Sashe 63
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina jinsa ne kawai danni jinake a raina muddin na tsallake na bar garin banga abin da zai dawo dani ba na dai ce masa to kawai dan ya sakeni dan ko rungumenin da,yayi daurewa kawai nake
Komawa nayi na kwanta shi kuma ya kasa gusawa ko nan da can juyowa nayi na kalle shi
Cikin turo baki nace ka tashi a kusa dani ni
K`ura mata ido yayi kawai sai lokacin ya lura har wata yar rama tayi idanun nan nata masha allah da suke daukar hankalinsa sun k`ara fitowa sai fuskarta tayi fayau dan ko alamar kwalli babu a idon alamar dai idon ya kwana biyu ba asa mai kwalli ba dan shi kanshi zaice tunda suka fara wannan tashin hankalin ko kwalliyar data saba ta daina yi iya kacinta tayi wanka ta zira kayanta
Nikaina bansan lokacin dana zuba masa idoba ina kallon sa saini ma naga kamar ya d`an rame yayi duhu jinayi tausayinsa na shirin ta somin cikin sauri na d`auke kaina sakamakon wani zafi da ya taso min a raina ya danne tausayin
Ni kike kora ko qaunah in tashi kusa dake ?
K`ara zumburo baki nayi na shiga k`unk`uni na juya kaina
Girgiza kanshi yayi kawai ya tashi ya fita
Tashi nayi kamar an mintsineni na shiga had`a kayanmu sai da na loda akwati biyu manya tukun ma dauki wata jaka na zuba takalma na tsaf dana yara ina ji kamar nayi tsuntsuwa na bar garin
*_😍MAMAN `DAN ALBARKA CW_*✍️
09/11/2022, 2:23 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*
*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*
*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*
_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_
_*PAID PAGE 37*_
Da sallama ya shiga d`akin hajjo dake uwar d`aka ta fito tana gyara hijabinta alamar fita zata yi
Binsa ta shiga yi da kallo daga sama har k`asa ganin yanayin sa ya tabbatar mata babu lafiya to ka zauna mana
Ahmad dake tsaye ya nemi waje ya zauna yana mai cewa fita zakiyi hajjo ?
Eh fita zanyi inason zuwa wata barka ne lafiya dai ko? Tace tana mai neman gefen tabarmar da yake zaune ta zauna
Magana ya fara Dama aminatu keson zuwa gida insha allah gobe zan raka ta
Hajjo da fitar da tayi shiri zatai dama wajen bokanta take shirin komawa dan ita gaskiya tagaji da jiran datake akan lamarin ganin ahmad cikin damuwa da kuma fara batun tafiyar aminatu yasa ta fara jin sanyi a ranta amma jin cewar shi zai rakata yasa murnar ta komawa akan cewar asirinne ya kama
Sai kuma wani tunani ya fad`o mata to inhar aminatu zata tafi gida gobe gobe kenan babu lafiya tunda inda tafiyar shirice ai zata ji
To meya faru da zata je gidan?
Kawai dai tace tana son zuwanne ya fad`a cikin son `boye damuwar dake addabar shi a rai gashi babu wanda zai iya bud`ewa sirrin sa yaji
Anya lafiya ahmad kake ?
Kodai wani abunne ya had`aku kake k`ok`arin `boyemin shin kana da wadda ta fini ne um ?
Ba haka bane hajjo babu abinda ya had`amu kawai dai gidan take son zuwa nikuma naga ya kamata taje d`in tunda kinga tunda akai auran wajen shekaru hud`u fa hajjo bata je gida ba
Kullum tace zata je ke kecewa ba yanzu ba shiyasa ban barta ba amma yanzu insha allah goben zankaita
Ai shikenan tunda kace haka amma ni karkasani cikin maganar ka na cewa nike hana ka bar matarka zuwa ganin gida la la la la ko d`aya sannan ynzu meye amfanin fad`amin d`in daka yi ai babu amfani
Tunda ka riga da ka yanke hukuncinka na gobe zata tafi ai yayi allah raka taki gona
Amma kasani bazaka rakata ba sai kace wani jela ka kaita tasha kasata a mota inyaso intaje kanon ta tari abun hawa ya kaita gida tunda ita ta shiryawa kanta tafiyar
A a hajjo tayaya zan barta ta tafi ita kad`ai bayan bata ta`ba zuwa ba bata san kan garinnan ba sannan can kanon ma rabonta da ita ya dad`e bazata gane komai ba
Nima kuma yakamata inje kodan su baba na gaishe su tunda akai aurannan fa bankoma ba
Hajjo da dalilin daya sa tace ahmad bazai jeba shine tsoronta kar su salisu su tona mata asiri tunda tasan dole in aminatu taje gida zata fad`i wani abu su salisu kam tasansu tsaf sai su kunce mata zani
Babu fa inda zaka je na fad`a maka
Haba hajjo wai meyasa kike haka ne nifa ba yaro bane naga kosu shamsu kina bari suna zuwa inda suke so amma ni saiki hanani haka fa niger har yanzu babu wanda yaje gaisuwa fisabilillah
To dan ubanka duka na zakai sai ka nuna min kai ka haifeni yaron banza kawai mijin hajiya yarinya k`arama duk ta rikita,ma tunani tana juyaka tashi ka bani waje ni
