← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 78

Sashe 20

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
09/11/2022, 2:16 pm - Maman Dan Albarka Ce: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EucvvhNS397F3LJeJGZuUS

*09131164861 Royal jelly yana ciko da mace tayi dumdum breast naki ya ciko hip's dinki yaciko da wanda tayi bleaching fatarta ya yamutse*

*Ko kinsan female care na taimaka ma wanda niimar jikinsu ta tsane*

*Fat bunner ina macen da kitse ya mata yawa ajiki tayi kiba sosai tafiya da kyar tashi da kyar to ki gar zoyo ki mallaki fat bunner*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

*_😍MAMAN DAN ALBARKA CE😍_*

_*FREE PAGE SUN KUSA KAREWA MAZA KIYI KOKARI KI MALLAKI NAKI YAR UWA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI RAHUSA 300 KACAL NORMAL GRP POSTING SAU BIYAR ASATI VIP 400 POSTING KULLUM MASU SO TA PRIVATE 1000 SAU BIYU KOWACCE RANA INKUMA DUKA LITTAFIN BIYU KIKESO FANSAH DAKUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI BIYA 500 NORMAO GROUP VIP 800 KARKI BARI ABAKI LABARI YAR UWA YANZU WASAN YA FARA 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻MAZA KI TURO KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK SAINA JIKU😍*_

*_Littafin tushen mu daya labarine daya danganci Wata zuria wadda babu abin daya yiwa zuriar nan lullubi face Cin amana zalunci rashin tausayi rashin tsoron allah sannan ga sassanyar soyayya labarin Aminatu da surukarta labarine da zaka zubda mata hawaye sannan ga kannen miji suma sun sako ta gaba shin dama haka yakamata surukai su zauna da matan ya,yansu? Duk sai kun tsunduma cikin wannan labari mai suna TUSHEN MU DAYA_*

