← Book details Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 78

Sashe 12

Tushen Mu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ah lallai masha allah allah yasanya alkhairi ta fada cikin zallar bakin ciki da nata kudirin daban

Bayan tafiyarsu ta shiga daki tarasa inda zata sa kanta tayi nan tayi nan can ta bushe da mahaukaciyar da riya cike da mugunta tace

Wallahi wallahi Talatuwa ke wawiyace amma zan koya miki hankali Badai dan dukiyar musa kika aura masa kanwarkiba wato babu gado bari a koma aci a inda yake samu

Hhhh ta kara fashewa da dariya indai ni asabe ina raye ko arzikin musa bazanbari suyi ba bare har a fantama da dukiya kuma su da garinnan sai bayan raina muddin ina raye kanwarkima ta tafi kenan mu zuba mugani shege ka fasa

Sukwa ana can su malam musa ana shirye shirye daurin aure inda bayan daurin auren Mero da malam musa suka rankayo nigeria

***********"*************

Kwatsam saiga malam musa daga zuwa ganin gida ya dawo da mata Inda ya tunkari hasana yamata bayanin baikara aure ba don ya wulakantata ba

Da dai sauran kalaman kwantar da hankali

Allah sarki hasana mace me hakuri da takwakkali tace babu komai ina zata zauna malam ?

Yace dayan dakin da kike aje kwanika zaki dawo dasu nan sai ita ta zauna a nan

Tace babu komai ya hadasu ya musu nasihar zaman lafiya

Hasana ta kwashe kayanta yasaka Mero wadda Dawowarta Kano sunanta ya rikida ya koma hajjo sakamakon sunan mahaifiyar hasanar ne saboda haka suke cewa mahaifiyarsu shiyasa ta saya sunan ya koma hajjo

Tun daga nan sunan ya bita

Da ta kwantar da hankalinta ana zaman lafiya amma daga baya ta tsiro da salon munafurci da Kisisina yau ta hada malam musa da,hasana husuma gobe ta hadashi da abdullahi kaninsa

Hakadai tazamemusu masifa a gida hasana nasane da ita ke duk wannan munafurcin

Amma don azauna lafiya bata biyemata ba saidai tana taka tsan tsan da abinda zai hadasu

**********""""*""*********

Ana nan abdullahi ya hadu da wata bakatsiniya tana kawo tallar abinci shagonsu me suna zainabu Zainabu irin yan matannan ne masu budadden ido sannan ga rashin kamun kai gata girma batayi aure ba

Amma a haka abdullahi yace yaji yagani ita yakeso

Inda yayanshi yashigemai gaba akai auran ta tare a dakin da abdullahi ke kwana yazama gidan su uku kenan

Tunda zainabu ta shigo sai hajjo tasa mu abokiyar cin mushe suka hadewa hasana kai

Inda zainabu ma na shige shigen malamai ta silar hakanne nema ta auri abdullahi tuni suka dinke takara dora hajjo akan hanya

Rana daya aka wayi gari hasana ta tubure ita bazata kara kwana garin ba tagaji da zama da malam musa gida zataje

Malam musa yayi yayi taki hakura hakadai ya shiryata ya kaita gida da kansa ko in hankalinta,ya kwanta kwana biyu zata yarda su dawo

Ya tsaya jiranta har wasu kwanaki amma bata canja zani ba

Liman yace yayi hakuri ya koma in hankalinta ya kwanta ya dawo ya dauketa

Haka malam musa ya dawo gida jikinshi a sanyaye saboda gaskiya shi yanason matarshi amma dole tasa ya hakura zuwa lokacin da zata yarda ta dawo

Ai hasana na barin gida hajjo ta baje kolinta ta samu yadda takeso

Sun kara curewa ita da zainabu sai abin da suka cewa mazajensu za ayi takai ta kawo malam musa na mugun tsoron Hajjo baya taba
Mata musu akan abin
Datace komene ne

*************************

Bayan Tafiyar malam musa hasana ta warware tana harkar ta kamar ba itaba sai dai ko maganar komawa gidan malam musa bataso sam

