← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 78

Sashe 72

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutanen gida da kansu suka farga da halinta da kuma yadda ta maida d`an,ladi hoto maza ke zuwa har k`ofar gida suna d`aukarta
Unguwa duk ta cika da maganar kowa zund`e sa ake akan ya bar matar shi sa,sakai tana yawo ansha tarar shi a fadamai anganta da maza bashi da dai yadda zaiyi

`bangaren hajjo kam dama tace tana wa aishar magana ranar haka tasa ta gaba ta zage hajjon tsaf ta k`ara da gorin komai iyayanta ne sukai rufawa d`an,ladin asiri tayi ta aure shi rashin arziki dai kala kala take wa hajjo hajjo kam babu damar magana dan daga ta taso ita ma zata taso

*************"""*********

*_NIGER_*

Koda muka je gidan su malam liman alhamdulillah cikin farin ciki aka tarbemu baiwar allah inna matar shi ta k`ank`ame su kalim gam a jikinta sai nan nan take dasu
Nan ta kira sauran yaranta dan duk maza ne dama hasanar ce kawai mace sai usaininta koda suka zo sunyi farin cikin ganin yau allah ya bayyana jinin yar uwarsu

Dagewa inna tayi akan nan gidanta zamu zauna bata yarda muje ko ina ba dole da dare yayi sai baba da su yaya yusuf da mama rukayya ne suka tafi dan salima ma tace bazata tafi ba tare dani zata zauna

Kwanan mu biyu gidan malam liman ya gano matsalar kalim nan ya d`ora kulawar shi akan wadda baba malam yake bamu muna kano nida shi har walid kullum safiya sai ya bamu rubutu munsha a cewarshi tsarine daga dukkan wani mugun abu da za a nufo mu dashi sai dai ya koma kan wanda yayi shi

Alhamdulillah kuma mun fara ganin canji sosai dan kalim na d`an k`ok`arin yin magana wani lokacin sai dai bata fitowa sosai kuma ba a fahimtar abin da yake cewa

Nikam ko ahaka ina cikin farin ciki sosai dan da ko uhm baya cewa ai muna sa ran watarana bakin nashi zai bud`e baki d`aya

Kamar kuma yadda yayi alk`awarin taimakawa inna asabe alhamdulillh ita ma tafara amsar nata maganin da kuma addu,o,in daya bata tana k`ok`arin yi sosai ta maida hankali wajen tubarwa allah akan irin abubuwan datayi

Inna talatuwa kam abin ba acewa komai dan yanzu gaba daya halittarta ta juye ganin

Bata iya aikata komai yasa dole aka aikawa yarta cewa tazo mahaifiyarta babu lafiya koda tazo taga halin data ke ciki ta razana dole tasa ta sanar da mijinta zata zauna da ita na kwana biyu ta kula da ita tunda babu abinda take iya aikatawa sai an kwntar sai an tayar

Kamar yadda akayi alk`awarin in mun huta za aje gidan da inna asabe ta binne takardun kadarorin haka kwa akayi

Duk da cewa mu mata bamu bisu ba daga malam liman sai babanmu sai baba aliyu da yaya yusuf sai inna asaben aka je gidan

Nan ta kwatanta musu inda ta binne kasancewar gidan ya dad`e shekara da shekaru babu mutane cikinshi da k`yar aka gano inda ta kwatanta d`in sai da sukayi hak`a mai zurfin gaske tukun suka riski akwatin nan aka fito da ita suka taho

Bayan dawowar sune kuma malam liman ya kira wasu malamai masana akan rabon gado nan aka yi rabo na fisabilillah aka cirewa su babanmu nasu aka damk`ashi ga babanmu akan ya rik`ewa y'an uwan shi aka cirewa y'ay'an asabe dana talatuwa sai dai wani abu kason baba aliyu ya shigo gidan dasuke zaune

Nan yace shi yana son inna talatuwa ta fitar mai a gida tunda yanzu ba bu gadon y'ay'anta ciki
Hakuri su malam liman suka bashi akan ya barta tunda jinya take yanzu

Suma y'ay'anta ganin irin wulak`ancin da akewa mahaifiyar su duk da sun san ita ta jawa kanta amma basa jin dadi babbar y'arta tace zata d'auketa haka ta d'auketa sai dai tana zuwa da ita mijinta yace sam bazai yiwu ba tayaya zata wanke kashin babba kuma tamai abinci muddin tana son zaman gidanshi tasan inda zata kai mahaifiyarta dole tasa sai tasawa ta maida ta inda matan k'aninta ne kawai a gidan tana ji tana gani ta zama bolar su shikam babu ruwanshi da yar uwar shi ce abincine dai yazama dole amma babu mai kulawa da ita har sai in y'ay'anta sun zo

Alhamdulillah yau satin mu uku a niger munyi kyau abinmu munyi bul,buk damu nida ahmad kam yanzu duk babu wannan tsanar dana masa na nemeta na rasa
.
Kuma yaune abin farin ciki kalim ya bud'i baki yayi magana ruwa ya gani ina sha kawai sai ji nayi yace momy zan sha ruwa bak`aramin farin ciki ba muka kasance ranar har kuka sai da nayi saboda tsabar farin cikin hakan dukanmu mun yi murna sai fatan allah k`ara tsare gaba

Inna asabe ma alhamdulillah ta fara gani kad'an kad'an

Sai dai ranar da idanunta suka bud'e baki d'aya ranar ne kuma inna talatuwa ta gamu da makantar dan dama sharad'in kenan da boka ya bata abun dai yazo ya hadar mata goma da ashirin

