shi ta nemi waje ta zauna

A a bazama zakiyi ba
Tashi zakiyi kije kiyomin
Cefane tasaba kalim a baya ta goye kamar gaske

To hajjo kawoshi ingoya shi muje mu dawo

A a barshi aina goya shi tunda dama baita ba shan bayana ba bari
Yau dai d`aya yaji yaya bayan nawa yake

Haka ta aiki salaha
Salaha na fita ta maza ta kunto shi ta shiga binsa da kallo tubarkallah yaron tayi mamakin yadda ya girma kamannin sa da ahmad sun k`ara fitowa sosai
Duka da gida daya suke bata ganin shi tunda aminatun ba bari take ana daukar shiba
Kullum cikin tattala shi take

Nan ta dunguremai kai
Shegen yaro ashe haka ka girma lallai samun waje yau kam dai gani gaka allah ya hadamu
Maga me kwatarka
Ta fada tana mai ciroshi acikin zanin goyon
Chapter 55 · 0% Book details