Tashi yayi ya nufi k`ofa cikin `bacin rai shifa gaskiya abunnan ya ishe shi tunawa da baba dayayi yasa ya yanke shawarar zuwa wajenshi kawai har zai nufi d`akin aminatu tunawa da rikicinsu yasa ya yanke
Zuwa wajen baba kawai yasame shi a can dan babu ta yadda za ai yabarta ta tafi ita kad`ai ina sam
Koda yaje ya samu baba na sallamar wasu mutane bayan yagama ne yasamu ya shiga shagon kujerune guda biyu a gefe baban ya nemi d`aya ya zauna ya nuna masa d`ayar zauna ahmad
Zama yayi yashiga gaida mahaifin nashi
Bayan ya amsa ya kalle shi dan yasan dole akwai damuwa tunda har ahmad yaka sa jira ya dawo gida nan ya tambaye shi ya kora mai bayanin har fad`ansu da aminatun bai `boye mai ba
Nan baba ya kwantr mai da hankali kasan su mata k`aramin tunanine dasu kabarta taje gidan goben kuma ka shirya ka raka matarka har gaban iyayanku ka gaisar min dasu sai dai bana son ka sanar wa da mahaifiyar ka zaka d`in kabarta akan bazaka jeba kaji ko
Da asubar kaje da sunan zaka raka matarka ne can tashar sai ku wuce abinku allah ya tsare hanya kaji ko
Amen ya allah baba
Nan ya baro wajen mahaifin nashi yana jin tarin damuwar da hajjo ta k`unsa masa na raguwa yasan dai akwai k`ura in ya tafi basani ba amma ya zaiyi da ita
Hajjo da fitar ahmad kenan ta tashi koba komai taji dad`i aminatu zata tafi in allah ya yarda bazata dawo gidannan ba shegiya
Cikin sauri ta fito a d`akin ta nufi inda tayi niyar zuwa gwara taje tasa aka fe shegiya acan intaje karta k`ara wai wayar garin
*************************
Washe gari da asuba kamar ydda ahmad yace muka shirya muka,nufi tasha koda muka je yiwa hajjo sallama ta fito bina tashiga yi da kallo
Naga kin d`auki kaya haka inkinje bazaki dawo bane ?
Shiru namata dan ita kanta jinake kamar in shak`eta wallahi
To allah y kyauta kai sati nawa ka bata intaje gidan?
Sati hud`u zata insha allah
Hmm kawai nace nidai jinsu nake haka muk je tasha ahmad dan karma hajjo ta zargi dashi da za ai tafiyar daga shi sai jallabiyar shi yadai sa dogon wando aciki da dane ni da kaina saina masa maganar ya canza amma yanzu ba hakan bane a gabana sam burina na bar garin kawai
Karfe shida da rabi motarmu ta tashi sai addu,ar saukarmu lafiya ni ina kujerar baya ahmad na gidan gaba da shi da kalim
Muka d`au hanya ikon allah muna fita a garin naji wata iska ta musmman na bugata kamar wadda na fito a cikin wuta nan da nan wani daddad`an barci yayi gaba dani
Alhamdulillah mun sauka kano lafiya saukar dare muka yi dan ana kiran magriba ne dan hanya sam bata da kyau a gidanmu muka sauka su baba sun yi murna da zuwan mu sai dai duk wannan abun da ake babu wata magana tsakanina da ahmad tunda muka sauka ma murnar ganin yan uwana tasa na manta da wani wai shi ahmad harkar gaba kawai nake yi
Shikam ahmad ganin ta shige cikin k`annen ta yasa ya nufi d`akin yaya yusuf dan anan aka sauke shi koda mama ruk`ayya ta bani abnci in akai masa ilham na aika ta kai danni da bahijja dai hira ta `balle su kalim kam muna sauka ilham sarkin k`ok`ari ta musu wanka da ruwan d`umi daya ke yanayin garin ya nuna alamun sanyi na haramar shigowa
Nan da nan suka yi barci
Bayan baba ya dawo mun gaisa ya tambayeni mutanen gida duk nace suna lfy lau
Ahmad ma yazo ya gaishe shi inda yaji dad`i sosai ganin shi ya rakoni gida
Bamuyi barci ba sai wajen k`arfe biyun dare tukun muka hak`ura badan mun gajiba sai dan baba dayawa bahijja magana akan ta barni na rintsa itama bahijja tubarkallah ta zama budurwa
Washe gari ne suka fahimci kalim baya magana nan dan bantaba fada musu matsalar shiba sai da muka tashi da safennan anata mai magana sukaga ko uhm baice ba nan na korawa baba bayanin duk abinda ya faru cikin kuka ban `boye masa komai ba abu d`aya nasan na boye masa shine zamana tsakanina da hajjo
Hankalin baba ya tashi nan da nan ya shiga min tambayoyi akan dawa dawa nake mu,amala? agidan suwaye abokan fad`ana? sannan me baba musa yace akan abun ? Wanne mataki suka d`auka ?
Banso yamin tambayoyinnan ba sam tunda ni da kaina nasan bani da wasu abokan fad`a sai su kansu su hajjon dan ko cacar baki bani da abokin yi a gidan
Ganin hawaye na zuba idanuna yasa yace intashi in tafi shima zaiyi bincike dan ko ramar dana yi ta tabbatar masa bawani dad`in garin nake jiba
Sannan ya fuskanci kamar nida ahmad d`in bawani zaman lafiya muke ba
************************
Ni kwa shamsu ko har yanzu ahmad basu samu motar bane kaga har yanzu k`arfe goma fa bai dawo ba tun asuba ko lafiya?