← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 78

Sashe 4

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eh kwa tsaya ku zuba min ido ina babatu mana marasa mutumci wato daga zuwan yarinya shine kai mai mata dan bata gaidata ba harda marar min ya meye dalilinka? Koni dake da ita bansa mata hannu ba sai kai saboda kayi aure?

Ban fita daga mamakin abinda ya kawo hajjo ba sai ga wata sabuwa wai ahmad ya mari salaha shima mamaki ya hana shi magana sai can da kyar ya fusgo maganar

Hajjo ita salahar tace na mare ta? yaushe ni da kaina na mare ta? hajjo fada kawai namata kuma naga tashigo bata gaida mai dakin ba shiyasa

Lahaula wala kuwwata illah billahil alaihil azem
Yanzu ahmad salahar ce zata maka karya ka mareta kace baka mareta ba sannan ka kalli tsabar idona kace me dakin wace me dakin? Nace wace me dakin to ahir dinka ina ce Badaga gidan ubanta tazo da shiba nan ta tarar dashi kuma wallahi tallahi kaji rantsuwar dan musulmi inka kara samin hannu kan yara saina saba maka Shanyayye kawai

Kekuma na dawo kanki wallahi duk takamar ki da bokayen dakike takama dasu sainayi maganin ki mu zuba nida ke Matsiyaciyar yarinya mara arziki gadon tsiya kawai uwar gurmi

Ta kada kai ta wuce ta barni tsaye nida ahmad cikin jimami da tsananin mamaki

Shine ma yayi kokarin jawo hannu na muka koma daki kowa yayi jigum anrasa mai fara yiwa wani magana

Can nanisa nace kayi hakuri kaji ..

Ya dago ya kalleni ni abin da hajjo tayi yanzu yasa na fara shiga wasi wasi akan barinki da zanyi in koma gurin aiki kinga fa ina,nan ma yaya aka cika bare bana kusa wlh ina tsoron abin da zaije ya dawo

Na tashi na karasa kujerar da yake kai na tsugunna na dafa gwiwowin sa da hannayena nace karka damu babu abin da zai faru kaji My insha allah zanyi kokarin gujewa abin da zai kawo matsala tsakanin mu inace sai nayi ba dai dai ba hakan zata faru ko? To insha allah zaka same ni me biyayyah indai dan wannan ne kar ya dameka na karasa fada cikin murmushi duk da ina jin ciwo araina na kewar mijina da zanyi yanzu jibi zai tafi wazai dinga lallashina? ina zanje inji dadi? Sai na tuna allah bazai taba bari su cutar dani ba

Ya dago yana kokarin yin magana nayi saurin dakatar dashi ta hanyar sa hannuna a bakina alamar yayi shiru nace bari nasama ruwan wankan ko kafin lokacin sallah yayi

Yace to jeki juye min

Na tashi na dauko flasks din ruwan zafin da bana rabo da zuba ruwa aciki na je na juye na sirka masa na kai bandakin na dawo na taimaka masa ya rage kayan jikin sa

Ya fita wanka kafin yadawo na gyara inda muka ci abinci na dauke kwanukan

Na fito mai da kayan da zai sa na ajiye mai dan nasan dole ma inya shirya yanzu ya fita saboda jarabarsu sunce baya fita tunda yayi aure wani lokacin hajjo da kanta take zuwa saita tisa shi gaba ya fita tukun ta koma wajenta

Bayan ya fito ya shirya ya nemi waje ya zauna nace yau ba fita ?

Yace babu inda zan iya zuwa yanzu kinga fa jibi ne zan tafi daga yau zuwa gobe ne fa kawai ni ba inda zan iya zuwa yanzu kibarni dama ni ba son fitar nake ba nafi son inzauna dake abuna mutum ma yayi auren anhanashi sakewa da iyalin shi ya karashe cikin damuwa

Na kalle shi ganin halin da yake ciki yasa na yi shiru dama nima nafison ya kasance a gidan sabo da banason shigowar da maman Aisha keyi min ita da hajara saboda ba komai ke kawo su ba sai gulma da zarar sunga ahmad ya fita zasu shigo min

Suyi ta kawo min gulmar jama ar gidan wani lokacin harda na hajjo suna bugun cikina suna son suji wata kalma daga gareni suje suji dadin idarwa

Dana fahimce su insun shigo saina daure fuska bana ma basu fuska saboda kullum suna gindin hajjo insuna zaune da hajjo zaka rantse da allah da kawar su suke zaune basu da aiki sai gulma da yada jita jita na mutane

al adar su sam bata burgeni sunji hausa sosai da hausa suke magana saboda hajjo bata iya mayar da yarensu na Nupanci amma taji shiyasa indai ina wajen suna magana sai dai su canza baki a amsar hajjo nake fahimtar gulmar wani suke

*************************

Da dare yayi ahmad ya tambayeni mai zanci tunda yasan bamu da sauran abinci kuma gashi ba tukunyar kaina nake dorawa ba nace duk abin dakaga ya dace ka siyo mana yace aini bansan me kika iya ciba kuma kin ga garinnan bawai kamar can kano bane ba wasu abinciccika ake sai dawa ba

Na kalle shi nace to me ake saidawa yace akwai wata mai masar shinkafa inkinaso da sauri nace yawwa don allah ita zaka siyomin nace dame takeyi yace da miya da,yaji

nace yaji kuma?

