← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 78

Sashe 6

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacinne kuma salaha dake barci a uwar daka ta fito tana mika ta wuce itama nasan alwalar zatai
.
Sai sannan hajjo ta ga damar miko min kokon tana jefo min wani kallo

Na amsa na juya
*************************

Ina komawa daki na tarar har ahmad yayi wankan sa yana zaune yana danne dannen shi a waya
Yace kindawo?

Nace eh na ajiye kokon

Yace bari naje na amso miki abin da zaki karya inkinji plashing dina ki fito ta wajen katangar ki amsa .....

Nace tom saika dawo

Na cire hijabina na dan kwanta akan doguwar kujera ina wuce gajiya

Can naji ring din wayata na tashi nasa hijabina na fito na tsagaya ta can bayan dakina katangar wajen bawata mai tsayi bace saboda masifar hajjo ahmad bai isa ya shigo min da abu a leda ba tun banfi kwana hudu ba da in zai shigo zai shigo da ledar shi a hannu kai tsaye zai wuce yaba hajjo nata shima sai ta amsa ta duba intaga nawa yakai nata tofa saita rage acewar ta ai su sunfi mu yawa ga kannen sa haka zaibata ta rage ta bashi sauran

Amma hajjo duk da haka hajjo saboda bakin cikin karma a kawomin koda kadan dinne inji dadi ta fara tsiro da ai yana bannar kudi ita ta yafe yadaina ba,ta kudinshi gwara ya dan kara wani abu a kudin daya ke bata na abinci akara yawan abinci adinga zubamana wanda zai kaimu dare

Farko ya amshi shawararta ya kara kudin amma dayake inda na godewa allah shima yana ganin abincin ba karawar tayi ba akan yadda tasaba zuba mana gudun kuma karta ga ya cigaba da shigowa da leda yasa ya bullo dubarar dinga mikomin ta katanga saboda dakin hajjo setin kofar shigowa ya ke kallo duk wanda ya shigo idonta na kai

.
Wataran kuma akwai wani yaron makotanmu shu,aibu shine ahmad din ke mikawa abun da ya siyo bayan yashigo sai yaron ya mikomai

Shima saina duba naga babu wanda yake yunkurin shigowa lungun tukun nake zuwa

Haka naje nasa kujera na taka na mika hannu ya miko min na amsa tukun ya shigo

Haka lokacin dora girki nayi naje gurin hajjo na amshi komai kamar yadda tasaba bayar da komai a kididdige na dora na kammala yauma shinkafa ce da miya sababbiya wadda tunda nazo gidan ba ataba canjawa na kullum ita ake sai lokacin da kwalin taliya na nan to ana dan hadawa da ita haka ta raba kamar yadda
Ta saba

Sai dai yau ba azuba mana kanzo ba

************************

Yau jikina duk a sanyaye na tashi sakamakon yaune ahmad zai koma wajen aikin sa hutun da ya dauka ya kare Aikin painti yake amma a karkashin wani kamfani mai suna _(Fine coat paint_ ) inda In kwangilar wani aiki ta taso kamfanin kan amsa sai sutura Ayi sukuma ke biyan su ahmad yanzu haka aiki ne ya taso a abuja

Nagama zuge jakar kayan
Na tashi na dauko brush da makilin dinsa na nemi gefen jakar nasa na dauko duk wani abun dana san zai bukata kama daga sabulun wanka soso da manshafawa da dai sauran su

Zuwa lokacin ya kammala wankan da ya shiga na tashi na taimakamai ya goge jikinshi duk cikin sanyin jiki nake wanda shima naga jikin nashi a sanyaye yake gudanar da komai ya kammala shiri

Yace bari naje na sallami hajjo na dawo nace tom yasa kai ya fita

Lokacinne na daga kai na kalli agogo karfe tara na safe

*************************
Yana zaune gabanta ana ana bugamai lissafi

Yanzu kwana nawa zakuyi inka tafi?

Yace bansan yanayin wajen ba hajjo ko kwana nawa zamuyi bansaniba ya karasa fada yana dago kanshi dake duke

Tace to kaga kenan kudin abincin zaka barmana ishashshe dan kar muzo muna kame kame

Yace to hajjo kamar nawa za abar muku tace kadai kawo ishashshe nace

Ya dauko dubu goma sha biyar yace gashi hajjo kuyi maneji kafin innaje muga abin da hali yayi inya so ko turowa ne innaga takama sai na karo muku

Ta kalle shi ta kalli kudin babu alamar zata amsa

Amma dai kasan ba haka kasaba bayarwa ba ko?

Yace nasani hajjo kinga tunda akayi bikinnan bawata fita mukayi ba kudin dake waje na ne mukayi ta ci banda allah ya taimakeni da gudummawar da aka dan babbani inaga da tunima na koma wajen aiki dan zaman haka ai bazai yiwu ba sannan kinga yanzu ga aminatu dole inzan tafi zan bar mata wani dan abu saboda in bukatar hakan ta taso tayi

Ta ce a a kaikuwa banda abinka me aminatu zata yi da wani kudi yoh inama ta sani bare tace ga abin datake so sannan ga abinci gida anayi kaga babu maganar bukatar wasu kudi kawai ka karo mana dansu isa

Yace duk da haka hajjo akwai wani abun da dole sai ta nema tunda ba na nan kuma,bawasu yan uwa take dasu ba bare su zo kota samu wani dan abu

