Sashe 27
Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari ina kammala duk wani abu danasan zanyi a wajen hajjo misalin karfe biyu da rabi na rana na koma bangarena na binciko kayan da gwagwgo binta ta hadamin dama tacemin inhar na kwana biyu shine zanfara aiki dasu nan na fita na nemi yaro cikin gidan na aika ya siyomin madarar gari wadanda tace insha da madara na harhada nasha sannan na bubbude sauran su zuma da tsumi duk na sha
Na dauki garin lalle da tabani da ganyen magarya dan lokacin akwai wutar nepa na jona heater bayan ya tafasa na debi ganyen magaryar na zuba a dan kwanon silba na zuba tafashshen ruwan akai tafasawa yakamata inyi amma dan bana girkin kaina shiyasa bakuma zai yihu inkai wajen hajjjo ba
Bayan na zuba wa ganyen magaryar ruwan zafin saina dauko turaren wuta na na itace na bude kwalbar na dibi madaidaici na zuba akan ganyen magaryar sannan na dauki alimun dan karami na jefa na barsu suka dan yi mintuna zuwa lokacin ganyen ya jiku a cikin ruwan dashi da turaren saina sa rariya na tace ganyen
Saina juye iya ruwan na dauko tsamiyata itama na zuba mata ruwan zafi tafashashshe kamar yadda nayiwa ganyen data jiku na murjeta na tace ruwanta akan ruwan ganyen magaryar na dauko madarar turarena kala uku wadanda dama gwagwgo binta tabani sune dan hadinnan na tsiyaya su suma na dauko garin lallen nasa cokali ina dan zubawa ina juyawa bayan ya yi kauri sai kamshin turarukan dana zuba ke tashi saina tsiyaya ruwan zafin kadan na dauko lemon tsamina guda wanda dama tun jiya na ba yara suka siyomin shikadaine bani dashi
Na matseshi a dan kwano na tace kwallayen na zuba ruwan lemon tsamin akan hadin na kara juyashi da kyau tukun nasa murfi na rufe
Zuwa lokacin ankira la,asar na tashi nayi alwala nayi sallah bayan nayi sallah
Nasawa net din sakata dan bansan wanda zai shigoba
na debi hadinnan na daura zani wanda nasan dashi zan cigaba da aiki
Na murje jikina da hadin inda hannuna baikaiba kuma na barshi sainaje wanka bayan na murje jikina na zauna har tsawon mintuna 15 tukun na juye ruwan wankana tunda nasan babu kowa a lungun saini na tafi bandaki da sabuluna na na hadi da shima acikin kayan yake
Bayan nashiga na karasa shafe duk inda bai samuba tukun na tsaya tsawon mintuna 5 sannan na fara murje jikina da hannuna duk saida n murje garin lallen tukun duk da inajin zafi a fatata tukun na sa ruwa na wanke jikina na fara wanka
Bayan nafito nikaina nasan na murzu har wata iskace ta musamman ke shigata inda nabi jikina da lafiyayyan man shafawata na shafe nan danan fatata ta dau kamshi na musamman
Bayan nagama shiryawa
Can saiga salaha wai hajjo na kirana
Nace taje tace ina zuwa
Na tashi na dau hijabina na rufe kofa na kama hanyar dakinta
Da isata sai na tarda ta zaune ita da bakuwa
Na gaida bakuwar ta amsa tana mai karemin kallo
Hajjo tace kishirya za a gidan suna anjima nan bayan layi ni bazan samu zuwa ba kibi mutanen gida ku tafi
Na kalleta nace ai bantambayeshi ba hajjo
Ta hayyayyakomin meye wani baki tambayeshiba kijimin wani sabon sanabe huwaila to koshi ahmad din dan ubanshi bai isa insaki abuba ya hana ninace kishirya ku wuce
Azuciyata nace to meyayi zafi har haka daga bantambayeshiba sai zagi ina laifina anan antaba fita,dama bada izinin mijiba ko kuwa dai tsarinsu kenan ina aka taba cewa uwar miji ke yarjewa matar danta zuwa unguwa duk da kwa uwarshi ce nidai nasan nayi karatu gwargwado dole saida izinin miji zaki fita haka dai na yanke shawarar kiran ahmad a waya na fadamai tunda ai basai nace na fadamai ba
Na juya zantafi ko fita bangamayi a dakin ba naji bakuwar nacewa wannan itace amarya taku?
Bansan me hajjo tace mata ba nidai na kama hanyar dakina wallahi bazani ba taya zanmata biyayyah insabawa mijina haka kawai bayan nasan hukuncin hakan
Nan na bude daki na sa sakatar net na kira number ahmad bata shiga na yi nayi bata shiga ba nayi kwanciyata azuciyata nakudiri kome zatayi wallahi bazaniba inda ma na tambayeshi da sauki
Ko minti goma banyi da kwanciya ba naji muryar maman Aisha da hajara
Maman aisha kecewa amarya kifito mun shirya
Na tashi na leko na ce bansamu number shiba ki wuce allah ya raya
Maman aisha ta kalleni toh nan da gidan sunan da zamuje sai kin wani tambayi miji cab sannunki
Hajara ta kalleta kinsan hausawa akwai iyayin tsiya su ai haka suke duk inda zaki saikin tambaya
Tace cab aikwa akwai aiki agabanki indai saikin jira namiji tukun kije inda zaki
Nidai na shige daki abina na barsu suna surutunsu
Can kamar mintuna biyu saina jiyo hayaniyar hajjo tana nufo dakina kafn ma in tashi ta bugo kofar tashigo ta sameni a kwance
A a a lallai ishashshiya wato dai nidin ban isa ince ayi ba ayi ince kibisu ki aiko minsu cewa ka bazakijeba a zo afadamin saboda nidin sa ar ubankice ko?
