← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 78

Sashe 77

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai farka ba sai can yamma ikon allah wannan farkawar tashi sai ya farka cikin hayyacinsa amma babu sunan wadda yake kira sai sunan aminatu a kira mai ita ya nemi gafararta shi ya san ya 'bata mata babu wanda bai bawa tausayi ba a wajen ganin yak'i shiru likitocin suka bada shawarar aje a d'auko wadda yake kiran sunan nata tazo

Dole tasa ina gida aka zo aka d'aukeni allah sarki nikaina yanzu na daina jin haushin sa jin ashe duk abinda yake bayin kansa bane duk cikin irin cutarwar da mahaifiyar sa ta masa ne

Koda naje naganshi kam kuka na fara da k'yar na iya k'arasawa kusa dashi

Yana ganina ya shiga yunk'urin tashi amma ya kasa ganin yadda yake wahala yasani k'arasawa jikin gadon ganin haka yasa ya bud'e baki da k'yar cikin zafin ciwo ya shiga neman yafiyata akan irin abubuwan da ya min tausayinsa ne ya tsirgamin da kuma soyayyar tsakanin yan,uwanta ka na yafe maka kayi shiru shine kawai nake cewa nima ina kukan

Ganin jikinsa na shirin rikicewa likitan da ya rakoni d'akin yace in fita haka

Cikin kuka na fita ahmad da shima zuwa lokacin duk jikinshi ya yi sanyi ga kuma tausayin d'an uwanshi shi ya maidani gida

Komawata gida da awa guda muka ji jiniyar motar asibiti mazan suka fara shigowa kowannen su ka gani fuskarsa tayi jajir nan suka fad'a mana allah yawa d'an,ladi rasuwa

Ba k'aramin girgiza mutane mutuwar tayi ba allah sarki rai bak'on duniya duk wannan rikicin da mukai kamar ba ayiba yama bar duniyar lokacin da baiyi zato ko tsammani ba munsha kukan rashin sa ya tafi ya barmu adai dai lokacin da kowannen mu ya kamu da son kasancewa dashi
Mutuwa kenan

Bayan kaishi nan su baba suka cigaba da kar'bar gaisuwa dole tasa suka fasa tafiyar

Duk wannan abun da ake hajjo ma batasan wainar da ake toyawa ba dan ankulleta a can uwar d'akinta iya kaci a mik'a mata abinci shima baba musa da k'yar ya yarda ta zauna dan yace dole ta bar masa gida

Har tsahon kwana biyu da rasuwar babu wani daya zo daga 'bangaren aisha matar d'an,asaben hakan yasa su baba suka aika a fad'awa iyayanta dan su san ya rasu ta fara takaba sai dai koda aka je gidan nasu sunce bata zoba bama susan bata gidan ba

Sun zo gaisuwa sannan suka k'ara da ban hakuri dan jin irin abinda ta aikata wa yaronsu saboda son zuciyar su sai suka ce ko aljanun tane suka sata aikata hakan kuma suka d'auketa nan aka tabbatar tana cikin hankalinta tayi sannan bashir yace yaga fitarta k'alau ta fita

Fututtukewa iyayan nata sukai akan basu yarda ba sharri ake sonyiwa yarinyar su ai shima mijin yasan tana da aljanun ya aureta su duk tsoronsu kar ace yarinyar su tayi kisa atafi kotu

Ganin abin nason zama hayaniya baba musa yace shi ya yafe su kwantar da hankalinsu d'an,ladi kwanan sane ya k'are allah ya kyauta

Babu kunya babu tsoron allah kam suka shiga kwasar kayanta saida suka kwashe komai da komai tsaf kayan sawarshi kawai suka bari

_*😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE*_✍️
13/11/2022, 6:35 am - Maman Dan Albarka Ce: *_WANNAN LITTAFIN NA KUDINE KI SIYA KIKARANTA CIKIN AMINCI AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KACAL TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 2375144550 LAWALI AHMAD ZENITH BANK KITURO EVIDENCE TA WANNAN NUMBER 09138320449 INKUMA KATIN MTN NE SHIMA TA WANNAN NUMBER 09138320449_*