Watan mu guda cur a niger muka shiga shirin komawa gida munsha tsaraba daga dangi ta ko,ina sai son barka inna asabe ma da yanzu tana gani ba k`aramin shak'uwa mukai da ita ba malam liman kam yace zai bimu saboda yana son taimakawa baba abdullahi da kuma baba musa akan asiran da aka musu sannan yaga inda muke zaune haka kwa akai dashi muka taho

Nan muka rabu dasu cikin kewar juna akan insha allah zamu dawo zuwa nan gaba

*_😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE😍✍️_*
09/11/2022, 2:24 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

_*PAID PAGE 46*_

_*Niger state*_

Masifa kawai take ko had'iyar yawu bata yi ni za a rainawa hankali wallahi kayi kad'an musa ya za ai kace min bakasan inda ahmad yake ba yau wajen tsahon wata guda kenan kuma kaci gaba da rayuwarka lafiya babu wani tashin hankali me kake nufi kenan?

Mero koba komai nid'in mijinki ne be kamata kidinga d'aga min murya haka ba bafa ki fini shiga tashin hankali ba akan rashin samun wayar ahmad

Ya kike so kiganni so kike kiganni ina kuka ina ihun neman shi tukun ki yarda nadamu kifa sani duk son da kikewa ahmad baki kai yani ba tunda nine mahaifinsa nafi kowa sanin ciwon shi shid'in ba yaro bane duk inda,yake insha allah yana nan lafiya zai dawo cikin aminci insha allah

Au haka zaka ce dan nadamu da rayuwar ahmad yau harni kake cewa bankaika sonshi ba ?

Saboda tsabar butulci irin naka musa lallai kam ka kyauta duk irin wahalar dana ke da yaronnan ko da yaushe k'ok'arinka shine ka nuna min iyakata alhamdulillah nima dai na haifa baza ka fad'amin komai ba in da kace ban haifa ba yanzu allah yabani kuma indai nice kujera nake kodan zama zaka nemeni

Kinga ni yanzu zan fita sai allah yamin dawowa

Banza tayi dashi har yasa kai ya fita

Zama tayi ta cigaba da mitar ta ita kad'ai karma allah yasa a ganshi shegen yaro nidama yan kidnapping d'inne suka kama ka su kashe shege tunda baya jin asiri

************************

Mun sauka kano lafiya tare da tarin nasarori da farin ciki yan uwa kowa yaji d'adin dawowar mu da kuma samun lafiyar kalim

A gidanmu malam liman ya sauka
Babanmu yasamu baba abdullahi duk da bai fad'a masa irin abinda su inna asabe sukai ba ya dai mai bayanin rabon gado
Sannan yamai bayanin tafe suke da malam liman

Baba abdullahi yaji dadin bayanin k'anin nashi ga kuma malam liman dayake kamar mahaifinsu jin cewar anzo dashi yaji dad'i maganar gado ma ta faranta mai duk da dai da yace baya son dukiyar amma yanzu sai yaji dad'i aranshi ganin irin tarin arzikin da suka samu nan yace

insha allah in su ahmad zasu koma zanso muje baki d'ayan mu muyiwa yaya musa bayani inyaso muyi shawarar abin daya kamata in takama su sai da kadarorinne sai su saida su dawo da komai nigeria dan bazai yiwu su dinga jigilar zuwa canba

Satin mu d'aya da dawowa baba yace ya kamata mu koma haka tunda mun huta mun yanke shawarar dukanmu zamuje dan suma suna son zuwan dan baba musa
Malam liman ma yace zai bimu dan yana son ganin musan kafin ya koma

Gobe insha allah zamu tafi babanmu da baba abdullahi sai inna zainabu dani da ahmad
Da malam liman

Dalilin inna zainabu na binmu shine
salima ta fayyacewa komai aikam tayi farin cikin jin labarin dan dama lokacin da za ai tafiyar tabbas ta hararo hakan na iya faruwa saboda bata manta sharad'in boka ba akan inhar ahmad ya ga kakanshi asirin hajjo zai tono shiyasa tabawa baba abdullahi shawarar kar yasanar da baba musa cewar yasan inda ahmad yake dan tafison asirin hajjon ya tonu kowa ma ya huta

Ko dalilin daya sa tace zata bisu yanzu shine so take taje taga yaya za a kaya yaya hajjo zata d'auki lamarin shiyasa koda baba abdullahi yace bazata jeba ta dinga lallaba shi akan zata je duk da cewar itama tana tsoron tonuwar asirin nata akan irin abubuwan da aikata

Kaiwa take da kawowa cikin d'akinta ta kai gwauro ta kai mari yau ita keda
Baba abdullahi gashi gobe zasu tafi niger state duk da cewar tasan ta tuba akan abubuwan data yi amma tana cikin fargabar karsu je hajjo zafin tonuwar asirinta yasa ta bankad`o nata laifin ba lallai ya aduba cewar ta tubanba bakomai take tsoro ba illah rabuwar su da baba abdullahi bata son hakan ta faru tana son mijinta

Bata son abinda zai rabata da shi da girmanta dan inhar yaji abinda ta aikata musu shida d'an uwashin da kuma gudummawar data bada akan cutar da ahmad tabbas hukuncin ta shine rabuwar su kuma ita sam bata shiryawa kanta hakan ba
Chapter 72 · 0% Book details