Kuma sannan ne tafara kananun ciwo yau da lafiya gobe babu inda mahaifiyar ta ta gano cewa lallai tana da juna biyu

Tasamu malam da maganar cikin tsananin farin ciki tana fadamai shikenan ga hanyar komawar hasana dakinta

Malam ya maza ya kwabeta da karta sake yaji maganar su binne maganar cikin hasana danshi yasan tana da makiya su bar maganar a tsakaninsu zai cigaba

Da mata addu a dan yasan cewa tabbas wannan rashin zaman nata wajen mijinta ba banza ba

Haka kuwa akayi hasana tacigaba da rainon cikinta batare da sanin kowa ba ko su asabe basuda labari saboda bawani damuwa sukai da ita ba

Sannan itanma tunda tadawo bata wani fitowa ko tsakar gida bare suji labarin cikin wajen yan gulma
***********************

Malam musa tunda yakoma baikara tunanin komawa gida wajen hasana ba saboda anciremai tunanin hakan kwata kwata

Hajjo kuma duniyata tasamu yadda takeso sai dai ko batan wata bata taba yiba kusan shekara guda kenan da auransu amma shiru tayi

Buge bugen tayi neme nemen maganin abanza shiru kake ji

Inda ta addabi malam musa ita haihuwa take so kodai shine baya haihuwar da dai sauran maganganu

Yakan cemata komai lokacine

Ahaka har zainabu tasamu nata cikin zo kuga iyayi da kisisina saita fara yiwa hajjo gorin ciki abin na kona zuciyar hajjo amma takan danne saboda

Tana amfanuwa da zainabun ba kadanba

Zainabu taciga ba da renon cikinta cikin cin burin haihuwar da namiji dan ita dukiyar su abdullahi takeson handamewa itama nata burin daban

Har addu a take allah karya bawa hajjon

Kai allah yarabamu da Mugun mutum abin da allah ne ke kyautarshi ga wanda yaso saboda tsaurin ido irin na dan adam sai ya iya daga hannu ya roki allah karya ba wani wa,iyazubillah

************************

Haka hasana ta cigaba da rainon cikinta watarana ta shi da nakuda inda mahaifiyarta ta ita karbi haihuwar ta haifi danta santalele inda bayan haihu aka gyareta tsaf

Sai bayan komai ya lafa tukun aka je gidan su asabe aka fadi haihuwar

Lokacin da sukaji bakaramin firgita suka yi ba sun shiga rudu shin wacce hasanar ce ?

Aka hasana dai matar malam musa

Suka kwashi mayafai sukaje donsu tabbatar duk da suna cikin rudu yaya akai ta haihu bayan duk irin kudaden da suka kashe

Sun tarar da mai jego cikin koshin lafiya ita da kyakykyawan jaririnta

Inda aka tarbesu cikin mutumci duk kokarinsu na kar su tona halin da suke ciki na bakin ciki da hassada kiri kiri hakan ya kasa boyuwa

Dan talatuwa ma da aka miko mata yaron kin amsa tayi tana allah ya raya dai barshi basaina dauka ba ainaganshi ma barcinsa yake

Haka suka dawo kowacce ta kasa zaune ta kasa tsaye gashi yanzu sundaina sakin jiki da junansu bare su kulla wadda zasu kulla

************************

Bayan tafiyar su mahaifiyar hasana tashiga shakku akan irin yadda suka zo da kuma yanayin su

Da liman yadawo tafada masa komai dan ita gaskiya bata yarda da suba sam dagani akwai wata akasa

Liman yajamata gargadi me tsauri karta yarda insun kara zuwa tabasu jinjirin sannan ita kanta hasanar indai basun zo sunganta a tsakar gidaba

Karta barsu suganta tce tayi barci shi yanzu burinshi malam musa ya waiwayo gida yazo yaga gudan jininshi
Tunda ba zamanin waya bane bare asanar mai