*_INKUMA DUKA LITTATTAFAN BIYU KIKE SO FANSAH 2022 DA KUMA TUSHEN MU DAYA ZAKI TURO 500_*

*🪴TUSHEN MU DAYA🪴*

_*😍MAMAN DAN ALBARKA CE*_

_*LAST PAGE 50*_

Aisha kam lokacin da ta fita daga gidan bayan barin bashir data yi tsaye
Cikin tsoro da fargabar kar a biyota ta nufi titi ta tari mashin

Bata zame ko,ina ba sai gidan gonar alhaji bala tana sauka da a kwatinta taci karo da shi yana k'ok'arin fitowa a motar shi alamar fita yake sonyi

Ganinta yasa ya fito motar yana tambayarta yaya akai ta dawo

Catayi mai babu komai kawai ta d'auki shawarar shine ta gudo kamr yadda tasaba

Yaso lura da rashin nutsuwarta amma ganin ta kama hannunshi ta nufi hanyar parlourn yasa cikin jin dad'i ya bita da yau yake da shirin komawa gida wajen iyalansa dan yau kwanan sa biyu gidan gonar yana shek'e ayarsa haka yake yi sai yace musu yay tafiya yazo yayi iskacin sa inya so ya koma

Ganin aisha da kuma akwatinta ya tabbatar mai ta dawo wajenshi kamar da cikin rawar jiki da nan nan da yake da ita suka shige parlourn

Shikuma ya fita ya sanar da mai gadin shi akan duk wanda yazo neman shi yace bayanan dan shi kad'ai yasan yadda yake morewa da aisha

Kwananta biyar a gidan a kwana na shiddanne da daddare bayan sun gama shek'e ayarsu yan fashi suka dirar musu sun sumar da mai gadi tukun suka samu damar shigowa

Suka ritsa su har d'akin barcin alhaji balan inda suka buk'aci kud'i shikuma ya musu gaddama ganin ya na 'bata musu lokaci suka harbi aisha a kafarta ta dama wadda gaba d'aya ta rikice ta gigice tun da,ta gansu ga kuma harbi ta samu ihu take suka d'ora bindiga akanta akan tana k'ara ihu sai sun harbeta

Nuna alhaji bala sukai suka ce muddin bai fito da dukiyar shi ba zasu kashe aisha sannan kuma dole ya fito da dukiyar

Cikin rawar murya yake kallon aisha wadda ke had'a uwar zufar azabar harbin da aka mata tana layi kamar zata mutu yace ku kasheta na yarda ni ku barni wallahi bani da kud'i

Jin maganar shi duk da azabar ciwon dake addabarta cikin jin takaicin abinda yace wai akasheta ina son da yace yana mata ina alk'awarinsa na bazai iya rayuwa in babu ita ba dama duk yaudara ne

'Dagowa tayi suka had'a ido nan ya shiga girgiza mata kai alamar tayi hak'uri bashi da yadda zai yi ne

Cikin wata iriyar tsanar shi ta nunawa yan fashin inda yake ajiye kud'in dama tasan wajen tadai rufa asirine ganin yadda hankalinsa ya tashi ashe batasan kud'i ya fita muhimmanci ba a wajen sa

Ganin rainin hankalin da ya musu yasa bayan sun binciko kud'in har zasu juya su tafi sunkai bakin k'ofa d'ayan su ya juyo ya harbi alhaji bala a k'irji ita kuma aisha ya k'ara mata a d'aya k'afar

Dukansu suka fad'i shi alhaji bala ko shurawa baiyi ba yace ga garinku aisha kuma tsabar azaba nan ta zube kamar matacciya

Mutanen unguwar ne aka samu d'aya daga cikinsu ya kira yan sanda inda kafin su zo ma har yan fashin sun kammala abinda za suyi sun tafi