Eh yaji da miya ko sugar duk wanda kike so

Nace a a ni banason yaji yaza aci waina da yaji da kuli ne dai amma kasiyomin da miyar

To me za ahado miki dashi?

Nace duk abin dakaga ya dace

Yace to saina dawo

Nace adawo lafiya

*************************
Bayan tafiyar shi na zauna nayi tagumi ina tunanin wannan wace irin rayuwa ce kayi aure ma ace gidan ubanka yafi gidan mijin sakewa duk da dama akan samu hakan ta daliin rashin wadata ko kuma shi gidan uban naka yakasance wadatar shi yafi na mijin

Amma ace sau daya za adora tukunya ta zarce kuma baza ayi na dare ba wannan shine mutum zaici har dare inkuma,ka cinye sai ka nemi wani abu al adar garin kenan sau daya suke girki in anyi kuma sai gobe

Yaran hajjo mazan wadanda ke wajen aiki sukan aiko a amsar musu in dare yayi kuma sai wajen me shayi umar kuma da salaha dama takan ware musu nasu na dare daban

Baba kuwa dama inya bar gidan sai can dare yake dawowa saboda yanayin sana ar shi ta saida kayan provision Kuma

Bani da matsala da baba wlh tunda nazo bazan ce ga abin da yataba yimin ba saboda shi ba mutum bane mai magana sam yadda kukasan hajjo ta shanye shi bashi da katabus ko akan yaran ita ke zartar da komai bai isa ya tofa ba yadda taga dama take yi dashi duk matsin data kemin bashi da labari bare ya tsawatar kuma ko yaji bana tunanin zai iya magana saboda mugun tsoronta da yakeji

Ina zaune ahmad ya shigo yayi sallama na tare shi na amshi ledar hannun shi ina mai sannu da zuwa

Na dauko flet na dauraye shi na juye wainar da sai tiriri take da tsokar nama hudu akai daga yana yin miyar na fara shakkar wainar wata irin miyace kamar ruwa sai abu abun alayyahu da dan fatsi fatsin kayan miya sai ruwan miyar danaga yana yawo a flet din

Ba abun ince banci ba bazaiji dadi ba nadai bude dayar ledar sai naga kankana ce aciki da abarba sai robar yugourt dan jarkar nan guda biyu da sanyin sa

Na kara dauko flet na juye kankanar dan ayanke suke na cire yugourt din aledar

Na ce bismillah muka zauna lomar farko a wainar danayi nakasa hadiye wa wani irin mugun tsamine yafara min sallama sai uban attaruhu da aka cika a miyar ga ta salam sai warin dan yen kayan miya da karnin naman alamar ba a silalashiba akayi miyar dashi

Nadai daure na hadiye ta farkon ganin zan cutar da kaina yasa na tsame hannuna nace bari nasha kankanar da abarbar bazan iya cin wainar ba

Yace nima fa ba iyacin wainar nan zanba gaskiya bansan haka take ba tunda nake bantaba siya ba sai yau janyo mana flet din musha frunt din da yugourt din

Na kalleshi nace yaya za ai da wainar ?

yace ki rufeta da safe azubar dan bazai yiwu akaiwa a wakin hajjoba kinsan da zan shigoma Shu aibune naba ledar nace ya mikomin ta bayan katangar can na shigo kuma saida na fara zuwa gurin hajjo tukun danma karta ce nayi wata siyayyar shiyasa ban biyo ta gurinta ba

Nace to shikenan amma inba dole ba babu kyau wulakanta abinci

Bayan mun kammala na tattara wajen na dawo na zauna
Muna cikin magana sai ga yan Nepa sun kawo wuta na tashi na jona chargen waya ta da tashi na kashe fitilar nasa charge na zuba ruwa a heater na jona ruwan zafi

Ruwan nayin zafi na juye na jona wani naje nayi wanka ina ina fitowa na juye mai nashi na kai

Fitar shi kenan sai ga Shamsu yazo yayi sallama

nasa hijabina na leka na kalle shi da kaset a hannun sa na zaci yayan shi yake nema nace yana wanka

Yace ba wani abu zai bani ba dama kallo nazo nasamo sabon film ne na kalle shi yaro kamar shamsu dan shekara kusan goma sha takwas shine zai shigomin daki a lokaci irin wannan da kowanne mai rai ke neman hutu bayan haka ma kamar shamsu inhar za abi addinin mu na musulunci bai kamata ace harda shi a masu zuwa kallo dakina ba tunda bawani daki ne dani ba bare ince na bar musu intafi wancan

Muna nan tsaye saiga yayan shi yace a a shamsu ya akai yace yaya ahmad film dinnan nazo kallo shine tace bakanan

Ahmad yace eh wanka nashiga ina ji tana ce ma ina wanka amma yanzu barci muke ji kabari da safe in ankawo wuta sai kazo ka kalla ya kare fadar cikin son gamsar da,yaron ya juya yana magana allah yasan mai yake cewa

Nayi saurin janyo hannun ahmad nace baka tunanin abin da zaije ya fadawa hajjo kaga fa karta zo tana ma fada kota ce nina hana

Kinga bari na rufe kofar wallahi babu yaron da zaizo ya samu gaba ya hanamu sakewa da darennan yanzu fa,karfe 9.30pm ya ya za akunna mana kallo kallonma shamsu ni koda rana da suke janyo abokansu da sunan kallo ba ason raina bane

Ya karasa rufe kofar ya dawo mukai shirin barci muka kwanta

*************************
Chapter 4 · 0% Book details