Hasana taciga ba da shayar da yaronta wanda ranar suna na zagayowa yaci sunan sa Ahmad wanda liman ne ya rada masa yayi komai da yakamata uba yayiwa yaro kama daga suturarshi zuwa ragon suna da dai sauran hidindimu

Wanda daga bangaren su asabe babu ko allura data fito daga wajensu sunan sunyi jika

sunsha zuwa gidan liman da sunan ganin jariri amma ba abasu kamar yadda liman yabada umarni hakan na musu ciwo dan suna da nasu

Kudurin nazuwan kowacce burinta ta hallakar da yaron

Haka dai har ahmad yacika shekara Daya yana tafiyarsa ko ina

Asanne ne kuma hasana ta fara wani irin ciwo tun tana yi a tsaitsaye har ta kaita ga kwanci inda kullum cikin nemar mata magani ake

Amma fa shiru akace wai malam yaci shirwa

Tafi tafi har yazama ko magana bata iyawa
Lokacin dole tasa aka cire ahmad a nono tunda yana cin abincinsa

Gashi kuma har zuwa lokacin Malam musa bai waiwayo gida ba

Bayan doguwar jinya allah yayiwa hasana rasuwa inda malam yaji mutuwarta yarinya mai masa biyayyah duk cikin ya,yansa itace mafi soyuwa agare shi

Haka dai har bayan arba,in a lokacin ne kuma su asabe suka zo wai suna bukatar abasu ahmad su rike jikansu ya taso a gidan ubanshi

Inda malam liman yayi tsalle ya dire akan bazai taba badashi ba

Sunyi sunyi da sukaga babu riba sai suka hakura bawai dan sunbar maganar ba

Inda malam liman yadage da nemawa ahmad magungunan tsari da addu,o,i ingantattu

wanda koda mutum yaso cutar dashi da asiri to bazai taba tasiri akan shiba

Ahmad yataso yaro me hazaka da kokari ga wayo duk inda malam liman yasa kafa to fa zai aje tashi baya taba yarda yafita batare dashi ba

Zuwa lokacin yana da shekaru biyu

*************************

Hajjo har yanzu shiru babu labari wanda zuwa lokacin Zainabu ta haihu amma
Mace ta haifa duk da bataso hakan ba tanada Shekara daya takuma samun wani cikin

Hankalin Hajjo fa inyayi dubu ya tashi

Malam musa baida muba dan yasan haihuwa lokacice inyayi allah bai manta dashi ba zaibashi

Kwana biyu inya kwanta yana yawan mafarkin hasana da wani abu ahannunta tana mikomai amma kafin ya mika hannu ya amsa sai yaga ta bace beganta ba

Haka dai hankalinsa duk yayi gida

Yasamu abdullahi da maganar inda suka yanke shawarar zasuje gidan daga nan sa duba gonaki tunda ba noman suke yiba aliyune me kula da gonaki wanda shi ba noman yakeba haya duk ya bada gonakin
Yake amsar
Kudaden yana murkushewa

Bayan yanke shawarar malam musa ta tuntubi hajjo da batun tafiyar inda fa nan hankalinta ya tashi tana tsoron karfa yaje

Ya dawo da hasana shiyasa tasa boka ya ciremai tunanin hasanar sam amma data sani tsanar garin tasamai gaba daya

Gashi yace mata da asuba zasu tafi babu damar tayi komai tana ji tana gani suka tafi

*************************

Bayan zuwan sune suka samu labarin haihuwar hasana da kuma rasuwarta malam musa yayi kukan rashin mace irin hasana mace tagari

Inda ya nemi afuwar malam liman akan rashin waiwayarsu da baiyi ba

Malam liman yamai uzuri

Inda Ahmad tunda malam musa ya dauke shi ya makalkaleshi yaki bari ko sauke shine yayi

Malam musa ga abun farin ciki kuma ga akasinsa babu hasana amma hasana ta haifa masa yaro inda babu inda ya baro kamannin mahaifinsa sak

Ahmad ya kasance fari irin mai sirkin ja ja dinnan Yana da kyan shi gwargwado masha allah
Chapter 12 · 0% Book details