Da taga dai alamar ba bayarwar zaiba sai catai to bani wanda zaka bata din in ajiye mata inya so in tana da bukatar sai kace tazo gurina ta amsa dan inka barmata ma abanza ne bawani sanin darajar su tayi ba

Dan dai a rabu lafiya ya dauko dubu biyu cikin dubu biyar din daya yi niyar barwa aminatu ya ce to gashi hajjo

Ta amsa tana hadawa da wadancan to kokaifa

Ya tashi yace to hajjo na riga danayi sallama da baba da muka hadu masallaci inyazo ace masa na wuce

Ta ce to shikenan allah ya tsare hanya ya bada sa a ya amsa da amin

Ya dawo daki ya tarda ni ya zauna ya dauko sauran dubu ukun dake aljihun sa ya miko min yace Gashi ko wata bukatar zata taso miki nasan dai kayan shayin dana kawo miki jiya zasu daukeki wasu yan kwanaki kiyi hakuri kinji insha allah bazan dade ba koda ba akammala ba zan dawo na ganku

Na amsa kwallah na taruwa a idona ina,kokarin maida ta nace tom nagode allah yakara budi da wadata ya tsare ya kare ka aduk inda kake ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya yabada sa a akan abin da akaje nema

Ya jawoni jikinsa ya rungume ya amsa da ameen ya allah Dear zanyi kewar ki sosai wallahi da ba don nema ya zama wajibi ba da baikamata na tafi na barki ya ha ba amma karki damu bazamu dade ba

Na kara kankame shi ina,kara tusa kaina a kirjinshi ina kokarin hana kukan da ya tahomin fitowa

Ya dago fuska yana girgiza min kai karkiyi kuka mana kinji Baby na

Na,kara shagwabe fuska ina,tabe baki alamar kuka

Yayi saurin jefa bakinsa cikin nawa yana shafa bayana ahankali

Tuni na hadiye kukan yadau mintina biyu tukun ya zare bakin shi nayi lamo a kirjinshi

Ringing din wayar shi shi shi ya fargar damu

Ya sa hannu a aljihun wandon shi ya fito da ita ya daga

Ok kun karaso to ganin fitowa .

Shine abin dana ji yace yana mai raba jikina da nashi a hankali

Tuni kukan ya taho min har ga allah na kasa rike shi nasan zanyi kewar mijina ga fargabar halin da zan fuskanta daga su hajjo

Ya kalleni ina hawaye yace kidaina kukan kinji karki karya min gwiwa

Nace to ina share hawayen na dauki hijab dina nasa na dauki jakar shi ta matafiya ina mai binshi a baya muka fito

Naraka shi iya lunguna gudun karna bishi wajen hajjo inyi laifi na juya daki cike da kewa jiki a sanyaye

Haka na daure zuwa rana naje nayi ayyukan dana saba yau abincin an zuba min shi kamar na roka nidai na amsa na taho dan batasan bashine a gabana bama

*************************
Kwanaki sun shura yau Kwanan Su ahmad biyar da tafiya tunda suka tafi fa su hajjo suka bude sabon babin takuramin

Ya zamana maimakon girki da wanke wanke da shara da kokon safe da nakeyi har wankin hajjo dana salaha da ta isa tayi dana umar duk nikeyi

Nice gyaran dakin ta gugar uniform din su salaha

Bani da wani hutu daga wannan sai wannan

Gashi har addu a nake allah yasa kar akawo Nepa da dare saboda daga ankawo bani babu barcin wuri sai su zo su cikamin daki da sunan kallo

Gado nane ban yarda su hau akwai kujeru guda biyu cikasu suke sumin kaca kaca da daki ga abokansu da suke gayyato wa gasu dan ladi ne kawai baya zuwa cikin su shidda

Karshema salaha nan tace zata kwana babu wanda ya fadamin cewa zata tayani kwana kawai dai naganta bayan sun gama kallo tana kokarin hawamin gado ta kwanta

Nayi sauri gurin janyota nace lafiya?

Salaha kike kokarin hawa gado

Sai catai ai hajjo ce tace tazo ta kwana dani ta tayani kwana

Nace to ke haka aka ce miki anayi saikiyi kokarin hawa gado

Budar bakinta sai catai ita ai hajjo catai ta kwanta gado dan ita bata kwanan kasa

Na kalleta nace to kikoma kan kujera in kwanan zaki tayani amma wallahi kinji na rantse bazaki hau min gado ba inkuma kujerar bata miki ba kitafi dama bani na kira ki ba

Ta fita ta banko min kofa da karfi na kalleta

Azuciya ta nace wallahi ko hajjo ta zo banga fitsararriyar yarinyar da zata haumin gado ba inba rashin tarbiya da da'a ba ina wata salaha zata hau gado fisabilillah

Gadon mijina zan bari ta hau hmmm nayi kwafa na hau gado na kwanta banma rufe kofa ba ina tsammanin hajjo zata biyo bayanta

Aikwa bangama tunaniba sai jin maganar ta nayi

Wuce muje inji in tazo da gadon ne daga gidan ubanta hajjo ke maganar ta kokarin shigowa

Nayi saurin dirowa na coge bakin kofa

Tana karasowa tace kikace salaha bazata ta kwanta miki a gado ba saboda Ubanki salisu ya siya ko?

naga ubannaki saboda tsananin talaucin sa da shegen son banzansa ko katifa wannan bai siya miki ba bare ayi maganar gado
Chapter 6 · 0% Book details