← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 78

Sashe 5

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah yayi dare gari ya waye asubar fari ahmad ya tashe ni mukaje mukayi alwala muka gabatar da raka,atanil fijir sannan ya wuce masallaci nikuma na jira bayan na idar da sallah na gabatar da azkhar dina

na tashi da sauri na kunna heater dan nasan karfe shida nayi zasu dauke insun dauke bansan ina zan sa ruwan zafi ba

Na fara da tattara dakin cikin azama na gyara gadon na dauke kwanukan wanke wanken na fitar dasu kofar daki na share ledar tsakar dakin na dauko tsumman danake goge leda dashi na jika shi a bokitina karami na dan zuba kllin aciki na goge ledar tas na na kunna turaren tsinke na fesa room freshener na fita

Na dan kauda kwanikan nasa tsintsiya na fara share sumintin kofar dakina ina cikin sharar sai ga ahmad ya shigo na ajiye tsintsiyar na bishi daki ina mai sannu da zuwa

Yana murmushi ya amsa sannu da aiki

Na tsugunna nace ina kwana ya dagoni yasani ajikinshi yace lafiya lau ya kika tashi ya gajiya kuma nayi saurin sa hannuna na rufe fuskata

Yace yi sauri ki karasa sharar ki zo mudan kwanta kafin gari ya gama waye wa

Nace a a fa kamanta zanje gurin hajjo kaga jiyafa mukayi magana yakamata kafin ta nemeni infara zuwa

Ya ce hmm to saikin dawo
.
Nace ka kwanta ka huta kaji

Yace to

Ina fitowa na karasa sharar na koma daki na dauko hijabina nasa na zo na tattara yan kwanikan wanke wanke na na doshi wajen hajjo

Inda take wanke wanke na fara aje kwani kan sannan na karasa bakin kofar dakin ta na dan tsugunna hajjo ina kwana

Nayi yakai sau uku tukun can daga kuryar daki ta amsa lafiya lau

Na tashi naje inda take aje tsintsiya na fara share tsakar gidan na zagaya lungun da Sani yake kiwon ragonshi da akuyoyin sa dana hajjo na share kashin su cikin kyankyami duk sun zubar da ruwan shansu a gurin wajen duk ya dame

Ina gamawa na naje gindin murhu na sa itatuwa dan bata yarda da girkin gawayi ba indai ba miya ba shima awanda take kashewa ne na icce

Na kunna wutar na dauko tukunyar da take dora ruwan koko na dauraye na zuba ruwa ina cikin dorawar ne

Baba yayi sallama na dago na baro gindin murhun nazo na tsugunna kafin ya ida shigewa daki na ce ina kwana baba ina kwana?

Ya kalleni cikin kulawa yace lafiya lau aminatu kuntashi lafiya?

Nace lafiya lau baba

Ya ce masha allah yana me shigewa daki

Na tashi naje na karasa inda take aje gasarar koko na tace ruwan dake sama na debi gasarar gwargwado na zuba abotikin da take dama koko na kara ruwa akan sauran

Nashiga falonta na tarraro sauran kwanikan cin abinci naga na Bashir bai cinye ba na nemi wata yar karamar tukunya na juye na rufe na aje mata dan nasan tana sane da shi hajjo kenan nace a raina ina mai fitar da sauran kwanikan

Na tatara su guri daya na fara wanke wanken ina kammalawa zuwa lokacin ruwan kokon ya fara tafasa na je na dama cikin fargaba dan bansan me zata ce yayi ba yau kullum cikin korafin ban iya dama koko ba take tadinga mita acikin mutanen gida kenan kowa naji tana hadamin da gori

na dauko guntun abinci na dora na tattara gurin nakai botikin kokon dakinta

wannan kokon da shine kowa zai karya sai in mutum yana da chanjin shi in masu kuli sun kawo da gyada mai gishiri ko Wata waina da ake kawowa ta Wake wai ita,banbara tukun mai kudi ya siya

Inbaka dashi kasha kunun kajira abincin rana

Ina saukewa Na fito naje dakina na dauko kofin kokon Ahmad na kawo na ajiye a wajen na fita na zauna a kujerar tsakar gidan zuwa lokacin bakwai da rabi na safe tayi

Maman Aisha ce ta fito daga daki tana mika da hamma bakinta duk miyan bacci idonta harda abin kwantsa sunan wai tayi alwalar asuba da sallah komawa barci tayi

Ta kalle ni a a Amarya har anfito kice har kin kammala aikin

Na kalle ta nace ina kwana? Ya kwanan su Aisha

tace lafiya lau

Tana kallona ta dauki buta tayi hanyar bayi..

Na bita da kallo mace har mace daga haihuwa uku ta maida kanta kamar wata uwar mata ba tsafta ba gyara fisabilillah kinada yara uku har wani lokacin barcin bayan asuba kike dashi ba ayin maganar shirya yara makaranta ba kullum sai sunyi latti dama na dauke kaina sakamakon karar kofar dakin samarin gidan da aka bude

Sai sannan Suka tashi kowa ya fito su su hudu alamar dan ladi yana can barcin asarar sai lokacin
Data kada masa zai tashi

Ba kunya yake sallar shi a dakin hajjo rana tsage tsage har takwas da rabi wataran nayi kafin ya yi sallah abin takaici bantaba jin hajjo ta tsawatar musu ba amatsayin su na maza da ya kamata ace sallar asuba bata wuce ba

Baba indai zaije masallaci yana buga kofar su kullum inaji daga dakina amma basa tashi

kowa da dan gajeran wandon shi abin babu wani tsari Suka shiga daukar butoci kowa ya nufi inda zaiyi alwala

Baba ne naga yafito daga dakin da shirin sa na zuwa wajen sana,ar sa na kalle shi nace baba adawo lafiya

Yace allah yasa

Yana fita kamar jira hajjo take ta kwala min kira ..

