Sashe 64
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haba hajjo wanne irin basu samu mota ba ai tuni motoci sun gama tashi yanzu sai dai na yan kasuwa kuma
Ina ga dai ya biya wani wajen kinsan uzurin sa baya k`arewa
Hakane kam allah ya kyauta
Wasa wasa tun hajjo na zuba idon dawowar ahmad har dare shiru sai lokacin gabanta ya shiga faduwa haka kawai take jin fad`uwar gaba
Tasa a kira mata layinsa shiru baya shiga nan ta tada hankalinta kamar ahmad d`in shi k`aramin yarone
Koda baba yadawo tasame shi da maganar abu d`aya ya sanar mata shine ahmad ya raka aminatu gida ne shine kawai amsar yayi kwanciyar shi dan yasan halin bala,inta tsaf zata hanashi barci aikwa bata barshi barcin ba ranar itama bata rintsaba kwana tayi tana masifa akan ahmad ya raina ta ne sannan shi mahaifinshi shi ya bawa daraja har ya tafi batare da izininta ba sa malam musa tayi gaba da koke koken saboda ba ita ta haifeshibane kuma lallai ya bawa ahmad umarnin ya dawo gobe gobe
Banza yayi da ita dan ya riga da yabawa ahmad shawarar ya cire layinsa da su hajjon suka sanshi da shi dan yana da layinsa dama na kasuwanci da ban nan da nan kam ya aikata
*************************
Kwanan mu biyu gidanmu muka shirya har ahmad tare da rakiyar ilham muka je gidan baba abdullahi
Da sallama muka shiga
mama aisha dake shara ta d`ago tana amsa sallamar cikin murmushi lale,lale da mutan niger state barkanku da zuwa ta k`araso ta amshi walid fade kafadar ilham
Mama zainabu jin abin da mama aishar kecewa yasa ta fito daki itama a a kice manya bak`i mukayi ta fad`a itama cikin tata murnar nayi mamakin ta sosai dan ban ta`ba ganin mama zainabu ahaka ba tana min fara,a ba sai na danganta hakan da ganin ahmad da tayi
tsugunnwa mukayi muka shiga gaidasu nan suka kaimu parlourn baba abdullahi dan safiya ce shi ma yana gida
Bayan mun je mun gaisheshine ni na barsu na tashi muka yi cikin gidan d`akin mama aisha na sauka danni banyarda da mama zainabu ba sam wanda ke nuna maka k`iyayya tun kana yaro ai bazaka manta ba
Nan mama aisha ke tambayata amma zan musu kwana biyu ko
Canai wuni zanyi amma ganin bata ji dadiba yasa na amince zan kwana biyun amma sai dai ilham ta d`auko min kayana dana su kalim
Baba abdullahi sun gaisa da ahmad nan yake tambayar shi akan bayanin da babanmu ya mai na batun cutar kalim nan ahmad ya fad`a masa komai da kuma irin k`ok`arin dayayi na son ya gano waya aikata amma bai gane ba
Ran baba abdullahi ba k`aramin `baci yayi ba nan ya shiga yiwa ahmad d`in fad`a akan inda ya matsa aida ya fahimci wanda yayin hakuri ahmad d`in ya bashi
Ganin yadda ranshi ya `baci har zai tashi sai kuma ya sunkuyar da kanshi yana sosa kanshi
Lafiya kuwa ahmad mene ya faru ko akwai wata matsalar ne dan babanku yace min tunda kuka zo ya fahimci kamar akwai matsala tsakanin ka da aminatun
Nan ya shiga magana cikin jin kunya da kame kame Uhm um dama dama baba amintun ce gaba d`aya na rasa gane abin da yake damun ta baba da na zaci akan ban kawo ta gida bane take min hakan amma yanzu har muka zo dinnan sai na fahimci sam ni dinne batason gani baba dan ko magana bata son min bansan mena mata ba
Dan allah baba kubata hak`uri in ma wani abunne nake mata wanda bata jin dad`i tayi hakuri ta fad`a insha allahu zan daina
Kaji min zancan banza ai dama matsalar daga gareta ne ita kema rashin kirki ka tabbatar babu abinda kake mata dai ko?