*Masu son a tallata musu hajarsu ko kuma link din group dinsu zasuyi magana ta wannan Number 09138320449*

```Bismillahirrahamanirrahim```

*Free page 13*

Baba Musa ne da baba abdullahi da Babanmu zaune a gidanmu inda malam musane ya bukaci da suzo gidan namu tunda babu kowa zasu tattauna wata magana kafin yabar kano

Dukansu sun bada hankalinsu kan son jin maganar da zaiyi

Malam musa ya kalli su mahaifina yace Ku kannena na amma kuma zumuncinmu ya koma sai a hankali sanadiyyar nesa da mukai da juna da kuma rashin ziyartar juna da bamu maida hankali iyalanmu mata munkoya musu ba

Inda duk cikinmu inba dan ladi dana zo dashiba yaranmu basu san junansu ba wanda bakaramin abin kunya bane tunda zama su iya haduwa awani wajen batare da sun san cewa sudin yan uwa bane

Abinnan ya dade yana cimin tuwo a kwarya nakanso koda nidinne indauko yaran inkawo su susan yan uwa amma duk lokacin danayi yunkurin hakan sai hajjo ta kawomin uzurin makarantar yara da sauransu to amatsayinku na yan uwana dole tasa nake fada muku komai sannan saida taimakonku ne zumuncinmu zai dore

Nayi wani tunani wanda nake da tabbacin inhar muka bi hanyar insha allah yaranmu zasu san juna sannan zumuncinmu zai cigaba da gudana zamuna samun ziyartar juna koda tsakanin yaranne

Baba abdullahi yace ta yaya ,haka zata kasance?

Yace Bawani abubane sonake Salisu ya bawa Ahmad dina auren aminatu dan ina ganin inhar aminatu na can tabbas zumuncinmu zai kara karfi sannan inason in za ai auren a hadamin da ilham saboda ta dunga ganin yar uwarta a gefe kafin tasaba da can

Babanmu da yaji maganar wani banbarakwai bawai bazai iya bawa dan yayanshi auren yarsa bane sam in akwai wanda ya cancanci hakan bai wuce shiba amma abin dubawar aminatu yarinyace bazai iya bada aurenta yanzu ba koda kwa a garin kanone bare har can uwa duniya Niger state sannan shi yasan yanayin da yayan shi ke ciki yana tsoron a cutar mai da yarinya dan yasan halayen hajjo tsaf kuma bazai wuce ace gida daya zasu zauna ba sannan aminatu ko makaranta bata kammala ba yanzu ma suka shiga aji na uku a secondary taya ya zai aurar da ita yanzu

Abdullahi ne yace tabbas tunaninka yayi yaya amma aminatu tayi kankanta me zai hana in auren ne ga hajara tunda ita ta isa auren amma aka aurar da aminatu yanzu ai yaya ba amata adalciba ga kuruciya sannan ga makarantarta

Baba musa yace nima ba irin auren nan nakeson ayi ba ko daya shi kanshi ahmad din ba auren zaiyi yanzu ba sai ya samu aikin sa sannan bawai nufina irin auren nan ba na hadi akan dole ko daya bazan shiga hakkin kowa ba

Dole ahmad yazo yaga aminatu tukun inta masa ita ta ganshi inya mata sannan saimu basu lokaci yaci gaba da ziyartar kano har su dai dai ta daga baya sai ayi maganar auren

Na dai nemi in fada muku ne saboda burina kenan bawai ayi auren yanzu ba

Kai kuma abdullahi banki ta takaba amma hajara na tabbata bazata rasa masu sonta anan ba bazai yihu azo mata da zancen nan ba bayan haka ahmad din kanshi fa bawai ya shirya auren bane sai nan da wasu yan shekaru kafinnan itama aminatun ta kammala makarantar ta

Babanmu da baice komai ba tunda suka fara magana sai da yaji ance saina gama makaranta sai lokacin yasa baki

Yace hakane yaya maganar ka muma zamuso ace zumuncinmu yaci gaba ta hanyar ya,yanmu susan junansu inda koda bayan ranmu zamuncin zai cigaba

Aminatu diyarka ce kukuke da alhakin bada auren ta insha allah inhar ta kammala karatunta na mika wuka da nama gareku duk yadda kukai da ita dai dai ne

Masha Allah allah ya tabbatar mana da alkhairinsa shine abin da baba abdullahi yace

Sai kuma maganar ilham inbadamuwa kabani ita intafi da ita hajjo ta riketa

Babanmu ya dago yayi murmushi yace kayi hakuri yaya bawai bazan iya baka ilham bane a a kawai dai banason nesa da yarana kaga kuma ilham yanzu take da shekara biyu da yan watanni zan dai bada auren aminatu amma maganar raba yarana yaya bani da burin hakan nafison su taso agabana ina ganinsu kusa dani ya kare fadar cikin damuwa

Baba abdullahi da yafi kowa sanin mahaifina akan son yaranshi dan ko lokacin da mahaifiyarsu na raye baya kaunar ace yaranshi sun kwana wani guri ko da gidan shi ne saboda makon ya,yanshi yayi mamaki daya ji bai musa bada auren aminatuba daya ji yayi shiru shine dalilin da yasa yace ya bada hajara saboda bayason damuwar kanin nashi karyace kuma bazai bayar ba yaya musan bazai ji dadi ba

Amma bisa ga mamakinsa sai yaji ya amince ya dago ya kalli yayan nasu yace yaya batun tafiya da ilham ka aje shi tukun tunda kaga suna wajen kakarsu karsuga ko anga sun gazane abarta
Inyaso in auren yazo sai abawa aminatun

Baba musa yace to shikenan allah ya shige mana gaba

Inda bayan gama tattaunawarsu sukawa baba musa rakiya yaje gidan abdullahi suka dauki dan ladi suka rakasu har tasha

************************

Bayan tafiyarsune su abdullahi suka cigaba da tattauna zancen inda babanmu ya fito yafadawa dan uwanshi tsoronshi akan hadin inda abdullahi ya kwantarmai da hankali insha allah babu abin da zai faru sai alkhairi

Babanmu yace allah ya tabbatar mana da alkhairin suka amsa gaba daya da amen

************************
Su hajjo sun dawo inda kwana daya ta kara a kano ta koma niger state

Kamar yadda boka yace wa zainabu hakance ta kasance tana fara aiki da magungunan sai ga baba abdullahi yazo yanemi daya maidata inda babu wani ja ta amince iyayanta da ya,yanta sunyi matukar farin ciki
Inda aka kara daura auren ta tare dakinta

Mu muna gidan kakanmu har lokacin

*************************

*BAYAN SHEKARA DAYA*

Zuwa lokacin burin su hajjo ya cika na rusa tsakanin mahaifina da baba abdullahi inda zainabu tasamu tayi duk abin da boka yace mahaifina yasha ziyartar dan uwansa amma indai zasu hadu abdullahi sai ya rufeshi da fadan babu gaira babu dalili yana muzantashi koda acikin mutanene acewarsa yadauki ya,yanshi ya dankawa dangin matarsa ya hana yan uwansa ciki daya sannan yaki yin aure da dai maganganu marasa ma ana

Tun babanmu na kokarin yimai bayanin da zai fahimta ta hanyar nuna mai halaccin da su baba malam suka mai a rayuwa da irin hidimar da suka mai har yazama mutum suka bashi yarsu amma baba abdullahi baya saurarar sa shi burinsa ya amso yaran kawai yayi aure ya rikesu shi kwa yace bai shiryawa aure ba yanzu

Inda baba abdullahi ya tabbatarmai muddin bai amso muba yayi aure ya rikemu to fa babu shi babu shi kowa yayi harkarshi babu yadda mahaifina baiyi da baba abdullahiba don yaganar dashi dan yasan dan uwansa mai sanyin haline duk wannan maganar bata kai ace anyi haka ba amma haka baba abdullah ya fututtukemai yaki saurararshi

Inda babanmu ya kai maganar ga kakanmu amma bai fada masa cewa akan amso mu bane dan karyaji ba dadi yadai fadamai abdullahi yace sai yayi aurene inda shikuma yace bai shiryawa hakanba inda yanemi kakanmu yakira shi yabashi hakuri dan allah bayason suna fada

Haka kwa akayi kakanmu yane mi baba abdullahi da kyar yazo cikin jin haushin tsohon dan zainabu na fada mishi kullum tsohonnan shikecin amfanin kaninshi dan ya dauke ya,yansa yana cin ribane kawai

Inda baba malam yashiga yiwa abdullahi nasiha akan zumunci da dai sauransu yace yabari lokacin da shi baban namu ya shirya yin auren zaiyi in lokacin hakan yayi

Inda baba abdullahi yashiga aibata mahaifina da maganganu marasa dadi ya gaggayawa kakanmu magana ya kade rigarshi yayi gaba

Kakanmu yayi matukar mamaki inda baisan abdullahi da wadannan halayen ba amma sai yayi tunanin dan adam kan canza a kowanne lokaci

Yakira mahaifina yabashi hakuri yace karya biye masa yadinga zumunci dashi inshi bai nemeshiba kuma karya hanamu zuwa gareshi zai sakko

Haka kwa akayi babanmu na zuwa amma wataran ko arzikin fitowar baba abdullahi baya samu

Abin mamaki kuma mu inmunje gidan sai baba abdullahi yayi ta nan nan damu sai in mun zauna yayi ta fadamana laifin babanmu wai mahaifinmu yaki jin maganarshi da sauransu

Nakance yayi hakuri
Chapter 20 · 0% Book details