Koda suka zo sun tarda mai gadi a sume wanda bindiga aka buga masa har ya suma

Bayan shigowar yan sanda sun bincika tabbas alhaji bala ya riga mu gidan gaskiya nan aka shiga bincike da sauransu aisha kam tna da sauran numfashi nan aka kwasheta sai asibiti

Mai gadi ana shek'amai ruwa ya farfad'o nan aka shiga jefa mai tambayoyi nan ya kwashe labari tiryan tiryan ya fad'a daya ke alhaji bala babban mutum ne a binciken su suka gano sai da aisha tazo gidan tukun yan fashi suka farmar dan mai gadi ya tabbatar musu da tadaina kwana rana d'aya bayan tafiyar ta kuma ta dawo

Ataikaice dai bincikensu ya nuna musu aisha ce ta shirya kashe shi dan sun samu labarin kashe mijinta data yi da ruwan zafi

Nan da nan labari ya cika gari duk da tana kwance a asibiti amma anbaza jami,an tsaro akanta akan ana jiran harta samu lafiya ashiga kotu da ita

Koda iyayanta suka samu labarin abinda ya faru bak'aramin tashin hankali suka shiga ba

Koda suka zo asibitin da k'yar aka bari suka ganta saboda matakan tsaron da aka zuba

Duk kuma yadda mahaifinta yaso a binne maganar ina ya kasa dan alhaji bala yafishi komai da komai ta 'bangaren kud'i

Ko gama samun lafiya bata yi baTuni aka shiga kotu ba awani ja shara,ar ba kasancewar ba k'aramin mutum bane haka suna ji suna gani aka yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya basu da yadda zasuyi

_duniya kenan i ta iyayanta sun gudar mata hukuncin kisan data aikata daya ke alhaki kuikuyo ne gashi ta riski abinda bata da masaniya ma akai ta amshi hukuncin sa allah yasa mu dace mu fi k'arfin zuciyar mu_

Bayan rasuwar d'an,ladi da sati biyu muka samu labarin abinda ya faru da aisha dukanmu allah ya kyauta muka ce

Har lokacin hajjo na cikin hauka tuburan take yanzu dolen dai a k'ullen aka barta sai in za a bata abinci ake bud'eta anma d'auketa a d'akinta anmaida ta d'akin marigayi d'an,ladi saboda baba musa da ya dage shi sai ta barmasa gida
Da k'yar aka lallashe shi ya barta yace ad'auketa a d'akin shi

Ta kai ta kawo yanzu ko kashi da fitsari a inda take take yinsu gashi babu damar ashiga wajenta ta kama mutum da kokawa

Har zuwa lokacin su babanmu na garin saboda alfarmar da baba musa ya nema akan su jira shi ya tattara abubuwan shi daya kamata tukun su tafi tare yafi son su tafi dukan su

Tun rasuwar da sati d'aya Mama aisha ta koma ita da malam liman da shi daga can zai wuce niger ne tunda dama abinda ya kawo shi dan ya ga komai ya dai dai ta ne a rayuwar su baba

Ahmad ma ya yanke shawarar barin garin mu koma,kano baki d'aya
Dan haka shima yasaka filinsa a kasuwa duk da ya fara ginin nan da nan kam aka samu mai siya ya saida muka shiga shirin barin garin

Ya rage gobe zamu tafi nima,nakira kafinta akan saida kayan d'akina saboda nasan bamai yiyuwa bane intafi dasu nan da nan aka kwashe kayan muna cikin tattara wajen ne naji sallama

Na d'ago dan amsawa abin mamaki hauwa nagani cikin shiga ta mutumci da hijabinta iya gwiwa babu wannan rawar kan da iyayin nata sam sai dai ta rame tabarma na shimfid'a mata ta zauna muka gaisa nan take cemin taji labarin
Chapter 77 · 0% Book details