Na tashi na shiga salaha nagani kwance tana narkar barcinta a kan gadon hajjo

To meye saikin wani biyoni har uwar daka kije falo kijira ni

Na tafi na tsaya

Ta zo ta sameni ina kofin kokon naki naga kin kawo nashi shi kadai nace eh ki hada mana kawai tunda bawani sha nake sosai ba

Ta kalle ni a,wulakance kedai kam kinyi asarar halinki bantaba jin cewa mutum kamarki ba baya shan koko ba sai ke wato kin samu waje harda zabe Shi ubannaki salisu ai dai nasan ba arzikn shayi yake da shiba bare kice min shi kuke sha,

Nayi shiru raina na kuna babu abin da na tsana irin kiran sunan mahaifina da hajjo keyi kai tsaye tana kokari gurin aibata shi ina jure komai da hajjo kemin amma inhar zata sa mahaifina sai naji abin ya fi konamin rai

A gidammu bamu da karfin shayi amma mukan dora tukunya sau uku a rana safe da rana da kuma dare da safe akan dama kunun tsamiya saboda mahaifina yafi sonshi amma duk wanda yaga bazai shaba akwai dumame nakan dora mana dumamen ina gama dama kunun

Ni dumamen ma nafi ci don gaskiya ba kasafai nake shan kunun ba sai randa nayi sha awar shi inba mu tashi da dumame ba akan aika bahijja ko Ilham su amso mana waina da kuli musha kunun da ita

Nayi firgigit na dawo daga tunanin dana tafi sakamakon maganar shamsu danaji

Yana cewa hajjo jiya fa dana je dakin yaya ahmad kallo wallahi ido da ido yaya ahmad yace wai dare yayi bazan kunna musu kallo ba kuma fa da badon aminatu ta hanani shigaba kafin ya fito wanka da inma yazo ya tarar dani bazaice komai ai.

*Wannan littafin na kudine idan kinason cigaba da karantawa zaki same shi akan farashin normal group 300 VIP 400 masu so ta private 1000 ki turo kudin ta wannan account number 2375144550 ki turo evidence ta wannan number 09138320449 katin MTN ta wannan number 09138320449*

*Idan kuma littafin mu guda biyu kikeso TUSHEN MU DAYA da FANSAH 2022 Zaki turo normal group 500 VIP 800 ta private 1000*

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
09/11/2022, 2:15 pm - Maman Dan Albarka Ce: *🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE😍_*

*Free page4️⃣*

Amma haka ina ji ina gani sai hakura nayi nazo ma in fada miki jiyan sai kuma naga kinyi barci

Au aida ka tasheni wlh da ko uban barcine sai ka kalla jimin sabon iskanci
Aiba daga gidan uban kowa aka kawo kayan kallon ba bare a nuna isa da takama nan aka zo aka tarda ahto

Nasan dani take magana ma ana dai banzo dasu ba sai na yi kamar ban fahimta ba

Nace Hajjo zuba mana kokon

Ta juyo ta kalle ni tayi kwafa ta fara kokarin bude botikin kokon

Jinayi an wani bangajeni anshigo sakamakon ina dan gefen bakin kofar shigowa bawani bane da wannan aikin face dan ladi wanda duk cikin su jinina sam bai hadu dashi ba

Mamaki ya kamani duk fadin hanyar nan baiga inda zai wuce ba sai ya gogi jikina ta hanyar bangazata

Na dago ina kallon shi kozai nuna alamun ya bangajeni ko kusa saima yadda ya ke tafiya yana bubbudawa da singlet dinshi da dan gajeran wandon shi fuskarshi da alamun dai yanzu yayi alwala sallah ya shigo yi

Ya kalli Hajjo yane hajjo naga tawani tsayawa mutane ahanya lafiya kuwa?

Hajjo da taga lokacin daya bangajeni amma ko nuna alamar hakan bataiba bare tamai magana sai cewa tayi

Kasan shi munafuki duk inda yake sai an ga shaida wai ashe jiya shamsu yaje dakinsu ahmad ya koro shi wai bazai musu kallo ba

Dan ladi ya juyo yana watsamin wannan dan iskan kallon nashi daya saba yace kinsan farin shiga inaga gidan tsoho babu kekuwa hajjo ba dole ba adinga nuna isa tunda ansamu duniya ya kareshe maganar yana me kyalkyalewa da dariya harda buga kafa

Shamsu dake tsaye ya mikawa hajjo kofi yace gashi ni hajjo zubamin kokona yau natashi ko asi banida ita kibani Naira ashirin zan siyo kuli na hada

Ta amshi kofin ta fara zubamai ta bude gwangwanin data ke aje kudi ta dauko naira hamsin gashinan sauran ka rikemin chanji kana siyo wa ka kawomin chanjina

Ya amsa ya juya ya fita

Dan ladi kuma babu kunya ko kaya bainema ba bare yakara suturta jikinshi ya tada sallah
Chapter 5 · 0% Book details