Baba gaskiya bansan mena mata ba
Shikenan tashi kaje kaji allah ya muku albarka zan kirata naji dalilin ta nayin hakan
_*😍MAMAN `DAN ALBARKA CE*_😍✍️
09/11/2022, 2:23 pm - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*
*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*
*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*
_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_
_*PAID PAGE 38*_
Koda baba abdullahi ya kirani kuka kawai nasaka masa akan nidai bazan koma ba nagaji da garinne kawai
babu irin tambayoyin da baimin ba ko akwai wani abu dana ke `boyewa ne amsar dai d`ayace ita ce kuka ganin haka ya fara lallashina da banbaki akan inyi hak`uri da kome ne tunda nak`i fad`a in koma
Ganin dai nak`i amsar maganar sa yasa ya rufe ni da fad`a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba har su mama aisha suka ji
Shigowarsu parlourn kowacce k`ok`arin tambayar meke faruwa take nan ya kora musu bayani mama aisha ce ita ma tashiga lallashina akan inyi hak`uri abarni inna huta na koma
Mama zainabu kam da yake ita za a iya cewa tasan dawan garin tunda duk tana da labarin irin zaman dana ke duk da yanzu hajjo ta daina sako ta cikin hidimarta tun bayan sa`banin da suka samu akan zubda cikin aminatu na farko bata bata had`in kaiba bata k`ara nemanta ba
Sai da ta tabbatar kalim ya kurumce tukun ta kirata cikin murnar ta fad`mata taci nasarar nakasta yaron
A lokacin bata bata goyon baya ba gaskiya ta fito ta fad`a mata akan ita fa ta daina biyemata tuni taga ishara ta tuba ta koma ga allah babu hannun ta a k`ara cutar da zuri,ar su abdullahi dan tana so koba komai ta tsira da auranta koda komai zai watse gwara tun wuri ita ma hajjon ta tuba ta gyara kurakuran ta tun lokaci bai k`ure mata ba duk da tasan cewar shiryuwar ta ta sai allah kawai dan tayi nisa bata jin kira
A lokacin kaca kaca sukai da junan su dan hajjo catai munafuncin ne kawai dan taga ita burinta ya cika shine take son juya mata baya yanzu ta fara neman hanyar ganin bayan zuri,ar su dan haka wallahi karta ji karta gani in ta manta da sharad`in ta tayi wani yunk`uri na tona mata asiri tagani
Wallahi babu abinda ita ma zata fasa
Tun daga lokacin basu k`ara waya da junan su ba tama goge number hajjo d`in tasa a ranta ta daina insha allah kuma ko ita bata tona mata asiri ba zata yi addu,ar allah ya kawo sanadin da asirin nata zai tonu
Koda taji abdullahi na batun kurmancewar kalim bata yi mamaki ba
Ta dai ja bakinta tayi shiru zata taya su da addu,ar allah ya bashi lafiya inda rabon hakan
Jin baba abdullahi na k`ara balbale aminatun da fad`a yasata dawowa da hankalinta kansu
Kallon shi tayi tace
Abbansu hajara kayi hak`uri ku barta ta zauna d`in mai d`aki fa shi yasan inda yake masa yoyo tunda kuka ji tace bazata koma ba akwai abinda yake faruwa watak`il bazata iya fitowa ta fad`a bane kubarta ta huta d`in inta buk`aci komawar saita koma
Kinga zainabu iskancine kawai ya motsa sai ta koma anma fasa barinta ta huta d`in k`afar ta k`afar shi
Jin hakan daya ce yasani k`ara rushewa da kuka dan ji nayi kamar yace za akaini kabarina
Mama aisha ce ta girgiza kai karka ce haka abban hajara ka duba tunda akai aurannan yarinyar nan ko ta waya bata taba kawo mana k`arar komai ba kuma,kaima kasan ko tsakanin harshe da hak`ori ana sa`bawa
Mu barta d`in kamar yadda maman su hajara tace inya so in ta huta sai ta koma shi mijin nata in yayi kwana biyun sa kace ya wuce kawai ta gaggaida dangi ta danyi kwana biyu kaga kan lokacin hankalinta ya kwanta
Kallon su yayi ya shiga nazarin maganar kowaccen su tukun ya d`aga min hannu akan in tafi tashi nayi cikin farin ciki nayi hanyar waje na barsu a parlourn suna k`ara tattaunawa
Kici bus mukai da aunty salma da aunty hajara kowacce sa hijabinta har k`asa da jaka a hannun su alamar dai daga makarantar islamiyya suke aunty hajara da anfasa auranta tun lokacin da akasaka auran haka kawai daga baya auran baifi sati biyu ya rage ba mijin ya dawo wai ya fasa yaji labarin sunyi cikin shege har hajara na da d`an shege shi bazai auri karuwa ba
Lokacin bak`aramin tashin hankali suka shiga ba jin irin sharrin da aka lak`aba musu bama salimar data yi abun ba har ita hajarar ya shafa
Baba abdullahi yaji takaici k`arshe yace allah ya kyauta ya kawo musu miji nagari aka tattara kayansa aka basa
Mama zainabu kam kuka tasha shi taga ishara k`iri k`iri yayanta sunk`i auruwa da k`yar da taimakon mama aisha ta hanyar ban baki da take mata ta fauwalawa allah
Amarya ma anci burin auran dan har lokacin bata bar rawar kaiba sai dai ta rage yawon jin anfasa auran data ci buri take d`oki bak`aramin hauka tayi ba dan tana son shi sosai ganin ba sarki sai allah ta tattara ta ji jone din salima ta koma islamiyya tare da istigfari da neman za`bin allah a lamarinta
Kowacce cikin farin cikin ta ta tare ni sai abin yabani mamaki harda salima mai shamin k`amshi da hantara ta ada yanzu harda ita a masu yimin oyoyo
Jana sukai mukai d`akinsu kowacce na k`ok`arin jana a jikinta ganin dai sun sake min yasani sakewa cikinsu muka shiga fira duk da firar tawa jifa jifa ce
Nan suka d`auki walid dayayi `bul,`bul dashi tu arkallah kowacce na santinsa sun tambayi kalim nace sun fita da babanshi koda ahmad ya dawo sun gaisa cikin mutumta juna suna kallonmu suna sha,awar dama suma suyi auran su huta duk da gidan bawa ta takurawa suke fuskanta ba amma sun gano mutumcin mace shine gidan mijinta dan duk k`awayensu sunyi aure hajara shekararta ashirin da takwas salima ce me ashirin da shida
Kamar yadda baba abdullahi yace ya kira ahmad ya fad`a masa yayi hak`uri ya koma ya barni inna huta zandawo da kanshi zai kira shi yazo ya d`auke ni