Naji zafin zagin datamin nidai na sunkuyar da kaina ina,mamakin su maman aisha yaushe nace bazaniba abin danace daban wanda sukace daban
Dataji nayi shiru nan ta hau sirfamin masifa tana zagina ta gama banko dago kai na kalleta ba dataga haka ta fita tana kara aibatani shegiya matsiyaciya kawai tana hadamin da gorin kayan dakin data saba
Bayan fitarta na fashe da kuka wannan wace irin masiface fisabilillah meye abin zagin mahaifina sannan kayan dakin data ke magana ai susuka cuceni ina kayan suke datakemin gori koda take zakalgalewa baba dai koban auri ahmad ba zai iyamin kayan daki a matsayinsa na yayan mahaifina amma kullum maganar hajjo banzo da kaya ba tana zagina a cikin mutane ba komai watarana sai labari
***********************
Yau na tashi cikin tsananin farin ciki dan yau ahmad ke sanar dani gobe da asuba zasu taho dan haka allah allah nake na kammala ayyukana inzo in karasa gyaran jikina nariga danayi tsifa amma har tunanin bawa maman aisha kaina nake dan tun da tamin karya wajen hajjo nakejin haushinta nida ita yanzu sai gaisuwa dan bana bata fuska sam na tsani munafurci
Bayan nagama komai kawai saina yanke shawarar tunda ina da dan sauran kudi a hannuna intambayi ahmad kawai inje shagon salon dake kofar gidanmu a wanke min kan bakina alekum tunda dama shima yafison hakan
Bayan nakira na tambayeshi yace saina dawo na shirya na nufi wajen hajjo nace hajjo zanje wajen iya fati zata dan wankemin kai
Ta kalleni ikon allah kanne sai kinje anwanke miki ke bazaki iya wankewa ba saboda bannar kudi?
Nidai bance mata kala ba nace saina dawo
Naje aka wankemin kaina na dwo baki alekum
Da dare ina zaune na kunna kallo a wayata kasancewar yanzu na kashe ayimin kallon dare kwata kwata hakan yasa banama kunna wa saidai na kunna na wayata jinai an bankomin kofa
Na dago kai na saida gabana ya fadi nayi saurin rarumo hijabina na saka ina kallonshi ina kokarin boye tsoron dake idona
Ba wani bane dan ladine inban mantaba rabona da nasashi a idona tun ranar da sukaje asibiti da hajjo aka mai dinki
Nayi dubarar dauko wayata na kunna recording na aje ina jiran naji da wacce yazo
Ya kalleni a wulakance da wata fuskarshi da har yanzu bata saceba da uban dinki ni sai yayi min wani mugun muni idanun nashi duk sun shige ciki
Keee yace cikin daga murya na dago kaina na kara kallonshi
Yacigaba da magana nasan kinsan komai yanzu kinsan nine nashigo miki daki kuma har kika min lahanin da bazan taba mantawa ba a rayuwata amma wallahi tallahi inma kina tunanin cewa kin yanki banza ne ki sauya tunani dan saina cika burina saina wulakanta ki
Maganar tonon asiri kuma wallahi ki ka sake naji maganar nan a bakin wani wallahi saina lahantaki kamar yadda kika lahantani ke kima ce zaki tona min asiri kinsanni bana gudun abin kunya danma kinsamu zandan rage miki zafi tunda wancan sakaran da baisan abin daya ajeba ya tafi yaki dawowa ashe kallon danake miki ba haka bane na zaci kin waye
Ashe dai kan atoshe yake to wallahi saina cika kudirina ko kina so koba kyaso muddin muna gida daya ya karashe maganar yana mai buga kujerar danake kai da kafarshi ya juya zai tafi
Anan nayi saurin sa hannu na seved din recording din danayi naga inna barshi ya tafi da tunanin tsoron shi ya hanani magana tabbas yaci banza kuma zai cigaba da mini barazana da hakan
Na kalleshi nace da ikon allah ta allah bataka ba tunda naga alamar bakasan mutumci ba bakuma ka dashi bare ayi maganar kunya abin kunya matar yayanka kake nema bayan nagane ka asirinka ya tono madadin da bantonama asiriba ka fita hanyata amma shine harda karfin halin shigomin daki yanzu innaso zan iya yi maka ihu intara ma mutane kuma wallahi kasan ranane tsaf zasu taro kuma duk abin danace ta zauna amma bazan tonama asiriba yanzu nayi maka alkawari da ikon allah sai asirinka ya tono cikin sauki kowa sai yasan hakan da nayi niyar ba maiji amma yanzu tunda harka tako kuma ka kara ikirarin dawowa da son cika burinka to mu zuba shege ka fasa na karashe cikin hargagi kwallah na fitomin a ido wacce irin masifa kenan
Duk abin danake cewa karfin hali kawai nake ina tsoron yayi yunkurin cutar dani tunda ko ihun zanyi kafin wani yazo ma akwai tazara tsakanina dasu
Ke dan abu kaza ta ubanki nikike fadawa magana ya yo kaina da sauri na matsa
Ya kalleni zamu gauraya ya fice tare da bankomin kofar
Nace ta allah bataka ba dan iska
Yana karasa fita na zauna na fashe da kuka nikam nashiga ukuna allah ka kawomin dauki abun infada hajjo tace karya nake bansan abin da fadar zai haifar ba amma zan ajiye record din danayi saboda watarana dan wallahi indai ya kara yunkurin cutar dani saina masa abin dayafi na da dan inna fadawa ahmad bansan dawane ido zai kalleniba bayan haka bansan mai fadar zata haifarba tunda ba wanda ya ganshi allah ne shaidata kawai
*************************