← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 78

Sashe 40

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga aminatu shegiyar yarinya data gagareta duk irin kudin datake kashewa a kan cikin ya zube shiru kake ji har ture aljanu ta sa ammata su cire abin dake cikin su ajiye mata wata dabbar amma insuka zo ko rabar inda take basa iyawa saboda karfin addu arta ina

Dan tabbas tabari aka cigaba da tafiya haka har malam musa yaci gaba da maganganunsa to tabbas wataran zai iya furtawa ba ita ce ta haifi ahmad ba wanda hakan dai dai yake da kasheta dan bata cika burinta ba kenan zata tashi duk tsahon shekarunnan a banza tayi su ina bazai yiyu ba walllahi ta furta da karfi

Ya zama dole wannan takardar filin ta zama mallakin ya,yana kota halin kaka inbanyi arziki da ubansu ba ainayi da wannan dan iskan

Haka tayi ta sambatunta ita kadai sai shawarar data yankewa zuciyar ta ta karshe wadda tana ganin itace me billewa tunda yanzu zainabu bawani saurararta take ba karta biye mata gwara ta nemawa kanta mafita cikin sauki

*************************
_*KANO*_

Baban hajara ban fadamaka maganar nan ba dan katashi hankalin ka ba na fadama makane dan asan yadda za ayi tun wuri a kwatowa yarinyar nan hakkinta inta haihu abawa uban cikin

Ya dago idanunsa sunyi jawur aysha wanne yanci kike maganar a amsowa salima itafa ta kai kanta wacce irin tarbiyace banbawa yarannan ba amma wai yau an wayi gari cikin shege a gidana yar cikina

Innanillahi wa inna ilaihirraji,un allahumma ajirni fi musibati wa aklif li khairan minha

Allah kagani ni ba mazinaci bane bantaba kama hannun diyar wani ba da sunan batanci ya allah ka jarabceni da yara marasa jin magana bansaniba ko kuskurena ne danayi tun farko ke bibiyata na rashin zabar mace tagari ya allah ka yafemin tabbas manzon allah salallahu alaihi wasalam ya horemu da munemi mace tagari amma nasan zainabu itace kaddara ta allah ka yafemin badan halinaba ya kare cikin zubar hawaye

Mama aysha da tsananin tausayin mijinta ya kamata ta dafa shi kayi hakuri baban hajara hakane kowanne bawa da kaddararsa tabbas ka yarda da kaddara ubangiji kan jarabtar bayinsa ta inda yaso dan haka kayi kokari ka cinye jarabawarka insha allah zakaji dadi zuwa gaba

Sannan dan allah wai menene dalilinka na fada da gaba da dan uwanka salisu baka da wani dan uwa fa kaf garinnan da ya kaishi amma abin mamaki shine makiyinka ka sassautawa dan uwanka ka kyautata zumunci sai allah ya dube ka ya rangwanta maka ko ya,yanka fa basu da wani waliyyi sai salisu tunda yaya musa baza asashi a lissafiba banan yake ba dan allah kadaina abin da kake

Ya dago ya kalleta cikin zubda hawaye abin na masa kuna a ranshi aysha nima bansan dalilin dayasa nakewa salisu haka ba wallahi jina nake kamar ana tunzurani inna gama nikaina ina nadama ki tayani da addu a dan allah harta kudin auren yarinyar nan aminatu wallahi suna wajena bansan meyakaini ga rikesu ba kuma suna nan harda wadanda akace inmunje insai mata kayan daki wallahi banci ba kuma bansiyaba suna nan a account dina kuma har yau salisu baitaba tadamin maganar ba saboda biyayyarshi gareni tunda na nuna mishi bacin raina har yau bai kara maganar ba

Subhanalla kana nufin kaci kudin marainiyar allah baban hajara to inhar kudin suna,nan ka tabbatar ka maishe su inda ya dace kabata hakkinta a matsayinta na diya haba baban hajara bansan ka da halayen nan ba fa

Zan maida aysha kuma zan gyara tsakanina da dan uwana insha allah da kaina zanje harcan garin in aiwatar da abin da ada yakamata nayi tun farko tabbas ke din macace ta gari sainaji dama ke na fara aure ayshatu nasan da bazan koyi sha awar auren zainabu ba

Da sauri ta rufe masa baki karka ce haka inka ce haka ina za akakai rabon haihuwar su nafee da allah ya kaddara daga tsatsonta zasu fito

Astagfurullah allah na tuba ka yafemin kura kuraina

Yanzu ina ita salimar?

Tana dakina

Kira min ita

To

Nan mama aysha ta tarda salima dake dakinta ta baje tana kwance hankalinta kwance kamar ba ita bace ta rusa farin cikin gidan

Babanku nason ganinki

Jitai gabanta ya yanke ya fadi duk iskancinta tana tsananin tsoron baban nata saboda tasan halinshi da zafi baya daukar wargi ko suma abin da suke samun daurin gindin mahaifiyarsu shine kan gaba wajen lalacewarsu inda tarbiyar mahaifinsu zasu bi tabbas bazasu jawo abin magana ba amma ai duk kudin da suke samowa mama zainabun ke amshewa batare da bin ba asin hanyar da aka samo suba

Nan ta tashi cikin sanyi jiki dan mama aysha na fada mata sakon tayi gaba haka ta tashi sukuku tayi hanyar dakin mahaifin nasu inda ta kai kallonta ga dakin mahaifiyar ta alamar dai tana ciki dan ga takalman ta nan amma bazaka taba cewa tanama gidan ba tun jiya da abin ya faru tayi mugun sanyi

Da sallama ta shiga tana rabe rabe

Ya dago ya kai kallonshi gareta cikn kunar zuciya ya nuna mata waje kusa da kujerar bakin kofa yace zauna

Ta zauna tana ra'be ra'be

Ina,mamanku?

Tana daki

Kije kikaramin ita tukun na

Jin abin dayace yasa mama aysha mikewa dan tabasu waje ina zakije kekuma

Inason zuwa nadan karasa ayyukan da suka ragemin ne

Shi yasan babu wasu ayyuka da zata karasa tunda bawasu yara kanana take dasu ba tundaga kan haihuwar Muhammad da salim allah baikara bata haihuwa ba yasan tana gudun rigimar zainabune karta zo wani abu ya faru

Koma ki zauna ayi komai a gabanki haka ta koma ta zauna ba dan ranta ya soba

Can saiga mama zainabu da salima a gaba

Mama zainabu ta wuce ta samu kujerar dake kusa da ta shi ta zauna ya zamana sun sashi a tsakiya mama aysha na gefe

Salima data samu gefen kujera ta rakabe sai raba ido take yana shege a rabon gado

Ya dago ya kalli zainabu kana yakai kallonsa ga salima shin maganar dana ji gaskiyace?

Zainabu ta kalleshi duk da tasan cewa ta tsuniyar gizo bata wuce koki tace wacce magana kenan baban hajara?

Ya kalleta cikin takaici ganin tana ma kokarin raina masa hankali

Ya ina tambayarki kina dawo min da taki tambayar ?

Maganar dana ji akan cikin da salima tayi har ke dakike mahaifiyarta saboda kedin uwar banza ce kike kokarin tilasta ta a zubar da cikin shin gaskiya ne wannan mummunan aikin ne yake faruwa agida na agida ni abdullahi yarinyar dana haifa ta cikina tayi ciki ba aure harke mahaifiyar ta kike kokarin zubar wa dan rashin tsoron allah

Ba kiduba iri tarin zunubin dake cikin zinar ita kanta da yarinyar ta aikata ba sai kokarin kara aikata wani laifin ta hanyar zubar war wanda duk bawani ya jawo lalacewar tata ba saike zainabu ya nunata da hannu cikin kunar rai yaciga da magana

Cuta dai kun riga da kun cuceni zainabu kun rusamin tsarina da komai zainabu bazan ce miki komai ba zainabu allah ya gani ina kokari kan tarbiyar ya,yana dai dai gwargwado amma bani da dabara akan kaddarar da allah ya aikomin allah ya bani ikon jurewa amma kisani salima zata raini cikin jikinta zata haifeshi a gidannan babu inda zata je sannan ta fadi uban dan ko yar abasa abinsa inya kai lokacin yaye inyaso inta gyara rayuwarta ta nutsu tayi aure inbata nutsuba wallahi zanbada aurenta ga duk wanda naga dama sauran hajara itama kitabbatar inta dawo wallahi wallahi nabata nan da wata biyu ta fidda mijin aure ko itama na hadata da duk wanda nasamu bazaku maida ni mutumin banza ba kuma salima a dakinki zata zauna ba dakin aysha ba kokina so ko bakya so muddin wani abu kuma yasamu cikin jikinta abakin aurenki dan nasan halinki da kafiya
Ya karasa cikin bacin rai

Tashin hankali akace wanda ba asa masa rana mama zainabu bata taba tunanin maganar zata kai wajen baban su hajara ba koma takai batayi tunanin zai dauke ta da tsauri hakaba taya zaice shima salima saita haife abin daya ke cikinta mekenan ? Shi baya gudun abin kunya ne kokuwa kuma a dakinta zata zauna ita kam ta kade har ganyenta ta shiga ukunta

Tana cikin tunanin ta jiyo muryarshi

Kekuma na dawo da kanki kin kyautawa kanki kenan salima kin kyautawa tarbiyar da na baki irin sakayyar da kika min kenan a matsayina na mahaifinki ya fada muryarshi na dada cunkushewa cikin takaicinta
Tunda haka kuka zaba keda mahaifiyarki saiki fadamin uban cikin dake jikinki dan asanshi a nemeshi yasan da zaman sa ya kare yana mai dauke kwallar data taho masa

Salima da tunda abun ya faru sai yanzu taji wata irin kunya tare da tarin nadamar abin data aikata sun mata rubdugu jitake inama kasa ta zage ta shige musamman data ga mahaifinta na share hawaye yau ita baba ke zubdawa hawaye
Tayi nadama babu adadi tasani yayi kokari a rayuwarsu iya iyawarshi yabasu ilimi ya basu tarbiya ya kyautata musu mama aysha ma data rikesu kafin dawowar mahaifiyarsu itama tayi kokari akan tarbiyarsu amma dawowar mamansu gidan ita ta rusa komai batason gaskiya tana kallo suke abun da suka ga dama bata kwabarsu in mama aysha zata yi magna takance mata ba ,ya,yanta bane ta bar mata ya,ya su wala haka zasu fita babu kwaba lokacin da suka so suke dawowa babu ruwanta ita burinta su shigo da dan abun lasawa ko kudi ta sa hannu ta amshe babu bin ba asi wanda wannan halinne nata yasa suma suka bada himma wajen ganin sun kyautata mata sun sata farin ciki inda a irin hakane saurayinta faisal ya yaudareta da sunan ta rakashi gida ya dauko wani sako daga nan saiya sauketa gida lokacin sun dawo daga yawonsu inda yayo mata siyayyar kayn kwalam da makulashe ta bishi tasan dai data dan zauna ya miko mata lemo a kofi yace bari yaje yadan leka su hajiya mahaifanshi ya barta a dakinshi dayake part dinshi daban daga nan bata kara sanin kanta ba saida ya kawar mata da mutumcinta inda bayan ta bude idonta ta ganshi gefenta yana narkar barcinsa hankalinshi kwance
Chapter 40 · 0% Book details